Skip to content
Part 5 of 21 in the Series Kishiyar Katsina by Hadiza Isyaku

Ruƙo hannunta Khamis ya yi a lokacin da take yunƙurin sauka daga kan gadon, cikin dagewa akan son fahimtar da ita ya ce, “Aisha don Allah ki saurare ni, wallahi ko kusa ban faɗa miki haka don in wulaƙanta ki ba, kuma…”

“Na ce ka sake min hannu.”

Ta faɗa tare da fizge hannunta.

Direwa ta yi daga kan gadon sannan ta ɗora da,

“Kuma wacce magana ce zan ji daga bakinka? Bayan ka tabbatar min da butulcinku na ‘ya’ya maza. A baya har cewa kake idan akwai matan aljanna a duniya to ina ɗaya daga cikinsu, amma sai gashi ƙarin aure ya sa ka ƙaryata kanka,

don haka ka riƙe kalamanka. Kuma ita ma ‘yar gwal ɗin ta tanadi mai hure mata ƙasar da za ka watsa mata a idanu idan ka gama yayinta.”

Kuka mai tsuma zuciya ne ya ci ƙarfinta, ba don ta so ba ta dakata da maganar duk da akwai sauran raddi ma zafi a bakinta.

Sosai kukan da take yi ya ɗaga hankalin Khamis. Manufar kalamanta ne ya ci gaba da juyawa a zuciyarshi, wato tana nufin ya gama yayin ta shi ya sa ya faɗa mata haka. Ya buɗe baki zai yi magana kenan ta juya, rufe bakin ya yi tare da raka ta da idanu har ta fice tare da banko ƙofar da ƙarfi. Dafe kansa ya yi haɗe da lumshe idanu,

‘Yanzu fassarar da Aisha za ta yi min kenan? Yanzu ni Khamis ne na gama yayinta?”

Cikin ransa yake wannan maganar, lokaci ɗaya kuma yana jin wani irin ƙunci na taso mishi a ƙahon zuciya.

“Kai ya zama wajibi na faɗa mata ba haka bane tun kafin ta ɓata min suna a wurin danginta.”

A gaggauce ya sauko daga kan gadon ya nufi ɗakinta. Murɗa handle ɗin ƙofar ya yi, sai dai bai samu zarafin shiga ba saboda key ɗin da ta sa bayan ta shiga.

Sautin kukanta da yake jiyowa ne ya ƙara ƙuntata mishi zuciya, kamar shi ma zai yi kukan ya ce, “Kai! Innalillahi wa inna ilaihir raji’una, Allah kana gani.”

Saboda shi bai ga wani abin da rayuka za su ɓaci haka akansa a kai ba. Ƙwanƙwasa ƙofar ya fara yi a hankali saboda dare ne, kuma ba ya son Maryam ta jiyo motsinsa, kasantuwar sauti na sauƙin karaɗe wurare a irin wannan lokacin. Ita kuwa tana jin shi, sai dai bai da ‘yancin da za ta buɗe mishi ƙofa don a ganinta ya gama wulaƙanta ta. Ƙin buɗewar ne ya fara fusata shi, a hasale ya ce,

“Aisha kina jina amma ba za ki buɗe ba ko, to ba damuwa, ni dai Allah ya san zuciyata, ko kaɗan ban yi nufin wulaƙanta ki a maganata ba, amma tunda haka kika sa a ranki matsalarki ce.”

Jiki ba ƙwari ya dawo ɗakinsa, jagwab ya zauna a gefen gado tare da furzas da iska mai zafi. Shi ba fushin ne damuwar shi ba, muguwar fassarar da suɓul da bakanshi ta ja mishi ita ce damuwa, tabbas duk wanda ya ji asalin maganar zai ce ya wulaƙanta ta ne saboda ya yi sabon aure. Tsaki ya ja tare da faɗin,

“Matsalar duk wanda zai ce haka ne.”

Don ko kusa ba ya tsoron zargin mai zargi madamar a kan gaskiya yake.

Duk irin zafin da yake ji a ransa, amma bai bari damuwa ta samu mazauni azuciyarsa ba bare har ta hana shi bacci. Don haka ne ma ya kashe fitilar ɗakin sannan ya dawo ya kwanta. Sai dai bai san Maryam ta fara saba mishi da rashin bacci shi kaɗai ba sai da ya ji ba kowa a gefensa, Idanunsa a lumshe ya cigaba da laluben gefe.

Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke saboda ko da hannunsa zai ƙara tsayi ba zai ji kowa ba. Ƙunshewa ya yi a cikin bargo, ƙasan ransa kuma yana hasaso Maryam kwance a gefensa. Wanda yake ji a jikinsa itama shi take tunani a halin yanzu, don ta faɗa mishi ba za ta iya bacci ba idan ba a gefenshi ba.

********

Tabbas tunaninsa a kan Maryam gaskiya ne, domin tunda ya fito daga ɗakin ta nemi walwala ta rasa. Ba komai ya tafi mata da wannan walwala ba sai zazzafan kishin da ya turnuƙe mata zuciya, saboda ko shakka babu irin kulawar da yake ba ta ce zai ba Aisha.

“Illar auren mai mata kenan, komai na shi sai ya raba biyu ya ba ta rabi.”

Cike da takaici Maryam ta faɗi haka sannan ta kashe fitilar ɗakin.

********

Kan gado ta hau tare da gyara ma Haneefa kwanciya, kasantuwar a tare za su kwana saboda tsoro da take ji. Ko kusa babu bacci a idanunta, sai ma wata irin kewar mijinta da ke ƙoƙarin danne kishin da ke kwance a zuciyarta. Wayarta ta ɗauka, kai tsaye hotuna ta shiga, inda ta ci gaba da kallon kyakkyawar fuskar Khamis mai ɗauke da wushirya a tsakanin haƙoransa, sosai ta riƙa jin ina ma a zahiri take kallonsa. Yar matsakaiciyar sumba ta kai ma wani hoto wanda Khamis ya ɗauke su a lokacin ta na kwance a kan ƙirjinsa.

“Ina sonka mijina.”

Ta faɗa tare da kafe hoton da idanu.

Irin abin da Aisha take neman tsarin Allah a kanshi kenan, kullum fatanta kada Allah ya kawo ranar da zuciyar Khamis za ta haɗu da zuciyar wata mace har su yi tunanin juna. Sai dai tunda Allah ya san yadda ya halicci mazan bai karɓa mata ba. Sai ma ya sanya hakan ya zama jarabawa a gare ta, wadda idan ta yi haƙuri za ta cinye ta har ta sha romon.

“Haƙuri dai ne kullum shawarar da ku ke ba duk wanda ke cikin ƙunci, to na bi haƙurin da gudu ba ko takalmi.”

Amsar da Aishar ta yi ba wata da ta yi mata comment a kan post ɗin da ta tura Facebook da tsakar dare kenan, saboda idan ba fidda maganar ta yi ba, Allah ne kaɗai ya san halin da za ta shiga a wannan lokaci. Ɗabi’arta ce yaɗa duk wata damuwar da ta same ta a social media da sunan neman mafita, a ganin ta nan ne za ta samu shawarwari iri daban-daban, ba tare da ta san masu ba ta shawar ba. A nan ne kuma suka haɗu da Zuzee, tun suna abota a facebook har suka fara ziyartar juna. Kan ka ce me Zuzee ta cusa ma Aisha aƙidu daban-daban. Daga cikinsu har da na ƙin matan Katsina wai suna da asiri, mafarin ta ɗaura karan tsana akan Maryam kenan.

********

Maryam kuwa tana gama azkar ɗin safiya ta ɗauki wayarta ta kunna.

“Mammy ma ta na facebook”. Haneefa da ke gefenta a kan sallaya ta faɗi haka.

“Da gaske?”

Maryam ta tambaye ta, lokaci ɗaya kuma tana karanta wani post da adadin masu comments da likes ɗinsa ya ɗauki hankalinta

A zuci Maryam ta shiga karanta post ɗin, inda yake cewa,

‘Don Allah sisters ku bani shawara, ina cikin matsananciyar damuwa, a can baya lafiya lau nake zaune da maigidana, amma yana ƙara aure abubuwa suka fara canzawa, sai dai wanda ya fi muni shi ne, bayan dawowarsa ɗakina sai yake nuna mini baya jin daɗin kasancewa da ni…’

Ɗan ɗauke kai Maryam ta yi daga kan screen ɗin, lokaci ɗaya kuma ta gyara zama tare da faɗin, “Tirƙashi.”

Tambayar ta Haneefa ta yi da cews,

“Anty me aka yi?”

Amsa ta bata da,

“Wani ikon Allah nake gani Daughter.”

Cikin ranta kuma tana mamakin yadda wasu matan basu ɗauki sirrinsu na aure a bakin komai ba, ko yaya matsala ta faru tsakaninsu da miji ko kishiya sai su zo group ɗin da ke da dubunnan membobi suna neman shawara. Duk da hakan ba kowane lokaci yake da illa ba, saboda ana samun shawarwarin da suka dace, amma wani sirrin bai kamata a kawo shi a media ba, in dai mai shi ta san me take yi.

Rungumo Haneefa da hannu ɗaya ta yi, sannan suka maida hankalinsu ga wayar. Ci gaba da karanta post ɗin ta yi, bayan ta gama ta dawo Comment section domin ganin abin da members suke cewa.

‘Ke rabu da ɗan-banza, zumuɗin Amarci ne, yana gama yayin ta zai dawo miki.”

Comment ɗin da wata ta yi kenan wanda shi ma ya ɗauki hankalin wasu suka fara yi mata reply.

Wasu na dariya, wasu kuma na faɗin,

‘ Wallahi kuwa.’

ita kuwa wadda ta yi post ɗin mentioning sunanta ta yi tare da faɗin,

‘Nima haka na faɗa mishi, kuma wallahi ranar da zai kawo kanshi zai gane shayi ruwa ne.”

Baki Maryam ta taɓe, cikin ranta kuma ta ce,

‘ Indai Amaryar irin mu ce ba ranar da zai dawo miki wallahi.”

A zahiri kuma ta danna mata ‘Haha’ sannan ta fito don ci gaba da karanta Comments.

Wani wurin ta yi dariya, wani wurin kuma haushi ya kama ta, domin kaso mai yawa na masu comments zagin mijin suke, wasu kuma na faɗin asiri ne Amarya ta yi, tunda ana haka.

A ɓangaren poster ma, sosai reply ɗin da take ma wasu ya nuna ma Maryam tana zargin Amaryar ta mata asiri ne domin an faɗa mata garinsu amarya sun shahara da asiri. Sannan a yadda ta lura, poster ta fi na’am da shawarwarin masu iza ta akan ta juya ma mijinta baya har sai ya gane kurensa. Ƙuri Maryam ta yi ma wayar, a zahiri screen ɗin take kallo, amma a baɗini wani tunani na daban take yi, saboda reply mai ɗauke da,

‘Yar Katsina ce, kuma duka kwana goma da auren.’ Ya nuna kamar post ɗin ya shafe ta.

Rikici ne ya kaure tsakanin matan Katsina, da kuma masu faɗin, ‘Kishiya ‘yar Katsina ko jaraba, idan ma baki iya bin malamai ba to ki haɗa kayanki tun kafin ta kore ki.’

Take tulin raddi mai zafi ya cika bakin Maryam, amma son warware shubuhar da ta mamaye mata zuciya ya sa ta buɗe profile ɗin mai post wanda ke ɗauke da sunan Shatu Usman. Ɗif wutarta ta ɗauke lokacin da ta yi arba da picture ɗin Haneef da Haneefa a jikin profile picture ɗin.

Haneefa na gani ta ce “Laa! mammy ma tana da wannan hoton.”

Maryam ba ta samu damar tanka mata ba, sai ma ta cigaba da kutsa kai a cikin profile ɗin. Duk wasu shaidu da ke nuna Aisha ce poster sun tabbata saboda har ga sunan Khamis Abdullahi a matsayin mijinta. Maganganun Aisha sun ɗaure mata kai, tunani ta shiga yi ko ta nuna mata ita ce Amaryar, kamar yadda wasu ke sara da mutum a sama, sai sun gama baje kolin damuwarsu a group, ashe duk akan idanun waɗanda ba sa so su gani, ƙarshe abin ya ƙare da rikici, shi ya sa ba kowace damuwa ba ce ya kamata mu riƙa kai ta social media.

Maryam ta san in dai ta nuna ita ce Amarya, to rikici ne za a yi wanda zai baro media ya dawo cikin gida, kuma ko shakka babu abin ba zai yi ma kowa daɗi ba.

Fasawa ta yi tare da ɓarkewa da dariyar mugunta.

“Kina Atlantic Ocean madam, tunda har ƙaddarar kishi ta haɗa ki da ‘yar Katsina.”

Haneefa ma dariya ta riƙa yi, a baɗini Maryam ta ce,

‘Yarinya uwarki ta shiga uku.” Sannan ta dube ta suka cigaba da kwasar dariya.

Tunanin comment ɗin da ya kamata ta yi ta shiga yi, bayan ta samu abin cewa ta fara rubuta mata,

“Baiwar Allah ki yi haƙuri, duk sa’adda namiji ya ƙara aure to sai kin toshe kunnuwanki, domin za ki ji abubuwa kala-kala, da kin yi haƙuri kuma za su zama tarihi. Kuma ka da ki fasa girki, ki yi abinci ki ƙoshi ke da yaranki, har ma da Amarya, hakan ne zai hana ita Amaryar ta gane akwai matsala a tsakaninki da mijinki.”

Dongon Comment ta so yi, sai dai rashin sanin abin da za ta ƙara rubutawa ya sa ta dakatawa. Fitowa daga facebook ɗin ta yi sannan ta a je wayar. Gyaran ɗakin ta shiga yi, tana gamawa ta yi ma Haneefa wanka tare da shafe mata jiki da mayuka masu daɗin ƙamshi.

Riga ta maida mata, sannan ta ce, “Je ki wurin Mammy ta canza miki kaya, kuma ki ce ina gaida ta.” Buɗe mata ƙofa ta yi, bayan ta fita, ta maida ƙofar ta rufe.

Da farincikin sanin halin ƙuncin da Aksha ke ciki ta faɗa banɗaki ta yi wanka. dama zulluminta ace Khamis ya samu farinciki a wurin Aishar, wanda hakan ba ƙaramar barazana ba ce ga zuciyarta. Kuma tunda ta fahimci Aishar na da sakaci a wurin miji dole ta ƙara jajircewa domin burinta shi ne Khamis ya zama mallakinta ita kaɗai. Irin wannan buri na Maryam sam bai dace ba, babu dalilin da za ki iske mace da mijinta, kuma ki ce so kike ya barta. Ba a hana ki zama tauraruwa ba, amma ki ji tsoron Allah, ka da ki yi abin da zai wulaƙanta uwargidansa saboda ke. Namiji Allah ya yi shi don mace huɗu ne, idan kin ce ke kaɗai za ki mallake shi kin shiga haƙƙinsa, ita ma da kike son raba ta da shi kin zalunce ta. Don haka mata mu yi ma kanmu faɗa.

Simple make-up ta yi, sannan ta sanya doguwar riga ta atamfa, wadda ɗinkin ya yi daidai da shape ɗin jikinta. Tana cikin ɗaura ɗankwali ne ta ji ana knocking ƙofa.

“Waye?”

Ta tambaya, duk da jikinta yana ba ta Khamis ne, saboda ta ɗan jiyo muryarsa sama-sama.

Ƙayataccen murmushi ta saki lokacin da ya amsa mata da, “Mutum ne.”

Sai da ta ƙarasa ɗaura ɗankwalin sannan ta miƙe. Ƙare ma kanta kallo ta yi a jikin dressing mirror, ƙasan ranta kuma tana yaba kyawun da ta yi wanda dole ya ƙayatar da Khamis.

Cikin takun ƙasaita ta je ta buɗe ƙofar.

“Good morning.”

Khamis ya faɗa tare da ware hannayensa alamun ta shigo a jikinsa, lokaci ɗaya kuma ya sakar mata tattausan murmushin da rabon ta da irin sa tun daren jiya.

Martanin murmushi ta sakar mashi tare da ƙin shiga a jikinsa kamar yadda ya buƙata.

Sosai kwalliyarta ta tafi da dukkan nutsuwarsa, har ta kai ga ya aje hannayensa ba tare da ya sani ba.

Hakan ya ba ta damar juyawa tare da ci gaba da tafiya mai cike da jan hankali ta koma cikin ɗakin. Bin ta ya yi kamar raƙumi da akala, lokaci ɗaya kuma idanunsa na kan hips ɗinta yana kallon yadda take juya su. Ji yake kamar ya ruƙo ta, sai dai gudun ɗaukar alhakin Aisha ya sa shi dole ya haƙura.

A gefen gado suka zauna, cikin shauƙin da ta sakar masa a jiki ya ce,

“Irin wannan salo haka ai sai ki sa na susuce. Kin yi kyau ba kaɗan ba Princess, bacin ina gudun shiga haƙƙin Uwargida, da a nan zan zauna na yi ta aikin kallon ki.”

Har cikin ranta ta ji daɗin wannan yabon da ya yi mata, murmushi mai sauti ta yi tare da ɗan rausaya kai.

“Godiya nake baby, fatan ka ta shi lafiya.”

“Wallahi lafiya ƙalau Princess, sai dai na yi kewarki.”

Ruƙo hannunta mai taushin gaske ya yi sannan ya ɗora da,

“Hala kema kin yi kewa ta.”

Kallon shi ta yi, cikin ranta kuma tana tuna irin yadda bacci ya ƙaurace mata a daren jiya sakamakon kewar sa da yake tambayar ta.

Ɗan kwantowa ta yi a jikinsa don itama ta ga kewarta a idanunsa saboda wani irin kallo mai kashe jiki da yake yi mata,

“Uhm, ko kaɗan jiya ban yi bacci ba saboda rashinka a kusa da ni. kai kuwa na san uwargida ririta ka ta riƙa yi har ka yi bacci, ƙila ma tunda ka shige ba ka sake tunawa da ni ba.”

Wannan magana daidai take da bugun ciki, domin so take ta ji ko zai faɗi wani abu na aibu a kan Aisha. Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke tare da ɗora haɓarsa a kanta, shi kaɗai ya san baƙin cikin da shi ma ya kwasa wurin Aisha a daren jiya, sai dai ba ya jin zai iya faɗa mata, saboda ya ɗaukar ma ransa ba zai riƙa yawo da sirrin matansa a tsakaninsu ba, muddin dai ba Alkhairi zai faɗa.

Kuma hakan shi ne daidai, domin duk namijin da ke kai kawo da sirrin matansa a tsakaninsu kamar ya jawo ma kansa rigima ne, a wani ƙaulin ma zai iya zama munafikin mata. Idan kuwa namiji ya yi irin halin Khamis, to ko za a samu rikici ba kamar wanda namijin ya zama sanadi ba.

“Tabbas fa uwargida ta ririta ni, amma duk da haka ban kasa tuna ki ba saboda ke ta musamman ce.”

Ko kusa Maryam ba ta so jin wannan amsar a bakinsa ba, don haka ne mamaki ya kama ta, har ta fara ƙaryata cewar ko ba Aisha ce ta gani a facebook ba, domin yadda ya yi maganar babu alamun wasa a ciki.

Murmushin yaƙe ta yi, tare da ƙara lafewa a jikinsa, cikin ranta kuma tana hasashen riritawar da ya ce ya samu a wurin Aisha, take kishi ya taso mata wanda da ƙyar ta iya ɓoye shi.

Shirun da ya ratsa su ne ya ba Khamis damar faɗin,

“Mu je ga breakfast can Aisha ta shirya.”

Kamar ta ce ba za ta fita ba, amma gudun ya ji ba daɗi ta miƙe, ya so riƙe mata hannu, amma ta ƙi bari saboda ita ma ba za ta so ranar girkinta ta ga hannun Aisha a cikin nasa ba.

Sosai ta yi mamakin yanayin Aisha, saboda ko kaɗan babu alamar damuwa a tare da ita.

“To ya haka?”

Ta tambayi kanta. Domin in dai ita ce ta gani a facebook to ba za ta fito ɗaki ba bare har ta yi wani girki.

‘Ki ka san kalar nata salon?’

Wani sashe na zuciyarta ya tambaye ta.

Abin da ba ta sani ba shi ne, shawarar da ta ba ta a facebook ce ta fito da ita, wadda ba don ita ba da ko ƙeyar Aishar ba za ta gani ba. Murmushin da ta ke yi ma yaƙe ne, don Maryam ɗin ba ta lura ba da ta fahimci haka.

Magana Aisha ta yi mata,

“Amarya sai yanzu ake fitowa?”

Wayancewa Maryam ta yi tare da gaishe ta domin ba ta san amsar da za ta ba ta ba.

Kitchen Aishar ta koma, inda kuma Maryam ta wuce dining ta zauna, Haneef da ke kujerar hannun damar Khamis ya ce mata, “Anty yau nima a ɗakinki zan kwana.”

Dariya ta yi sannan ta ce,

“Toh Haneef, Allah ya kai mu daren lafiya.”

Dubansa Khamis ya yi,

“Ba gaisuwa sai za ka kwana a ɗakinta?”

Gaishe da ita ya yi, ta amsa cike da son yaron. Haneefa kuwa cewa ta yi,

“Ni dai na gaishe ki a ɗaki ko Anty?”

Maryam ta ce,

“Eh daughter mun gaisa, ta gefen idonta kuma tana kallon yadda Khamis ya kafe ta da idanu yana dariya. Zuwan Aisha ne ya tsaida komai. Inda kuma fuskarta a yanzu ba yabo ba fallasa, wanda Khamis ya san duk saboda shi ne. Maryam ta lura, amma sai ta basar. Serving yara Aisha ta fara yi, wanda a can baya sai ta fara serving Khamis kafin su.

“Uhm, madam sauri nake fa.” Khamis ya faɗa yana ‘yar dariya.

Kicincine fuska ta yi kamar ta kurɓi kunu mai zafi.

“To me zai hana ka yi serving kan ka tunda sauri kake.”

Khamis ya so ta wayance ta yadda Maryam ba za ta gane me ya faru ba, amma sakarcinta ya sa tun ba a je ko ina ba za ta fasa ƙwai.

Wasa ya maida abin ya ce,

“Ni da nake da ku, me zai kai ni serving kaina?”

Kallon Maryam ya yi tare da faɗin,

“Ko ba haka ba Amarsu.”

Yanzu kam Maryam ta samu yaƙinin Aisha ce ta gani a facebook sakamakon kasa danne fushinta da ta yi.

Amsa ta ba Khamis da,

“Lallai dai kam.”

Lokaci ɗaya kuma tana dariya.

Serving ɗinsu Aisha ta yi. cikin ranta kuma tana jin tsanar wannan zaman cin abincin a tare, wanda kuma ko shakka babu sai ta kawo ƙarshensa, idan ya so kowa ya riƙa cin abincinsa daban.

Bayan sun gama breakfast ɗin ne Khamis ya bi ta ɗaki, sai dai ko kallon arzki bai ishe ta ba, bare ta tanka mishi. Sauri yake zai fita, don haka ne ya zaro kuɗi ya aje mata a kan mirror,

“Gashi nan idan za ki ƙara cefane.”

Duk da a gidan babu abin da suke buƙata na cefane.

Ɗakin Maryam ya nufa, inda ya same ta ita da yara sun rashe a ƙasan carpet suna game ɗin Ludo.

Sosai yake jin daɗin yadda ta jawo yaransa a jiki fiye da ma mahaifiyarsu. Domin Aisha tana da halin watsar da yara musamman idan da waya a hannunta.

“Abba ka zauna mu yi game ɗin.” Haneefa ta faɗa lokacin da ya ɗan russuno yana kallon su, kasantuwar in dai yana gida to da shi ake game ɗin, kuma duk Maryam ce ta zo musu da wannan salon.

“Sauri nake Mamana, idan na dawo sai mu yi.”

Miƙewa ya yi tare da duban Maryam da ta tattaro dukkan nutsuwarta a kansa, har Haneef ya maida ta gida ba tare da ta sani ba.

Cikin sigar zaulaya Khamis ya ce, “Ba za a yi mani rakiya ba?”

Ɗan maƙe kafaɗa ta yi.

“Uwar gidan fa?”

Marairaicewa ya yi.

“Ni naki nake so.”

Ta san muhimmancin lokacin mijinta, don haka ba ta sake jayayya da shi ba ta miƙe ita da yaran. Fita suka yi, inda rakiyarta ta tsaya a falo saboda taka tsantsan, su kuma yaran suka raka shi har bakin mota. Bayan tafiyarsa suka dawo ɗakin Maryam suka dasa game ɗin.

Tun da Khamis ya tafi bai sake waiwayar gida ba saboda gudun ɓacin rai, sai dai su kan yi waya akai-akai da Maryam don ya ji lafiyar iyalansa. Hakan kuwa ko a jikin Aisha, da ya dawo da kada ya dawo duk ɗaya.

Da daddare ma yana dawowa bai samu ganinta ba, saboda ta sanya ma ƙofar key, kuma ba irin faman da bai yi da ta buɗe ba amma ta ƙi.

Da takaicin wannan ya kwanta, inda a wannan dare ya nemi bacci a idanunsa ya rasa. Wayar Maryam da itama tsoro ya hana ta bacci ya kira, saboda Aisha ta ɗauke yaranta tun bayan Isha’i ya kira.

Cikin muryar da ita kaɗai za ta iya jiyo wa ya ce,

“Ba ki yi bacci ba?”

Daga can ta fashe da kuka ta ce, “Tsoro nake ji.”

Har cikin ransa yake jin ɗacin kukan Tamkar ya buɗe idanu ya gan shi a gabanta, sai dai zuwansa wurinta ne zai tona asirin faɗansa da Aisha.

Lallashin ta ya riƙa yi da maganganu masu kwantar da hankali har ta samu nutsuwa.

Da tunanin ina Aishar take da har ya samu damar faɗa mata waɗannan maganganun suka yi sallama. Aisha kuwa yadda ta barshi da rungumar pillow a yau, haka duk ranar girkinta yake kwana shi kaɗai, har zullumi yake ranar girkinta ya zo saboda ba abin da zai kwasa sai takaici.

Sosai yake jin ba daɗin haka, saboda har ga Allah yana son ta, kuma nisan da ke shiga tsakaninsu ba ƙaramin taɓa zuciyarsa yake yi ba. Ɗaukar ma ransa ya yi idan girkinta ya zagayo zai kawo ƙarshen matsalar, idan kuwa ba ta sauko ba to zai haƙura, saboda kulawar da Maryam take bashi kaɗai ma ta ishe shi.

<< Kishiyar Katsina 4Kishiyar Katsina 6 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.