Skip to content
Part 36 of 53 in the Series Ko Da So by Fadimafayau

Zaune suke a carpet ɗin ɗakin Khulsum na rubutu, Aiman nata tsalle tsalle tsakanin Khulsul da gado, inda Hafsa ke gefe tana addu’a idar da Sallar ta kenan Abdallah na da Faruk na kan kujerar madubi, idar da addu’a ɗin da ta yi ne ta miƙe tana ninke sallayar da ta yi sallar akai duban su ta yi duk sun yi wani jugun jugun kamar waɗanda ke a gidan mutuwa, “ina buƙatar sawa kaina jarumta da haƙuri ko dan yaran nan” abinda ta ce da kanta kenan afim tace “Yaya zaman me kuke anan?”

Kallon ta Faruk ya yi kafin ya ce ” ba komai Mami”

Girgiza kai Hafsa ta yi ” a’a da komai in muka zo gidan nan dama wuri na keke zuwa ku takure?”

Wannan karan Abdallah ne ya yi magana ” yanzu ai ba zuwa mukai ba, dawowa mukai”

Dan ɗaga gira tayi tare da furzar da iska kaɗan ” dan kun dawo sai aka ce ku takure, kumma ci abinci kuwa?”

Aiman ne ya miƙe “Mami bamu ci ba tun ɗazu nake cewa suzo muje muci sunƙi” hijabin jikinta ta aje jikin alharga kafin ta ce “kuje ku ci abincin ku nima ina buƙatar privacy,” ba wanda ya ce wani abu suka miƙe sukai falon ta bisu da ido tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya.

A falon suka zauna inda Faruk yaje dining area ɗin ya zuzzubo musu ya dawo falon, Abdallah ne ya miƙe ya nufi in da Faruk ɗin ya baro, “nafa zuboma ina kuma zaka?” Faruk ya faɗa da ɗan karfi.

Juyowa Abdallah ya yi ” Mami zan zubawa tun safe banga ta ci komai ba” Faruk bai ce komai ba ya miƙawa Kulsum da Aiman na su, suna ci Mum ta shigo da alamu daga unguwa take Faruk da Kulsum ne suka mata sannu da zuwa inda Aiman ya miƙe Mum mai kika siyo mata ” hararar sa ta yi in ubanka ya ban ajiya ai sai in sayo ma” taja tsaki ta wuce ɗaki yadda take jin Haushin Muktar haka ma yaran.

A kwance Abdallah ya tarar da Hafsa hannun ta bisa fuskar ta da alamu tunani take, kamar yadda ɗabi’ar su take da Sallama ya isa, a hankali ta amsa tare da janje hannun nata bisa fuskar tata, yunƙurawa ta yi taɗan gyara zama, ahankali tace “a’a Abdallah bana ce kuje ku ci abinci ba eyyi?”

Kwanon da yake ɗauke dashi ya ajiye gefen ta “yanzu zanje inci kema kici wannan”

Buɗewa ta yi ta kalla sannan ta mayar ta rufe ” tom shikenan zanci, kaje ka ci naka”

“Tom zanje inci anma dan Allah Mami ki tashi kici ko yaya ne, tun jiya ina kula ba abinda kika ci, in kin bari yunwa ta illata ki mu zaki sa wani hali, ki barmu muji da korar Abie dan Allah” kallon yaron ta yi itakam da ba ita ta haifi Abdallah ba sai tace yayi shekaru talatin dudu yanzu zai shiga 13yrs baima kusa shiga ba.

“Tom shikenan naji zanci, tashi kaje kar naka ya huce” maimakon ya tashi buɗewq ya yi da zummar ɗebowa ya bata cikin fushi ta ce ka tashi “ka tafi nace zanci a’a”

Narai narai ya yi da ido, ya miƙe jiki ba kwari ya yi bakin ƙofa, tausayin yaron ne ya kamata ko mai ta tuna cikin sanyin murya tace “Abdallah ” juyowa ya yi fuskar nan ta yi abin tausayi, buɗe abincin ta yi tare da ɗiba ta kai baki ” ka gani zanci, ko banci da yawa ba, karka damu kaji” gyaɗa kai ya yi tace ” yawwa to maza kane kuci naku”

Falon ya wuce yadda yaga aiman yayi jigum yasan da wani abu duban yaron ya yi ” Aiman menene mai yasa baka cin abincin?”

Narai narai Aiman ya yi da idanu cikin muryar ɓacin rai irin ta yara yace “ba Mun bace ta zageni, kuma ba abinda na mata” shiru Abdallah ya yi kafin ya ce ” bakai ta zaga ba, ranta ne a ɓace” murmushi Aiman ya yi ” Au” sai kuma yasa dariya ya koma cin abincin sa.

*****

Zaune Bilkisu take ta rafka uban tagumi, tun ɗazu baccin ya kasa ɗaukan ta, ranta a cinkushe yaje, haushi da takaicin maza duk ya cika ta, kallon Tariq da ke kwance gefen ta yana bacci ta yi, ta kuma jin wani ƙululun takaici, haannu da yakai gefen ta yaji alamun bata nan ya sa shi miƙewa.

“Habibty lafiya mai ke damun ki?” Ya faɗa a rikice lokacin da ya tashi zaune a rikice banza ta masa tare da hararsa , rikicewa ya kuma tare da jawo ta jikin sa “haba habibty, mai na miki?, koma mene dan Allah kiyi haƙuri ki faɗa mun wallahi ba da sani nayi ba, kinji tawan” takaici ne ya kuma rife ta lokacin da ranta ke faɗa mata yanzu fa duk wannan abin zai iya mata abinda Muktar yama Hafsa.

A hankali ya matso ya kuma sata jikin sa, dan Allah Allah tawan kiyi haƙuri, kinji karki sa zuciyata yanzu ta buga, kinsan ko yaya damuwar ki take tawa nunkuwa take, abin mata da miji sai kuma jikin ta yayi sanyi duk taji tausayin mijin nata ya kama ta, murumushi ta yi ” No bakai bane kawai raina ne ba daɗi” kamo hannun ta ya yi tare da yin ajiyar zuciya, na ɗauka nine though damuwar ki ko bani bane sila matsala ce tashi muyi salla ki faɗawa Allah ko mainene mu roƙeshi ya sauƙaƙa,” numfashi mai nauyi ta aje haka ne komai girman matsala akwai Allah sam ɓacin rai yaso yasa ta manta da hakan.

A hankali suka sauko daga gadon zuwa toilet sukayo alwala tare da dawowa falon, shine ya shinfiɗa musu sallayar ya ɗauko mata hijabin ta a inda take ajewa ta sanya, cikin sujjadar ta roƙom ta shine Allah ya sauƙaƙawa aminiyar tata, ya ganar da Muktar ya mayar da ita, in ba mai ganewa bane kuma Allah ya cire ma Hafsa son sa.

Koda suka idar ma duka Addu’oin da a dai ɗaya ne, nemawa Hafsa Mafita. A wurin bacci ya ɗauketa Tariq ya shafa addu’a tare da zare mata hijabin ya ninke, a hankali ta ɗauki filo ya ɗaga kanta ya aje mata.

Ɗakin yaran su ya leƙa kamar yadda ɗabi’ar sa take indai ya farka sai ya duba su, ganin suna lafiya ya dawo bed room ɗin su gefen Bilkisu yaja ya kwanta.

Washe gari bayan ya dawo daga masallaci ya tarar ta yi sallah ta koma bacci murmushi ya yi tare da gyara mata zanin rufar sanyin asuba da ke ɗan kaɗawa yasa ya kuma rage air conditioner ɗin ɗakin kafin ya yi waje kai tsaye kitchen ya wuce ya hau tiri tirin haɗa musu abincin kari, walida Babbar ɗiyar su ce ta shigo, “Good morning Dad” murmushi ya yi ” Good morning sweetheart”

Matsowa ta yi ” Dad kaje ka taso Ummi, zan ƙarasa” murmushi ya yi ” kun gana Tilawar ne?”
Gyaɗa kai ta yi ” eh mun gama harma Jawahir ta koma bacci”

“Yayi kyau kema kije ki huta, nama gama ai” ya faɗa yana juye kwan dake cikin kwano cikin kaskon suya, murmushi kawai yarinyar ta yi ta fice daga kitchen ɗin.

Ganin yana fito da kayan yasa yaran zuwa suka amsa, miƙa musu yayi tare da yin bed room din su, tana kwance tana baccin ta alamun jiya bawani isasshen bacci ta yi ba, har ya sunkuya zai tashe ta sai kuma ya fasa sabida tunanin da yazo ransa na kar kanta ya yi ciwo, juyawa kawai ya yi ya koma falon.

Walida ce ta yi serving ɗin su, suna ci suna hira sai dariya suke yadda yake hira da su tamkar da wasu sa’oin sa yake, sun kusa gamawa ta fito hangar su da ta yi, da kuma ƙarasowa kusa yasa taɗan tsuke fuska tare da faɗin ” eyye abinma ƴar son kai ce da wariya, wato kaida taran ka in kun ƙoshi ni ko oho ko”

Dariya ya yi tare da miƙewa yayo inda take ” Habadai mu mun isa mu ce haka in kina so yanzu sai adawo da cin abincin farko, ai girmam ki ne” dariya ta yi ” ah to gaskiya adawo da shi in ana so in yadda”

Jawahir ce ta miƙe tare da jan kujerar da Bilkisun ke zama ” Hajiya Ummi ta fito cin abinci zai dawo farko,” ta faɗa tare da yin alamun Bilkisun ta zauna, suka sa dariya duka.

*****

Yauma kamar kullum tun tafiyar Hafsa gidan ya zame masa tamkar kufai, rasa mai yake masa daɗi yayi, tayin da daren ya zame masa tamkar awanni dubu, sam bacci ya gaza ɗaukan idanun sa yayin da jiri da rashin karfin jiki yasa shi kasa yin sallar da ya yi niyar yi, a zaune ya yi nafilar rasa ma mai zai roƙa yayi, sassauci kan son Hafsa ko kuma sassauci bisa damuwar da ke damun sa, samun kansa ya yi da roƙawa Hafsan Haƙuri da juriya bisa rashin sa.

Bayan ya dawo daga Masallaci ya yi sa’a bacci mai nauyi ya ɗauke shi bai farka ba sai wurin goma, wanka ya shiga bayan ya fito ne ya haɗa ruwan zafi wanda yaji madara ko bread bai haɗa da shi ba ya kurɓe, kasancewar cikin sa ya naɗe yasa yana gama sha amar ya tawo masa, ya yi toilet da gudu.

Sai da ya wanke bakin sa sannan ya dawo ya yaɗa black tea ya sha kaɗan, can doguwar kujera ya koma ya kwanta, gizon da hayaniyar yaransu da kuma Hafsa a jikin sa ke masa yasa ya miƙe, dinning ya nufa ya ɗauki makullin motarsa tare da barin gidan.

Kamar wada tunanin sa ya guje, kawai ganin sa ya yi a ƙofar gidan su Hafsan yana horn, mai gadi da ya buɗe yagan shi ne ya washe baki “aa Alhaji Muktar kaine” wannan da mai gadi ya faɗa ne ya dawo da shi hayyacin sa a nutse suka gaisa kafin yace “Please kayi haƙuri na fasa shiga I will come back later” ya faɗa yana ƙoƙarin juya motar Mai gadi kawai ya bishi da ido cike da mamaki, shidai Muktar ɗin da ya sani baya shaye shaye bare yace wani abin yasha ya kasa gane ina zashi, taɓe baki yayi tare da gyaɗa kai lafin ya mayar da ƙofar ya rufe.

Jan motar Muktar ya yi da gudu ya bar wurin sai da ya yi nisa sannan ya faka bakin titi tare da dukan goshin sa…

<< Ko Da So 35Ko da so 37 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×