Skip to content
Part 55 of 58 in the Series Ko Da So by Fadimafayau

“Ni kam na gaji…” ta fada cike da shagwaba tana kara sauri don ta kamo Mukhtar din. Gidan su yana da nisa da titi hakan yasa sai sun yi yar tafiya kafin su samu mota.

“Kiyi hakuri mun kusa fa.” Ya so ya kama hannunta amma ba zai iya ba saboda a waje suke. A dole ya rage gudun tafiyarsa ya daidaita ta da tashi sannan suka cigaba da tafiya.

Hafsah ta lankwashe. “Dama ban saka takalmin nan ba wallahi.” Dariya kawai Mukhtar yayi wadda ta bata haushi bata kara cewa komai ba har sai da suka isa titi suka hau mota. Shiru ne ya cika motar hayar har suka isa unguwar su Mukhtar.

Sai da suka sauka sannan Mukhtar ya kalle ta cike da sonta wanda itama take haushinsa ya tafi sannan yace, “duk don na same ki na siyar da babur dina amma in sha Allah nan bada jimawa ba zan sayi wani. Ba zaki dinga wahala ba.” Jinjina masa kai tayi hade da yin murmushin da ya kawata mata fuskarta.

Da yake sai sun tsallaka titi zasu karasa gidan sai Mukhtar ya bi yaji duk abun ya dame shi musamman yadda yaga ta rude da ganin manyan motocin da suke wucewa. A dole ya kama hannunta sannan suka fara shirin tsallaka titin. Kana ganin Hafsah kaga fargabar rashin sabo a tare da ita. Kallonta kawai yayi ba tare da yace komai ba har suka shiga gidan da sallama.

Gidan cike yake da yan uwan Inna wanda basu koma gida ba tukunna.

“Maraba lale da amaryar Mu’utar..” wata a cikin tsofin dake zaune a tsakar gida suna cin goro ta fadi. Da murmushi Hafsah ta sauke kanta kasa sannan ta durkusa ta gaishe su dukka.

“Madallah da ke. Ku higa, Kulun tana uwaddaka. Yanzu tayi wanka…” a haka aka shigar da Hafsah dakin wasu yan uwan mahaifin Mukhtar na zaune daga gefe suna nuna ta da baki don sam basu manta kalar tarbar da akayi musu ba. Kuma basa jin zasu taba yafe mata ko danginta.

Sallama ta sake yi sannan ta zauna a kasan ledar da ke falon tana jira. Tuni Mukhtar ya fice ya barta. Duk yadda tayi dokin zuwa, da yadda ta tsara sai da taji jarumtarta duk ta gudu.

“Sannu da zuwa Hafsatu.” Inna ta fito da fara’ar ta tana karasowa.

“Inna ina wuni? Ya gajiyar ku ta biki?”

“Mun gode Allah Hafsatu. Sannu da zuwa. Kai yarannan kuna ina?” Inna ta daga labule tana neman wanda zai kawowa Hafsah ruwa. Ganin duk kannen Mukhtar din basa nan ne yasa tace bari ta fita ta siyo mata ruwan a ranta.

“Bari naje na dawo, kinji.” Hafsah ta gyada mata kai tana wasa da yatsunta. Fitar Inna ba jimawa sai ga su Talatu, Hanne da Furera sun shiga falon suna gatsine.

Gefen Hafsah suka zauna sannan Hanne tace, “amaryar zinare, ya amarci?”

Furera tayi saurin karbe zancen, ” wani amarci kuma a gurin yayan masu kudi? Kema dai da neman zance… ai wallahi Yaya Mukhtar ba karamar cutar sa akayi ba.”

Shiru Hafsah tayi saboda ko kadan bata fahimci me suke nufi ba kuma ko da wasa tunanin ta baije ko ina ba.

Dariyar dai da suka kwashe da ita ce ta kona mata rai amma duk da haka bata tanka su da komai ba.

Ana haka sai ga Inna Rabi nan ta shigo itama tana hurhura hanci.

“Ku bani waje.” Babu musu duk suka fice saboda sunsan wace ce ita.

A hankali Hafsah ta gaishe ta tana satar kallonta ta gefen ido. Siririyar mace ce, doguwa kuma fara sol da ita. Fuskar ta dauke da zanen fulatanci.

Ki saurareni nan, ta kama kunnen Hafsah ta cigaba.

“Kar ki ga wai Innar Mukhtar tana da saukin kai ki nemi mallake mata yaro ko ki tatike shi da kunji kunjin ku mara amfani. Ki sani duk randa naji alamar abunda ban amince da shi ba zaman ki ya kare a gidan sa. In ma kuna asiri, gidan sa kika zo. Mu zuba ni dake. In kinzo da salama, mu zauna lafiya.”

A take jikin Hafsah ya fara rawa kafin kace me kwalla ta fara zuba a idonta. Sallamar Inna da Mukhtar ne yasa tayi saurin goge fuskarta a yayinda Inna Rabi ta washe hakori tana cewa.

“Shira muke abun mu ni da amarya.” Mikewa tayi ta fice kafin ma su karasa zama.

Kallo daya Mukhtar yayi wa Hafsah jikinsa yayi sanyi amma yayi kamar bai gani ba. Haka zatayi hakuri kam. Ba ma zai nuna yasan wani abu ya faru ba.

A haka dai ta cigaba da zama a takure har Inna ta kawo mata ruwan da shinkafa. Ta dan tsakura tace ta koshi. Bayan maghrib Mukhtar ya dauke ta suka tafi.

****

Tun bayan zuwansu dinnan sai su Furera da Hajara kanwar Mukhtar suka tsiri zuwa gidan duk bayan kwana uku. Haka Hafsah ta zags take ta yi musu hidimar girki. In zasu tafi kuma sai ta dauki abu ta basu.

Yau dinma sun zo sun gama cin meatpie da tayi ne sun mike kafa a falo ita kuma tana kitchen tana wanke abubuwan da suka bata.

Hajarah ta karewa kofar kitchen din kallo sannan ta mike ta shige dakin Hafsah. Furera ce tabi bayanta. Kai tsaye durowar kayan Hafsah suka nufa inda suka bude suna ta duba kayanta. Hajara ce ta zaro wani lace daga ciki dama shi taje nema. Tun sanda ake hada lefe ta kwallafa ranta akan sa kuma Yayan ya hanata. Taci alwashin sai ta sake lace dinnan.

Leda ta shiga dubawa wanda hakan ya janyo turare ya fado ya fashe. Hakan ya jawo hankalin Hafsah ta fito. Da mamakinta ta shiga dakin ta gansu tsaye da set biyu biyu na kayanta. Cike da rashin fahimta take kallonsu su kuma ko a jikinsu.

Furera ce ma ta danji wani iri sannan tace, “dama aron kaya muka zo.” Hajara ta kalli Hafsah da wani irin raini, suka rabe ta suka fice.

Mamaki ma yasa ta kasa motsin kirki har taji ficewarsu a gidan. Bata san sanda ta zube a wajen ta fara rusa kukan bakin ciki ba.

Ta dade tana kukan kuma ko da Mukhtar ya dawo yake tambayar ta me ya faru ce masa tayi babu komai amma dai tace su Hajara sun zo. Tuni ya gano abunda ya faru amma kuma babu yadda zaiyi ne. Yan uwansa, rabin jikinsa ne.

Rungumeta kawai yayi yana tsokanarta ko dai yan ukun sa ne suka kusa zuwa.

“Yan biyar dai.” Ta fadi tana hararar sa. Kan ka ce me suka shiga tsokanar juna suna dariya.

*****

Sosai tayi missing din Hafsah especially ma da bata nan akayi bikin. Tun safe take ta faman shirin zuwa wajen kawarta ta. Its been three months yanzu tun da akayi auren Hafsahn ita kuma lokacin tana exams ne. Kuma immediately suka tafi Umrah so bata wani sami time me yawa ba and Hafsah kamar share ta take yi bata so tazo gidan.

“Oh Hidaya. Duk wannan bai isa ba?” Mami take tambaya ganin yadda Hidayan take ta hada packages zata kaiwa Hafsah.

“Mami i missed the wedding fa. Plus wannan snacks din nasan tayi missing dinsu.” Ta dauki package din butter cake tayi waje dashi zuwa motar da driver yake jiranta. Duk wani abu da tasan Hafsah tana so sai da ta daukar mata harda su flower da after dresses ta siyo mata a Dubai wai as an apology in ma Hafsahn haushin ta take ji na rashin zuwa da wuri.

“Bye Mami.” Ta fada finally tana ficewa daga gidan. Tunawa da cewa bata gane kwatancen gidan bane yasa ta kira mommyn Hafsah tana tambayar ta. Mummy din cike da haushi tayi mata bayani sannan ta ajiye wayar.

Da yake Mal Isa driver dinta yasan gari sosai bai wani sha wahala ba suka isa lungun su Hafsah.

Kwance take a kan sofa tana playing game taji knocking. Sai da gabanta ya fadi kafin ta mike. Kwana biyu bata jin dadin jikinta ga su Hajara sun matsa da zuwa.

Jiki ba kwari dai taje ta bude. Ganin Hidaya ne yasa ta ma daskare a wajen tana jin wani irin dadi. A guje Hidayan tayi hugging dinta wanda immediately yasa Hafsah kawai ta fara zubar da hawayen murna da relief.

“Nayi missing dinki sosai Haf…”

Hafsah ta goge hawayenta tace, “dalla can karki karya ni.” Tana boye murmushinta.

Ciki ta koma ganin Hidaya tana ta shigo da abubuwa. Sosai Hafsh tayi murnar ganin ta da abubuwan da ta kawo mata. Da yake basa boyewa junan su komai nan Hafsah ta ke fada mata ai ta zata sisters inlaw dinta ne ma suka zo.

“Kice kuna good time!” Hidaya ta fadi so excited. Duk da bataga wani alamar change a tare da Hafsahn ba kawai the idea that her bestest cousin is married is amusing to her. Kuma abun burgeta yake.

“Wallahi na gaji. I’m feeling weak these days su kuma they keep coming with their friends. Nayi musu girki na yi wanke wanke…”

Hidaya tayi shiru before tace, “in sunzo daga yau kice su wanke abunda suka bata. Diplomatically fa.”

Haka dai sukayi ta hira har girki sukayi daidai sanda Mukhtar zai dawo. Kafin ya dawo Hidaya ta tafi cike da kewar Hafsah. Daidai lokacin kuwa mommy ta kira Hidayan inda kuma Hidayan ta ke bata labarin yadda Hafsah take rayuwa har ma kirkin da takewa inlaws dinta.

Ashe kuwa mummy abun ya bata mata rai. Za’a mayar mata da yarinya baiwa! Da kanta zataje ta jawa innarsu da mukhtar din kunne!

<< Ko Da So 53Ko Da So 55 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×