Skip to content
Part 45 of 53 in the Series Ko Da So by Fadimafayau

“Ni na rasa wannan rayuwa, ka saki mace kuma kazo ka zauna kamar maraya.” Inna ta sake yin mita tana kallon yadda Mukhtar din duk ya bi ya susuce saboda rashin nutsuwar zuciya. Tun sanda ya fada mata abunda ya faru ta soma saka shi a addua saboda tasan girman son da ke tsakanin su sai dai ita ma ta sani aure yana iya rabuwa ko da so. Sosai Mukhtar din yake bata tausayi saboda yadda ya koma.

Shirun da yayi yasa ta tabe baki sannan ta zauna kan kujerar dake falon kafin tace. “In har kasan ba zaka iya sanya abunda ya faru tsakanin ku a bayan ranka na ka mayar da ita,toh ka gaggauta neman wata don kuwa in ka cigaba a haka, ba zaka ganu ba.”

Sai da ya danyi jim sannan ya murmusa. “Inna bani da ra’ayin zaman aure yanzu. Da ko wacce mace ma.”

Karar wayarsa ne ya hana Inna magana. Ya zaro wayar ya zuba mata ido kamar ba zai dauka ba sai ya tashi ya fita sannan ya dauki call din.

Cikin sanyin muryarta me dadi tayi sallama gami da cewa, “Babu secretary na kwarai da zai ji dadin aikin sa idon Ogan sa yana cikin wani hali. Please Sir, be back.”

Kamar ba zai ce komai ba sai ya dan bata rai saboda yadda zancen nata ya bashi mamaki. Sarah da banda gaisuwa babu abunda yake hada shi da ita a office din yau ita ce ta kira shi? Ya share abun a ransa sannan ya mata sallama.

Komawarsa ciki ya hadu da Hajara da ta fito daga wanka. “Yauwa Yaya dama ina ta neman ka!”

Ya harareta sannan suka shige ciki.

*****

Abdallah ne da kannensa zaune suna cin abinci, sai cin abincin suke kamar an musu dole. Kulthum ce ta fara zare hannunta sannan Ayman ma ya cire yana kallon su.

“Ni gaskiya mami tazo mu koma gun Abiy, abincin gidan Abiy yafi dadi.” Ayman din ya fadi da dukkan gaskiyarsa.

Maimakon Kulthum ta doke shi yadda ta saba sai itama tace, “kuma we eat chicken on weekends amma anan babu sai dai a plate din mummy..” ita bata fuskarta tayi tana nuna bacin ranta.

Abdallah yayi shiru yana sauararen su zuciyarsa tana wani irin ciwon rashin ganin iyayensa a tare. Abun ya dameshi sosai don ko murmushi sai ya debi kwanaki yake yi. Gashi ita Mami ma bata damu ba har ma ta fara kula wani Dr Karaye. Ya tsani mutumin haka kawai. Don me Mami zata dinga dariya dashi.

Abiy ma babu ruwanshi dasu. Baya zuwa. Baya kiransu. Mummy kuma kullum fada take yi musu tana cewa babansu bai damu da su ba. Tunanin ya saka ya mike daga wajen. Da sanda ya shiga dakin Mami ya zaro wayarta sannan yayi typing number Abiy dinsu.

Sai da yayi masa miss call hudu sannan ya dauka a kira na biyar.

Kafin Abdallah yayi magana har ya soma. “Hafsah na gaya miki bana son kara ganin kiran…” Bai karasa ba, Abdallah yaji kamar ya kashe wayar. Da kyar ya kwato numfashinsa ya tattara shi waje daya sannan yace.

“Abiy nine. Ina wuni.”

Shiru ne ya ratsa na dan lokaci kafin Mukhtar din ya amsa.

“Abdallah, kuna lafiya?”

“You forgot us Abiy.” Wannan karan ma rasa abun cewa Mukhtar din yayi saboda wata irin kunyar yaron da ta kama shi. Ya sani shi me lefi ne saboda bai taba yunkurin zuwa wajen su, Hafsah ta hana ba. Bai yi amfani da shawarar Rashida ba ma na zuwa makarantar su ba. Ba shi da wata amsa da zai kare kansa da ita.

Yana cikin wannan halin ne Abdallah ya sake magana.

“Mami ma tana da friend. Mu kadai ne yanzu. We are so lonely Abiy. Kai ma kayi friend din ne?”

Wani irin abu ne ya soki zuciyar Mukhtar. Ba sai ya tsaya tunani akai ba ya san tsananin kishi ne ya baibaiye zuciyarsa. Taya ma Hafsah zata so wani? Bata ganin shi ya kasa moving on? Bata gani shi ba zai iya bawa wata zuciyarsa ba? Amma ita har ta bawa wani dama? Ashe dama son karya take masa?

“You’re not alone Abdullah. Zan zo school dinku gobe.” Da kyar ya bashi amsa.

“Bama zuwa school yanzu. Mum sai randa ka aiko da driver maje.”

Tsabar baqin ciki da takaici Mukhtar bai san sanda wayar ta sulale daga hannunsa ba. Innalillahi wa inna ilaihi raji’un. Ya akayi ya bari differences din da ke tsakanin sa da matar sa ya shafi yaransa? Ya akayi ya manta da batunsu na makaranta, shan su, tufafin su da ko wanni responsibility dinsu dake kansa? Ya akayi ya aikata abun da sai dai yaji labari yana faruwa a gari? Sam bai taba tunanin yana cutar da yaran ba sai yau. Bai taba tunanin babbar kwabar da yayi ba kuma iyayen Hafsah suka zuba masa ido ba sai yau. Yanzu da wani ido zai dube su?

Nan take wani irin zazzabi ya rufe shi. A ranshi yake ayyanawa wannan abun ya zo karshe. Ba zai iya ba. Ya gaji.

Ya gaji sosai.

*****

Yamma ce, rana tayi sanyi sosai. Iska me dadi tana ta kadawa. Hafsah tana zaune a garden din tana waya da Dr Karaye sai murmushi take tayi. Da kyar suka yi sallama saboda fitar da yace mata zaiyi. Tana ajiye wayar sai ga Faruk nan ya iso gareta.

Shima zama yayi akan patio din garden din ya kura mata ido sannan yace,

“Mami you look happy.”

Tayi murmushi gami da kamo hannunsa.

“Zuciyata a nutse take Faruk.”

“Mami are you gonna marry him?” Hafsah sai da taji gaban ta ya fadi. Da kyar ta boye shock dinta a gaban yaron. Bata taba tunanin suna sane da ita har haka ba kuma zasu fahimci halin da ake ciki.

Faruk ya kura mata ido sosai. “Yafi Abiy? In kika koma wurin shi mu wajen wa zamu je?”

Ganin babu yadda zatayi tace, “if by any chance zan bishi, daku zan tafi.”

Da sauri Faruk yace, “but he isn’t our Dad.”

Hafsah bata son sanda ta doke bakin Faruk ba sannan cikin fada ta cigaba, “wacce irin magana ce wannan Faruk? Duk irin gifts din da yake kawo muku ba kwa appreciating? Isn’t that a sign that yana sonku? Meye wannan shirmen? This is not part of my training, Faruk.”

“I am sorry Mami. I just prefer Abiy. Don Allah ki zo mu koma gidanmu. We love it better there.”

Hawaye suka taru a idon Hafsah. Abunda ta dade bata ji ba ya taso mata. Ta rungume Faruk din, hawaye suna zuba a idonta a hankali. Da kyar ta tsayar dasu sannan ta goge ta juyo dashi tace.

“Destiny, Faruk. Ka cigaba da addu’a kaji?” Ta kama hannunsa suka shiga gidan.

Yaran nata ta kira suka zauna suna ta hira inda take kula da Abdallah da Kulthum kamar sun takura.

“Hey Abdallahn Mami, me ya same ka?” Ya girgiza kan shi tare da yi mata karamin murmushi. Kafin ta kara cewa komai ma ya tashi ya bar mata dakin.

“Kulthum dear…”

Ta bude mata hannayenta sai dai yarinyar zuba mata ido kawai tayi tace,

“Mami mu koma gida.” Faruk ya kalli Hafsah da take kallonsa da tuhuma. Ya daga hannunsa in defense alamun ba shi ya zuga kannen nasa ba.

Ayman ne kadai ya koma kan cinyarta yace,

“Mami i miss Anty Becky. Zamu school gobe?”

A daidai lokacin ne Hafsah taji wani irin abu ya dake ta. Ta tuna haushin mahaifinsu ya sanya ta kasa samun Abba da batun driver ɗin. Ganin yadda yaran suka chanja yasa taji wani irin kadaici ya ziyarce ta.

“Zakuje school Ayman.” Ta bashi amsa. Shi kuwa a guje ya tashi ya tafi sanar da yayyinsa za su koma school.

Ta dade tana nadamar abunda ta aikata wa yaran. Ta dade gulit yana cinta. Don me zata bar lefin ubansu ya shafe su a matsayin ta na uwa? Ta share hawayenta.

Wayar ta ta soma ringing. Da kyar ta duba ID din. Gabanta sai da ya fadi da taga me kiran nata.

<< Ko Da So 44Ko Da So 46 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×