Skip to content
Part 9 of 21 in the Series Kishiyar Katsina by Hadiza Isyaku

Zuzee na jin Aisha ta ce Khamis ya kusa dawowa ta yi saurin faɗin, “Eh a bari sai jibi ma, ko wani lokacin kafin ta dawo dai.”

Tana rufe baki ta shiga haramar tafiya a ƙasan ranta saboda bata so Khamis ya iske ta a gidan.

Aisha da ta ƙagu ta ga me ke cikin ɗakin Maryam ta ce,

“Goben dai don Allah.”

Don rabon ta da ɗakin tun ranar walima da ta raka Khamis.

Ɗan jim kaɗan Zuzee ta yi, daga bisani ta ce,

“Gaskiya gobe ba zai yiwu ba, ni tsoro nake kada muna cikin buɗe ɗakin mijinki ya dawo mu shiga uku.”

Sai da Aisha ta nazarto lokutan dawowar Khamis sannan ta ce, “Shi fa idan ya fita da safe, bai ƙara dawowa sai yamma, don haka kada ki ji komai.”

Zuzee ta ce,

“To bari mu gani.”

‘Yar hira ce suka taɓa, a ciki suka yanke abar buɗe ɗakin sai idan Khamis ya yi tafiya, saboda Zuzee hankalinta bai kwanta ba, tsoronta kada suna ciki ya dawo, tunda gidansa ne, babu kuma mai iya yi mishi shamaki da dawowa a duk lokacin da ya ga dama.

Shirin tafiya Zuzze ta fara. Aisha da ke jin ko kwana za su yi suna hira ba za ta gaji ba, saboda wurin da ya fi yi mata ƙaiƙaiyi ne Zuzee ke taya ta sosawa ta ce,

“Kai Zuzee ba dai tun yanzu ba.”

Ɗan yamutsa fuska Zuzee ta yi sannan ta ce,

“Ke wallahi tafiya zan yi, Aisha ta ce,

“Duka fa ƙarfe biyar.”

Idanunta a kan fuskar wayarta ta ƙarashe maganar.

“Ni fa mijinki ne bana so ya taras da ni a gidan nan.”

Zuzee ta faɗa tare da yafa mayafinta da ke hannunta. Abin da Zuzee ke gudu ne ya afku, domin ƙarar buɗewar gate suka ji, wanda ko shakka babu Khamis ne ya dawo. Damuwa bayyane a fuskarta ta dubi Aisha,

“Kin ga abin da nake gudu ya afku.”

Sosai Aisha ta yi mamakin yadda Zuzee take kyarma don Khamis ya shigo.

“Toh wai don Allah sau nawa yana iske ki a gidan nan, sai yanzu za ki tsiro da ba kya son ya iske ki, haba don Allah.”

Karɓar mayafin Zuzee ta yi ta aje tare da jawo mata hannu alamar ta zauna. Zuzee na jin maganar Khamis shi da yara ta zauna tare da ɗan kama kanta.

Khamis kuwa tuni Haneefa ta faɗa mishi wai Anty Zuzu ta zo. Sosai “Zuzu” da Haneefa ke cewa ya bashi dariya, don bata iya faɗin Zuzee ba. Da sauran dariya a bakinsa ya shigo falon. Zuzee na ganinsa ta ƙara kame kanta, tsoronta kada Aysha ta yi wani abu, wanda ko shakka babu za’a ce ita ce, tunda tare ake ganin su.

Tun kafin Khamis ya zauna ya dubi Zuzee ya ce,

“Aaa! Malama Zuhura ce a gidan mu!”

Zama ya yi a hannun kujera, lokaci ɗaya kuma hannayensa na cikin na Haneefa tana jujjuya shi.

‘Yar dariya Zuzee ta yi tare da ɗan russuna kai,

“Wallahi kuwa ni ce, Ina wuni?”.

Ya ce, “Lafiya lau, kwana biyu?” Zuzee ta ce, “Alhamdulillahi”.

Kusan a tare suka miƙe shi da Aisha da fuskarta ke ta annuri, sannu da zuwa ta yi mishi, ya ce, “Yauwa madam.”

Sannan ya nufi ɗakinsa, ba tare da damuwa da lamarin Zuzee ba kamar yadda take tunani.

Ɗan duban Zuzee Aisha ta yi ta ce,

“Ina zuwa.”

Sannan ta bi bayan Khamis.

Wayarsa da key ɗin motarsa ya aje kan gado. Duban Aisha da ta shigo yanzu ya yi, sai ya ga wani irin nishaɗi kwance a fuskarta.

“Madam irin wannan nishaɗi haka?”

Ya faɗa lokacin da yake cire agogon hannunsa.

‘Yar guntuwar dariya ta yi ta ce, “Kai Abban Haneef ina nishaɗin anan?”

Dariya ya yi sannan ya ce,

“Gashi nan kwance a fuskarki.”

Ita kanta ta san duk wunin yau ranta bai ɓaci ba saboda Maryam ɗin da take kira alaƙaƙai bata nan, uwa uba kuma ga Zuzee da suka kashe abubuwa da yawa suka binne tare.

Zama ya yi a gefen gado sannan ya buƙaci ta bashi ruwa a fridge.

Matsowa ta yi dab da shi ta ce, “Abincin fa?”

Kai ya girgiza.

“A’a, daga gidanmu nake.”

Ruwan roba ta ɗauko mishi a fridge, za ta miƙa mishi kenan Haneefa ta turo ƙofar.

A ɗan fusace ta tambaye ta,

“Ya aka yi?”

Saboda ta hana su shigowa ɗaki kai tsaye ba tare da sallama ko ƙwanƙwasawa ba, musamman idan Khamis na ɗakin.

A tsorace Haneefa ta ce,

“Anty Zuzu ce ta ce tafiya za ta yi.” Aisha ta ce,

“To ki ce mata gani nan zuwa.”

Sai da Haneefa ta fice daga ɗakin Sannan Aisha ta dubi Khamis da ya kafe ta da idanu ta ce,

“Bari don Allah na sallame ta.” Murmushi ya yi tare da faɗin, “Okay.”

Aisha na fitowa ta ga har Zuzee ta yafa mayafi ta kuma ɗauki jaka.

“Kin dai matsa sai kin ta fi.”

Zuzee ta ce,

“Kada ki damu zan dawo.”

Ranar da za ta dawo ɗin suka sa, sannan Aisha ta koma ɗaki ta ɗauko dubu ɗaya ta bata.

Har bakin gate ta raka Zuzee sannan ta dawo cikin gidan. Guje-guje ta taras da Haneef da Haneefa suna yi a falon, ce musu ta yi,

“Banda faɗa.”

Sannan ta shiga ɗakin Khamis.

Iske shi ta yi ya ɗan gyara zamansa tare da jingina bayansa da kan gado, idanunsa da ke lumshe ya buɗe tare da faɗin,

“Ta tafi ko?”

“Umm ta tafi.”

Aisha ta faɗa tare da zama a gefensa. Sake lumshe idanun ya yi, lokaci ɗaya kuma ya faɗa duniyar tunanin Maryam, da tuni ta faɗa mishi sun sauka.

Duban shi Aisha ta yi, lokaci ɗaya kuma ta riƙe robar ruwan da ke hannunsa ta ce,

“Bacci Abban Haneef?”

Sakar mata robar ya yi sannan ya buɗe idanun ya ce,

“Wallahi kuwa.”

Ɗan gyaɗa kai ta yi ta ce,

“Bacci da yamma, ka dai yi haƙuri dare ya yi.”

Sosai ya buɗe idanunsa tare da sauke su a kanta, yanzu kuma kyau da fari ya ga ta ƙara mishi, da yake bai gani ya ƙyale sai kuma ya fara tsokanar ta da,

“Anya Aisha ba ajiyar ƙannen Haneefa a cikinki?”

Ɗan shagwaɓe mishi ta yi tare da faɗin,

“Me ka gani kuma?”

‘Yar dariya ya yi ya ce,

“Masha Allah, wani irin fari da kyau kika yi.”

Ƙarar wayarsa ce ya hana ta bashi amsa, inda ta bi shi da idanu lokacin da ya ce,

“Jama’ar Kt ne.”

Ras ta ji gabanta ya faɗi, ba don ranta ya so ba ta ce,

“Yanzu kam ai sun isa.”

Kai kaɗai ya ɗaga mata lokacin da ya kanga wayar a kunne ya ce,

“Shikenan ana shiga gida sai aka manta da Hubbi ko?”

Baki Aisha ta taɓe tare da ɗauke kai.

Sai dai ɗauke kan bai hana ta jiyo muryar Maryam tana faɗin,

“Tuba nake bebina, bari na yi in nutsu tukunna sai in kira ka.”

Murmushi mai sauti ya yi, wanda ke nuna yana jin daɗin wayar. Tambayar ta mutanen gida ya yi, amsa ta bashi da,

“Duk na same su lafiya, Ina yarana da Ummansu?”

Cewa ya yi,

“Ga madam ɗin nan.”

Tare da miƙa ma Aisha wayar, ba don ta so ba ta karɓa ta ce, “‘Yan tafiya ya gajiyar hanya?”

Maryam da farincikin ganin ta kusa da ƴan gidansu ya bayyana har a muryarta ta ce,

“Gajiya ta bi lafiya, ina yarana?” Aisha ta ce,

“Suna falo.”

Saƙon gaisuwa Maryam ta bada a ba su Haneef, inda Aishar ita ma ta ce Maryam ta gaishe mata da ‘yan gidandsu.

Wayar ta miƙa ma Khamis da ke ta washe baki, sannan ta miƙe za ta fita, ruƙo hannuta ɗaya ya yi tare da yi mata nuni da ta zauna.

Sai da suka yi sallama da Maryam sannan ya ce,

“Ina za ki je?”

Amsa ta bashi da,

“Fita zan yi.”

Ɗan marairaice fuska ya yi.

“Sai ki barni ni kaɗai?”

Sosai yanayinsa ya ba ta dariya, inda ta ce,

“To ba ga amaryarka nan a waya ba.”

Sauko da ƙafafunsa ya yi ƙasan gado tare da gyara zama yana fuskantar ta.

“Ai ba wata amarya a nan sai ke, don haka ki zauna mu yi hira kafin magariba ta yi.”

Aisha ta ji daɗin wannan yanayin, hirar su mai cike da soyayya suka yi, inda ya maida kansa kan cinyarta suka ci gaba da maida yadda aka yi. Sai da aka fara kiran Magarib sannan suka fito daga ɗakin.

******

A birnin Katsinan Dikko kuwa, ɓata lokaci ne ma faɗin irin farincikin da Maryam ta samu kanta lokacin da ta ganta zaune a cikin gidansu. Su ma ‘yan gidan ba ƙaramar murna suka yi ba, hatta maƙwabta sai ga su suna shigowa yi mata sannu da zuwa. Gidansu Maryam gida ne madaidaici, su ba za ka kira su masu irin kuɗin nan ba, sannan idan ana maganar talauci ma ba a sa gidansu a lissafi.

Mata biyu ne a gidan, mahaifiyarta wadda suke kira da Mama, sai kuma uwargidan wadda ita ma gaba ɗaya yaran gidan suke kira da Hajiyarmu.

A kowane ɗaki akwai ‘ya’ya, sai dai tsabar haɗin kan matan gidan ya sa ba za ka iya banbance ɗakin da kowannen su ya fito ba.

Kuma wannan haɗin kan ya samo asali ne daga adalcin da maigidan yake kwantatawa ga iyalansa, saboda kowa ya shaide shi dattijon arziƙi ne a garin ma baki ɗaya.

Zaune ahalin gidan suke a babban falon maigidan, inda gaba ɗaya hirarsu ta Aisha ce da har yanzu Hajiyarmu ta kasa manta irin wulaƙancin da ta yi musu a ranar walimar Maryam. Zaune Alhajin su Maryam ya ke akan kujera Two seater, Inda Hajiyarmu da Mama suke zaune a kan three seater.

Yaran gidan waɗanda suka haɗa da Maryam, Zahra’u da sauran yayye da ƙanne suna zaune a ƙasan carpet. Hajiyarmu ce ta dubi Alhajinsu Maryam ta ce,

“Wallahi Alhaji ban taɓa ganin fitsararriyar yarinya irin kishiyar Maryam ba.”

Dariya gaba ɗaya ɗakin aka ɗauka, don sun san kwanan zancen, ashar da ɗibar karama ce Aisha za ta yi ta sha a bakinta, kasantuwarta mace mai tsegumi, tana da kirki, amma ba ta ɗaukar raini sai idan ta kama.

Zahra’u ce ta dubi Asma’u da ke gefenta ta ce,

“To fa! Yau kishiyar Maryam ta shiga uku.”

Asama’u na dariya ta ce,

“Ke dai bari.”

Maida dubansu ga Alhajinsu suka yi lokacin da ya ce,

“Ai yadda kuka bada labari kam ba ta kyauta ba.”

Hajiyarmu da ta ƙara tsinano baki saboda tijara ta ce,

“Ina fa ta kyauta Alhaji, yarinyar nan ba ta ga tsufanmu ni da Hajiya magajiya ba, wai mun bata amana, wallahi sai ta murmura idanu ta ce ‘ban karɓa ba.'”

Nuna yadda Aishar ta murmura musu idanu ta yi.

Mama na kwasar dariya ta ce,

“Kai Hajiya baki da dama.”

Hajiyarmu ta ce,

“Wallahi Maman Maryam, ai gudun yin abin kunya biyu ne kawai da ba abin da zai hana ni kwasa mata mari.”

Alhaji ya ce,

“Kawai sai ki daki ‘yar mutane?” Hajiyarmu ta ce,

“To ba sai ta ga tsoffin zamani ba.”

Sosai ta ci gaba da nanata maganar, wanda take nuna zallar ɓacin ranta akan abin da Aisha ta yi musu, wani wuri a yi dariya, wani wuri kuma a jinjina mata, saboda ta iya faɗin gaskiya.

Mamansu Maryam da ba ta cika sanya abu a rai ba ta ce,

“Ai kanta ta zubar ma ƙima.” Alhaji ya ce,

“Aikuwa dai, don ma shi Khamis ɗin tsayayyen namiji ne, ai da ƙila zaman ba zai yiwu ba.”

Hajiyarmu ta ce,

“Itama Maryam ɗin ai tsayayya ce, duk shegen da ya sa mata yatsa a abaki sai ta taune ɗan banza.”

Mama da ke ta nishaɗantuwa da sababin Hajiyarmu ta ce,

“Ai rainon ki ce ita.”

Hira mai cike da nishaɗi suka ci gaba da yi, a nan ne Khamis ya sha ɗimbin albarka a wurin mahaifan Maryam, domin uwar tsarabar da ta kawo musu ta ƙara tabbatar musu da sun yi sa’ar suruki. Fatan samun suruki irin Khamis suka yi ma Asma’u da Zahara’u, saboda su kaɗai ne ‘Yan matan da suka rage musu a yanzu, sauran matan biyar duk sun yi aure. Dama su goma sha takwas ne a gidan. Mata goma, maza takwas. A mazan ma guda uku sun yi aure suma, sai samari biyu, da kuma ƙanana uku.

Bayan su Maryam sun gama hirar ne suka baro ɗakin mahaifinsu. Tsakar gida suka zauna, Maryam na dariya ta ce ma Asma’u da ke gefenta,

“Wai haka Hajiyarmu ke bada labarin nan?”

Don har yanzu ba ta daina dariya ba.

Sai da Asma’u ta gama dariya sannan ta ce,

“Ai nan baki ga komai ba, lokacin da abin na sabo har kuka take idan tana bada labarin, wai da tsufansu amma ‘yar cikinta ta musu fitsara.”

Maryam na dariya ta ce,

“Allah ya kyauta.”

Ɗakin Mama suka koma, suka sha hirarsu ta ‘yan’uwa.

Wurin goman dare ne wayar Maryam ta soma ruri, ko ba a faɗa mata ba ta san Khamis ne. Fitowa ta yi daga ɗakin ta koma can ƙuryar ɗakin Hajiyarmu saboda ba kowa a can, idanunta lumshe yayin da take kwance a kan gado ta yi magana cikin muryar da wanda take magana da shi ne kaɗai zai iya jiyo ta ta ce,

“Ina jin ka.”

Daga can cikin wayar Khamis ya ce,

“Ji nake kamar bani da lafiya.”

Cike da damuwa ta ce,

“Subhanallah, me ke damun ka?”

Tana jin sa’adda ya ƙara sassauta murya sannan ya ce,

“Ciwon rashin ki a kusa da ni ke damun zuciyata.”

Murmushi mai sauti ta yi tare da faɗin,

“Uhm, to yanzu ba gani a kusa da kai ba.”

Ya ce,

“Hakane baby, yanzu kina ina?”

Idanunta a lumshe ta ce,

“Ina cikin zuciyar mijina.”

Sosai Khamis ya ji daɗin wannan amsar, sai da ya ɗan sumbace ta a wayar sannan ya ce,

“Lallai kina cikin wuri mai daraja, wurin da babu makhaluƙin da zai iya samun muhalli a cikinsa face ke kaɗai. Nan fa ya shiga zayyana mata irin bala’in kewarta da yake yi.

Itama ɗin ji ta riƙa yi ina ma a tare take da shi a wannan lokacin. Jin motsin Hajiyarmu ne ya katse musu jin daɗin hirar, ce mishi Maryam ta yi,

“Sai da safe.”

Ya ce,

“Tun yanzu?”

Ta ce,

“Ga Hajiyarmu nan, kuma kunyarta nake ji.”

Khamis ya ce,

“Mijinki ne fa.”

Ta ce,

“To zan kira ka, amma ka tafi wurin uwargida yanzu, na san tana can tana jiranka.”

Ɗan shagwaɓe mata ya yi.

“Uhm ni ba zan ta fi.”

Dariya Maryam ta tuntsire da ita tare da katse kiran lokacin da Hajiyarmu ta ɗage labulen ɗakin tana faɗin,

“Motsin wa nake ji?”

Saukowa Maryam ta yi daga saman gadon ta ce,

“Ni ce Hajiyarmu.”

A falo suka zauna ita da Hajiyarmu, sabuwar hira suka dasa, yayin da Hajiyarmu ke dama fura.

“Wallahi Maryam aure ya amashe ki, haka ake so dama.”

Hajiyarmu ta faɗa idanunta na kallon Maryam kasantuwar akwai wutan nepa.

Murmushi kawai Maryam ta yi, cikin ranta kuma tana ƙara gode ma Allah da ya ba ta miji mai kulawa, tunda duk wanda zai gan ta sai ya yi Allah sambarka.

Maganar Aisha Hajiyarmu ta yi mata, cewa ta yi,

“To ita wannan ‘yar banzar ya zamanki da ita yake?”

Maryam na kwasar dariya ta ce, “Ba laifi kam, wata rana tsiya wata rana daɗi.”

Hajiyarmu ta ce,

“To kar dai ki bari ta raina ki, na san ki dama ba ki ɗaukar raini.”

Tunawa da maganar asiri Maryam ta yi, sai da ta gyara zama sannan ta ce,

“Wai cewa take asiri na yi na raba ta da mijinta.”

Baki Hajiyarmu ta taɓe.

“Haka suke cewa, sun kasa riƙe mazansu, sai miji ya auri Bakatsiniya ta bashi kulawa sai a ce asiri, to ko da wasa kada ki ɓata ranki da wannan, ku tafi a asirin kike yi.”

Maryam ta ce,

“To Hajiyarmu.”

Ci gaba da hirar suka yi har Hajiyarmu ta gama damun furar, a kofi ta zuba wa Maryam ta sha. Sai wurin ƙarfe sha ɗayan dare sannan Maryam ta shige ƙuryar Hajiyarmu ta kwana a gadonta.

******

Kunun gyaɗa da ƙosai aka yi musu da safe, sosai Maryam ta sha shi, saboda rabon ta da shi tun kafin ta yi aure. Wata irin kulawa Maryam ta ke samu a wurin ‘yan uwanta, hatta yayyenta maza da ba wani shiri suke ba saboda sun cika sa doka a gidan, amma sai gashi suna ta nan da nan da ita.

Har Mujahid, wanda ɗa ne a wurin Hajiyarmu ya ce a cikin ƙannen Khamis yana son guda. Alƙawari Maryam ta yi mishi idan ta koma za ta haɗa su. A daren kwanan Maryam na biyu ne ta shiga ɗakin Hajiyarmu za ta kwanta. Hajiyarmu ta ce,

“A’a Mairo, yau ɗakin mahaifyar ki za ki kwana.”

Ɗan ɓata rai Maryam ta yi.

“Kai Hajiyarmu to nan fa?”.

Hajiyarmu bata shakkar faɗin gaskiya don haka ta ce “Kin san uwa da ɗa sai Allah ko, kuma akwai Sirri tsanin ɗa uwa ko, toh ki je ku gana da mahaifiyarki”.

Sosai Maryam ta fahimce ta. Ɗakin mahaifiyarta ta dawo, inda kuma suka sha hirarsu ta uwa da ɗiya. Sosai Mahaifiyar Maryam ta yaba halin Khamis, saboda ɗimbin alkhairin da yake musu, ce mata ta yi,

“Wallahi Maryam kin yi sa’ar miji, don haka ki ƙara riƙe shi gam, kishiya kuma ki barta da halinta, ke dai kada ki cuta mata. Kin ga dai yadda muke zaune a gidannan, ko Alhaji bai taɓa jin kanmu ba, ba kuma saɓanin ne bamu samu ba, faɗa kam muna yi, amma mun ɗaukar ma ranmu barin abin a tsakaninmu domin samun kwanciyar hankalin iyalanmu.”

Bayan sun gama hirar ne suka kwanta. Kwanan Maryam uku da zuwa ta fara kai ziyara gidajen ‘yan uwa da abokan arziƙi. Gidan wata cousin sister ɗinta ta je mai suna Zainab, sosai suka shaƙu da juna, kai ka ce a gida ɗaya suke, don ba abin da Zainab bata sani ba na rayuwar Maryam.

Zanaib wadda ake kira da Maman Abba tana kwance a falo ta ji sallama, ta ɗauki muryar, sai dai ta kasa yadda don bata san da zuwan Maryam a gidanta ba.

Daga Zainab har yaranta Abba, Mahamud da Afrah ba wanda bai yi murna da ganin Maryam ba, musamman Afrah, saboda Maryam na ɗaukarta suna zuwa gidansu kafin ta yi aure.

A falo suka zauna, Zainab ta ce, “Maryam ni ai ba zan iya gane ki ba.”

Maryam na dariya ta ce,

“Kai Anty Zainab, ai ko kowa ya kasa gane ni na san banda ke.”

Zainab na dariya ta ce,

“Gaskiya ne, ƙawarki Afee ma ta gane ki bare ni.”

Gaisuwar yaushe gamo suka yi, nan Abba da Mahamud suka gaida Maryam. Kamo Hannun Mahamud ta yi, Abba kuma na gefenta shi da Afrah suna ta ‘yar dariyar murna.

Tambayar shi ta yi “Mahamud kwana biyu, ina makaranta.”

Cikin ‘yar muryar Mahamud ya ce, “Lafiya lau Anty Maryam”

Juyawa Maryam ta yi ga Abba ta ce, “Uhm, su Abba babban yaro.” Dariya kawai Abba ya yi. Tambayar shi ta yi,

“Ina Haidar.”

Haɗe baki Mahamud da Abba suka yi wurin bata amsa,

“An yaye shi.”

Da hanzari Maryam ta juya ta kalli Zainab,

“Wai Anty Zainab?”

Zainab da tausayin Haidar ya ta so mata ta ce,

“Wallahi kuwa.”

Cikin ‘yar damuwa Maryam ta ce, “Yanzu Anty Zainab har ya isa yaye?”

Zainab ta ce,

“Ya isa Maryam, yana gida ma na kai shi.”

Maryam ta ce,

“TohAllah ya sa a sha na shanu lafiya.”

Gaba ɗaya suka ce,

“Amin.”

Zainab da sauyin yanayin Maryam ke daɗa birgeta ta ce,

“Oh ni ‘yasu, ni kam me angon yake baki ne?”

Maryam ta gane inda ta dosa, amma sai ta ce,

“Kai Anty Zainab me kika gani?”

A taƙaice Zainab ta ce,

“Ƙiba.”

Sai da ta yi ‘yar dariya sannan ta ɗora da,

“Na san ba ni kaɗai ba, kowa ma ya faɗa miki haka.”

Maryam ta ce,

“Kwanciyar hankali ce kawai Anty Zainab.”

Zainab ta ce,

“Ai haka ake fata Maryam, Allah dai ya ƙara zaunar da kowa lafiya a dakinta”, Maryam ta ce,

“Amin.”

Ɗan shiru suka yi, can Zainab ta tuntsire da dariya.

“Wai ina uwargidanki, muna nan Hajiyarmu ke bada labari, wai an musu wulaƙanci.”

Sosai Maryam ta kama dariya ita ma, cewa ta yi,

“Tana can na baro ta da tsiyarta.”

Hirar Aisha suka dasa, nan Maryam ke ba ta labarin irin takun saƙar da suke yi, da kuma yadda Aishar ke kwaikwayon ta idan ta yi wani abin.

Nisawa Zainab ta yi,

“Kada ki ji komai don ta kwaikwaye ki, ke kika fara, kuma ke ce tauraruwa a wurin miji.” Maryam ta ce,

“Wallahi kamar kin sani, ba ki ga yadda yake ji da ni ba.”

Zainab ta ce,

“Kin iya takunki ne shi ya sa.”

Labari fa suka sha na ‘yan’uwa, har suka zo kan batun kayan mata. Da yake in dai a wannan harkar ce, to Anty Zainab ta ciri tuta, shi ya sa maigidanta ya ce ita da kishiya sai dai a lahira.

Akwai kazar Nonon raƙumi da Maryam ta gani a littafin da Haupha ta ba ta, maganarta ta yi ma Zainab, aikuwa Zainab ta ce ta san yadda ake dafa ta. Ware ranar da za a dafa kazar suka yi kafin Maryam ta koma.

Fitowa suka yi, inda Maryam da kanta ta shiga kitchen ta yi musu girki, saboda dama Zainab ba ta jin daɗin jikinta saboda yayen.

Da yamma liƙis Maryam ta fara shirin tafiya, Afrah da dawowarsu daga Islamiyar yamma kenan ta kama kuka wai sai ta bi ta, lallaɓata ta yi, sannan Abba da Fati mai aikinta, da kuma Mahamud suka raka ta bakin titi. Wani shago suka shiga ta siya musu sweet, sannan suka koma gida.

Ba ta daɗe a bakin titin ba ta samu Napep, shigarta ciki ke da wuya kiran Khamis ya shigo wayarta.

Ɗagawa ta yi tare da ɗan shagwaɓewa ta ce,

“Uwargida ta sa ka manta da ni ko?”

Daga can cikin wayar ya ce,

“Ita har ta isa?”

Maryam ta ce,

“Duk yau ba ka kira ni ba fa, a whatsapp offline ka ke.”

Haƙuri ya ba ta, sannan suka ci gaba da hira, har aka je inda za a sauke Maryam ba tare da ta sani ba, sai da mai Napep ɗin ya ce, “Hajiya mun zo.”

Sannan ta fito ta sallame shi.

Batun Khamis ya manta da Maryam a zahiri zai iya zama gaskiya, domin a lokutan da yake gida bai cika kiranta ba.

Ya yi haka ne domin Aisha ta cigaba da samun farinciki a tare da shi, saboda ya lura da wata irin nutsuwa da ta samu, wadda ko shakka babu don Maryam bata nan, to gudun gurɓata mata wannan nutsuwar ne ya ke ba ta dukkan kulawar da ta dace.

Ita ma Aishar tunda ta ga yana damuwa da ita, sai ta kara ƙaimi wurin faranta moshi. Sannan yadda take ganin yana sonta dole ita ma ta so shi.

Lura da hakan ne ya ba Khamis damar ce mata,

“Sholya wallahi kamar ba ke ba, na lura a ‘yan kwanakinan ba ki da damuwa ko kaɗan.”

Ce mishi ta yi,

“Ai in dai gidan nan zamu zauna a gidan nan daga ni sai kai sai kuma yaranmu, to ba zan yi damuwa ba, amma idan ina ganin wulgin wata, to wani irin kishi ke hana ni saƙat a zuciya.”

Kai ya jinjina tare da dariya ya ce, “Kishinki yayi yawa.”

Dariya kawai ta yi, don ita kaɗai ta san irin yadda ganin Maryam a gidan yake ƙona mata zuciya.

Maganganu masu sanya farinciki ya shiga faɗa ma Aisha, cewa ya yi,

“Ni ban ga abin damuwa don kina ganin wulgin wata a gidannan ba. Kada fa ki manta ke na fara so, ke na fara aurowa, kin ga duk wata da za ta zo sai dai ta biyo bayanki fa, don haka ki sani ke ce number one a zuciyata.”

Sosai Aisha ta ji daɗi, har ta riƙa tunanin lallai Khamis ya fi sonta, sai dai ko idan asiri ne Maryam ta yi, wanda idan tana gidan zai riƙa ganin gazawarta.

Fitarsa ke da wuya ita ma Maryam ya aje mata nata maganganun masu ɗauke da kewarta a text message, inda ya ce,

“Ina ta kewar hasken idaniyata, na zaƙu two weeks su cika na zo na raɓi jikin ki.”

Haka fa lamarin Namiji ya ke, in dai yana da mace fiye da ɗaya, to Allah ya bashi hikimar da zai tsara kowacce, har ta ji babu tauraruwar da ta kai ta haske a wurinsa. Amma sanin haƙiƙanin wadda ya fi so sai Allah, sai kuma idan shi da kansa ya faɗa ko ya nuna, kuma hakan bai kamata ba domin yana haifar da rashin zaman lafiya.

Reply ɗin da Maryam ta yi mishi ne ya sa shi faɗin,

“Indai namiji ya iya bi da mata, to ba abin da ya kai tara su daɗi.” Domin kowacce za ta dage da faranta mishi.”

Hatta batun buɗe ɗakin Maryam ma tuni Aisha ta manta da shi, sai da ta ji batun Khamis na shirin tafiya Katsina sannan ta tuna, shi ma wani irin azarɓaɓi da ta ga yana yi ne ya sa ta faɗin,

‘Ko ‘yar Katsina ta murɗa kambunta na asiri ne?’

A ranta ta yi wannan magana, lokaci ɗaya kuma tana hangen Khamis a farfajiyar gidan yana waya.

Wayar Zuzee ta kira ta faɗa mata Maryam fa ta kusa dawowa, jibi ma Abban Haneef zai je Katsina ɗauko ta.

Zuzee ta ce,

“To yana tafiya ki kira ni, gara a rage ma Barno dawaki.”

Haka aka yi, ƙarfe taran safiya a gidan Aisha ta yi ma Zuzee,

Sai da Zuzee ta cika cikinta, sannan suka shiga aikin da suka yi niyya. Tsaf suka samu ɗakin Maryam, sai dai ‘yar kurar da ba a rasa ba, lokokin mirro suka fara jawowa, nan ba komai sai tarkacen kayan tsifar kai.

Wardarobe ɗinta suka buɗa tare da hargitsa kayan, a cewarsu za su maida. A nan ɗin ma ba abinda suka gani. Duban Zuzee da ke ta raba idanu a ɗakin Aisha ta yi, “Zuzee mu fita tunda ba mu samu komai ba.”

Ɗan shiru Zuzee ta yi tana nazari, daga bisani ta ce,

“Mun kuwa duba ƙarkashin gado?”

Aisha ta ce,

“A’a.”

Ƙarfin halin ɗage mata gado suka yi. Sallallami Zuzee ta shiga yi wanda har ya firgita Aisha. Tambayarta ta yi,

“Me ye Zuzee?”

“Riƙe mini katifar ki ga ikon Allah.”

Jikin Aisha na kyarma ta riƙe katifar, aikuwa sai ga ƙaho da katuwar laya ɗaure a jikinsa.

A tsorace Aisha ta saki katifar bayan Zuzee ta fito. Hannunta dafe da ƙirji ta ce “Na shiga uku, me ye wannan Zuzee?”

Hannunta na nuni da ƙahon ta ƙarashe maganar.

Zuzee ta ce,

“Miye fa idan ba asiri ba, ai na faɗa miki idan ba tashi tsaye ki ka yi ba sai yarinyar nan ta raba ki da duk wani farinciki naki.”

Sosai ta cusa tsoro da firgici a zuciyar Aisha.

Hankalin Aisha a tashe suka ɗan gyara ɗakin, sai dai ko rabin yadda suka taras da shi ba su gyara ba.

Yanzu kam Aisha ta yadda Maryam asiri take tunda ga hujja ta gani, abin da ya rage mata shi ne ɗaukar matakin kare kanta, wanda Zuzee ke ƙoƙarin ɗaura ta akai. Khamis kuwa ya daɗe da isa birnin Katsina, inda ya samu tarba ta musamman a wurin dangin Maryam.

A Hotel ya kama ɗakin da zai kwana, sai dai ya shirya wuninsa a gidansu Maryam, inda aka gyara mishi ɗakin ɗaya daga cikin matasan gidan.

Burin Khamis shi ne kawai ya keɓe da matarsa, ai kuwa Maryam na shigowa kawo mishi abinci ya jawo ta jikinsa, Rumgume ta ya yi a ƙirjinsa, kusan a tare suka lumshe idanu suna jin wata irin kewar junansu.

<< Kishiyar Katsina 8Kishiyar Katsina 10 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×