Skip to content
Part 10 of 22 in the Series Ko Ruwa Na Gama Ba Ki by Hadiza Isyaku

Saboda tsabar kiɗima da Jummai ta yi sakamakon jin labarin mutuwar mahaifinsu, sai ga tsohon cikin da ta daɗe tana ɓoyo a fili mutane suna gani.

Kwata-kwata ta kasa yadda da cewar ya mutu, domin a yadda suka baro shi, ko kusa ba alamun tsanantar ciwo a tare da shi.

Kuka sosai ta riƙa yi tana faɗin “Wallahi ƙarya ne, babanmu yana nan da ransa bai mutu ba.”

Wannan kukan shi ya ƙara jawo taruwar mutane a ƙofar gidan, wanda dama wasu tuni sun hallara saboda jimamin mutuwar Malam Amadu. Haƙuri wasu suka riƙa bata, wasu kuma suka shiga gulmar ta suna faɗin, “Ta tabbata tana da ciki tunda gashi nan, kuma ko shakka babu baƙincikinta ne ya kashe mahaifinta.

Ita kuwa da masu ba ta haƙurin, da masu gulmar duk bata san suna yi ba, abin da kawai take faɗi ya za’a yi wanda suka baro yana magana, kuma ace ya rasu.

Abin da bata sani ba shi ne, bayan tafiyarsu ciwon zuciyarshi ya taso, wanda dama da ƙyal likitoci suka samu ya lafa. Aman jini ya riƙa yi ta baki ta hanci, a wannan karon likitoci sun yi iya ƙoƙarinsu, amma abin ya ci tura, ƙarshe ma ya ce ga garinku nan.

Haukacewa Asabe ta yi tana faɗin “Malam bai mutuba, malam ka tashi, idan har ka tafi toh nima zan biyo ka, don ba zan juri ganin baƙincikin da ke tare da mu ba.”

Magana aka yi ta bata, amma bata ma san suna yi ba. Motar asibiti aka kawo aka sa gawar, Asabe kuma suka shiga motar Dr. Ameer, don a hannunsu Malam Amadu ya cika.

Ana gama magrib kenan aka iso da gawar Malam Amadu, su Jummai na tsaye waje don sun kasa shiga gida, duk da Asiya matar Kabiru ta so su shiga ciki, amma tashin hankali ya hana su.

Ana fiddo da gawar mutane aka ɗau salati, saboda ƙofar gidan cike take da jama’a, kuka wasu suka kama yi, wasu kuwa sai dai ajiyar zuciya, don ba ƙaramin rashi aka yi a garin ba. Malam Amadu kowa ya shaida halinsa mutumin kirki ne.

Har cikin gida wasu suka bi gawar, Jummai kuwa tana ganin gawar mahaifinta ta kurma wani irin ihu tare da sulalewa ƙasa somammiya.

kanta wasu suka yo aka yayyafa mata ruwa, a hankali ta buɗe idanunta da suka ƙanƙance saboda kuka,   gwaggonsu mai suna Indo ta gani kusa da ita,  wato Yayar Malam Amadu.

Duban Gwaggonsu ta yi ta ce “Gwaggo da gaske gawar baba ce na gani?”

kasa magana gwaggon ta yi, sai ma kukan da itama ta ke.

Taƙarƙarawa Jummai ta yi ta tashi zaune ta ce “Ina gawar mahaifina in nemi gafara a wurinsa,” don ta yadda cewa ya mutu, kuma ta ɗora ma kanta alhakin mutuwarsa.

Ɗakinshi aka nuna mata, jiri na ɗibarta ta nufi cikin ɗakin, samun ƴan’uwanshi ta yi zagaye da gawar suna ta kuka.

Cike da tsanarta suka buɗa mata, don suma gani suke baƙincikinta ne ya kashe shi.

Tsugunnawa ta yi tare da dafa gawar tana kuka mai tsuma zuciya.

Rahamar Allah ta cigaba da roƙa ma mahaifinta tana faɗin “Allah ka jiƙan mahaifina, ka yi mashi rahama, sannan ka sa Annabi ya san da zuwansa ya Allah.”

Wani irin tari ne ya sarƙe ta sakamakon kukan da take, bayan tarin ya tsagaita ta cigaba da faɗin “Na ɗauki alhakin mutuwarka babana, ka yafe mani laifin da na yi maka, don Allah ka gafarce ni.”

Maganganu ta riƙa yi masu ɗauke da zallar nadama, wanda sai da aka janye ta, don kamar ma ba cikin hayyacinta take faɗinsu ba.

A ɓangaren Asabe kuwa tana ɗakinta, mata ne zagaye da ita suna bata haƙuri, kallonsu kawai ta ke, amma bata iya tantance me ke suke faɗa, asalima gani take duk sun takura mata da surutu.

Haka wannan baƙin dare ya shuɗe ba tare da wani ya rumtsa ba a garin, yara da manya duk mutuwar ta shiga jikinsu.

Jummai kuwa duk tsoron da take ma gawa, sai gata zaune a gaban gawar mahaifinta tana yi mashi addu’a har garin Allah ya waye.

Jiran dangin mamacin na nesa ne ya sa aka jinkirta shirya shi, sai da misalin ƙarfe goma na safiya aka kimtsa komai.

Da za’a fito da shi sai da aka riƙe iyalansa, don baki ɗaya sun taso suna son riƙe shi. 

Jummai kuwa da mararta ta murɗa, sai ga ruwa ya ɓalle. da yake cikinta ya shiga wata tara.Tana ganin wannan ruwa ta ƙara ruɗewa, cikin bukkarta aka nufa da ita. wani irin raɗaɗine ya taso mata ta yi ta nishi tana juye-juye, da yake an fahimci haihuwa ce sai matan da suka kai ta suka fito, sai Uwani, Indo da kuma wata tsohuwa aka baro a ciki.

Shi kuwa ana fidda gawar na’ibinsa ya yi masa sallah, jama’a ba masaka tsinke. Daga garuruwa aka halarci jana’izarsa, su Dr. Ameer da wasu likitoci ma duk sai da suka zo rakiyar Malam Amadu a makwancinsa na gaskiya. 

Dawowarsu kuwa ta yi daidai da haihuwar Jummai, inda ta haiho danta namiji.

Take kuwa gari ya sake ɗauka cewar Jummai ta haihu, kan kace me kuma mata suka yi ta tururuwa a gidan don ganin ƙwam.

Baƙinciki goma da goma a wurin Asabe ga na rashin miji, gana kuma na tonuwar asirinsu a idon duniya.

Tunda ta sulale zaune sakamakon jin haihuwar Jummai, bata sake ko motsi ba, magana aka shiga yi mata, amma shiru bata ko motsi.

Ruwa aka yayyafa mata, bayan ta sauke ajiyar zuciya aka shiga bata magana, cewar ta ɗauki wannan a matsayin ƙaddara, tana kuka ta ce “Wace irin ƙaddara ce haka mai tonon asiri, ya za’a yi in yafe ma Jummai bisa ga tozarta mu da ta yi a idon duniya.”

Rufe mata baki aka yi, don gudun kada ta sake aibata ɗiyarta.

Kuka sosai ta riƙa yi kamar ranta zai fita.

Sanin kukan ne kaɗai abin da zai rage mata damuwa wata tsohuwa ta ce ma masu bata haƙuri “Ku ƙyale ta,kukan shima magani ne, idan ba haka ba zai iya kume mata a zuciya.”

Ƙyale tan aka yi, har sai da ta gaji don kanta ta yi shiru, amma kuma kamar zata mutu saboda ciwon zuciya.

A ɓangaren Jummai ma hakan take, ji take dama ba’a haife ta a wannan duniya ba, ta yi kuka har ta gode ma Allah.

Jaririn na kukan son Nono, amma baƙinciki ya hana ta karɓarshi, ita a yadda take ji ma dama mutuwa ta yi a wurin haihuwar.

Miƙa mata Jaririn Uwani ta yi “Ki bashi ya sha.”

Ƙin karɓarshi ta yi, Uwani ta ce “Miye haka, ba kya jin irin kukan da yake?” 

Tana kuka ta ce “Aunty Uwani dalilinsa ne na rasa dukkan farincikina.”

Wani irin tausayinta ne ya kama Uwani, lallashinta ta shiga yi “Shi bai da laifi Jummai, ƙaddararmu kenan, ki ba ɗanki nono ya sha, domin ke ce gatanshi.”

Karɓarshi ta yi, Uwani ta nuna mata yadda ake yi, ana kuwa sa mashi a baki ya riƙe saboda yunwar da yake ji.

Take ta ji tausayin yaron tare da son shi a zuciyarta.

Dangin Malam Amadu kuwa suna can ƙungiya-ƙungiya suna zagin Asabe da Jummai, gaba ɗaya sun ɗora alhakin mutuwar Malam Amadu a kansu.

Tunda Jummai ta haihu kuwa Gwaggo Indo ce kaɗai a cikinsu ke hidima, domin halinta ɗaya da Malam Amadu, sauran kuwa mugun abu ya hana su shigowa. a ɓangaren Jumman kuwa haka tafi so, don suna shigowa sai sun ƙara mata baƙinciki.

Uwani kuwa ta dage sai hidima ta ke ma Jummai, duk abin da ake yi ma maijego ta yi da kuɗinta, don ta fahimci Jumman a yanzu bata da sauran wani gata.

Batun ƴan gulma ma saida Uwanin ta taka musu birki, don ta fahimci kaso mai yawa ba gaisuwa ta kawo su ba, gulma ce kawai suka zo yi.

Bayan haihuwar Jummai da kwana biyu, Alhaji Mai Nasara ya buƙaci da Uwani ta kawo mashi Jariri ya gani, kafin a san abin yi akan Habeeb da Jummai.

Zaure Uwani ta kawo mashi jaririn, aikuwa tun kafin ya karɓe shi gabanshi ya girɗe ya faɗi.

Yana karɓarshi kuwa ya shiga sallallami, domin da ana haihuwar mutum sau biyu, toh da sai ya ce Habeeb ne aka sake haihuwa. 

Uwani ta fahimci me yake ma Sallallami, domin tunda aka haifi yaron ta ga yana kama da Salim ɗin da take goyo, wanda kuma da Salim ɗin da Habeeb duk da Alhaji Mai Nasara suke kama.

Tabayarshi ta yi “Lafiya Alhaji” duk da ta san me yake mawa.

Cikin tashin hankali ya ce “Gimbiya wannan yaro da Habeeb yake kama, kin ga ba makankara ɗanshi ne, kai amma yaron nan ya ci amanarmu, Allah ne kaɗai zai yi ma Habeeb irin abin da ya yi mana”.

Yana gama faɗin haka ya fashe da kuka, domin Habeeb ya gama tozarta shi a idon duniya, a matsayinshi na mutumin da ya shahara a garinsu.  “Ina ma nine wanda ya mutu ba tare da ya ga wannan ƙunci ba.”

Karɓar jaririn Uwani ta yi, don kyarma kawai hannunsa yake, haƙuri ta riƙa bashi tare da maganganu masu tausasa zuciya.

Share hawaye ya yi tamkar ƙaramin yaro, sannan ya tashi ya fita.

Uwani da tausayin mijinta ya kamata ta ce a zahiri “Kaicon ɗan da ke sa iyayensa kukan damuwa” tana gama faɗin haka ta koma ciki.

Hoton yaron Alhaji Mai Nasara ya sa Uwani ta ɗauko mashi a waya duk don ya kafa ma Hajiya Mairo Hujja, domin har yanzu taƙi yadda da Habeeb ne ya yi ma Jummai ciki.

Duk abin da Uba ke yi idan an yi masa haihuwa sai da Alhaji Mai Nasara ya yi ma Jummai, toshe kunnuwansa ya yi ba tare da ya saurari gulmar mutanen gari ba.

Birni ya koma a ranar ya samu Hajiya Mairo da ƙawayenta suna ta shewa a falo, su duk damuwar da ake ciki bata shafe su ba.

Suna ganin shi suka sha jinin jikinsu, gaishe shi suka yi, ba tare da ya amsa ba ya wuce ciki.

Baki ɗaya daga cikinsu ta taɓe “Ke Hajiya Mijinki fa sai a hankali, tafiya zamu yi tun kafin ya huce haushinsa a kanmu”.  tana gama faɗin haka suka tashi.

Lallaɓarsu ta yi akan su zauna, amma saboda tsoron da suke mashi suka ce zasu dawo.

Rakiya ta yi musu, bayan ta dawo ta same shi zaune a falo.

Fushin da taga yana yi ne ya sa itama ta ƙara shan mur, wucewa ta zo zata yi. Ya ce mata “Ki zauna zamu yi magana.”

Wani kallo ta yi mashi sannan ta zauna, wayarshi ya miƙa mata mai ɗauke da hoton jaririn Jummai.

A wulaƙance ta karɓi wayar, ras! gabanta ya faɗi don Habeeb ta gani a lokacin yana jariri

Tambayar shi ta yi, “A ina aka zaliƙo wannan hoton kuma?”

Zuciyarshi na wata irin ƙuna ya ce “Jikanki ne na wurin Jummai, kin ga kamar Ubansa Habeeb ya yi kaki.” 

Wata irin Ashar ta saki “A’a Habeeb ɗin ne Jummai ta sake haihuwa, Alhaji kun kaini ƙarshe fa, ta ya yarinya zata yi cikin shege kuma a liƙa ma yarona, toh wallahi ba zan lamunta ba.”

Alhaji Mai Nasara ya ce “Toh ai batun an liƙa ma yaronki ma bata taso ba, tunda gashi nan a zahiri, a baya na so ayi D.N.A Test, toh Allah ya hutar da ni, don haka na shirya ɗaukar ƙwaƙƙwaran mataki a kan yaronki wallahi”.

Cikin masifa ta ce “Yoh wane mataki kake dashi da zaka ɗauka” ya ce “Zaku gani ke da shi”,  yana gama faɗin haka ya tashi ya fita.

Tijara ta shiga yi da zage-zagen da ta saba, sai da ta yi mai isarta sannan ta kira Habeeb a waya, faɗa mashi ta yi cewar Jummai ta haihu, kuma yaro yana kama dashi, don haka ya faɗa mata gaskiya.

Kukan munafunci ya fashe da shi tare da faɗin “Umma kema kin yadda da zan iya aikata haka?”

Ta ce “Toh Habeeb sanin gaskiyar mutum sai Allah.”

“Hakane Umma, amma wallahi bani na yi mata ciki ba, kuma kin manta da sharrin waɗannan mutanen”.

Rantsuwa ya cigaba da yi mata akan ba shi bane, asali ma babu wata alaƙa a tsakaninshi da Jummai.

Da yake yafi ta wayau, sai gashi ta yadda da maganarshi, ƙarshe ta faɗa mashi Abbanshi ya ce zai ɗauki mataki, kuma ko da wasa kada yabi wannan matakin tunda ba shi ne ba.

Washe gari ranar addu’ar ukun Malam Amadu, tunda safe Alhahi Mai Nasara ya kama hanyar ƙauye tare da buhunnan Goro da kuma dabino.

Ana gama addu’ar uku Alhaji Mai Nasara ya tashi tare da shelar a saurara, da yake kusan duk an sanshi sai kowa ya yi tsit.

Gyaran murya ya yi tare da fara magana ya ce “Ina mana gaisuwa tare ƙarin tayin jimamin rashin da muka yi, da fatan Allah ya jaddada rahama a makwancin Malam Amadu.”

“Amiin” kowa ya ce.

Cigaba ya yi da magana “Sannan ina neman izninku akan zan ɗaura auren Jummai da Ɗana Habeeb, domin gyaran kuskuren da suka taru suka aikata a rayuwarsu.”

Hayaniya wurin aka kama yi, dangin Hajiya Mairo suka taso da nufin ƙin amincewa.

Alhaji Mai Nasara Ya ce “Mairo ce taku ba Habeeb ba, don haka baku isa ku hanani aiwatar da abin da nayi niyya ba.”

Maigari ne ya tashi tare da goyon bayan Alhaji Mai Nasara, don tuni ya yi nadamar cin fuskar da ya yi Malam Amadu a masallaci.

Dangin Asabe ma kusan duk sun goyi bayan hukuncin Alhaji Mai Nasara da ya yanke, domin a tunaninsu shine babban rufin asirin Jummai.

Take aka ɗaura auren Habeeb da Jummai, wanda Maigari ya wakilci Jummai, shi kuma Alhaji Mai Nasara ya wakilci ɗansa Habeeb.

Wannan ɗaurin aure kuwa sai da ya kusa tarwatsa zuciyar ɓoyayyen masoyi wato Dr. Ameer Sarkee, wanda tun farkon haɗuwarshi da Jummai ya ke jin wani abu a kanta, sannan kuma dalilin sonta ne yake ta kai da kawo wa kamar shi ma a danginsu yake….

Ƴan cikin gida kuwa sai suka samu abin tsegumi, wasu suka ce hakan ne daidai, wasu kuma suka ce abu dai bai yi ba.

Jummai kuwa ta ce data zauna da Habeeb gwara ta mutu.

Asabe ma na jin zancen ta ce su ƙarata can, don ita tuni ta yafe Jummai.

Ranar kwana bakwai da haihuwa aka sa ma yaro “Ahmad” sunan Malam Amadu kenan, wanda Jummai ta zaɓar ma yaronta.

Saida komai ya lafa sannan Alhaji Mai Nasara ya kira Habeeb a waya, ko gaisuwa basu yi ba, ya ce ma Habeeb “Na baka mako ɗaya ka zo ka tafi da Matarka da ɗanka” yana faɗin haka ya kashe wayar.

Wani irin tsoro ne ya kama Habeeb, tunanin fuskar da zai kalli mahaifinshi da ita ya shiga yi, domin ya yadda cikin Jummai nashi ne, sakamakon binciken da yayi a wurin masana, an tabbatar mashi kusanta ɗaya ce ma ke kawo ciki, saɓanin tunaninshi na baya.

Kuma a yadda gamsu da Jummai bai tunanin zata iya ba wani namiji kanta.

“Toh ya zanyi, zan amsa nine ko kuwa?” sanin halin mahaifinsa idan ranshi ya ɓaci ya ce “Wallahi ko sama da ƙasa zasu haɗe ba zan amsa ni ne ba.”

Da wannan ƙudiri ya fara kimtsa kayanshi da nufin dawowa gida.

Ɓangaren Hajiya Mairo kuwa, tana jin an ɗaura auren Habeeb da Jummai ta dira ƙafa akan wallahi ɗanta bai auren karuwa.

Alhaji Mai Nasara na dawowa ta ci kwalarshi akan bata yadda ba, wani wawan mari ya sauke mata a kumci, don ya kai ƙarshe akan iskancinta.

Ya ce “wallahi akan wannan case ɗin zaki iya rasa aurenki.”

Rama marin da ya yi mata ta yi “Wallahi baka isa ba ka taɓa ni in ƙyale ka ba”.

Wani irin baƙinciki ne ya kama shi, kai kawai ya girgiza tare da faɗin “Ki saurari Allah wallahi, sannan ki saurari hukuncin da zai biyo baya” lokaci ɗaya kuma ya ingiza ta ta faɗa a kan kujera. 

Habeeb kuwa a tsorace ya dawo gida, sai da ya yi kwana biyu bai haɗu da mahaifinsa ba, a ranar na ukun ne suka haɗu a falon Hajiya Mairo, domin tattauna maganar.

Kame-kame Habeeb ya fara yi yana rantse-rantse.

Alhaji Mai Nasara ya ce “Ni ba wata kalma da zan ji daga gare ka, Asiri ne tunda ka tona mana shi mun gode, Matarka da ɗanka suna jiranka, don haka ka shirya ɗaukarsu ka koma inda ka fito.”

Magiya Habeeb ya shiga yi yana cewa shi bashi bane.

Alhaji Mai Nasara ya ce “Rufe mani baki, ja’irin banza, tuni na dawo rakiyarka wallahi.”

Hajiya Mairo ta ce “Wallahi ni kuma yanzu zai saki Jummai, tunda ba shi bane, kai ko shi ne Ubanwa ya ce ta bashi kanta.”

Alhaji Mai Nasara ya ce “Sakin Jummai daidai yake da sakinki, don haka Habeeb idan kana son uwarka ta zauna a gidanku, toh kada ka saki Jummai.”

Hajiya Mairo ta ce “Auren banza da wofi, ni kam ai na gaji da wannan tsinanannen auren naka, don haka muddin ni na haifi Habeeb, toh sai ya sake ta yanzu Wallahi.”

Baki Alhaji Mai Nasara ya ta taɓe don kallon dabba yake mata, sai da ya maƙe kafaɗa sannan ya ce “Ya rage naku ke da ɗanki.”

Biro da paper ta miƙo ma Habeeb, don tuni ta tanade su “Ka saki Jummai yanzu.”

Tashin hankali Habeeb ya samu kansa, yanzu me zai zaɓa, auren Jummai tare da dawwamar mahaifiyarshi a gidan aure, ko kuwa sakin Jummai wanda shine yake daidai da sakin Mahaifiyarshi.

Ƙin karɓar paper ya yi aikuwa ta daka mashi “Idan baka sake ta ba toh cikinka ne, kuma sai na tsine maka albarka tunda har ka kusanci mace ta hanyar zina.”

Kuka Habeeb ya ɓarke da shi, kallon mahaifinshi ya shiga yi, aikuwa ya ɗauke kansa, ƙasan ransa yana jin wata irin ƙuna.

“Idan naƙi sakin Jummai, toh cikina ne, mahaifiyata zata yi fushi da ni, idan kuma na sake ta, mahaifina zai yi fushi da ni. Gashi kuma a duniya ba macen da nake so sama da Jummai, yanzu ya zanyi?

Tambayar da ya shiga yi ma kansa a ƙasan zuciya kenan, ɓangare ɗaya kuma idanunsa na ta fitar da hawayen ruɗani.

<< Ko Ruwa Na Gama Ba Ki 9Ko Ruwa Na Gama Ba Ki 11 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.