Skip to content
Part 52 of 53 in the Series Ko Da So by Fadimafayau

Bari mu koma baya muji ya akai Mummy ta yadda akai auren Hafsa da Muktar, sannan wanne dalili ne yasa akai sakin aurenan mai cike da so da ƙauna.

Hafsah ta zata fushin mummy ba zai dore ba sai gashi kusan sati biyu kenan tun ranar da saka dokar hana Mukhtar zuwa gidan. A tsaitsaye Hafsah take rama saboda ko abinci bata iya ci ga kuka da tasaka a gaba tana tayi tsawon kwanakin nan.

A rana ta sha bakwai ne tana kwance, wani irin zazzabi ya rufe ta sai gata tana ta karkarwa. Shiru shiru bata fito ba ranar har dai mummy tayi zuciya ta je ganin dalilin kin fitowarta don har ma ta ci alwashin yau zai ta zane Hafsah a cikin gidan. Shigar ta dakin ta tsayea kallon yadda ya dada hargitsewa, wani tsaki ya kufce mata sannan ta kalli gefe ta dauki charger ta nufi gadon Hafsah.

Ganin Hafsah a sheme a gadon ne ya tabbatar mata da cewa ba bacci take ba. Nan take hankalinta ya tashi ta soma girgiza Hafsah wadda jikinta yayi zafi sosai. Sai dai me? Ta riga ta suma. A kidime mummy tayi waje har tana hardewa ta kira Abban yazo aka dauki Hafsah sai asibitin Nassarawa.

Abu kamar al’amara sai jikin Hafsah ya rikice har sai da aka basu gado. Ulcer ce tayi mata mugun riko hade da jininta da ya hau. Sai da suka yi kwana uku a asibitin sannan Hafsah ta fara samun kanta.

Zaune take da kwanon abinci a hannunta wanda sam baya mata dadi saboda halin da take ciki. Yawanci ma drip ake saka mata saboda rashin appetite din da take fama dashi.

Gefenta mummy da Abba ne zaune akan plastic chair. Kana ganin su kaga yadda suka damu da jinyar da take fama da ita. Idanu kawai Abba ya zuba mata yaga yadda ta zabge lokaci guda.

Gyara zaman sa yayi da nufin ya tambayi Hafsah mene matsalar har abun ya kai ga haka. Ya akayi sam beiji labarin rashin lafiya ba sai kawai suma?

“Abba, uncle Mukhtar bai zo ba? Baku gaya mishi ba?” Ta tambaya cike da rauni. A fusace mummy ta kalle ta sannan ta gyada kai tana satar kallon mahaifin nata wanda shi kuma yake duban Hafsah da idon tausayi.

Yasan ciwon so gaskiya ne.

Shima ya faru kansa. Abu ne da ba zai taba mantawa ba. Gashi tarihi ya maimaita kansa.

Ya tashi ya koma kusa da Hafsah sannan ya dafa kafadarta. “Zai zo. Zan kira shi… kar ki…” bai samu damar qarasawa ba saboda yadda mummy ta miqe a harzuke tana magana.

“Na rantse da Allah babu abunda zai sake hada ta da wancan yaran. Dama duk wannan abun jinyar son shi nayi?”

Hafsah ta fashe da kuka. “Mummy dan Allah kiyi hakuri. Wallahi dukkan numfashin da na ke shaqa tafe yake da son shi.”

Abba sai ya koma gefe yana mamakin Hafsah da wani irin murmushi mai tarin ma’anoni a kan fuskarsa.

“Wato shine oxygen dinki ko? Toh dan Allah karki fasa mutuwa saboda rashin sa. Na rasa me wannan talakan ya miki. Wani irin naaci ne wannan ba zai zauna da talaucin sa ba har sai ya janyo ki ciki?”

Kwankwasa kofar akayi hakan yasa tabi Hafsah da harara sannan taje ta bude kofa. Doctor da tayi admitting Hafsah ce tazo discharging dinta. Sai da ta gama yi musu bayanai sannan ta basu sallama. A hanya ma dai kuka Hafsah ta cigaba da yi, mummy kuma ta cigaba da fadan yar ta ba zata auri talaka ba ko da kuwa mutuwa zatayi.

Abba shiru yayi yana nazarin situation din har suka isa gida. Ganin fushin da mummy take ciki yasa da kanshi ya raka Hafsah har daki ya samu ta kwanta sannan ya zauna gefenta.

“It’s amusing to see you this way and at the same time pathetic. Hafsah, so guba ce. Kinsan dai guba In ta shiga jiki zagayawa take tayi illa. So, zuma ne. Dadinsa baya misaltuwa. Amma shawara daya da zan baki shine ya zamana akwai balance a soyayyarki. Ya zama mai nutsuwa ce. Ya zama da hankali aka gina ta. For a woman, son ki ga namiji ya tafi tare da kamun kai da jan aji. Wannan kalar? Bai dace da ke ba. Ki kwantar da hankalin ki tukunna…”

Magana ce wata iri don zata iya cewa bata fahimci abunda Abba yake cewa ba saboda amsar da ta bashi.

“Abba don Allah gobe zani school mu hadu…”

Murmushi ya sake yi sannan ya bar dakin ba tare da yace mata komai ba.

*****

“Mukhtar!” Inna ta sake maimaitawa da karfi gami da cillar da tsintsiyar hannunta. Sai da ta wanke hannun sanna mn ta zauna kusa dashi.

“Wallahi ba zan lamunta ba. Ka sanar dani gaskiyar abunda ke damunka.”

Mukhtar yayi shiru sannan yaja numfashi mai tsawo. “Inna ki sani a adduarki.” Da haka yayi sauri ya miqe ya saka silifas dinsa sannan ya fice daga gidan.

Hajara dake gaban kejin kajinta ta gama rufewa sannan tazo ta zauna akan tabarma kusa da inna sannan tace,

“Inna Yaya soyayya ya fara.”

Innar tayi murmushi. “Uwar gulma, ban tambaye ki ba. Banda abunshi meye na damuwa?”

Hajara ta tabe baki ta kuma cewa. “Yar me makarantar su ce fa.”

Gaban Inna sai ya fadi. Da kyar ta samu ta boye damuwar da ta taso mata. Lallai Mukhtar ya debo abun da zafi. Ba ta da ta cewa kuma. Haka ta mike ta koma bakin murhu tana neman dora abincin dare.

Gyara itacen takeyi amma bayan sakanni kadan sai kalmar “uhnm” ta subuce mata. Abun ba karami bane!

*****

“Na dade da sanin Hafsah is weird amma ban taba tunanin hauka ma yana damunta ba. Of all men wai ace wannan yaron da gaba da bayansa talauci ne, shi take so?”

Mummy ta furta tare da ajiye tray din da ta kawowa Abba fruits salad a gefen kafarsa. Murmushi ya yi wanda ya tunzurata ta kalle shi.

“Yau kam kamar harda kai aka a linke a kasan abun sallah. Sai wani murmushi kake tayi kamar baka fuskanci iftila’in da ya sauko mana ba.”

Ya jawo ta kusa yace, “Hadizata kenan.”

“Kina sauraro na?”

Ta gyada masa kai a ranta tana cewa babu yadda za’ayi ta yadda ya kallameta ko ya tilasta ta akan ta yarda da Mukhtar.

“Shi arziki da kika gani qayyadadden abu ne ga ko wanne bawa. A rubuce yake, kowa da arziki da zaici kafin ya mutu. Wani nasa me yalwa ne, wani nasa kadan ne, wani nasa me jinkiri ne, wani nasa me zuwa ya tafi ne. Wani ma sam ba’a rubuta masa cin arziki bane.”

Tayi shiru tana sauraron sa. Ya cigaba,

“Tunda kika ga haka ta faru toh Allah kadai yasan mene gaibu. Watakila arzikin Hafsah yazo karshe, watakila kuma hutun arzikin ta ne yazo. Ma’ana dai zata rayu dashi har zuwa sanda zai samu wadata me yawa. Ki fahimta, ko me kudi ta aura idan arzikin da aka yanka mata ya kare, sai ya talauce. Saboda a qaddararta yake.”

Cikin fushin da ta dauka mai tsanani ta soma bashi amsa.

“Eh naji wallahi gara ta auri me kudin daga baya ya talauce babu wanda zai sani sai ni da zan rufa mata asiri. Amma as a start, sam ban amince ba a dinga fada a gari yar Hadiza ta auri talaka. Sam! Na tsani talauci da babu.”

Duk yadda Abba yaso ta fahimce sam taqi fahimta ta dinga kaucewa misalan sa har sai da ta kaishi bango. So yake ayi maganar nan ta qare a yau domin shi ya yi na’am da Mukhtar. Haka kawai yaron yayi masa sannan tun kafin Hafsah ta nuna tana da ra’ayinsa yaga dacewarsu tun a karatun su na farko. Shi din zai tamaka masa ko dan yar sa tayi rayuwa me kyau.

“Kina nufin da ni talaka ne ba zaki aure ni ba, Hadiza?”

Ta tabe baki. “Kaima kasan dai aljihun namiji yana kara karbuwar sa wajen mace. Ina son ka sosai haka ma kudinka suka kara ja na. Kai ma ka sani babu wani boye boye.”

“Hadiza ki dinga tuna tushen komai idan zaki yanke hukunci.”

Labarin Hadiza (Mummyn Hafsah).

“Ni wallahi Goggo na gaji da cin fara da mai.” Ta fada tana tura farentin gefe sannan ta shige cikin daki tana cire uniform dinta. Yau sukayi candy duk farin cikin da take ciki ya tafi sakamakon abincin da tazo ta tarar a gidan.

“Hadizalo kenan.” Goggo ta fadi tana bin inuwarta da ido. Can ta fito ta zauna tana lissafa kudin da take sayar da awara da yanma a cikin gidan.

“Dubu goma ne cif. Dubu biyar zan biya kudin party da zamuyi sai kudin dinki.”

Goggo ta murmusa. “Dinkin me?”

“Kayan da zamu saka mana. Anko fa zamuyi. Banda kudin atamfar amma anjima idan Faruk yazo zan tuna mishi.” Ta fada ba kunya.

Goggon taji wani abu ya tsaya mata a rai. “Ki kama mutumcin ki Hadizalo. Duk wannan abun ba dole bane, in kika cinye jarin fa ya za’ayi kenan?”

“Goggo kenan. Ai wallahi don kawai wannan ranar na kama sana’ar ko dan na fita kunya. Ko wacce zatayi banda ni. Shiyasa ma har yau babu wadda tasan ina awara gashi har na tara abunda na tara.”

Goggo ta tashi ta nufi bakin famfo don tayi alwala tana yiwa Hadiza addu’ar shiriya.

Hadizan tabi tsakar gidan nasu da ido. Babu laifi gidan nasu sai dai kawai kalar abincin su ce take bata mata rai gashi babu wani abu na jindadin rayuwa.

Itama sallar ta tashi tayi sannan ta samu waje ta zauna tana karanta wasikar da Faruk ya bata jiya da zai tafi.

Murmushi ne yake yawo a fuskarta har sanda ta jiyo sallamar wani yaro a tsakar gida yana cewa ana sallama da ita. Kanwarta ce ta amsa tace waye?

“Wani mutum ne a mota.” Tana jin haka tayi sauri ta mike ta leko wajen.

“Kace tana zuwa.”

Wata alwalar ta sakeyi ta zumbula hijabi kannenta suna kallon ikon Allah. Da yake Malam bai shigo ba tukunna, Goggo kuma ta shiga bayan gida a lokacin.

“In kika fita kinci amanar yaya Faruk fa.” Inji daya cikin su. Sai da ta yi kasa da muryarta sannan tace. “Yanzu fa zan dawo.”
Daga saƙon ƙofa Hadiza ta ɓoye tare da zuro kanta kaɗan ta leƙo dan ganin me son ganin ta dan in bai mata ba ita kam ba abinda zai sa tama fito, matashin saurayi ta gani kusan sa’an Faruk ɗin ta ne sai dai wannan ruwan tarwaɗa ne bakamar Faruk da yake Fari tas ba, shima wannan dogo ne kyakkyawa ne shima tsaye tsaye yake jikin motar sa mai kyau wadda bata san sunan ta ba, sa’ai aikai shima ɗin idanun sa zube suke kan ƙofar fitowa daga gidan wannan ya basu sa’ar haɗa idanu inda ya sakar mata murmushi ta ko yi saurin komar da kanta ciki tare da riƙe ƙirji zuciyar ta na bugawa da sauri.
Ƙur ya ƙurawa ƙofar idanu fatan sa ta fito dan ya afu sosai ya ganta ɗan ɗora idanun sa da ya yi yanzu kanta yasa yaji yana son ganin nasa fiye da ada, tagi minti biyu tana tsaye kafin ta yi jarumtar fitowa, sosai ta masa kyau yauma ɗin tabbas dole ya ruɗe kan yarinyar nan da ya zata kallon tsoro ya mata ashe tafi yadda yake siffanta, ya Allah kasa rabona ce ya faɗa a hankali. A nitse ta ƙaraso tare da yin Sallama amsawar da ya yi ne yasa ta gaidashi, ya amsa yana murmushi kafin yace “kin ganni da yamma lis ko? Tun kwanaki nake tason zuwa wallahi to Alhajin mune ya aikeni sai yau na dawo ina kai masa aiken nayo nan” a hankali ta ɗago ta kalle shi ranta cike da mamakin yadda yake magana tamkar sun shekara da sanin juna. Kamar yasan mai take tunani ya ce ” Baki sanni ba ko tun kwanaki na ganki zaki tafi makaranta to ganin kina cikin uniform kar in makarar da ke yasa na tambayi inda kike sai yau Allah yasa nazo.
“Ikon Allah” kawai ta iya cewa ranta cike da tunane tunane tabbas wannan irin namijin da da take so ne gashi da alamu ɗan masu kuɗi ne koma mai kuɗin da kansa, ƙofar gidan su Faruk ta kalla ahankali idanunta suka faɗa kan shagon sa da ke manne ƙofar gidan tasan ba haufi in dai sukai aure dole anan zasu zauna tunda dai Faruk bashi ne dashi ba, sai dai tuna yadda sukai da Abban ta yasa ta saurin dawowa hankalin ta a nutse ta ce “azahirin gaskiya shine akwai wanda muke tare kuma ……” Marin da ya sauka kan kuncin tane yasa ta yin shiru tare da fashewa da kuka kafin ta kalli me marin Faruk ne da alamu wani marin yai niyar kwaɗa mata ganin hannun matashin saurayin riƙe da hannun Faruk ɗin cikin fushi Muhammad ya ce haba bawan Allah kome ta maka ai ka yi da fatar baki dukan mace ai ba’asan namijin kwarai da shi ba koda ƙanwar ka ce ta wuce duka yanzu.” Yarfar da Hannun Muhammad Faruk ya yi tare da juyowa ya harare shi kafin ya mayar da hankalin sa kan Hadiza cikin faɗa yake faɗin “shegiya mayaudariya wato kinga mota dole ki zo kina ta masa kwarkwasa to wallahi kisani waɗannan masu motar ba auren ki zakiyi ba, kyannan naki da kike gani shi kawai suke so da sun samu zasu watsar da ke mai auren ki sai mu ɗin talakawan” sai yanzu Muhammad ya gane inda aka dosa wannan shine wanda take ƙoƙarin yi masa bayani, kafin ya ce wani abu Hadiza ta yi cikin gida tana kuka riƙe da kuncin ta, ganin ta yi cikin gida yasa Faruk kufula yayo kan Muhammad da faɗa ganin haka yasa Muhammad shigewa motar sa yabar gun ran Faruk ya yi mugun ɓaci.

Hadiza na shiga gida da Abban su ta yi tozali Bama ta kula da sanda ya shiga gidan ba, tambayar ta ya hau yi mai faru cikin kuma take faɗa masa Faruk ne ya dake ta, a tunzure yake faɗin abin yaron nan ya fara isata, na faɗa masa ya dena dukar min yarinya yaƙi sai kace kansa aka fara soyayya to wallahi bazai yiwu ba ni ko aura maka yarinya nayi bazan laminci duka ba ballanta ko kuɗi baka kawo ba kawai maƙotaka nake dubawa” Gwaggo da ta fito daga ɗaki ne tace ai Malam dole ya dake ta duk abinda yake yarinyar nan bata gani se taje kula wani” cikin kuka Hadiza ta ce Allah zuwa na yi ince kar ya kuma zuwa shine Faruk ɗin ya zo” Numfashi Malam ya firzar “Hadizan wallahi na kuma samin labarin kin je kin kula wani sai naci mutincin ki” fuu ya bar gidan yayin da Hadiza ta shige ɗaki ranta fal tunanin matashin saurayin da yazo wanda ko sunan sa bata sani ba tare da tunanin yadda zata rayu da fushin ran Faruk tana sonsa dan son nema yasa ta danne son ta da kuɗi ta yadda zata aure shi.
Abban su Hadiza na fita gidan su Faruk ya nufa, aikawa ya yi a masa sallama da mahaifin Faruk ɗin, bakamar yadda suka saba ba sai wani huci mahaifin Faruk ɗin yake sun gaisa ba wani a nutse ba Abban su Hadiza ya hau bayani a nutse na son ajawa Faruk kunne ya dena dukan Hadiza, cikin kufula Abban Su Faruk ya hau faɗa ” mufa ba dole inma fasa auren nan za’ayi a fasa dan bazai yiwu tun kan yarinya ta shiga gidan sa afara kafa masa dokoki, shine namiji dole ya dake ta, indai har ba haka ba to Allah ya haɗa kowa da rabonsa” mamaki ne ya cika Abban Hadiza wai dole ya dake ta yake cewa, taɓ shi anya bama Allah ne ya taimake shi akai haka ba, dan kuwa bai haifi ƴar da wani ƙato zai dinga dukar masa ita ba da sunan aure kuma ya zuba ido” ya jima a tsaye inda Baban su Faruk ya barshi kafin ya bar gun bai shiga gida ba dan yasan ransa ne zai kuma ɓaci.

Tunda akai haka kullum cikin mita gwaggo take kan Malam yaje ya bada haƙuri tunda an doshi wata Faruk yaƙi zuwa har Hadiza tasa taje gida ta bashi haƙuri bata same shi ba, innar sa kuma ta ci mata mutunci, a kufule Malam ya ce ” wallahi bazan je in basu haƙuri na inda naso zan iya kaisu kotu tunda ɗiya ta ɗan su ya doka ba kuma wai na farko bane, in sun fasa ne ai bashi bane autan maza, zan ta mata addu’a har mijin ta yazo” bai jira amsar ta ba yayi waje abinsa.

Kamar kullum tun randa abin ya faru kullum sai ya zo anma kullum sakamako ɗaya ne Hadiza bata fitowa duk yabi ya faɗa dan kullum son yarinyar ruruwa yake aransa, ganin mahaifin Hadizan na fitowa yasa shi saurin ƙarasawa har ƙas ya rissina ya gaidashi, a mutunce suka gaisa mahaifin Hadizan ya ce ” kaine ka zo ka korar wa ɗiya ta miji ko?” A rude Muhammad ya ce wallahi Baba ba haka bane shine dai ya yiwa abin gurguwar fahinta tunda ni gaskiya kafin nazo gunta sai da na tabbatar da ba akawo kuɗin ta ba, duda nasan da zaman sa ganin da ba’ai wata magana ba yasa na yi tsanmanin inada damar gwada tawa sa’ar” girgiza kai mahaifin Hafiza ya yi alamun gamsuwa kafin yace “shikenan yanzu na amince ka dunga zuwa wurin ta ku fahinci juna na wata guda, daga nan in har kaji zaka iya auren ta itama ta amince to sai ka turo in kuma har lokacin baka iya tsaida ranka ba, to gaskiya karka kuma zuwa” daɗi ne ya cika Muhammad dan shi ko yanzu wallahi aka ce ya turo zai turo kawai dan bai sani ba ko zata so shi dan duk yadda yake son mace bai shirya auren ta ba in har bata son sa.

Wannan ranar itace mafarin fara soyayyarta da mahaifin Hafsah. Sosai ta fada kogin sansa.

Kusan babu ranar da Muhammad zaizo Faruk bai ci masa mutunci ba, anma shi ko a jikin sa dan Hadizan sa na sonsa yayin da unguwa ta ɗauka ai kuɗi suka gani shi yasa suka ƙi bawa Faruk.

Kamar yadda mahaifin Hadiza ya bashi wata guda kwana uku ya rage ta cika wannan yasa ya tunkari Hajiyar su da batun auren nasa dan yana son ta sami Alhajin su da maganar sai dai me ta inda ta hau batanan take sauka ba ita bata amince ba, bazai yiwu ba, ta masa mats yar Haulat ƴar gidan Ƙanwarta zai haura nan da nan gumi ya rufe shi dan shi kam duniya a matsayin mata ba zai iya zama da kowa ba in ba Hadizan sa ba.

Sam ya dena fita duk ya bi rame kamar wanda ya yi jinya. Hankalun Hadiza kuwa duk ya tashi ganin wata gudan ya cika Muhammad ya yi ɓatan dabo kardai ya canja shawara kar dai yaudarar ta yake da gaske kamar yadda Faruk ya faɗa.

Ganin yadda Faruk ya rame yasa Mahaifinsu zaunar dashi kan jin meke damun sa, ba tare da wani hanzari ba ya masa bayani a fusace ya nufi ɓangaren uwar gidan nasa.

Tana zaune tana kallo tana ganin sa ta saki fuska ya dakatar da ita ban ya hau sababi, cikin nutsuwa take masa bayani tun haihuwar Haulat ɗin ita da ƙanwar tata suka zaɓi haɗa zumunci salati ya saka “dama baku da hankali, yo ko kema ni na nemoki muka haɗa kanmu mukai auren mu bare kuma su yaran yanzu, jibi yadda kike son kashe ɗan ki da kanki, shin ita Haulat ɗin na son sa ne?.

Tsaki Hajiya ta yi “inafa itama haka ta yi ta bore wai da Nasir (ƙanin Muhammad) suke soyayya, kuma shine kuna sane kuke son ɓata rayuwar su, dama tana son sane se ince se ya aure su atare”

Kwafa Hajiya ta yi ai ni tunda naji Nasir take so ya kuma tabbatar min yana sonta, na janye batun auren nata da Muhammad, kawai dai yarinyar da yake so ce bata min ba, talakawa ne futun sannan Isma’il (ƙanin ta) ya tabbatar min da a binciken sa ya gano dan kudin sa take son sa bawai shi take so ba.

Tsaki Alhaji ya yi to sai me dan tanasan sa sabida kuɗi ai cikin abinda annabi Sallallahu alaihi Wasallama ya sa za’a iya aure dan shi harda kuɗi, shima kka bibiya kyau ta masa yabi kyan zai aura, Please Hajiya ki ƙyale yaran nan.

Anma fisabilillahi Alhaji zaka so matar ɗan ka bawai dan Allah take sonsa ba, murmushi ya yi ke kin shiga zuciyar ta kinga badan Allah din take ba, besides nifa bana ganin lefin wanda ya zaɓi kuɗi, ko ka zaɓi talaucin ƙarshe auren mutuwa yake musanman in ansamu wanda yarinya ta zaɓa talaka ne maras zuciya tunda yaƙi fita ya nemo, dole tana buƙatar taci, tana buƙatae tasa haka kuma baya yiyuwa sai an nemi kuɗi, kar in kuma ji kince wani abu kan batun yaron nan anjima zan samu Yaya Ummaru suje su nemo masa auren ta kar ki bari inji ko in gani.

Wata huɗu aka sanya auren Muhammad da Hadiza soyayta sai inda ta ƙaru, kai kace zasu lashe juna, wata huɗu cur aka kai lefe kwana hudu tsakanin aka ɗaura aure. Washe gari aka ɗauki amarya gidan su Muhammad aka fara kaita habaici kam ta shashi harsa masu faɗin sukam zasu so suga sanda asirin da ta yiwa Muhammad ɗin zai karye, da masu mamakin inda akai yaje yasamota musamman ganin gidan su, sun raina su sosai, tana jin wasu lokacin da ake fiddo da ita a zaure na faɗin gaskiya dai kam bahaushe ya yi gaskiya da yace matar mutun kabarin sa in ba haka ba ai mu ba’ar zama surukan gidan nan bane ranta ya ɓaci sosai kamar ta ɗago ta ce wani abu sai ta tuna ita ce fa amaryar.

A falon su ma dai habaice habaicen son kuɗin ne wata ce ta ce ai abin na bata mamaki yadda talakawa keda matsala suke kallon abinda yafi karfin su, wata can tace ki bari kawai ai talaka kwai son abin duniya.

Ɗaya daga cikin Antin Hadiza ce ta yi murmushi a nutse in da ta ce “yo baiwar Allah ai dole ɗan adam fa yaso kuɗi, tunda Allah da kansa yace jin daɗi ne na duniya, da talaka da mai kuɗi kowa nason jin daɗi, sannan talaka mai tunani shifa yake son kuɗi tunda har lokacin annabi Sallallahu alaihi Wasallama talakawa sun koka da yadda masu kuɗi suka tafi da lada, kinga ai dole kowa yaso kuɗi dan shima ya samu damar samun tagomashin da masu kuɗi ke samu”

Taɓe baki wadda ta yi maganar ta yi kan ta ce “ai sai mutun ya nemi nasa bawai ya dinga tunanin jingina jikin masu shi dan ya lasa ba” murmushi Antin Hadizan ta yi kan ta ce ” ai shi mai arziki ko kaɗan bai damuwa da me raɓar sa kullum ma so yake yaga an kusance shi dan yasan kyautawa wasu na nufin bunƙasar dukiyar sa” ganin abin zai koma gugar zana yasa Hajiyar Muhammad dakatar da abin ta yiwa Hadiza nasiha tasa musu albarka kafin a wuce da Hadiza gun Alhajin su Muhammad dan yi mata nasiha

Cigaba.

“Da kinsan gwagwarmayar da muka sha da Hajiya Babba da kinsha mamaki sai kuma gashi ta so ki kamar ba gobe. In da ta kafe akan bakarta na social difference dake tsakaninmu da tuni wani zancen ake, so Please Hadiza dan Allah ki bar yarin yar nan da zaɓin ta, ni san ni ta gada a wannan zafin son dan nasan yadda har yanzu nake jin ki araina.

Ta bude baki tayi mitar cewa gori zai yi mata ya mike tsaye sannan yace.

“Mukhtar zai auri Hafsah. Kuma da kanki nake so kije ki bata go ahead na dorawa daga inda suka tsaya. Sannan ki sanya mata albarka.”

Wasu hawaye ne suka tarar mata a ido, ko dan yadda tasowar ta a karamin family ya zame mata matsala da abin gugar zana cikin dangin miji, bazata kuma so wani nata ya taso haka ba, yaran Hafsa take kallo tasan indan Hafsa ta auri Muktar dole abinsa ta haifa ya taso a ƙaramin family ya yi mugun sa’a shine ya tasso a average family anma tunda haka Hafsa ta zaɓa ba yadda zatai.

Ba yadda zatayi. Da haka ta sallama.

<< Ko Da So 50Ko Da So 52 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×