Skip to content
Part 13 of 22 in the Series Ko Ruwa Na Gama Ba Ki by Hadiza Isyaku

Motarsu Jummai ta yi nisa da tafiya kenan Ahamad ya falka daga bacci. Daga cikin Hijabin ta fiddo mama ta fara ba shi, ya fara sha kenan ya saki, wanda kuma hakan alama ce da ke nuna yana son maida numfashi.

Fiddo shi ta yi daga cikin Hijabin tare da sanya shi a kafaɗa ta riƙa shafa bayanshi.

A yadda ya ke ta numfashi da ƙyal ne ya ɗauki hankalin wata Dattijuwa da ke kusa da su, cike da kulawa Dattijuwar ta kalli Jummai da ɗanta.

“Wai! Sannu yaro, sanyi ya maka mugun kamu.”

Murmushi Jummai ta yi “Eh wallahi, haka yake ta fama.”

Kai matar ta ɗan rausaya, “Allah Sarki”, tare da cigaba da kallon shi lokacin da Jummai ta maido shi a kan cinyarta, sosai ta ji tausayin yaron, lallai yana buƙatar kulawar likita, don a yadda yake numfashi muddin ba’a ɗauki mataki ba, toh komai zai iya faruwa da shi.

“Wane irin magani kike bashi,” matar ta tambayi Jummai.

Kan Jummai na ƙasa ta ce “Ban taɓa ba shi komai ba, amma idan muka sauka zan kai shi Asibiti.”

Matar ta ce “Gwara ki kai shi Asibiti, don yana jin jiki”, ɓangare ɗaya kuma cikin ranta tana mamakin halin mutanen ƙauye, yanzu mai fama da wannan lalurar ne za’a ce ba’a taɓa ba shi magani ba.

Wasa ta fara yi ma Ahamad lokacin da ya buɗe idanunsa yana kallon ta, aikuwa ya yi ta motsa ƙafafu alamar yana son wasan.

Ƴar dariya ta yi tare da miƙa hannu ta ce “Ko kana zuwa”, cikin wasa ta yi maganar, amma sai ta ga Jummai ta miƙo mata shi, cike da kulawa gami da tausayin yaron ta karɓe shi tare da ɗora shi a jikinta.

Tambayar Jummai ta yi “Ya sunan shi?” Ta ce “Ahamad”

Take yalwar fuskar matar ta ƙaru “Ashe Ammun Mama ne” ta faɗa lokaci ɗaya kuma ta sumbace shi a goshi.

Murmushi Jummai ta yi, ƙasan ranta tana jin son matar a ranta, bisa ga rashin ƙyamatarsu da ta yi, duk da kuwa gayun da take da shi. 

“Sunan Autana ne Ahamad” In ji matar.

Jummai ta ce “Allah Sarki” tana ƴar dariya.

Wasa matar ta cigaba da yi mashi, aikuwa sai gashi yana dariya. Jummai ta ce “Ashe kana dariya” don tunda take bata taɓa ganin dariyarshi ba.

“Ban gane yana dariya ba, ai Ammu akwai fara’a,” dariya su duka suka yi.

Shawarwari matar ta bata akan yadda zata kula da yaronta, ta hanyar shafe mashi jiki da Robb, sannan ta riƙa sanya mashi kayan sanyi, kuma ta riƙa ɗan sanya mashi ɗanyen mai a hanci, saboda a samu hancin ya buɗe.

Sosai Jummai ta ji daɗin haɗuwa da matar, sai ta ji dama kada su rabu saboda tana da daɗin mu’amala. A hannunta Ahamad ya yi bacci, bai falka ba sai da mota ta kusa sauka.

Miƙa ma Jummai shi ta yi “Ki bashi ya sha, amma ki riƙa bi a hankali, da ya ɗan karɓa sai ki cire, yadda zai samu damar yin numfashi.”

Yadda matar ta ce haka Jummai ta yi, aikuwa a haka har cikinsa ya cika.

Mota na tsayawa duk suka fito. Wata irin faɗuwa gaban Jummai ya yi, gata a garin Katsina, amma bata san inda zata je ba, take damuwa ta bayyana a fuskarta, matar ta lura da sauyin yanayinta, amma sai ta basar, tunda ba komai ne zaka sanya kanka a ciki ba.

Tambayar ta Jummai ta yi “A ina Asibiti yake a nan garin?”

Da yake hanyar unguwarsu matar ta wurin Asibiti ne sai suka shiga Napep ɗaya, wanda matar ta biya musu kuɗin. Jummai aka fara ajewa a asibitin, sannan aka wuce da matar unguwarsu.

A gidan Uwani kuwa, shiri take ta faman yi da nufin kawo ma su Jummai ziyara. Duk abin da jariri da mahaifiyarsa ke buƙata na yau da kullum sai da Alhaji Mainasara ya siyo ya bata ta kai ma Jummai da jaririnta. Sannan ya bada kayan abinci a kai ma Asabe, don yanzu suna buƙatar su tunda mijinta ya rasu.  

Uwani ta so su tafi Ƙauyen tare da shi, toh tafiyar da zai yi ce ta hana, sai dai ya sa driver ya kai su.

A ɓangaren Asabe kuwa,  bata san Jummai bata gidan ba sai da Uwani ta iso, bayan sun gama murnar ganin Juna Uwani ta ce, “Ina Jummai, ta zo itama ga saƙonta In ji Alhaji.”

Asabe da faɗuwar gabanta ke ta yawaita ta ce ” Tana cikin bukkarta.”

Ɗan ɓata rai Uwani ta yi “Wai Yaya Asabe har yanzu baki maido ta cikin ku ba, Allah kuwa wurin can akwai haɗari, sanyi kaɗai ya isa ya cutar da su, bare kuma miyagun ƙwari.”

Shiru Asabe ta yi tana tuna Ahamad da nufashinsa ke fita da ƙyal, ko da a sanadin cikinsa ne suka shiga ƙunci, amma ya matuƙar bata tausayi.

“Toh Uwani raina ɓaci yake idan ina ganinsu wallahi”, Asabe ta faɗa damuwa bayyane a fuskarta.

Uwani ta ce “Toh ya za’a yi, haƙuri shi ne kawai mafita” tana gama faɗin haka ta miƙe, ɗan tattasar zuciyar Asabe ta yi sannan ta fita daga ɗakin, kai tsaye cikin bukkar ta shiga, tsammaninta zata ga Jummai, sai dai kuma ba ita ba kayanta.

Wata irin faɗuwa gabanta ya yi, da sauri ta fito, lokacin Asabe itama ta fito daga ɗakinta.

“Yoh ina Jumman take, bata nan ciki.”

Asabe ta ce “Bata nan dai?” tare da ƙarasowa wurin bukkar, leƙawa ta yi, gabanta na wata irin faɗuwa “Toh ko ta fita ne” Asaben ta ce.

“Toh dama tana fita?” Uwani ta tambaya.

“Eh jiya na ga fitarta,” ashe duk saurin Jummai sai da ta gan ta.

Rashin ganin kayanta ne ya sanya su cika da mamaki, Asabe da ta san Jummai gata take nema ta ce “Toh ko gidan Kabiru ta tafi.”

Yaro aka tada ya je gidan Kabiru, Matarshi ta ce bata zo ba, duk inda ake tsammanin zata je, amma bata je ba. Tun ana ɗaukar abin da da sauƙi har ta kai ga ya girmama, Gaba ɗayansu duk sun rikice, musamman Asabe da ta fara saukowa akan tsangwamar da take mata.

Cikin ɗan lokaci kuma gari ya ɗauka Jummai ta gudu.

Kuka sosai Asabe ta riƙa yi tana faɗa ma Uwani “Duk abin da Jummai ta aikata a wannan karon ni ce sila, kullum cikin bani haƙuri ta ke, hatta jiya ma da kukanta ta zo wurina, amma na ƙi sauraronta.”

Ita kuwa Jummai tana can Asibiti suna fafatawa da likita akan sai an kwantar da Ahamad don ya samu kulawa a wurin likita.

Cewa ta yi “Ni dai likita ka rubuta mani magani kawai in riƙa bashi” don ta san kuɗin da ke gare ta ba zasu isa ba.

Likitan ya ce “Ba zai yiwu ba, bakya ganin yadda yake numfashi, ko so kike ki rasa ɗanki?”

Kai ta girgiza “Ai bani da kuɗi ne shi yasa”,  ya ce “Toh ina baban yaron”,  shiru ta yi bata ce komai ba.

Kallon ta likitan ya riƙa yi, sosai ya gane akwai wani abu a ƙasa, tausayinta ita da yaron ne ya kama shi, cewa ya yi “Za’a kwantar da yaronki.”

Marairaicewa ta yi “Ni dai A’a Likita.”

Ƴar shagwaɓar da ta yi ce ta bashi dariya, cewa ya yi “Kada ki damu, kyauta za’a yi maki komai, don haka yanzu zan haɗa ki da wata ku je a baku gado.”

A hankali Jummai ta lumshe ido, ƙasan ranta tana jin daɗi da kuma tausayin kansu ita da yaron, “Nagode sosai likita” ta faɗa idanunta na fitar da ƙwalla.

“Ba komai” ya ce, tare da  sanyawa aka ta raka ta sashen da ake kwantar da yara, cikin ƙanƙanin lokaci likita ya ba shi dukkanin kulawar da ta dace.

Wannan ɗaukar nauyin na kula da lafiyar Ahamad ta fito ne daga aljihun Al-ameen Muhammad, wanda aka tafka harƙallar *MAI AWARA* dashi, aikinsa kenan ɗaukar nauyin marassa lafiya, in da ya wakilta causin ɗinsa Dr. Umar, akan duk marar lafiyan da ya zo wurinsu, kuma suka ga yana buƙatar taimako, toh a sanar da shi zai taimaka, wannan aikin Alkhairi ya fara shi ne ta dalilin shawarar da Urgidansa kuma Amaryarsa Aminatu Basheer ta ba shi.

Mutane da dama sun ƙaru da wannan tallafi, ciki kuwa hadda Ahamad ɗan Jummai.

Sosai Jummai ta yabi mutanen Katsina, domin waɗanda ta yi maƙwabtaka da gadonsu sun nuna mata kara, ko ruwa bata taɓa saye ba, abinci da komai ƴan ɗakinsu ke bata, don sun lura bata da kowa.

Asibiti wuri ne da babu wanda ke fatan zama a cikinsa, amma a wurin Jummai ji take kamar ta ƙare rayuwarta a ciki, domin idan ta fito ba inda zata je.

Kwanan Ahamad bakwai aka basu sallama, sosai ya gyagije, duk wannan sarƙewar numfashi babu ita, godiya ta yi ma Dr. Umar akan taimakon da ya ba su.

Cewa ya yi “Masha Allah, amma wannan aikin duk na ɗan’uwana ne, don haka ki riƙa sanya shi a addu’a.”

“Insha Allah” Jummai ta ce, tare da yi musu fatan Alkhairi.

Jakar kayanta da kuma ledar magunguna ta ɗauka. Jiki a mace ta fito daga Asibitin “Ina zan je?” ta tambayi kanta, sanin bata da amsa ya sa ta yi jugum a bakin titi,  “Yau fa ake yin ta” ta faɗa a ranta, wuri ta samu jikin wata bishiya ta zauna.

Tun safe take nan zaune, har magarib, ganin duhu ya fara ya sa hankalinta ya fara tashi, shawara ce ta zo mata akan ta je tashar mota, sai ta shiga a sahun waɗanda zasu kwana, washe gari tunda Asuba su tafi wani gari.

Haka aka yi, tayi ƴan dubarunta har aka haɗa ta da wasu mata da za su yi tafiya.

Washe gari tunda Asuba aka shirya tafiya. Sai dai ta ƙi shiga mota ta zagaya bayan wasu motoci, tana jin ana kiran suna ye amma ta ƙi zuwa, haka ta yi ta yawo har gari ya fara haske.

Wurin masu abincin dake bakin tashar ta je da nufin siyen abinci, anan ta ji ana maganar ƴan gudun hijira na ta shigowa katsina.

Kasaƙe ta yi tana saurarar duk hirar mutanen ke yi, sai da ta gama sauraro sannan ta baro wurin, wuri ta samu ta ci Abincin, sannan ta sha ruwa.

Napep ta tsaida ta gaya mashi sunan unguwar da ta ji an ce ƴan gudun hijira na zuwa, domin zuciya ta saƙa mata cewar ta je can su haɗe, sai ta ce itama ƴar gudun hijira ce.

Ana shiga Unguwar mai Napep ya tsaya “Hajiya daidai ina zan aje ki, mun zo unguwar”, sauka ta yi tare da zaro kuɗi ta bashi.

Cikin wani layi ta bi gabanta na faɗuwa, tana ganin wasu yara zasu makaranta ta tsaida su, ƙin tsayawa suka yi, don kusan kowane yaro iyayensa sun hana shi tsayawa ga wanda bai sani ba, saboda duniya ta lalace.

Gaba ta ƙara da tafiya, wani gungun samari ta gani zaune suna shan hantsi.

Wurinsu ta tsaya tare tambayarsu “Don Allah ina ne gidan ƴan gudun Hijira?”

Kwatance ɗaya daga cikinsu ya yi mata, godiya ta yi sannan ta ce “Amma ban gane ba, don Allah ko zaka gwada mani.”

Har ya miƙe na kusa da shi ya riƙo mashi riga, ba ta ji me yake ce mashi ba, amma da alamun so yake ya hana shi.

Ƴar magana suka yi, sai ta ga ya sakar mashi riga, “Mu je” ya ce.

Gaba ya yi, ta bi bayanshi, ƴar tafiya kaɗan suka ƙara, tsayawa ya yi tare da nuna mata wani gida na ƙasa “Nan ne gidan,” godiya ta ƙara yi mashi ya tafi.

Saida ta ƙare ma ƙofar gidan kallo sannan ta shiga, gida ne mai ɗakuna huɗu wanda duka ba mai ƙyauren kirki, tsakar gidan cike da yara ƙanana, wasu na wasa, wasu na cin tuwo, wasu kuma sai kukan yunwa suke.

Abin kallo ta zame musu, don ko da take daga ƙauye, toh tafi su kyawun gani.

Gaishe da wasu mata dake zaune ta yi, bayan sun amsa a tsorace, ta ce “Ƴar gudun hijira ce, don Allah zan samu wuri?”

Karaf wata daga cikinsu ta yi “A’a babu,” kallon matar ɗaya daga cikinsu ta yi alamar hakan bai kamata ba.

“Daga wane gari kike?” wata tambaye ta, sunan garinsu ta faɗi, wanda tunda suke basu taɓa jin shi ba.

“Ayya, toh don Allah ki yi haƙuri, ba wuri a nan, muma a matse muke.”

Roƙon su Jummai ta yi, “Don Allah ko yaya ne, zan iya zama cikinku.”

A cikin faɗa matar da tayi magana da farko ta ce “Aka ce maki bamu da wuri.”

Jummai na ganin haka ta ce “Toh nagode” juyowa ta yi, kafin ta fita zauren ta ji wata ta ce “Ni ban yadda da ita ba, yanzu haka matar ɓarayinnan ce ta zo sa musu ido, tunda ance sun rubuto wasiƙa cewa zasu shigo unguwar da ƴan gudun hijira suke.”

Bata tsaya jin ƙarshen maganar ba ta fito, don bata fahimci inda zancensu ya dosa ba.

Wani gidan gudun Hijirar ta sake tambaya, nan ma da ta je koro ta suka yi, aikuwa ta fara shiga damuwa, ga Ahamad ya tashi, wuri ta samu ta zauna don ta bashi mama, ya gama sha kenan ya sako mata kashi, duk ya ɓata zanen da yake ciki “Wata sabuwa” ta faɗa a ranta, tare da tunanin inda zata samu ruwa ta wanke.

Tashi ta yi ta shiga wani gida da nufin wankewa, aikuwa fafur suka hana ta ruwa, haka tayi ta bin gidaje ana hana ta ruwa.

Haka ta rungume shi a kafaɗa, ɗayan hannun kuma ta ɗauki jakar kayanta tare da shiga wani layi, ajiyar zuciya ta sauke lokacin da ta hango famfuna biyu a ƙofar wani gida suna ɗigar da ruwa.

Da hanzari ta zo ta buɗe famfo ɗaya, aikuwa ruwa ya dunga zuba, fidda Ahamad ɗin ta yi ta wanke mashi, sannan ta goya shi da wani zane, shi kuma wanda ya ɓata ta wanke shi ta shanya a bangon wani kango.

Wani ɗan dakali ta samu ta zauna, zuciyarta cike da tunanin inda kuma zata faɗa.

Wata farar mata ta hango ta fito daga wani gida da ke nesa kaɗan da famfon, hannunta riƙe da yaro wanda ko shakka babu ɗanta ne.

Jummai na ganinta ta taso, gaishe da matar ta yi, tare da tambayar ta “Don Allah a nan unguwar ina zan samu gidan ƴan gudun hijira?”

Matar ta ce “Wallahi ban san gidan ba, amma ki bi ta nan ki tambaya za’a gwada maki.”

Godiya Jummai ta yi mata, sannan ta je ta ɗauki zanen da ta shanya ta sa a jakar kayanta. Hanyar da matar ta nuna mata nan ta bi.

Tana tambaya aka nuna mata, gida ne tun daga waje zaka gane ƙarami ne, ciki ta shiga tare da addu’ar Allah ya sa su karɓe ta.

Gaishe da matan da ta iske a tsakar gida ta yi, tare da bijiro musu da buƙatarta.

Cewa suka yi “Ba wuri,” ta buɗe baki zata roƙe su kenan sai ga wata tsohuwa ta fito daga ɗaki. 

“Ba’a haka, Allah ne ya rufa mana asiri, don haka muma mu rufa ma bayinsa.” tsohuwar ta faɗa lokacin da ta ƙaraso gaban Jummai.

Tambayoyi tsohuwar ta yi mata, daidai gwargwado Jummai ta amsa mata, tare da tabbatar mata da ba ta zo don cutar da su ba.

Sosai tsohuwar ta gamsu da Jummai, cewa ta yi “Toh ki zo ga wuri, amma bamu da abincin da zamu baki, ke zaki ci da kanki, kin yadda?”

<< Ko Ruwa Na Gama Ba Ki 12Ko Ruwa Na Gama Ba Ki 14 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×