Bayan sallar isha Abba yana zaune a falonsa sanye da tabarau yana duba takardun clearance din kayan su da zasu iso nan ba da jimawa ba, Sadiq ya shigo dauke da sallama. Sai da Abban ya amsa shi sannan ya nemi wajen zama ya danyi shiru.
Kallo daya Abban yayi masa yaga yana cikin damuwa. Yasan waye Sadiq yasan ba kasafai abu yake saka shi damuwa ba. Shine dan shi na biyu amma tamkar shine babban. Sadiq tun kafin ya kai haka yake da kamala da nutsuwa har ma fiye da mahaifin nasa. Haka kuma bayan Hafsah shi yafi shakuwa da mahaifin nasa kuma yake da interest akan ko wanne business da mahaifin nasa yake yi banda na makaranta. Yafi ganewa kasuwancin ma sama da boko duk da ya kammala jami’a da sakamako me kyau.
Maimakon ya nemi aiki sai kawai ya nemi a bashi jari ya fara juyawa.
Ganin haka ne ya saka Abban ya mika masa kula da harkar kasuwancin sa tunda tun yana secondary suke fita kasuwa tare. Babu yadda mahaifiyarsa bata yi ba akan zancen bin shi kasuwar saboda tafi so danta yayi karatu ya zama likita. Abun mamaki gashi dai ya karanci course din da take so amma baya practicing.
“Abba jiya an shigar mana shago amma alhamdulillah ba’a abunda aka dauka.” Ya sanar da mahaifin nasa don yau yana zuwa da safe ya lura da an taba wajen.
Nisawa Abban yayi sannan jijjiga kai alamar abun baiyi masa dadi ba sannan yace, “bakomai kar ka wani damu Sadiq. Nasan ba sakacin ka ne ya jawo ba. Tunda ma Allah yasa masu leqe ne ai alhamdulillah. Allah ya tsare gaba.”
“Ameen.” Sadiq ya amsa yana sauke ajiyar zuciya. Yasan Abban dama ba zai taba tuhumar sa ba amma kuma ganin a cikin gidan da kaf kannen Abban da suke manya shi Abban ya zaba ya bashi amanar shagon sa yasa yaji tamkar lefin daga gare shi ne. Shiru suka dan yi kamar ba wanda zai sake magana sai Abban ya mika masa takardun hannunsa.
“Ka adana mun su.” Da hannu biyu ya karba yana kara jin dadi a ransa don yasan Abba yayi hakan don ya sake karrama shi ya nuna mishi babu komai kar yasa damuwa a ransa.
Tashi Abban yayi ya duba dining table ko zai ga abincin sa an ajiye amma wayam. Da ido Sadiq ya bishi da kallo sannan yayi murmushi.
“Ai yau sarakan shirita ne a kitchen. Kar ma ka sa ran cin abinci nan da awa guda Abba.” Dariya suka yi a lokaci daya saboda kowa yasan da wa ake yi.
“A’a kar kayi wa auta ta sharri. Tashi ka tafi, sai da safe.” Da haka Sadiq ya tashi yana dariya sannan ya masa sallama cike da jin dadin yadda Abban nasu yake da saukin kai sosai.
Bayan minti sha biyar sai ga Mummy nan ta shigo da tray a hannunta. Kamar ko yaushe kamshin turaren ta me sanyaya zuciya ya cika falon. Fuskar nan tata a daure alamun ranta ya baci. Sallama tayi, Abba ya amsa sannan ta samu wuri ta zauna tana shan kunu.
Sai da taga Abban ba zaice komai ba sannan tayi tsaki. “Ni wallahi na gaji da shirmen yarinyar nan kai kuma ka dage sai an saka su aiki. Ka barni kawai na dauki me aiki da zata dinga taya su. Hafsah ba zata iya da hidimar nan ba. Kalli ace mai gidana guda sai kusan goma zai ci abincin dare?” Tayi tambayar cike da kissa da dabarar son ya barta ta dauki me aikin kamar yadda mata masu aji irinta suke yi ba wai su dinga saka yaransu aikin gidan ba. Kowa tana da mai aiki banda ita.
Murmusawa ya yi. Yasan daman inda zancen ya dosa. “A’a in dai Hafsah zata koyi aikin gida ko karfe daya aka bani abinci bani da damuwa. Maza miko min abincin yau a kasa zanci. Abunka da auta tayi wa babanta girki.”
Haushi yasa ko tanka shi batayi ba ta tashi ta dauko sannan ta zuba mishi. Fridge dinshi ta nufa ta dauko lemo da glass cup sannan ta kawo ta zuba mishi.
Ganin dai sam bai dauki zancen nata da muhimmanci ba yasa ta saki fuskarta kadan ta gyara zaman ta a gefen sa.
Tuwo tayi miyar agushi. Yana kallon miyar yaji wata dariya ta taho masa amma haka ya rike ta. Watarana sai labari. Agushin yayi hanya daban, ruwan miya ya ware sai alayyahu batso batso. Bismillah yayi yana fatan Allah sa kar cikin sa ya baci.
Sai da ya juya miyar ta dan hade yayi lomar farko. Babu lefi a baki amma a ido kam babu wanda tuwon zai bashi sha’awar ci.
“Kuma baki ji dadi ba.” Ya fada yana kai wata lomar a ransa yana tunanin irin halin Hafsah wadda kwata kwata bata dauko mamanta ba sam. Dama haka Allah yake abunshi.
“Hmmm.” Kawai tace ta yi murmushi ganin yana kallonta.
“Yau yan hirar basa nan an taba miki miji ko? Toh ba gashi ina cin abincin ba? Haba gimbiya ta ayi min hira mana.” Ya tsokane ta wanda yasa ta danyi dariya mai cike da raha da izza. Ko a gaban mijinta mace ce da take komai a lissafe.
“Toh yau dai sai ka gama cin abinci zan baka labari. Bari naje na dawo…” ta kalle shi fuskarta kawace da murmushi kafin ta mike tana yanga kamar sabuwar amarya. A hankali ta fice ta tafi dakinta.
*****
Zaune Hajarah take tana ta faman karanta littafin Hausan dake hannunta Mukhtar ya shigo. Sau uku yana sallama amma bata ji don tayi nisa a karatun ta. Sosai take jin dadin littafin Ummu Hani haka ma jarumar sosai ta burge ta.
Sai da ya harareta sannan yace, “sana’a ce?” Yana fusge littafin daga hannun ta. A razane ta dago ta kalle shi.
“Haba Yaya da ya yage kuma fa?” Ta turo baki.
“Sai ma na yaga naga me zaki iya yi.” Ya fada yana juyo bangon yaga ko meye a jiki.
Cikin littafin ya duba ya karanta layin farko ya tabe baki sannan ya mika mata.
“Wahalar da kai. Ina Inna?” Ya tambaya yana daga labule ita kuma Hajara tayi saurin ajiye littafin a gefenta don in ta cigaba da dubawa sanda yake mata magana tsaf zai yaga shi ba ruwansa da arowa tayi a wajen yar ajinsu wadda gwana ce wajen karanta littafan Hausa kuma tsabar samun wuri in ta siya littafi sai ka bata naira ashirin zata ara maka na kwana daya. Itama Hajara kudin motar zuwa makarantar ta rage tayi tafiyar kafa duk dan ta karanta wannan littafin da ake ta zancen sa.
“Taje gidan Kawu.” Girgiza kai yayi kawai yasan ba komai ne ya kai Inna gidan Kawun ba sai dan kawai ta fada masa cewa Mukhtar ya samu aiki. Ya san halinta sarai.
Wuri ya samu ya zauna ya danyi shiru yana tuno yadda wani mutumi yaci masa mutunci a wajen kafintan da yake tayawa aiki. Shi kenan in Allah yayi ka talaka kayi ta ganin wulakanci kala kala daga mutane daban daban kenan ya ayyana a ranshi.
“Yaya yanzu tafiya zakayi?”
Da farko bai fahimci me take nufi ba ma saboda yadda hankalinsa sam yana kan lissafin yadda zai inganta rayuwarsa da ta yan uwansa ne.
Kwana biyar sukayi suna zuwa orientation da handing over a makarantar wanda shi bai taba jin inda ake haka ba sai akan makarantar nan. Jiya kuma suka kammala zuwa. Zasu fara shiga aji ne in an koma hutun session wani satin.
“A’a Hajara, ba zan iya biyan kudin shago ba yanzu gaskiya. Jeka ka dawo zan dinga yi kawai ko bakomai ina ganin ku kuna saka ni farin ciki.” Amsar tasa tayi mata dadi sosai shiyasa tayi murmushi me sauti.
Kafin kowannen su yayi magana wani yaro ya fado cikin gidan ba ko sallama.
“Wai ana sallama da Hajara, inji Garba.” Ya fada. Ras gabanta ya fadi ta sunne kai kasa kar ma yayan ya kalleta su hada ido.
Ai kuwa da harara yake binta.
“Sai ki bashi amsa ai.” Ya fada cike da bada umarni wanda yasa jikinta ya fara rawa don ta san yau da kyar ne in bai dake ta ba. Ya sha yi mata gargadi akan kula samari tunda bata kammala sakandire ba amma bata ji. A boye take soyayyar ta yadda ba zai gane ba.
“Kace ba..ba… bata nan.” Ta amsawa yaron tana i’inar tsoro da fargaba.
Sai da yaron ya fita sannan Mukhtar ya kalle ta. “Na sha gaya miki kina da zabi. In kin zabi soyayya sama da karatun sai a miki auren ai na dena asarar kudina kamar yadda yayarki tayi.”
Girgiza kai tayi hawaye na zuba a idonta. “Wallahi na dena Yaya.” Ta bashi amsa tana tashi da sauri don tsoro da kunyar sa take ji. Da gaske tana son soyayya amma kuma tana kaunar karatun. Tana kallo yayarsu Bintu iya JSS tayi aka mata aure saboda shi take so. Yanzu Bintun kamar ma bata taba yin karatun ba. Sai aikin gida da yara. Ita bata son kalar rayuwar Bintu. So take tayi karatu me zurfi sannan tayi auren ko ta kammala sakandire sannan ta yi auren ta cigaba da karatun.
Burirrika gareta kuma Garba yace mata zatayi karatu a gidansa amma tana tsoron yayan ta. Kar ya zare hannun sa akan karatun.