Khamis kuwa ɗakin Maryam ya koma. Sai dai bai bari ta lura da damuwar da ya fito da ita daga ɗakin Aisha ba. A gefen gadon da ya bar ta zaune a nan ya same ta, bai kuma yi mamaki ba don ya san motsi mai ƙarfi ma wahala yake mata.
“Baiwar Allah, har yanzu kina nan?” Ya tambaye ta cikin sigar zolaya, lokaci ɗaya kuma ya tsugunna suna fuskantar juna.
Sosai ya bata dariya, sai dai zazzaɓi da murar da ke damun ta ne suka hana ta dariyar, sai ma ta shasshaɓe fuska kamar za ta yi kuka. Yana na ganin haka kuwa ya marairaice fuska tare da faɗin, “Sorry ‘yar gidan Khamis, har yanzu ƙafar ne?” Kai kawai ta iya girgizawa alamar “A’a.”
Sai da ya koma gefenta da zama ya sake tambayar ta, “To meye ke damunki?” Sannan ya kwantar mata da kai a faffaɗan ƙirjinsa.
Hannunsa ta kamo ta sa a wuyanta, murya can ciki ta yi magana, “Zazzaɓin nake ji kamar zai dawo.” Idanunsa a lumshe, yayin da kuma hancinsa ke shaƙar ƙamshin da ke fitowa a ƙananun kitson dake kanta ya ce,
“Oh Sannu! Yanzu zan fita sai in karɓo miki magani kin ji, har da na tarin da ke damunki ma.”
“Uhmm.”
Kaɗai ta iya cewa tare da lumshe idanu, saboda ɗumin jikinsa da ke ratsa duk wata gaɓa ta jikinta, cikin ɗan lokaci ta ji kamar ba zazzaɓi take ba. Khamis ma har yanzu Idanunsa a lumshe suke. Sai dai nutsuwar da yake ji a yanzu ba ta hana shi mamakin abin da Aisha ta yi mishi ba, a hankali ya sauke numfashi tare da tambayar kansa,
“Shin kishi ne ya sauya Aisha, ko wani daga gefe ne yake zuga ta?”
Kafin ya samu amsar tambayarshi ne ya ji Maryam na shirin zame jikinta daga nashi, buɗewar idanunsa kuwa ta yi daidai ta fitowar tari mai kartar ƙirji daga bakinta.
Sannu ya riƙa yi mata, bayan tarin ya lafa ya ce,
“Bari dai in tashi.”
Miƙewa ya yi, sannan ya taimaka mata ta gyara kwanciya, bargon da ke ƙasan ƙafafunta ya ja mata har zuwa kafaɗa. Zuciyarsa cike da ƙaunarta ya duƙo saitin fuskarta tare da faɗin,
“Honey, kada ki yi bacci, yanzu zan dawo In sha Allah.”
Ɗan ɗaga kai ta yi tare da jifar shi da tattausan murmushi, shi ma murmushin ya maido mata, lokaci ɗaya kuma ya manna mata kiss a goshi.
“A dawo lafiya.” ta yi mishi, sannan ta raka shi da idanu har ya fice daga ɗakin. Duniyar tunani mai cike da farincikin samun Khamis a matsayin miji ta lula. “Shin akwai abin da ya kai kasancewa da masoyi daɗi?” A cikin zuciya ta jefa ma kanta wannan tambaya. Sanin ‘Babu’ ita ce amsar ya sa ta yin godiyar Allah a fili, sannan ta ɗora da,
“Allah kada Ka bari wani ko wata a cikin bayinka su hana ni jin daɗin rayuwa da mijina.”
Saboda ta san a gabanta akwai ƙalubale mai girman gaske, don yadda Aisha ta fito da kishinta a fili da wahala su zauna lafiya da ita. Ita kanta a yadda take jin ina ma ita kaɗai ke da Khamis, sai ta yi da gaske sannan za ta dena ƙin duk wani abu da zai raɓe shi. A nashi ɓangaren kuwa, kai tsaye gidansu ya nufa, inda ya samu mahaifiyarshi, ƙannensa da kuma jikokin gidan a katafaren falonsu suna hira. Tun kafin ya zauna yaran suka gaishe shi, lokaci ɗaya kuma suka zura idanu kan blue ɗin food flask da ke hannunsa, tsammanin kowanen su girkin amarya ne a ciki.
Ummansa ma wadda kana ganinta za ka gane ita ya biyo a wurin kyau da kwarjini ta ce,
“Ango ne da kansa?”
Bai wani ji kunyar cewa,
“Ni ne Umma.” ba, tunda ba wannan ne aurensa na farko ba.
Baki a washe ya zauna kan kujerar da ke kallon wadda take zaune. Cike da ladabi ya miƙa mata gaisuwa. Amsawa ta yi tare da tambayar sa amarya da uwargida. Bayan ya tabbatar mata da lafiyarsu ne suka cigaba da hira jefi-jefi. Ƙananun yaran da ke falon kuwa ƙagare kowannen su yake ya ji Khamis ya ce ga girkin amarya, musamman autansu mai suna Salim da ke mutuwar son abincin maƙota.
Shi kuwa gaba ɗaya hankalinsa na wurin mahaifiyarshi da take yi mishi nasiha akan ya zama adali a tsakanin iyalansa, ko da wasa kada ya yi abin da ɗaya za ta ce ya zalunce ta ko kuma ya fifita ‘yar uwarta a kanta. Musamman Aisha da take uwargida, sai ya yi da gaske wurin sanya mata nutsuwa, domin kaɗan zai kuskure ta ce daga yin aure ya juya mata baya.
Sosai ya ji nasihar da ta yi mashi, sai dai akan Aishar ne bai san me zai mata wanda zai gamsar da ita ba. Damuwa bayyane a fuskarsa ya ya ce,
“Umma Aisha ta sauya hali fiye da tunani, yanzu haka girki na sa ta, amma ta ce ba za ta yi ba, wai sai dai Maryam ta fito ta yi tunda a ɗakinta na kwana, Maryam kuma kwance take ba ta da lafiya.”
Ummansa da tun jiya su Hafsat suka zo mata da labari ta kira sunansa,
“Khamis.”
Sai da ta ga ya maido dukkan nutsuwarsa a kanta sannan ta ɗora da,
“Ita fa mace ba za ka san haƙiƙanin halinta ba sai ranar da ka yi mata kishiya. Sai dai duk da hakan ina zargin wani a gefe wanda ke taimaka ma Aisha wurin bayyanar asalin halinta. Ya kuma zama wajibi ka binciki ko waye wannan, domin kada ya rusa maka zaman lafiyar gida.”
Shi ma Khamis zarginsa kenan, don tun a maganarta na Katsinawa na da asiri ya fahimci akwai ‘yan zuga a tare da ita, nannauyar ajiyar zuciya ya sauke tare da faɗin,
“Insha-Allah zan bincika Umma”.
Nusar da shi ta cigaba da yi ta ce, “Kuma kada ka biye mata, duk abin da ka ga ta yi har da kishi, ba za a ɗauki dogon lokaci ba kuma za ta dawo hayyacinta da ikon Allah, amma sai idan ka zama adali tunkuna.”
Ido ya lumshe tare da faɗin,
“Allah ya bani ikon yi musu adalci.”
Don a yadda soyayyar Maryam ta mamaye zuciyarsa, zai yi wahala iya daidaita ta da Aisha a wurin adalci, amma zai yi iya yinsa wurin ganin bai tauye ma Aishar haƙƙinta ba. Tunawa ya yi da alƙawarin da ya yi ma Maryam na ba zai daɗe ba, take kuwa hankalinsa ya kaɗa zuwa gida, duban Ummansa da hankalinta ya koma kan yaran dake ta guje-guje a falon ya yi yatce,
“Kun gama girki ne a zuba mana?”
Salim da ya ƙi tashi kuwa na jin Khamis ya ce haka ya haɗe rai, saboda a ƙagare yake ya ga me aka kawo. Salima wadda twin sister ɗin Salim ce me za ta yi kuwa in ba dariya ba, don ta lura da yadda ya kafe food flask ɗin da idanu.
“Su acici sai a maida yawu.” Ta faɗa tana yi mishi gwalo.
A fusace Salim ya kai mata duka, sai dai bai samu sa’ar taɓa ta ba. Ya ɗaga hannu zai ƙara kai mata wani dukan Khamis ya dakatar da shi. Ummansu da akan idonta rigimar ta fara ta ce,
“Waɗannan sarakan faɗan, ai in dai suna gida to kuwa bakin kowa ya gama yin shiru.”
“To Umma acici fa take ce mini.” Salim ya faɗa tare da fashewa da kukan takaici. Hafsat da itama ta san komai ta ce,
“Toh idan ba acici ba daga ganin food flask sai ka kama haɗe yawu.”
Dariya su duka suka sa, a nan ne Khamis ya fahimci inda rikicin ya samo asali. Lallashinsa yayi ya ce, “Rabu da su Autan Umma, kowa ya san kai ba acici ba ne, kuma idan amarya ta fara girki zan ce ta zubo maka naka daban.”
Juyawa ya yi kan Salima da ke ta dariya ya ce,
“Idan kika sake ce mishi acici sai mun sa ƙafar wando ɗaya da ke.”
Haƙuri ya ƙara ba Salim, sannan ya miƙe. Haneefa ce ta faɗo mishi a rai, tunawa ya yi da Aisha ta ce su Hafsat ta biyo, gashi kuma tunda ya shigo gidan bai ganta ba.
Tambayar Hafsat ya yi,
“Wai ba anan Haneefa ta kwana ba?”
Amsa ta bashi da,
“A’a, muna fitowa ta bi su Anty Rahama”
“Okay.” Ya faɗa sannan ya bi bayan Ummansa zuwa kitchen.
Tare suka haɗa abincin a basket, sannan Hafsat ta saka mishi manyan bottels cike da kunun aya mai sanyi a cikin basket ɗin. Godiya ya yi ma Ummansa, sannan ya sa yara suka kai mishi basket ɗin cikin mota.
Pharmacy ya biya ya sayi magunguna sannan ya nufi gida. Maryam na shirin fitowa da ga banɗaki ta ji an turo ƙofa. Sanin shi ne ya sa ta ƙara wadata fuskarta da fara’a tare da fitowa a hankali, sosai take jin daɗin tafiyar sakamakon ruwan zafin da ta zauna a ciki yanzu.
Shi ma tunda ya shigo idanunsa ke kanta har ta ƙaraso inda yake a tsakiyar ɗakin.
‘Lallai ƙafa ta yi sauƙi.’ Ya faɗa a ransa.
A zahiri kuma ya ce,
“Kin ga na daɗe ko?, sai da na karɓo mana abinci a gida tukunna.”
Ko kusa ita bata ga daɗewar da ya yi ba, don haka ne ta girgiza kai tare da faɗin,
“A’a, baka daɗe ba.”
‘Yar dariya ya yi ya ce,
“Anya kuwa?”
Itama dariyar ta yi sannan ta ce, “Ai idan ka daɗe zan faɗa.”
Karɓar basket ɗin da ke hannunsa ta yi, shi kuma ya fita ya kwaso musu plates da cups. A ƙasan carpet suka zauna cin abincin, shinkafa da miya ce mai rai da lafiya. Cike da soyayya suka ci abincin mai yawa, suna gamawa Maryam ta sha magungunan, duk da dai ta nemi zazzaɓin ta rasa. Kimtsa wurin Khamis ya shiga yi, Maryam ta ce,
“Ka bari in gyara.”
Idanunsa cikin nata ya ce,
“Ke da bakya jin daɗi, bari kawai in gyara.”
Tas ya yi ma wurin kamar mace, daga bisani suka sake zama a ƙasan carpet ɗin.
Maryam na manne a jikinsa ya raɗa mata ,
“Zazzaɓi yayi sauƙi ko?” Kai ta ɗan girgiza tare da faɗin,
“Da sauƙi dai.” don a lokacin ji take jikinta ya yi nauyi.
“Ko dai har ajiyata ta samu wuri ne?”
Ya faɗa cikin sigar zolaya. Shiru na ‘yan daƙiƙu ta yi, lokaci ɗaya kuma tana tambayar kanta “Ajiya?”
Ware idanu tayi tare da faɗin, “Laa! Wallahi ba wata ajiya.” Saboda ta gane me yake nufi.
Dariya su duka suka shiga yi, daga bisani ya ce,
“Anya kuwa dai?”
“Allah kuwa, wahalar da nasha ce kawai a wurinka.”
Sosai maganarta ta bashi dariya, ɗago mata da kai yayi, lokaci ɗaya kuma ya gyara zama suna fuskantar juna. Hannayenta ya kamo tare da yin magana cikin salon soyayya.
“Ke ɗin special ce Maryam, da ace ana zuwa aljanna a dawo, da na ce Aljanna kika kai ni na sha fresh Milk sannan kika dawo da ni, shi ya sa daga jiyan zuwa yau farashin son ki ke daɗa hauhawa a zuciyata. Ina son ki Maryam, son da idan na biye ta tasa ba zai bari in yi adalci a tsakaninki da Aisha ba, don haka nake roƙon ki da kada ki bari na aikata rashin adalci, duk sa’adda ki ka ga ina yunƙurin karkarcewa, to ki taimaka ki gyara ni, domin kada na tashi a sahun masu shanyewar ɓarin jiki a ranar alƙiyama.”
Gaba ɗaya zantukan da yake mata basu buƙatar sharhi, domin ta ga tsantsar ma’anarsu a cikin idanunsa. Don yadda yake kallon ta ko bai furta komai ba ta san yana ƙaunarta. Cike da farincikin samun matsayi na musamman a wurinsa ta ce,
“Nima ina sonka hubbyna, kuma In sha Allah ba za ka taɓa kuskurewa a tafiyarka ba, ko da hakan ta faru ma za mu yi maka uzuri kasantuwar kai ɗan adam ne, wanda kuma dole ne a samu ajizanci a tare da shi.”
Sosai ya ji daɗin maganarta, don haka bai san sadda ya kwanta tare da ɗora kansa akan cinyoyinta ba. Ƙuri suka yi ma juna, lokaci ɗaya kuma suka riƙa musayar kalmomi masu ɗauke da zallar soyayya. Suna a haka ne Maryam ta ji bacci ya cika mata idanu, sai da ta sauke hammar da ke bakinta sannan ta ce,
“Ka ga bacci nake ji.”
A hankali ya buɗe Idanunsa da ke lumshe ya ce,
“Nima baccin nake ji, amma mu yi Sallar Azahur tukunna, sai mu biya bashin baccinmu na jiya.”
“Okay.” kaɗai ta iya cewa, saboda abubuwan da yake mata sun kashe mata baki.
Kiran Sallar Azahur suka ji an fara, rabuwa suka yi da juna, ita ta shige banɗaki, shi kuma ya fita da niyyar tafiya masallaci.
Haneef dake ta wasa a falon ya ja suka nufi masallaci, a hanya ne yake tambayar shi,
“Me Mammy ta girka maka?” don ya fahimci kamar yaron na jin yunwa. Cike da damuwa Haneef ya ce,
“Indomie ce Daddy, ni kuma bana son ci.”
Sosai Khamis ya ji ba daɗi, don mutum ne mai matuƙar damuwa da damuwar yaransa, abin da suke so shi yake so, madamar bai saɓa ma tarbiyya ba. Ko a kan abinci ba a cika girka abin da ba sa so ba, idan kuwa Aisha ta girka, to sai dai ya siyo musu abinda suke so a waje. Haƙuri ya ba Haneef tare da tambayar shi,
“Me kake son ci yanzu?”
Amsa ya bashi da,
“Alkubus nake so Daddy.”
Saboda yana son Alkubus, sai dai ba a yin shi a gidansu saboda Aisha bata iya ba.
Yanzu kam Khamis bai shirya zuwa gidan abinci ba, saboda Maryam ta gama hargitsa mishi tunani, burinshi kawai ya koma wurinta domin ya samu nutsuwa. Haƙuri ya bashi, ya kuma yi mishi alƙawalin da yamma zai ɗauke shi su siyo, idan ya so sai ya ci sauran abincin da suka rage yanzu.
Zuwansu ƙofar masallacin ne ta katse musu maganar, Sallah suka shiga suka gabatar tare da sauran jama’a. Ana idarwa suka dawo gida.
Kai tsaye kitchen Khamis ya nufa, abincin da suka rage ya zubo ma Haneef a plate, da hannunsa ya riƙa bashi har ya ƙoshi, ruwa da lemu kuwa ya san Haneef ɗin ne zai nema da kanshi tunda akwai komai a wadace. Yana gama bashi ya wanko hannu a kitchen, daga nan kuma ya sa kai ɗakin Maryam, da gudu Haneef ya biyo bayanshi,
“Daddy nima zan je wurin Anty.”
Tabbas idan Haneef ya bi shi, to fa zai hana shi rawar gaban hantsin da yake son takawa a yanzu “Yanzu bacci take, ka bari idan ta farka zan kira ka.”
Yana faɗin haka ya tura shi alamar ya tafi.
Akan idonsa Haneef ya shige ɗakin Aisha, Khamis na jin sa’adda ta ce,
“Daga ina kake?”
Bai tsaya jin amsar da Haneef ya bata ba ya tura ƙofar ɗakin Maryam a hankali, kwance ya hange ta a kan sofa, ta yi lamo kamar mai bacci. Har ya je ya duƙa a gefen hannun sofar, inda kuma kanta yake aje bata motsa ba, ƙuri yayi ma kyakkyawar fuskarta wadda bai gajiya da kallon ta, cikin wata irin murya ya ce,
“Princess har kin yi bacci.”
Ita kuwa tana jin shi, sai dai gudun abin da zai biyo baya ne ya sa ta ƙara yin lamo. Ya lura ba bacci take yi ba, amma sai ya tafi a baccin take, shu’umin murmushi ya saki tare da miƙewa. Bata ankare ba kawai sai ji ta yi yayi sama da ita, lokaci ɗaya kuma yana faɗin,
“Bari in maida ki kan gado, kada wuyanki ya yi ciwo.”
Ta ɗauka daga nan sai gadon, sai ta ji yayi tsaye, duk da idanunta a rufe suke, amma tana ji a jikinta kallonta yake, cikin wata kasalalliyar murya ta ji ya ce, “Princess, ba kya so in ji ɗumin jikinki ko?” Don ya fahimci tun da suke zaune take ta zazzamewa ga abinda yake mata. A hankali ta buɗe idanunta ta sanya su cikin nashi, murmushi ya sakar mata sannan ya dire ta akan gado.
Hijab ɗin da ke jikinta ya cire mata, wanda kuma hakan ya yi sanadin bayyanar cikar halittarta a fili. Cike da son jinta a jikinshi ya duƙo har nunfashinsu na sarƙewa cikin na juna,
“Komai naki mai kyau ne baby.” ya faɗa a kasalance, tare da sumbatar ta a ɗan ƙaramin bakinta.
Kayan jikinsa ya rage, sannan ya sanya wayarsa a ‘do not disturb’ bargo ya ja musu, wanda a ciki sai da suka kusa kashe junansu da soyayya, sannan suka yi bacci mai cike da nutsuwa.
How do I continue pls
Ya zansamu sauran pls