"Ai fa dole kaya su dinga koɗewa, haba ace sawa ɗaya sai an wanke kaya, su kaya ba wani na azo a gani ba". Inna da ta fito daga ɗaki riƙe da ɗan likidiri ta ce da Muktar wanda ke ta faman cuɗa kaya, ɗagowa ya yi yana murmushi daga sunkuyen wankin, "ai Inna kayan ne sam ba sa mun daɗi in nasu su da ɗauka ko yaya maiƙon jikina ya taɓa kayan na fiso kan in kuma sawa in wanke".
Murmushi inna ta yi, "ai iyawa ne ba kai ba, in ka dawo. . .