Skip to content
Part 4 of 21 in the Series Kishiyar Katsina by Hadiza Isyaku

Dangane da Aisha kuwa, wunin ranar kaɗai ya fara tabbatar mata da gadarar ‘ya mace ba ta cika tasiri a wurin namiji idan yana da wata matar ba, domin tunda Khamis ya fito daga ɗakinta ba ta sake jin motsinsa ba bare har ya shigo inda take.

Saɓanin lokacin da take ita kaɗai, idan suka yi faɗa dole ta gan shi, sannan dole ya buƙaci wani abu a wurinta tunda bai da wata matar sai ita. Kuma a halayyar Khamis ma bai cika tsananta fushi ga iyalansa ba, a kullum ya kan horar da kansa jure duk wani zafi da mace za ta sa mashi, domin mahaifinsa ya taɓa ce mishi,

“Jajirtaccen namiji ne ke iya jure raɗaɗin dafin ‘ya mace.” Shi ya sa ba kowane ɓacin rai ne yake maida hankali a kansa ba. Idan kuma har ta kama, to yakan yi nisan da bacci kawai ke maido shi gidan.Ya zaɓi haka ne domin ta wannan hanyar ce kaɗai yake hora Aisha.

Saboda a rayuwarta ba abin da ta tsana irin Khamis ya yi nisa da ita, hakan na sa ta damuwa sosai. Kamar yadda yanzu ta rasa inda za ta saka kanta saboda baƙinciki da ya mamaye mata zuciya. Gaba ɗaya ji take duniyar ta mata kaɗan, daidai da abinci wunin ranar ba ta ci shi ba.

Kuka kuwa cikin yin sa take, a ƙasan rantar kuma tana faɗin, ‘Duka kwana biyu da yin aure amma har Abban Haneef ya maida ni saniyar ware.’ Ko kusa bata yarda laifinta ne ya ja mata ba, sai ma take ganin ita ma aka raina ma wayau.

Zaune take akan darduma tana jan carbi, muryar yaranta ta ji sun nufo ɗakin da gudu, duba ta kai ga ƙofa tana jiran shigowar su, cikin ranta kuma tana tambayar kanta, ‘Wa ya dawo da Haneefa?’

Bayan sun shigo ne ta samu amsar a bakin Haneef, inda ya ce, “Mammy daga Masallaci muka wuce ɗauko Haneefa ni da Abba.”

Ita kuma Haneefar ta ce,

“Akan hanya kuma Abba ya sai mana nama da ice cream.” Miƙa mata ledar da ke hannunta ta yi. Jiki a mace ta karɓa tare da tambayar ta,

“Ina Abban?” Saboda shi kawai take son gani. Haneef ya fi kowa sanin inda Khamis yake, don haka ya ce,

“Ya tafi ɗakin Anty ya kai mata nata.”

Ido Aisha ta rumtse, cikin ranta tana jin idan akwai ranar baƙinciki to yau ce, domin tunda suka yi aure Khamis bai taɓa nisa da su ba alhalin yana cikin gidan, ɗabi’arsa ce ma zama cikin iyalansa, hatta abinci idan yana nan tare zasu ci su duka a tire ɗaya.

Haneefa ce ta yi sanadin buɗewar idanunta da suka ƙanƙance saboda kuka,

“Mommy bari na kira Abba ya zo mu sha ice cream ɗin.”

Kai Aisha ta girgiza tare da faɗin, “Ko kin je ba zai zo ba Haneefa.” kamar Haneefa za ta yi kuka ta ce,

“Saboda me?”

“Saboda ya yi sabuwar Amarya.”

Sosai take son yin kuka, amma saboda ba ta son yaranta su ga hawayenta sai ta haɗe.

Lallaɓa su ta shiga yi, da ƙyar suka ci gasasshen naman da ice cream ɗin, cikin ransu kuma suna jin ba daɗin rashin ganin Abbansu a tare da su. Ita kuwa da ta ji yunwa na shirin taso mata da Ulcer sai ta haɗa Tea mai kauri ta sha, daga bisani kuma ta kwanta.

Washegari kuwa Maryam da ƙarfinta ta tashi, don haka ba ta tsaya jiran sai wani ya girka ya bata ba. Suna gama gaisuwar safiya ita da Khamis ta miƙe da nufin haɗa musu breakfast.

Khamis ya so ta ƙara warwarewa sannan ta shiga kitchen, amma ta ce, “Zan iya.”

Ba ta ɗauki dogon lokaci ba ta haɗa musu breakfast mai sauƙi.

Tana gamawa suka yi wanka tare da shiryawa cikin shiga ta alfarma, doguwar riga ce ta sanya Maroon colour, wadda grey ɗin mayafinta ya samo asali daga zaren da aka ɗinka rigar. Shima Khamis grey ɗin yadi ne marar nauyi, sai kuma maroon ɗin hula, turaruka masu sanyaya zuciya suka feshe jikinsu da shi.

Waya Maryam ta ɗauko ta ce,

“Mu yi selfie.” Karɓar wayar Khamis ya yi tare da rungumo ta da hannunsa ɗaya.Ta fuskar wayar suka ci gaba da kallon juna, sosai fuskokinsu suka dace da juna, sumba Maryam ta kai mishi ga kumci a daidai lokacin da ya ɗauki hoton.

Style kala-kala suka yi, sannan Khamis ya aje wayar ba tare da ya duba hotunan ba. Dalili kuwa ƙagare yake ya fita ya ga yaranshi da Aisha, domin ya san rashin ganinsa na jiya kaɗai ya bi da ita, saboda ya san hukuncin da ta tsana ne ya yi mata.

Duban Maryam da ke ta nishaɗi ya yi,

“Mu je ki gaida Aisha.”

Ras ta ji gabanta ya faɗi, domin ba wanda ta tsani jin sunansa sai Aisha, yaƙe ta yi tare da sa hannunta cikin nashi suka fito. A falo suka haɗu da Haneef da Haneefa, daga Khamis har yaran ba wanda bai yi farincki ba. Maƙalƙale shi suka yi suna dariya, Haneefa ta ce,

“Abba shi ne jiya ka ƙi dawowa muysha ice cream ko?”

Dariya ya yi sannan ya ce,

“Sorry Mamana, yanzu ai gani ko”.

Haneef kuwa complain ɗin rashin zuwan su masallaci da Asubah ya yi. Khamis na dariya ya dubi Maryam,

“Laifinki ne rashin zuwan mu masallaci.”

Ta ware idanu tare da buɗe baki za ta yi magana ya riga ta,

“Bacci na musamman nake idan ina gefenki, shi ya sa jiya da yau na kasa fita masallaci da Asubah.” Murya ƙasa-ƙasa ya ƙarasa maganar saboda yara da ke wurin.

Dariya su duka suka yi, har da yaran duk da basu ji abin da ya faɗa ba. Nuna musu Maryam ya yi,

“Ku gaishe da Anty.”

Gaishe da ita suka yi, Cikin son yaran ta amsa tare da tambayar su,

“Ina Mommy?”

Haneef ne ya ce,

“Tana ɗaki.”

Maryam ta ce,

“To je ka kirawo ta.”

Aisha na shirin fitowa daga ɗakin Haneef ya zo kiran ta, saboda ta ga zaman ciki ba abin da zai ƙara mata sai takaici. Wata irin faɗuwar gaba ce ta riske ta a lokacin da ta hangi Khamis da Maryam jere akan kujera suna dariya. Sai da ta yi da gaske wurin danne kishin da ya taso mata sannan ta ƙaraso ta zauna, cikin mutunta juna suka gaisa, daga bisani Maryam ta ce mata, “Breakfast na jiran ku.”

Aisha ba ta yi niyyar haɗa girki da Maryam ba, don haka ta ce,

“A’a, ayanzu nake shirin ɗora mana ni da yara.”

Cewa Khamis ya yi,

“To amarsu ta hutar da ke.”

Harara ta wurga mishi, don ta san da biyu ya yi maganar. Dariya ya yi tare da kashe mata ido, ƙasan ransa kuma cike da tausayinta, duk da ita ta ɗora ma kanta jidalin baƙin kishi. Kama hannun Maryam ya yi suka miƙe sannan ya ce ma Haneef da Haneefa,

“Ku zo mu yi breakfast.”

Cike da jin daɗi yaran suka bi su zuwa Dining.

Ita kuwa ɗakinta ta koma tare da haɗe kai da gwiwa ta dasa sabon kuka,

“Anya kuwa zan juri ganin mijina da wata?”

A cikin kukan ta riƙa jefo ma kanta wannan tambayar, sai da ta yi mai isar ta sannan ta kira mahaifiyarta a waya,

“Umma kamar zan mutu.”

Ta faɗa tare da fashewa da kukan tausayin kanta.

Lallashinta Ummanta ta riƙa yi, tare da yi mata nasihar ta danne zuciyarta, kada ta bari kishi ya haifar mata da ciwon da bai da magani sai nadama. Sosai ta ji maganganun mahaifiyarta, mafarin da rana ta chaɓa ado ta fito falo kenan. Khamis na ganinta ya ce,

“Ko ke fa!”

Saboda shi ma ya ji maganar Ummansa da ta ce kada ya biye ma Aisha.

Murguɗa baki ta yi tare da ɗauke kanta, dariya ya yi sannan ya ce, “Tuba nake Eshana.”

Maganganu masu tausasa zuciya ya ci gaba da faɗa mata, daga bisani suka koma dining saboda girkin rana ya kammala.

Ba ƙaramin mamaki Maryam ta yi ba, domin abin da gaba ɗaya suka fi so ne ta girka musu.

“Alkubus.” Aisha ta faɗa a ranta, take kuma haushi ya turniƙe ta, don yadda ƙamshin miyar ke tashi da kuma kyan da alkubus ɗin ya yi alama ce dake nuna Maryam ta iya girki. Kuma da girkin kaɗai za ta iya zarce ta matsayi a wurin Khamis.

Murmushin yaƙe ta yi, tare da maida dubanta ga yaran da ke ta murnar cikar burinsu na ganin an yi alkubus a gidansu. Khamis kuwa ƙuri ya yi ma Maryam lokacin da ta fara serving ɗinsu. Cikin ransa yana jin ya gama dacen mace a rayuwarsa.

“Irin wannan girkin bazata haka, da kyau ƴar mutan KT.”

Cike da farinciki ya jinjina mata, saboda Alkubus ne best food ɗinsa, shi ya sa kullum yake ma Aisha complain akan rashin iya girkin sa, har yana tsokanarta da sai ya auro wadda za ta riƙa girka mishi. Ba ma alkubus kaɗai ba, duk wani girkin gargajiya yana son shi, ita kuma ba komai ta iya a girkin gargajiyar ba.

“Ya Salam.”

Ya faɗa lokacin da ya kai lomar farko a baki, wani irin daɗi ne ya yi sama da shi, don Maryam ba ƙaramar natsuwarta ta sa wurin yin miyar ba.

“Abba da daɗi ko?”

Haneef da ke ta santi ya tambaye shi.

“Ai Haneef tunda nake ban taɓa cin girki mai daɗin wannan ba.”

Wannan amsa da Khamis ya ba Haneef kuwa daidai take da sukar mashi a ƙirjin Aisha. A fusace ta saki spoon ɗin da ke hannunta tare da miƙewa tsaye.

“Lafiya?”

Khamis ya tambaye ta a lokacin da ƙarar faɗuwar Spoon ɗin ta daki dodon kunnesu. Maryam da yaran kuwa bin bayanta suka yi da kallo lokacin da ta juya ba tare da ta ba Khamis amsa ba.

Baki Maryam ta taɓe, cikin ranta kuma ta ce,

‘Haushi kam yanzu kika fara jin sa.’

Saboda tunda Khamis ya fara yabon girkin ta lura da yadda Aishar ke ta haɗe rai.

A zahiri kuma cema Khamis ta yi, “Ka bi ta mana sai ka ji me ya faru.”

“Ke rabu da ita.”

Ya faɗa idanunsa na kan yadda yaran ke ta loma ba tare da sun damu da abin da ya faru ba.

“Aisha na da matsala.”

Ya faɗa a ransa tare da sauke gajerar ajiyar zuciya.

Matsa mishi Maryam ta yi akan sai ya je saboda alamu sun nuna an mata laifi. Ranshi a ɓace ya ce “Toh me aka yi mata? Haka kawai ta hargitsa mana lissafi.”

Maida hankalinsa ga plate ɗinsa ya yi, sai da ya ci mai isarsa sannan ya nufi ɗakin Aisha. Maryam da yaran kuma suka kimtsa wurin.

Zaune ya same ta ta kwantar da kai a kan gado. Cike da ƙunar rai ya zauna gefenta, lokaci ɗaya kuma ya dafa ta tare da yin magana,

“Aisha kin ƙoshi da abincin ne kika taso?”

Shiru ta yi kamar ba ta ji me ya ce ba, don takaiy maƙura wurin ƙuluwa. Sai da ya sake cewa, “Aisha magana nake.”

Sannan ɗago a fusace tare da faɗin,

“Yanzu ka kyauta abin da ka yi mini, a kaikaice ka faɗa ma amaryarka ban iya girki ba.”

Sosai ta saka shi a ruɗani, saboda bai san sa’dda ya ce bata iya girki ba, amma ba yadda ya iya dole ya yi gaugawar ɗaukar laifinsa don a zauna lafiya.

“Ki yi haƙuri to, duk abin da na faɗa ban yi don nuna kasawarki ba, kuma kema ai gwana ce, tunda duk rintsi bana cin girkin kowa sai naki, kin ga kuma ƙwarewarki ce ta kawo haka.”

Alfarmar da take son ya yi mata ne ta sa saukowa da ga fushin, murya a marairaice ta ce,

“Toh don Allah ka daina yabon duk wata bajintar Maryam a gabana, ina jin kamar ni ban iya ba ne.”

Kai ya girgiza tare da ɗan haɗe rai,

“Nan kam ba za ta yiwu ba, ni ba zan iya munafuncin da wasu maza ke yi ba na ƙin yabon matansu a gaban kishiyoyinsu, zan yabi duk wadda ta yi abin a yaba ko a gaban waye, don haka kisa a ranki kema zan yabe ki a gabanta muddin kin yi abin yabon.”

Faɗa sosai ya yi mata akan kada ta bari kishi ya ja mata raini a wurin Maryam, domin in dai za ta riƙa bayyana fushi a gabanta, to kamar ta siya ma kanta raini ne. Sannan ya ƙara tabbatar mata da ƙaunar da yake mata tana nan daram, idan ta ga ta ragu, to zafin kishinta ne ya ja mata. Daga wannan rana ce Aisha ta fara ɓoye kishinta, ko da ta ga abin da ranta bai so ba sai ta danne, sai bayan ta shiga ɗaki ta fashe gululunta a can.

Maryam kuwa cikin ƙasa da kwana bakwai ta gama samun matsayi a wurin Khamis da yaransa. Domin nutsuwarta ta sa ta fahimci me yafi so a rayuwa, sannan me ya fi martabawa. A ciki ta fahimci yana son girki mai daɗi, don haka ilimin da ta samu a gidansu da kuma Catering School ɗin da ta shiga ya yi amfani, domin shi da yara har zaƙuwa suke ta gama girki.

Na biyu kuma shi ne lokaci, Maryam ta fahimci yana martaba lokacinsa, shi yasa ba ta yi mishi wasa da shi, daga shi har yara suna fita akan kari. Sannan ba Khamis kaɗai ba, hatta yaran suna jin daɗin zama da ita, saboda ta jawo su a jikinta, Khamis ne kuma ya bata wannan sirrin, ya ce in dai tana son su zauna lafiya da Aisha, to ta kama yaranta. Wannan abu kuwa ya sa Khamis bai jin kunyar nuna mata jin daɗin sa ko a gaban waye.

A ranar da zai bar ɗakinta ne suna kwance ya ce mata,

“Cikin kwana bakwai kin tsoma rayuwata cikin jin daɗin da bai misaltuwa. Na so ace ke ce matata ta farko, na san da komai nawa ya tafi normal ba tare da tangarɗa ba.”

Murmushi kawai ta yi, don ta fahimci yana da tarin matsaloli, waɗanda idan ta nutsu za ta iya yi mashi maganinsu. Cike da rashin son rabuwa da ita ya ce,

“Zan yi kewaki hayaatee.”

Tare da kai mata sumba a baki.

“Nima haka mijina.”

Ta faɗa, lokaci ɗaya kuma ta ƙara shigewa jikinsa, ƙanƙame juna suka yi, cikin raɗa ya ce,

“Don Allah ki lasa min zumar bankwana.

Ta gane me yake nufi, don haka ba ta wani ɓata lokaci ba ta shiga jiyar da shi farinciki. Aisha na can itama tana yi mishi tanadin wani farincikin, domin Zuzee ta cika ta da kayan mata iri-iri, banda karatuttukan da ta bata wanda idan ta yi sama da Khamis, sai ya nemi taimakon Allah kafin ya dawo ƙasa.

Sai dai ganin hoton Khamis shi da Maryam a fuskar wayarsa lokacin da ya shigo ya sakar mata da dukkan lakkar jikinta, hakan ya hana ta bashi kulawar da zai gamsu da dawowarsa a wurinta.

Ko kaɗan Khamis bai ji komai ba lokacin da ya kasance tare da ita. Bai kuma ɓoye mata ba, ce mata ya yi.

“Aisha ya na ji ba wani canji, ko ba ki ci kaza da cicciɓi ba ne?”

Duk da a rufe ya yi maganar, amma a take ta gane inda ya dosa, bai ankare ba kuwa sai ji ya yi ta shaƙare shi tare da faɗin,

“Ni na san za a rina, waccan shegiyar Bakatsinar ba za ta bari mu zauna lafiya ba.”

Kwandunan bala’i ta ci gaba da sauke mishi, wanda sai da ya yi da gaske sannan ya ƙwaci kanshi.

Haƙuri ya shiga bata ya ce,

“Aisha don Allah ki fahimce ni…”

Tsawa ta daka mashi, tare da faɗin,

“Dalla Malam rufe mana baki, ba wata kalma taka da zan saurara, don haka zan fice maka daga ɗaki, kuma ba zaka sake gani na ba sai ranar da na ci kaza da cicciɓi.”

<< Kishiyar Katsina 3Kishiyar Katsina 5 >>

5 thoughts on “Kishiyar Katsina 4”

    1. Wslm, ki yi ma Aunty Ramatu magana ta wannan number +234 907 230 4845 , ɗaya ce daga cikin mahukuntan bakandamiya

    1. Bakandamiya Hikaya Team

      Waalaikum salam

      Sai kin yi subscribing za ki iya ganin ci gaban shi. Domin yin subscription din ki duba menu (menu na sama ta hagu, zane uku haka) za ki ga wurin da aka rubuta ‘subscribe’, ki latsa. A next page sai ki zabin subscription da ki ke so. Ki bi process din har karshe wurin da aka bada account number. Ki biya sai ki tura mana receipt ta WhatsApp No +234972304845

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.