Skip to content
Part 46 of 53 in the Series Ko Da So by Fadimafayau

Kallon wayar ta kuma yi a karo na biyu ganin sunan Tariq na yawo kan wayar yasa gaban ta kuma faɗuwa kallon agogo ta yi goma saura na dare wani tunani ne ya faɗo mata, wataƙil yana ɗaki Rauda ta ɗauki wayar wannan yasa bata ɗaga ba kiran Tariq na katsewa na Dr ya shigo murmushi ta yi sai dai shigowar Abdallah yasa kan ta ɗaga ta nuna masa gefen gadon alamun ya zauna kafin ta ɗaga.

Da sallama ta ɗaga wayar amsawa ya yi tare da faɗin “sarauniyar birnin zuciyata mun wuni lafiya?,” murmushi ta yi “lafiya ƙalau Alhamdulillah” ta faɗa ya yaran namu?” Ya tambaya.

Suna lafiya kaga ma Abdallah sarkin binbini ku gaisa ta faɗa tare da miƙawa Abdallah ɗin wayar ba tare da ta jira mai ko wannen su zai ce ba.

Rai a cunkushe Abdallah ya amsa, Ina wuni ya faɗa, Ba yabo ba fallasa Dr ya amsa da lafiya ƙalau daga haka ba wanda ya kuma magana cikin su Abdallah ya miƙa mata wayar Mami gashi zan dawo, amsar wayar ta yi ta kara a kunnen ta idanun ta kan yaron har ya fice.

Bin wayar Tariq yake da kallo yana son ya kuma kira amma yana tsoron ko bacci take kar ya tashe ta, lokaci guda zuciyar sa ta mai da shi baya lokacin da ya fara ganin Hafsa shrkaru wurin sha takwas zuwa sha tara da suka wuce zuwan sa na biyu wurin Bilkisu da ta haɗa su a waya video call, so yake ya gano a lokacin maine ya ja shi ya faɗa sonta yadai san love at first sight ne, kamar wancan dai lokacin yakasa gane murmushin ta ko muryar ta ce ta sa shi kamuwa da son ta.

Ada ya danne dan farin cikin kowanne su yanzu kam shi ba zai iya rasa Hafsa ba, yana son Bilkisu sosai sedai yana son Hafsa lokaci ɗaya yaji zai iya rayuwa da Bilkisu matsayin mata, sai dai sonta ya ginu ne a sannu bayan da shaƙuwa faru tsakanin su, anma Hafsa lokaci ɗaya cikin daƙiƙu ya kamu da sonta, yabar abin a matsayin shaiɗan ne keson sakashi yin aikin dana sani anma yanzu da auren Hafsa ya mutu ya yarda daga Allah ne.

A hankali ya tashi zuwa ɗakin Baccin su, Bilkisu na zaune tana maka script ɗin Student ɗin ta, “har ka shigo ta ce?”

Murmushi ya yi tunda kinƙi zuwa ki tayani hira na ce bari in shigo idanuna su ganki ko naji sauƙin kewa.

Murmushi ta yi “ah gani na yi kana fama da shauƙin so gwanda in dunga baka time kana tunanin sabuwar soyayyar ka,”

Hmm aransa ya ce Bilkisu kenan da kinsan yadda soyayyar nan ta jima a raina da baki ce zaki ban lokacin tunanin ta ba, a zahiri kuma ya ce kamar kuwa kin sani na ma rasa yadda zan faɗa mata, ɗazu na samu kwarin gwiwar kiranta. Gaban Bilkisu ne ya faɗi tabbas maza sai addu’a wato duk yadda suke da Hafsa tamkar uwa ɗaya uba ɗaya anma mijin ta da yafi kowa sanin haka ke iƙirarin neman auren ta, bata ƙarasa tunanin ba taji ya ce ” kinga na ma kirata bata ɗaga ba, ina tunanin ko ta yi tsammanin mistake ne ko zaki taimaka ki ban aron wayarki in kira ta nasan in ke ce tana gani zata ɗaga”

Takaici ne ya kama Bilkisu ji take kamar ta miƙe ta mammake shi, sam ta kasa magana dan kome zata furta a yanzu tas zata furta maras daɗi, sa’a zance ta taka ko kuma rashin sa’a ne muryar sa ta ji yana faɗin “bari ma kawai ina ganin maganar ba ta waya ba ta waya bace zanje gidan nasu gobe”

Miƙewa ya yi ki aje papers ɗin ki kwanta dare na yi kar gobe kanki ya yi ciwo, bari nima in watsa ruwa in fito.” Binsa kawai ta yi da ido ranta na mata suya.

Ba su jima suna waya ba yau dan sarkin jan hirar ransa a cinkushe yake tunda ta bashi Abdallah suka gaisa kishi ya cika shi, Allah ma ya sani ko tambayar ta ya yaran yana yine dan ita uwa ce zata ji daɗi ya nuna concern ɗin sa ga ƴaƴanta amma da ba abinda zai sa ya tambaye su, yadda yake jin haushin baban su na taɓa zama da Hafsan matsayin matar sa haka yake jin haushin su dan yanaganin rabon sune yasa tama auri uban nasu.

Suna yin sallama ya miƙe ya shige bathroom dan ɗauro alwala nafila ya hau yi Allah ya sassauta masa wannan kishin ji yadda yake jin zuciyar sa Tamkar ta tsage tare da bugawa da sauri abin ya bashi tsoro yasan yana son Hafsa da yaws ne shi yasa kishin sa kanta ya ninka ka koyaushe.

Ita kuwa Hafsa tana aje wayar Abdallah ta leƙa ta kirawa suka shigo tare kallon sa ta yi duk yaron ya zama wani iri, Allah ya sani tana jin tausayin su inta kalle haushin Muktar yafi ko yaushe nunkuwa a ranta domin bai dubi zurriyar su da halin da zasu shiga ba ya bi son ransa.

A hankali ta ce “ɗazu ka fita baka faɗan me ya kawo ka ba,” furzar da iska ya yaɗan yi “eh dama zuwa na yi in roƙe ƙi dan Allah Mami ki barmu this weekend muje gida gun Abie”

Cikin fushi da tunzura ta ce “ba zaku ba, mutumin da ya watsar da ku, ya nuna ku baku da wani mahimmanci a gunsa mai ne anfanin zuwa gunsa”

Kamo hannun ta Abdallah ya yi “eh Mami Abie ya watsar damu anma ba zai taɓa canja cewa shine baban mu ba, shi yasa nake ganin ko yini ne mudunga zuwa once in while gun sa muna yi, ko dan Ayman da Kursum”

“Tunda haka kuka ga ya fiye muku, baku san mutuncin kanku ba kuyi yadda kuka ga dama” ta faɗa tare da miƙewa ta bar ɗakin, yaron ya jima a zaune Allah ya sani shima yana jin haushin Abie anma ba yadda zasuyi shine baban su.

Yana fita ya tarar da ƴan uwan nasa har da yayan nasu Faruk sun bazowa ƙofar idanu yadda Faruk ɗin ya yi yasa Abdallah murmushi wataran shi kansa mantawa yake Faruk nefa babba, “Ta ce muje anma yini biyu, shima weekend” suka sa ihu duka.

Wa she gari kasancewar laraba ce Hafsa bata da lecture tunda ta tashi ta shirya su Aiman suka tafi ta koma ɗaki ta hau karatu ta taɓa na novel ta taɓa na makaranta wurin huɗu wayar ta buga kiran Dr ne, sam bata yi tsammanin zuwan sa ba, dan tasan yau ranar seminar ce a faculty of Agric.

Bayan sun gaisa ne take tambayar sa ya seminar an fito la’asar ko?,” Murmushi ya yi tamkar yana gaban ta “No yau babu shine na kasa zaman office din kin ganni ma a harabar gidan ku”

Duban agogo ta kuma yi biyar ma batai ba, batasan ta faɗa ya ji ba, sai jin sa ta yi yana faɗin “karki damu sai in jira ma takwas ta yi tunda kinfi don taɗin dare” dariya ta yi “No ka bani 4minute ganinan ai sema nafi ganin ka ido na ganin ido” bata jira mai zai ce ba ta sauko daga gadon duda a shirye take sai da ta kuma goga soson hoda a fuskar ta gyara hular ta kafin ta zari mayafin abayar da ke jikin ta ta yo falo.

Momi ta fara raga mata, tunda ta saki jiki take kula Dr. Wannan yasa ba yabo ba fallasa ta ce ta gaishe shi har da ta ɗauki lemo ta kai masa.

Yana tsaye kamar ko yaushe cikin manyan kaya ta fito hangar da ya yi riƙe da dadduma da tire ya sa shi takowa inda take ya amsa suks ƙarasa inda suke zama sai da ya shimfiɗa sannan suka kuma gaisawa.

Shi kuwa Tariq yau da ɗammarar zuwa ya samu Hafsa ya tashi wannan yasa uku ya dawo gida Bilkisu bata nan haka ma yaran shine ya haɗa musu abincin rana Sannan ya shirya tsaf dogayen rigunan da ya siyo rannan ya ɗebo yana shirin murɗa makulli a falon Bilkisu na ƙarasowa, sam baiji sanda ta faka motar ta ba, shaf ta manta yadda sukai jiya duban sa ta yi “towo ina kuma zuwa yamma lis haka,” tasan ba ɗabi’ar sa bace fita after ya dawo daga office. Murmushi ya yi “kin manta jiya nace zani gidan su Hafsa” ta ɓe baki ta yi annurin fuskantar ta ya ragu “au haka fa sai ka dawo ta faɗa tare da ratse shi ta shige ciki”

Bin ta ya yi ” yawwa kince rigunan in kai mata duka ko duk zasu mata”

“Eh kawai ta ce” ya dubi hannun sa tare da yin waje.

Hirar su suke gwanin ban birgewa kowa ya dube su zasu birge shi, tsayawar motar Tariq a ƙofar gidan ta yi dai dai da shigar motar da ke kai su Abdallah makaranta wannan yasa mai gadi bai kulle ba sai da Tariq ya shiga.

Aiman da Kursum na fitowa suka yo jikin Tariq suna Murna ga Abba ga Abba wannan ya dawo da hankalin Hafsa gun yadda take murmushi tana kallo wurin yasa Dr shaƙuwa zaton sa tsohon mijin Hafsan ne wato mahaifin su Aiman.

Sam Tariq bai kula da Hafsa da Dr ba wannan yasa shi cewa yaran Mamin ku na nan kuwa?.

Cikin zumuɗi Aiman ya nuno masa ita ga ta can ita da saurayin ta, Kallon gun dukan su sukai har su Abdallah inda mamaki ya cika su ta yanda Aiman ya san wani abu wai saurayi shikuwa Tariq ta shin hankali ne ya cika shi zuciyar sa ta hau harbawa da sauri…

<< Ko Da So 45Ko Da So 47 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.