Zaune take tana daka naman da zata sanya cikin meat pies ɗin da zata yi na tarɓar baƙin ta, yau cike take da murna duda cewar baƙin maza ne ji take tamkar ta jawo gobe, duda kusan kullum Muktar yana nan in ma baya nan itama tana makaranta anma sam bata jin daɗin rashin zuwan baƙi gidan su, duda bata taso taga ana yawan zuwa gidan su ba anma lokacin da yayan ta Sadik ya yi aure da taje gidan sa taga ana ta zuwar wa Anti Amira.
Muktar ne ya shigo rike da botikin markaɗe na waken suya, tun jiya take damun sa kan ya siyo wake ya siyo yau ta bada markaɗe yana son yaga ko awara zatai anma dai yana tunanin daƙyar ma in tasan awara, yawwa dan Allah kamin taimako ka dauko tukunya ka ɗora mun kaɗan tsaya a kitchen ɗin karya zube, mamaki ne ya cika shi shidai yasa in Inna zatai awara sai ta tace yanason yin magana yana tsoron mitar Hafsa yanzu sai sukai dare tana mitar dama bai yadda ta iya abincin gargajiya ba, jiki ba kwari ya je ya ɗora tare da dawowa kawo in daka miki kije ki kula da na wutar, kallon turmin ta yi, aima na gama fa albasa, yasan wayon ta ne kawai ba wani gamawa da tayi sam bata son yanka albasa.
Sai da ta tabbatar ya yi tafasar da take so kafin ta sa abin tatar koko ta tace cikin mazumin ta mai kyau can gefe ta ajiye kafin ta fito da dusar, hira suke abinsu suna ta dariya cike da nushaɗi tare sukai filling ɗin meat pies suka soye abinsu taliyar ƴan yara ta dafa musu wadda ta ji kifi da attaruhu, suka ci suka kora da lamurje.
Wurin takwas Bilkisu ta sauka gidan Hafsa wadda ke ta jaddada mata tazo da wuri, Muktar ne ya buɗe mata ƙofa tana ganin sa taji nauyi ya kamata sam ta mance fa yanzu ba da bane miji ne da Hafsa, fahintar nauyin da ta ji ne yasa shi saurin cewa a’a maraba gaskiya kin makara muda mukai tsanmanin da asuba zaki zo tun fa ran Monday muke ta roƙon ki, sakin ranta ta yi tare da cewa hmm ai nama yi ƙokari da yanzu takwas fa ta yi, da markaɗen shinfar da Hafsa ta ce tazo da shi tazo wanda zasuyi wainar shinkafa, hannu yasa ya amshi botikin a’a gaskiya bakiyi ƙoƙari ba kawai dai ba komai tunda ke ce mun miki uzuri, Bilkisun ce ta soya wainar inda Hafsa ta ɗora miya.
Mukhtar yana ɗaki yana jin su suna ta hira, ji yake tamkar ya fito yasa musu baki kewar matar sa duk ya cika shi, shi kansa har mamakin kansa yake, shi yasan shi ba maison hira bane, yama fi son zama shi kaɗai anma tunda Hafsa ta zama tasa yafison yin komai da ita, bakinsa sam baya iya shiru in suna tare zuciyar sa ko yaushe son hira take da abar son nasa. Gajiyar da ya yi je yasa shi fitawa tare da cewa mai zan taya ku dashi, da sauri Hafsa ta ce yanka albasa, ya ɗan harare ta ita dai tana son bashi yan albasa, amsa ya yi tare da fitowa tsakar gida ita kuma ta biyo bayan sa riƙe da botikin da ta ta ce waken jiya.
Sosai ya yi kauri tamkar kindurme, kallon ta ya yo kardai kice mun har kindurmo kika sa Bilkisu ta kawo bafa sarakai ne zasu ba su Salisu ne, dariya tayi waken jiya ne fa suya milk zan musu, shiru kawai ya yi yana goge hawayen albasar da ke bin idon sa tasa dariya yau kukan naka ma yafi na kullum, turo mata kwanon albasar ya yi na fasa taya aikin nan waya ce miki kuka nake, ya faɗa tare da shigewa daɗi, madarar ruwa biyu ta zuba a suya milk ɗin tata, tare da ta gari mai yawa sikari kaɗan sannan ta watsa furar ta wadda take ta gari kana iya ganin ta tsalli tsalli tare da busasshen inibi da apple da ta yanka ƙana ƙana, sai da ta sa a firji sannan ta koma kitchen kusan har Bilkisu ta gama suyar ta koma kan miya wadda dama ta kusa haɗawa.
Suya milk ɗin ta zubawa Muktar tare da wainar shinkafar ta miƙa masa, yana ci ya lunshe ido shi, bai san suya milk nada daɗi haka ba sai yau da yasha na matar sa, wato tasan da ta iya shine bata taɓa masa ba, kullun ya buɗe ido ya kalli Hafsa ji yake yafi kowa sa’a ta ko ina ta haɗu. Awarar kuskus ta yi inda inda Bilkisu ta taya ta sukai fried rice kafin su gyara kitchen Bilkisu ta shiga dan ta watsa ruwa yayin da Muktar ya fito ya tafi masalci.
Hafsa na wanka ya shigo Bilkisu nakan dadduma tana sallah daga bakin zauren ya tsaya ya ce sun ce sun kusa ƙarasowa bari inje mu tawo tare, bai jira amsawar kowa ba ya fice dan ba mai amsawar ma, da harzari Hafsa ta shirya itama ta yi sallah suka shige dayan ɗakin nasu ita da Bilkisu, cike da ƴar damuwa Hafsa ta dubi Bilkisu ni kinga na rasa in sunzo ma mai zance musu wallahi tun jiya muke practice to sai mun fara kaman gaske sai yasa dariya bai daukeni serious ba. Dafa ta Bilkisu ta yi kinsan mene don’t stress yourself kawai ki zama natural yadda kike mu’amala da kowa haka zakiyi da su inma sunyi blaming naki for not being nice to them Allah yasan that’s the best you can do, shiru Hafsa ta yi kafin ta ce ai shikenan anma dai bari kiga ta mike da zummar yin magana da gwada abinda zatayi Muktar ya shigo, sunzo zasu iya shigowa? Leƙawa Hafsa ta yi kan ta ce eh har ya juya ya dawo ni kinga ma sai da suka zo duk raina ya ɓaci wallahi, mu ba babban soro ba bare in ce mu zauna a zaure, dariya ta yi Muktar akwai kishi sosai, ai dan yau ɗaya dai ka yi haƙuri kaji, ajiyar zuciya ya yi tare da juyawa ya koma suka dawo tare da Sallamar su.
Wani sanyan yan ƙamshi mai ratsa zuciya da ingantaccen farin ciki ne ya tsiyar ci hancin su wanda ya haddasa lumshewar idanun su ba tare da sun so ba, Hafsa ce ta fuskar ta ba yabo na fallasa ta ce ah maraban ku, sanin halin Muktar na kishi ne yasa basu tsaya jan ta da hira ba suka bi shi zuwa ɗan karamin falon su, wani ƙamshi na daban da ya fi na ɗazu daɗi ya ziyarci hancin su kasa haƙuri Salusu ya yi ya juyo yace Amarya nikam gaskiya ƙamshin nan ya min daɗi da yawa na kasa haƙuri, ya za’ai insan maiyi in siyawa Madam, dafa shi Muktar ya yi fuska a ɗaure wacce Maddam kuma malam muje ciki Please, ƙamewa ya yi kaga Malam kabarni in tambaya wallahi ƙamshin ya tafi dani da yawa in ban tambaya ba zan iya dawo muku gobe, Ibrahim ne yace Please ka bari muji nima kawai tsoron ka naji na kasa tambaya, murmushin da bai shirya ba ya yi Muktar, wai shi Ibrahim kejin tsoro ɗan karamin tsaki ya yi, Hafsa ce ta yi murmushi ai ko wanne irin ƙamshi kuke so mai sanyin daɗi ku tuntuɓi Amni Scents, kana searching ɗin su a IG ka musu magana danjin ya zaka samu naka, murmushi sukai kafin Salisu ya zaro wayar sa bari kiga in searching yanzu ba sai gobe ba, sukai dariya duka, sai da suka zauna a ɗakin sannan Hafsa ta shigo ta gaida su kafin ta ɗan Matsa Bilkisu ta leƙo itama ta gaida su Hafsan ta ce Aminiya ta ce, cike da rawar murya Bilkisu ta gaidasu dan sam ita magana cikin maza na bata tsoro, in ka ɗauke Abban su Tariq shine mutun na farko da ta taɓa zama comfortable gaban sa, tun randa suka fara haduwa ta yadda he is her man dan sosai ta sake sukai hira, Hafsa ce tace mungode fa da ziyara da har nayi fushi, Salisu ne yace ki tuhumi mijin ki shine ya hana mu zuwa, Malam Hirar ta isa haka, dariya sukai Hafsa ta fi ce.
Zaune suke Muktar ya zuzzuba musu abincin suna ci, Ibrahim da ya kurbi Suya milk ya dubi Muktar ya ce Malam yaushe ka yi kuɗin siyo mana Yogurt fresh haka, dariya Muktar ya yi ba Youghrt bace waken suya ne, dariya suka sa duka Ibrahim ya kuma kurɓa, Malam kaima naga alamun santin kake kai da ka saba cin girkin bari mu gama ci sai in tambaye ka. Sun ɗan taɓa hira kafin su fito zasu tafi. Hafsa ce suka fito tare da Bilkisu ah har kun fito ta faɗa, eh mun fito kafin fara korar mu, Yar takardar da suks sanya kuɗi Ibrahim ya miƙawa Bilkisu Aminiyar gashi fa mun gode, ta kamar ba zata amsa ba ya ce Please a taimaka a amsa ta amsa badan ta so ba sukai waje suna faɗin Amarya abinci ya yi daɗi muna godiya Allah ya tabbatar da farin ciki cikin zaman ku. Suna fita ta saki ajiyar zuciya Bilkisu ta ce Madam mene haka ai kinma yi ƙokari fa sosai Allah in ni ce bazan ma iya rabin abinda kikai ba. Sai yanma lis Driver ɗin Bilkisu ya zo har jikin Mota Muktar da Hafsa suka rako Bilkisu Muktar nata faman godiya.
Ranar Monday da wuri Hafsa ta tashi Gyaɗa ta ɗauko ta mintsike kafij ta ɗora ta fito ta tsiyaye ruwan gasara ta ɗebi wadda zata ishe ta, kunun gyaɗa mai kyau a ido da garɗi ta dama musu, garin ƙosan da Innar su Muktar ta bashi ya kawo mata ta ɗauko batasan kansa ba dan bata taɓa anfani da shi ba, gwangwani guda ta ɗiba ta buga kafin ta fara soyawa kafin shida ta kammala komai har wanka ta yi, zaune suke suna karyawa Suna tattauna labaran da ake a tashar BBC Hausa, kallon agogo ta yi ganin bakwai saura ta ce wanke wanken in na dawo na yi mu tafi ko, ah ki bari sai bakwai ko? Girgiza kai ta yi No yau munyi da Bilkisu zamu haɗu a old campus itama zata shiga school Bus bana son mu makara kasan fita titin nan, Murmushi ya yi in sha Allah ba zaki makara ba nayi magana da Malam Umar tunda yana da adai dai ta sahu 7:0am ya dunga zuwa yana kaiki school. Daɗi ne ya cika Hafsa ta kamo Hannun sa cike da farin ciki Nagode sosai Allah ya saka da alkairi ya baka wuyan ɗaukan nauyin mu, murmushi ya yi na jin daɗin yadda ta ji daɗi, tabbas Hafsan sa Mutunce ta ko ina ta yi, tanan kam yana yabawa Mum ta yi ƙoƙarin raising Hafsa ta inda ya dace ta yadda zata iya rayuwa da kowa a kuma ko ina tamkar ba ƴar masu kuɗi ba yadda yake jin ana faɗin yaran masu kuɗi basu iya komai ba shi ba haka ya gani ba, yadda yake jin ana cewa yaran masu kudi basa respecting komai sai kuɗi ba haka ya gani ba. Tare suka fito ya aka sauke Muktar a Titi aka wuce da Hafsa BUK old campus, yau farin cikin ta da yawa yadda ta tsani tafiyar ƙafae nan sai gashi tun kan aje ko ina Muktar ya mata maganin ta.