Skip to content
Part 12 of 22 in the Series Ko Ruwa Na Gama Ba Ki by Hadiza Isyaku

Jiki a mace su Dr.Ameer suka fito daga gidansu Jummai, Ƙasan zukatansu kuma suna tausaya mata dangane daga halin da suka same ta a ciki.

“Wai Uwar yarinyar can kuwa ta san me ake kira da Ƙaddara?” tambayar da Dr. Misau ya yi ma Dr. Ameer bayan sun shiga mota.

Cike da tsananin fushi Ameer ya ce “Gaskiya ba ta sani ba, idan ma ta sani to bata yi Imani da ita ba”, kai Dr.Misau ya jinjina tare da lumshe ido ya ce “Lallai kam, yanzu don Allah a muhallin da take zaune ko dabbarka zaka iya ɗaurewa a wurin? Haba! wannan wane irin zalunci ne uwa take yi ma ɗiyarta.”

Ajiyar zuciya Ameer ya sauke “Ni ba wannan ne damuwata ba Misau, yunwar da suke ciki, daga ita har jaririn, yanzu ina zata da wannan alhakin, dole ma a san abin yi.”

“Toh me zamu yi, bacin iyayenta da danginta ne suka sanya ta a wannan halin”, In ji Dr. Misau bayan sun ɗauki hanyar fita daga layinsu Jummai.

Ameer ya ce “Waɗannan dangin nata ai basu da amfani ko kaɗan”, Misau ya ce “Wallahi kuwa basu da shi.”

Cike da jin haushin Asabe suka cigaba da maganar, Ameer ya ce “Ko Ina shegen mijin ma da aka aura mata, wallahi da zan samu ganin shi sai na nuna mashi kuskuren shi.”

Ƴar dariya Dr. Misau ya yi, don ya fahimci kishi ne ya sa shi yin wannan maganar “Ai bana tunanin akwai wannan auren, idan ma akwai shi to ba a ɗauke shi da muhimmanci ba.”

Ameer ya ce “Allah ma ya sa babu, yadda zamu taimaka mata da hujja.”

“Ameen” Misau ya faɗa, tare da kawo shawarar bayan wasu ƴan kwanaki su dawo, kuma idan zasu zo su siyo mata madarar da zata riƙa ba yaronta, tunda ba alamun ƙoshin Nono a tare da shi.

Haka suka yi ta tattauna maganar har Allah ya sa suka isa gida lafiya.

Jummai kuwa tausayin kanta ne dana ɗanta ya kamata sakamakon Maganar Ameer, kuka sosai ta riƙa yi kamar ranta zai fita, musamnan da ta kalli yadda yunwa da kuma mura suka yi ma ɗanta azababben kamu.

A yadda yake numfashi ko baka da imani sai ka tausaya mashi, domin ƙirjinshi da kuma hancinshi cunkushe suke da majina, wadda kuma ko kaɗan bata barinshi bacci, uwa uba kuma da ya kama mama sai ya saki tare da fashewa da kuka.

Tausayinshi da ke cike da ranta ne ya sa duk sadda ya fara kuka, itama sai ta kama yi.

Wannan mura ta samo asali ne daga tsabar sanyin da bukkar ke da shi, wanda kuma babu wasu makaran kirki da zasu hana sanyin shigowa, kusan ma za’a iya cewa tun kafin a haife shi sanyi ya kama shi.

Kwance yake akan cinyarta tana kallon yadda numfashinsa ke fita da sauri, ido ta lumshe tare da matse ƙwallan da suka cika mata ido. Ɗan dafa ƙirjinsa ta yi a hankali tare da faɗin “Ni da mahaifinka muka ja maka wannan lalurar, Allah ya yaye maka ka ji.”

Ɗan taɓa shin da ta yi ne ya sa shi motsi kamar zai tashi, rungume shi ta yi tare da fiddo mama ta sa mashi a baki, duk da ta san da wahala ya iya sha.

Cike da son maman ya karɓa don ba komai a cikinsa, yana fara sha kuwa ya saki tare da fashewa da kuka.

A kan kafaɗa ta maida shi tana shafa bayanshi a hankali. Cikin muryar kuka ta ce “Allah ya yaye maka wannan murar, ya kuma kawo mana mafita ni da kai ɗana.”

Kamar yana jin me take ce wa sai ya ɗan tsagaita kukan, ganin haka ta sake maido shi ta bashi maman, a wannan karon ma yana karɓa ya saki, sake maida shi ta yi, a haka har ya ɗan samu abin da ya samu, domin ba komai a ciki, saboda sai ta ci abinci sannan ruwan maman zai samu, toh rabon ta da abin ci tun kalacin safe.

Baccin da ya koma ne ya bata damar faɗawa duniyar tunanin da ta saba. Tsantsar tsanar Habeeb ce ta bijoro mata a rai, wadda take shirya yadda zata kauce ma aurenshi don ba zata iya rayuwa da shi ba.

Sannan kuma ta dawo akan tsangwamar da Asabe take mata, wadda itama ta gaji da ita, mafita kawai take nemar ma kanta da kuma ɗanta da ke neman agajin a sama mashi lafiya.

Ido ta lumshe tare da fara yaƙi da zuciyarta akan abin da ta daɗe tana ruwaita mata, “Toh ina zan je idan na tafi?”

Tambayar da ta yi ma zuciyarta lokacin da take ce mata ta ttara kayanta ta tafi tunda yanzu bata da sauran gata.

Kai ta girgiza “Ba inda zan je, zan cigaba da haƙuri har lokacin da mahaifiyata zata yafe mani, tunda ni na ja ma kaina”, tana faɗin haka ta sa bayan hannu ta share hawen da suka zubo mata a kumatu.

Tunawa ta yi da kuɗin da Dr. Ameer ya aje mata, Zanen da ke gabanta ta ɗaga tare da ɗaukarsu, ƙirgasu ta yi taga dubu biyar ne, wani irin daɗi ta ji a ranta, don ta samu kuɗin da zata nema ma yaronta magani, godiya ta yi ma Allah, sannan ta gode ma su Dr. Ameer, don sun taimaka wurin rage mata damuwar da ke ranta.

Jakar kayanta ta jawo tare da saka kuɗin a ciki, sannan ta miƙe ta goya yaronta saboda magarib ta ƙarato. Wajen bukkar ta fito, don dama idan ta gaji da zama ciki, ko kuma idan Ahamad na kuka tana fitowa.

Hangowa ta yi Asabe na raba ma yara Awara, amma har aka cinye ba’a bata ba, ta ji ba daɗi a ranta, duk da wannan ba shine karon farko da aka hana ta wani abu ba idan ana rabo.

Wani irin son Awarar ne ya kamata, tunawa da tana da kuɗi ya sa ta komawa cikin bukkar ta zari ɗari biyar a ciki.

Fitowa ta yi ta kira Basheer, har ya zo wurinta Asabe ta ƙwala mashi kira tare da hana shi. 

Ire-iren wannan ba abin damuwa bane a wurin Jummai, shiya sa ma take yin komai da kanta, wannan don ya kama da fita ne ya sa ta kiran shi, kuma tunda an hana shi, toh har fitar ma ta ɗaukar ma ranta ita.

Ɗan jinkirtawa ta yi sai da Asabe ta shiga ɗaki sannan ta fita.

Aikuwa mutane suka yi ta kallon ta, wanda ta san dama haka zata faru.

Kai tsaye gidan Dije Mai Awara ta nufa, Dije na cikin zuba ma wata yarinya Awara a leda ta ji ana faɗin “Laa ga Jummai.”

Ɗago da kanta ta yi, zuciyarta cike da tausayin Jummai ta ce “Ke ce Jummai.”

Murmushi Jummai ta yi tare da gaishe ta.

Amsawa Dijen ta yi, Jummai ta miƙa mata kuɗi a bata Awara.

“Ki bar kuɗin kin ji”, Dije ta ce, sannan ta ƙulla mata Awara mai yawa cikin baƙar leda, don ta ji labarin ba’a ba ta abinci a wurin yara, kuma duk da akwai ɗan duhu, amma ta ga alamar yunwa a tare da Jummai.

Karɓa Jummai ta yi, tare da godiya, zata tafi Dije ta tsaida ta, Damammiyar Fura ce ta bata cikin Jug “Ga wannan furar da na dama zan sha, amma zan sake dama wata anjima.”

Godiya Jummai ta riƙa yi mata, ta ce “Ba komai Jummai”,  ƴar Nasiha ta yi mata akan ta ƙara haƙuri.

Cike da jin daɗi Jummai ta baro gidan, sai dai a kan hanyarta ta komawa gida aka kawar mata da wannan jin daɗi, domin a daidai wani shago ne ta ji wani na faɗin

“Ga Jummai nan wadda nake baka labari ta yi ciki, har babanta ya rasu.”

Kamar zuciyarta zata fito ta kalle su, inda ta haɗa ido da wanda ake nuna ma ita, wanda ko shakka babu baƙo ne a garin, don bata taɓa ganinshi ba, ganin sun ɗan sha jinin jikinsu ya sa ta ɗauke kanta.

Da damuwar wannan magana ta isa gida, sa’ar da ta samu Asabe na ɗaki tana sallah, cikin hanzari ta shige cikin bukkar don bata son a san ta fita.

Sauke Ahamad ta yi daga goyon sannan ta rungume shi ta zauna. Jikinta na ɓarin yunwa ta kwance Awarar ta fara ci, tana gamawa da Awarar ta ɗauki furar ta ɗan sha, don ta ci Awarar da yawa.

Godiya ta yi ma Allah, sannan ta yi ma Dije fatan Alkhairi, don rabon da ta yi ƙoshi irin na yau tun mahaifinta na da rai.

Ƙulle sauran wadda ta rage ta yi tare da ɗora ta akan murfin Jug ɗin, don ta san zata neme ta.

Fashin Sallar da take yi ne ya bata damar kishingiɗawa gaban ɗanta ta kwanta, cikin ɗan lokaci kuwa bacci ya tafi da ita. Ta ɗan yi nisa a cikin baccin kenan Ahamad ya farka da kuka, a gigice ta buɗe idanu tare da tashi zaune ta ɗauke shi ta bashi Mama.

Kasantuwar ruwan Maman ya samu ne ya sa Ahamad sarkewa, aikuwa ya yi ta tari, kanka kace me numfashinsa ya ɗauke. Kuka ta fashe dashi tare da jijjiga shi tana kiran sunanshi kamar wani babba.

Ajiyar zuciyar da ya sauke ce ta sa ta tsagaita kukan da take, “Sannu Ahamad” ta riƙa faɗi, tare da maida shi a kan kafaɗa.

“Yanzu haka zamu yi ta rayuwa ba tare da wani gata ba?” tambayar da ta yi ma kanta kenan, bayan Ahmad ya ɗan dawo daidai.

Shiru ta yi tana laluben amsar da zata ba kanta, samun amsar ne ya sa ta miƙewa, Ahamad na rungume a ƙirjinta ta nufi ɗakin Asabe, da nufin bata haƙuri a karo na Uku, domin yafiyar mahaifiyarta ce kaɗai zata fitar dasu daga ƙangin da suke ciki.

Tura ƙofar ɗakin ta yi a hankali ta shiga, kwance ta samu Asabe a kan darduma. Ɗago kan da Asaben ta yi ne ya tabbatar mata da ba bacci take ba.

Cike da ƙasƙantar da kai ta durƙusa a gabanta.

Magana ta fara yi cikin rawar murya don a tsorace take “Inna na zo wurinki a karo na uku ina neman gafararki, don Allah ki yafe mani kuskuren da na aikata”.

Shiru Asabe ta yi kamar bata ji me take cewa ba,  ido Jummai ta lumshe tare da kwanto da Ahamad da ke numfashi da ƙyal “Don Allah ki tausaya mana ni da wannan yaron da bai ji ba bai gani ba Inna, ki dubi yadda yake numfashi wanda ban san ya zanyi dashi ba.”

A hankali a Asabe ta tashi zaune, dubanta ta yi ta ce “Zaki yi mani wata alfarma?”

Da sauri Jummai ta ce “Eh Inna” don a zatonta ta sauko.

“Toh ki tashi ki fitar mani daga ɗaki, don har yanzu ciwon da kika ji mani a zuciya bai warke ba.”

Wani irin kuka Jummai ta fashe da shi, sosai ta cigaba da roƙonta, amma taƙi sauraronta, ƙarshe ma ta daka mata tsawa tare da korota waje.

Kamar Jummai zata haɗiye zuciya don baƙinciki, tunani ta shiga yi anya Asabe ce Mahaifiyarta.

Cikin bukkar ta koma ta yi kuka mai isarta, a wannan dare ta kwana tana baƙincikin mutuwar babanta da kuma kakarsu, wanda da suna da rai da ba haka ba.

Shawarar zuciyarta ta hau ta zauna a kai, tun a cikin daren ta fara haɗa  kayanta, duk wani abu da take so sai da ta ɗauke shi ta ƙulle wuri guda, don ta kai maƙura, jira kawai take Asuba ta yi, a yanzu kam ta fidda rai daga yafiyar mahaifiyarta, farincikin da suka rasa ita da ɗanta zata nema a wurin Allah.

Zaune ta kwana tana jiran ƙarasowar Asuba,

Ana fara kiraye-kirayen Sallah ta fito ta shiga banɗaki, fitowarta kuma ta yi daidai da fitowar Asabe daga ɗaki.

Cikin bukkar ta koma ta ɗan zauna, can da ta ji shigewar Asabe a ɗaki ta tashi. 

Idanunta na kuka ta ɗauki yaronta ta goya, hijabinta da ke kan jakar kayanta ta ɗauka ta sanya, sannan ta fito daga cikin bukkar ta riƙa kallon tsakar gidansu.

Cikin ranta ta riƙa faɗin “Zan yi kewar gidanmu tare da mutanen cikinsa da na fi so a rayuwata.”

Sai da ta ɗauki ‘yan mintuna a haka, sannan ta koma cikin bukkar ta ɗauki duk wasu tarkace nata ta nufi ƙofa, kafin ta fita sai da ta sake waigowa ta kalli tsakar gidan, sannan ta fice tana kuka. 

Cikin wannan duhun ta keta cikin gonaki ta nufi babbar tashar motar garin, wadda ba kowa ne ya santa a can ba, sadda ta isa ana cikin sallar Asuba, da yake an ƴanta ta, sai ta samu wuri ta tsaya.

Bayan an gama ta ji Ana faɗin “Ina na Lagos”, can kuma ta ji wani ya ce Katsina”, “Kaduna”, haka dai ta ji ana ta kiran garuruwa.

“Toh wane gari zan je?”, ganin motocin sun cika saura ta katsina kaɗai ta ce “Allah ka sada ni da Alkhairin da ke cikn Katsina.”

Cikin motar ta shiga, cikin ɗan lokaci kuwa ta cika, Driver na zuwa ya tada mota suka kama hanyar Katsina.

Asabe kuwa a wannan dare bata yi bacci ba, tunanin yadda Ahmad ke numfashi ne ya tsaya mata a rai, sannan ɓangare ɗaya kuma tana jin wata irin faɗuwar gaba.

<< Ko Ruwa Na Gama Ba Ki 11Ko Ruwa Na Gama Ba Ki 13 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×