Skip to content
Part 15 of 22 in the Series Ko Ruwa Na Gama Ba Ki by Hadiza Isyaku

Fuskar Jummai cike da mamaki da kuma tsoro ta dube shi, don bata taɓa tsammanin haka daga gare shi ba.

Sassauta murya ta yi sannan ta ce, “Ashe dama haka kake, gaskiya ka bani mamaki, kuma yanzu na tabbatar da taimakon da ka ke mana ba don Allah ka ke yi ba.”

Murmushi kawai ya yi, saboda ya san bai taɓa taimakon wani don wata manufa ba face domin Allah. Asali ma ko da dukiyar haram baya sadaka sai da wadda ya san da guminsa ne ya same ta, ya zaɓi haka ne domin neman gafarar mahaliccinsa bisa ga mummunan saɓon da ya kasance yana aikatawa.

Shirun da ya yi ne ya fusata Jummai, don ya soso mata wurin da ya daɗe yana yi mata ƙaiƙayi, “Maza! wallahi duk halinku ɗaya, da farko ku jawo mace a jiki, sai ta sakankance da ku sannan ku bayyana mata mugun halinku.”

Murmushi ya sake yi, don har yanzu bata faɗi kalmar da ta bashi haushi ba “Ki dena shiga haƙƙin wasu mazan, domin ba duka ne ke da halin da kika ce ba, akwai na gari a cikin mu, masu kyakkyawar manufa.”

Shiru ta yi, ƙasan ranta kuma tana musun maganar shi na cewa akwai na gari a cikin maza, domin ita dai bata ga nagarin ba a cikin waɗanda suka jawo ta a jiki, bare ta bada shaida.

Nasiha ta fara yi mashi a kan ya ji tsoron Allah, sannan ya sani zina bashi ce, idan ka yi da wata, toh komin daɗewa kai ma sai an yi da ɗiyarka, ko matarka ko ƙanwarka.

Dakatar da ita ya yi ta hanyar ɗaga hannu, lokaci ɗaya kuma ya haɗe fuska sannan ya ce “Ke ki yi shiru da wa’azinki, saboda ba shi na gayyace ki kiyi mani ba, buƙatarki nake, idan kin amince to ki zo mu tafi, idan kuma baki amince ba ki kama gabanki.”

Kai Jummai ta girgiza, don ta ga alamar ya yi nisa, “Tir, Allah ya tsare ni daga sharrinka, ni ba ƴar iska ba ce, ka je can ka nemi ƴar iska irin ka”.  kashedi sosai ta yi mashi a kan ya fita harkarta, idan ba haka ba zai sha mamaki daga gare ta.

Bata jira jin me zai ce ba ta juya ranta a ɓace ta koma cikin gidan abincin. A gaggauce ta ƙarasa ayyukan da zata yi ta fito, don bata son sake ganinshi.

Wurin Hajiyar da ke da gidan abinci ta je tare da faɗa mata ta gama aikin. 

Sai da Hajiyar ta gama ƙare mata kallo sannan ta tambaye ta, “Ya na ga kin yi sukuku, ko baki da lafiya ne?”

Kamar Jummai zata yi kuka ta ce, “Wallahi ciwon kai nake fama da shi.”

Ɗan rausaya kai Hajiyar ta yi sannan ta ce “Ayya, toh Allah ya kawo sauƙi”.

“Amiin” Jummai ta ce, suka yi bankwana ta fito.

Ras! Gabanta ya faɗi, lokacin da suka haɗa ido da mutumin, domin har yanzu yana nan tsaye inda ta bar shi.

“Hasbuna Llahu wa ni’imal wakeel” ta faɗa a ranta, lokaci ɗaya kuma ta tsuke fuska tare da bi ta gabanshi ta wuce.

Shima ɗin tunda ya ɗauke kansa bai sake kallon ta ba, har sai da ta wuce sannan ya raka bayanta da shu’umin murmushi.

Tamkar marar lafiya Jummai ta isa gida, Yakumbo ce kaɗai ta lura da sauyin yanayinta, suna shiga ɗaki ta tambaye ta “Jikata, lafiya dai ko?”

Ido Jummai ta lumshe sannan ta ce “Bana jin daɗi ne Yakumbo.”

Cike da damuwa Yakumbo ta sake tambayar ta “Meke damunki?”

“Ciwon kai ne” Jummai ta faɗa, lokaci ɗaya kuma ta karɓi Ahamad a hannun Yakumbon, saboda a gida take barin shi.

Allah ya sauƙe Yakumbo ta yi mata, sannan ta ce ta sha magani, fita ta yi don duba girkin da take musu.

Zama Jummai ta yi da nufin ba Ahamad mama, kasa bashi ta yi, sai ma ta cigaba da jero ma kanta tambayoyi da ta yi “Wace irin ƙaddara ce ke bibiya ta, me ya sa duk mazan da nake haɗuwa da su suke neman mutuncina?”

Ƙuri ta yi ma Ahamad lokacin da yake taɓo mata fuska da hannu yana gwaranci, “Ba zan taɓa yafe ma mahaifinka ba Ahamad, domin shi ne farkon wanda ya fara tozarta mani mutunci” cike da zallar baƙinciki ta ƙarashe maganar a ranta.

Ido ta lumshe lokacin da kanta ya yi wata irin sarawa.

Ɗan zamewa ta yi suka kwanta ita da ɗanta, cikin ranta kuwa ita kaɗai ta san irin ƙunar da take ji, kukan yunwan da Ahamad ya fara ne ya sa ta tashi zaune ta bashi Maman, yana gamawa ta goya shi saboda magarib ta ƙarato.

Da daddare kuwa kasa cin abinci ta yi, Uwa uba kuma wurin bacci da idanunta suka ƙafe ƙaf! Tunanin da zullumin sake haɗuwa da wannan mutumi ne suka tsare mata rai, domin ko shakka babu sai ta haɗu da shi a gidan abinci, tunda can ne wurin zuwanshi.

Washegari da safe kamar ba zata je aikin ba, toh a dokar gidan abincin  ba fashin zuwa sai da ƙwaƙƙwaran dalili, kuma ko ba wannan doka, aikin ai shi ne marufar asirinsu.

Kawar da wannan zullumi ta yi, don bata da sauran haɗi da mutumin, don haka babu dalilin da zai sa ta ƙi zuwa aiki saboda shi.

Cike da ƙwarin gwiwa ta tashi ta yi wanka, tana fitowa ta shirya, Mama ta cika ma Ahamad ciki da shi. Sannan ta barma Yakumbo shi ta tafi.

Da isarta gidan abincin ta nufi wurin Hajiya domin gaishe ta. Fuskar Hajiyar ba yabo ba falallasa ta amsa mata,

Jummai ta ɗan ji ba daɗin yadda Hajiyar ta amsa, kasantuwar bata taɓa yi mata haka ba.

Ji tayi kamar ta tambaye ta lafiya, sai kuma zuciya ta hana ta.

A sanyaye ta juya zata tafi, faɗuwa gabanta ya yi sakamakon dakatar da ita da Hajiyar ta yi ta hanyar kiran sunanta.

“Na’am” ta faɗa tare da waigowa, ɓangare ɗaya kuma gabanta na cigaba da faɗuwa, saboda Hajiyar ta ƙara murtuke fuska.

“Daga yau kada in sake ganin fuskarki gidan abincina, na kore ki.”

Ido jummai ta zaro tare da dafe ƙirji ta ce “Laifin me na yi Hajiya?”

A gadarance Hajiyar ta ce “Au baki san me ki ka yi ba.”

Marairaicewa Jummai ta yi ta ce “Wallahi ban sani ba Hajiya, don Allah ki faɗa mani sai in baki haƙuri.”

Cike da isa Hajiyar ta ce “Ƙin amincewa da abin arzikin da aka neme ki da shi, shine laifinki, don haka idan kina son cigaba da aiki anan, ki karɓi kwangila, wadda bada kanki shine aikin, idan kuma baki amince ba, toh ki kama gabanki, don bama hulɗa da ƙauyawa ƴan baƙinciki.”

Baki Jummai ta buɗe tana kallonta don ta fahimci bakinsu ɗaya da wancan mutumin, zata yi magana kenan Hajiyar ta tare mata numfashi da faɗin

“Kin wani hangame baki kina kallona, toh bari ki ji, ba aiki kaɗai ake yi a gidannan ba, duk wata mace da kika gani anan, toh tana da wanda take hulɗa da shi muna samun kuɗi.”

Rufe bakin Jummai ta yi tare da jifar ta da kallon tsana “Ai kuwa kun yi asara, kuma wallahi da in aikata abin da kuke nema na da shi, gwara na bar muku gidanku.”

Nuna Jummai Hajiyar ta yi da yatsa, tare da yin magana cikin fushi “Ke kada ki gaya mani maganar banza yanzu a neme ki a rasa wallahi.”

A yadda take ta ƙwalolo idanu, lallai zata iya yi ma mutum komai, “Allah ya fi ki” kaɗai Jummai ta iya ce mata, sannan ta fito daga ɗakin, tana jin sadda Hajiyar ke ta ɓurma mata zagi, “Can maki” ta faɗa a ranta.

Kai tsaye bakin titi ta nufa da nufin samun Napep. Wata baƙar mota ce ta tsaya gabanta tare da sauke glass ɗin motar a hankali.

“Innali Llahi” ta furta lokacin da taga wannan mutumin ne a cikin motar

Ɗan russunowa ya yi tare da faɗin “Har yanzu ƙofa a buɗe take, idan kin amince ki shigo mu wuce gidana.”

“Ina neman tsarin Allah daga kaidinku.” Ta faɗa tare da matsawa gaba.

Taɓe baki ya yi, lokaci ɗaya kuma ya maida glass ɗin tare da jan motar ya tafi.

Da baƙinciki Jummai ta koma gida. A wannan karon ba Yakumbo kaɗai ba, hatta sauran ƴan gidansu sai da suka fahimci tana cikin damuwa.

Tambayar “Lafiya” suka shi ga jero mata.

Ɗaya bayan ɗaya ta zayyana musu abin da ya faru tsakaninta da mutumin da kuma Hajiya mai gidan abinci.

Basu yi baƙinciki ba da korar da Hajiya ta yi mata ba, sai ma sanya mata albarka da suka shiga yi akan kare mutuncinta da ta yi.

Gargaɗi Yakumbo ta yi mata bayan sun gama sanya mata albarka, ta ce mata “Babu Asararriyar mace irin wadda maza ke bata kuɗi suna mu’amala da ita, don haka duk rintsi kada ki saida mutuncinki jikata, sannan kada ki damu akan raba ki da aikinki da suka yi, muddin kika jajirce a wurin haƙuri, toh Allah zai kawo maki wata mafita ta inda baki zata ba.”

Maganganu masu ɗauke da lallashi gami da gargaɗi suka cigaba da faɗa mata. Kuka sosai ta riƙa yi, don sun fige duk macen da son zuciya ya kai ta ba Saurayi ko wani can kanta, jin maganganunsu ta riƙa yi kamar da ita suke.

A wannan rana wuni ta yi tana kuka, Yakumbo ta ce “Ko dai akwai wani abun banda wannan?”

Kai Jummai ta girgiza, don ba zata iya faɗa mata tarihin rayuwarta ba.

Magana mai daɗi Yakumbo ta shiga faɗa mata, dena kukan ta yi, sai dai ƙasan ranta tana jin kamar zuciyarta zata fito.

Tsawon kwanakin da ta ɗauka bata fita bane ya sa ta jin kamar a cikin kurkuku take, saboda gidan babu wani abin more rayuwa a cikinsa. Ƴar fitar da take yi a baya ce dama ta ke hana ta ganin aibun gidan, yanzu kuwa da bata zuwa ko ina sai ƙyamar gidan ta fara shiga ranta.

Sanin bata da inda ya fi shi ne ya sa dole ta riƙa cusa ma ranta sakin jiki da gidan.

Tsoron koma ma damuwarsu ta baya ne yasa ta yi ma Yakumbo magana akan zata fara neman wani aikin.

Fatan Alkhairi Yakumbo tayi mata, ta ce “Toh Allah ya bada sa’a jikata, ke dai ki tsare mutuncinki.”

“Amiin” Jummai ta ce, washe gari tun da safe ta fita neman wani aikin, gidajen da ke unguwarsu ta fara zuwa, kasantuwar kowa ta kanshi yake ya sa ba inda aka yi mata ƙwaƙƙwarar kulawa bare ma har a bata aiki.

Gaba ta ƙara, har Allah ya sa ta isa Unguwar masu hannu da shuni.

Wani gida ta fara shiga, kasantuwar gate ɗin da ta gani a buɗe.

Wata matashiyar mata ta gani tsaye a gaban wata mota, hannunta riƙe da makulli.

Matar na ganinta ta haɗe rai, don Jummai ta cika macen da babu namijin da zai ganta bata burge shi ba. Kuma ita matar mijinta idonshi idon mace, toh sai ya yi mata magana.

Gaishe da matar Jummai ta yi, aikuwa ta amsa a gimtse.

A yadda matar ta amsa mata ne ya tabbatar mata da bata da rabo a wannan gida, duk da wannan yaƙini da ta samu, amma sai da faɗa mata buƙatarta cewar tana neman aiki.

Aikuwa matar ta ƙara haɗe rai tare da faɗin “Bamu buƙatar mai aiki” rufe bakinta ke da wuya sai ga mijin ya fito.

Jummai bata tsaya ya ƙaraso inda suke ba ta ce “Toh” tare da juyawa ta fice daga gidan.

Shi kuwa mai kama da ɗan akuya ko matarshi bai yi ma magana ba ya biyo bayan Jummai, matar na kiranshi amma ya yi banza da ita.

Lokacin da ya fito har Jummai ta ɗan yi nisa, da sauri ya bi bayanta bakinsa na faɗin “Baiwar Allah.”

Gabanta na faɗuwa ta tsaya, don yanzu mugun tsoron maza take.

Tambayar ta ya yi me ta shiga yi gidanshi.

Amsa ta bashi da “Aiki nake nema.”

Idanunsa ƙyam a kanta ya ce “Wane irin aiki?”

A taƙaice ta bashi amsa da “Shara da wanke-wanke” don ji take kamar ta nutse a ƙasa sakamakon mayen kallon da yake mata.

“Gasakiya kin fi ƙarfin shara da wanke-wanke, me zai hana ki zo mu ƙulla alaƙa in riƙa biyanki.”

Wani mugun kallo Jummai ta yi mashi, wanda sai da ya sha jinin jikinshi.

“Ya Salam, kai maza duk kun lalace wallahi,” Zagin shi ta cigaba da yi, don ya ƙara fusata ta, da yake ɗan iska bai jin zagi sai ya kama dariya, yana ƙara yi mata maganar banza.

Tafiyarta ta yi, ta barshi nan, magana ta yi a fili ta ce “Ba banza ba matarshi ke haɗe rai, ashe Jarababben miji Allah ya haɗa ta shi.”

Fatan shiryuwa ta nema mashi a wurin Allah, domin Zina masifa ce mai girma.

Sai da ta yi nisa sannan ta shiga wani gida,

Mamaki ne ya kama Dattijuwar gidan da taga  yarinya kamar Jummai tana neman aiki.

“Wallahi muna da masu aiki kin ji,” matar ta faɗa ma Jummai cikin tausasshiyar murya.

Cike da damuwa Jummai ta fito wannan gida tare da tunanin inda zata faɗa kuma.

Wani layi ne ta shiga, ta ɗan yi nisa a ciki ta hangi wasu mata su biyu tsaye a ƙofar wani gida, kowace sanye da hijabi har gwiwa.

Tun daga nesa suka shiga kallon Juna ita dasu, kowa da irin fatan da yake da shi a ransa.

Tana zuwa kusa da su ta gaishe su, amsawa suka yi tare da kafe ta da idanu suna jiran jin me zata ce, don sun ga alamar magana a bakinta.

“Don Allah aiki nake nema” Jummai ta faɗa cikin girmamawa.

Kallon Juna matan suka yi, su kaɗai suka san fassarar murmushin da suka jefi junansu da shi, Maida dubansu suka yi ga Jummai, sannan ɗaya ta ce”Okay toh shigo mu ji irin aikin da kike so.”

Cike da jin daɗin ta samu aiki ta bi bayansu har cikin falon gidan.

A yadda falon yake sai ya tuna mata da gidan Aunty Uwani, saboda irin tsarinsu ɗaya.

Ƙasa ta zauna, suna gani suka ce “Ki zauna a kan Kujera mana.”

“Nan ma ya isa” ta faɗa kan ta na ƙasa, don ta lura su duka suna mata wani kallo mai wuyar fassarawa.

“Wane irin aiki ne kike buƙata” wadda tafi shekarun ta tambaye ta.

Amsar da ta ba wannan mutumin suma ita ce ta basu, wato shara da wanke-wanke.

Kai su duka suka jinjina, don su ba a nan suka kai ta ba, kamar mayu su duka suka fara lasar leɓe.

“Gaskiya aikin da ke garemu ya fi shara da wanke-wanke, idan kina buƙata zamu faɗa maki shi a yanzu.”

Da sauri Jummai ta ce “Eh ina buƙata Hajiya.”

“Toh aikin shi ne zamu haɗa ki da manyan Hajiyoyi kuna hulɗa, kuma zasu ɗauki nauyin duk wata buƙata ta ki, tun daga sutura, mota da kuɗin kashewa.”

Ɗayar ta ƙwace da faɗin “Hatta ƙasashen duniya idan kina so zasu riƙa yawo da ke.”

Sanin fassarar wannan yaren nasu ya sa gaban Jummai girɗewa ya faɗi, a tsorace ta ɗago ta kalle su.  Magana take son yi amma tsananin firgici ya hana ta, da ƙyal ta iya cewa “Ba-bba irin wannan aikin nake so ba.”

Ganin ta tsorata da su ya sa suka fara lallaɓa ta “Haba tsoro kuma, ki saki jikinki da mu, mu kuma zamu jiyar da ke daɗin duniya.”

“Toh daɗin lahira fa?” ta faɗa a ranta, tare da miƙewa tsaye.

A zahiri kuma ce musu ta yi “Ni dai gaskiya ba zan iya irin wannan aikin ba.”

Miƙewa suma suka yi tare da kafe ta idanunsu.

Gani ta yi su duka sun nufo ta, abinda ranta ya bata kama ta zasu yi, aikuwa ta bazama da gudu waje, takalmanta a hannu ta riƙe su.

Dariya suka kama yi, ɗaya daga cikinsu ta ce “Kamo ta nan” don sun ga ta tsorata ainun.

Aikuwa kamar walƙiya ta fice daga gate ɗin, su kuwa dariya haɗa ƙwalla, bayan sun nutsu suka shiga jin haushin ƙin amincewa da Jummai ta yi da su, saboda sun ga samun kuɗi a tare da ita.

Ita kuwa daga nan ba ta zame ko ina ba sai gida, Yakumbo na ganinta ta ce “Yaya an samu?”

“Yakumbo, an ce Katsina a kwai mutanen kirki, toh ni dai har yanzu Allah bai haɗa ni da su ba”.

Labarin mutanen da ta haɗu dasu ta faɗa ma Yakumbo.

Cike da damuwa Yakumbo ta ce “Bakomai, da sannu Allah zai haɗa ki da mutanen kirki a katsina.”

Gargaɗi ta ƙara yi mata, sannan ta ce “Aikin ma a bar nema, Allah yana tare da mu.”

Maganar Yakumbo ta bi don ta ɗauke ta tamkar Uwa, daga wannan rana bata sake fita neman wani aiki ba.

Sai dai kuma kullum cikin fargabar halin yunwar da zasu koma take.

Sannan wani abu da ke da damun ta a rai shine, son komawa gida, domin ta fahimci zaman kai abu ne mai matuƙar wahala, musamman ga ƙaramar yarinya irin ta.

Tunawa da tsananin fushin mahaifiyarta ne ya rage mata son komawa gidan, don tana da yaƙinin idan ta koma, toh sai ta sake maido ta inda ta fito.

A hankali rama ta fara shigar ta, saboda ƙarancin abinci da suka fara samu, da kuma tunanika da ta aje a ranta. Daka ta wankau ta fara aikawa gidaje a kawo, toh shima ko sau ɗaya ba wanda ya kawo,

Sauƙin da suka samu sauran mutanen gidan sun koma garinsu, sakamakon sasanci da gwamnati ta yi ta fulani.

Yakumbo ce kaɗai ta yi saura, itama jira jikanta da kuma tunanin halinda Jummai zata shiga ne suka hana ta tafiya, da tuni itama ta koma, tunda ta gaji da rayuwa cikin garinnan.

Ana cikin wannan yanayi ne Ahamad ya fara rashin lafiya, wani irin zazzaɓi mai zafi ya riƙa yi, ƴan kuɗin da take da su ne ta je chemist ta siyo mashi magani.

Tunda aka fara bashi maganin sau ɗaya zazzaɓin ya sauka, bayan kwana biyu kuma sai idanunsa da hancinsa suka fara fitar da ruwa.

Yakumbo na ganin haka ta ce “Wannan yaron ƙyanda ce yake yi.”

Tashi hankalin Jummai ya ƙara yi, don dama tunda ya fara rashin lafiyar take cikin damuwa.

“Yanzu a wannan halin da muke ciki ya za’a yi dashi Yakumbo,ɗari biyar ce rak ta rage mana, kuma ko kuɗin abin hawa ba zata ishe mu ba, bare kuma magungunan da za’a siyo mashi.”

“Kada ki damu, bari a samo nonon tunkiya a shafa mashi, idan ta fito sai a san yadda za’a yi”, Nonon tunkiyar aka samo aka shafa mashi, aikuwa cikin ikon Allah sai ga ƙyandar ta fito.

Man kifi aka nemo da zuma aka riƙa bashi, saboda ta ciki da maƙoshi. 

Sannan aka riƙa shafa mashi farin kwalli a idanu.

Tunawa Jummai ta yi da taimakon da suka taɓa samu a asibiti, aikuwa tunda safe ta ɗauki sauran ɗaribiyar ɗin nan ta tafi Asabiti.

Sai dai tashin farko ba Dr. Umar ta gani ba, tana tambaya aka ce mata an maida shi wani gari.

Likitan data gani kuma ya ce kwantar da shi za’a yi, Sanin bata da kuɗi ta ce, “Don Allah likita ka rubuta mani magani.”

Maganin ya rubuta mata ta fito, zuciyarta cike da tunanin inda zata samu kuɗin maganin, gida ta dawo tare da miƙa ma Yakumbo takardar.

“Allah ka zama gatanmu” Yakumbo ta faɗa bayan ta karɓi takardar.

Tashi Yakumbon ta yi, ta nufi gidan wani Alhaji dake kusa dasu, da nufin a taimaka musu, sai dai gidan a rufe ta same shi. 

Inda ta bar Jummai nan ta iske ta, ta yi ma Ahamad ƙuri tana ta kuka, don a yadda yake ta numfashi duk wanda ya kalle shi sai ya tausaya mashi.

“Wai kuka kike yi ne?” Yakumbo ta tambaye ta.

Sai da ta matse hawayen da ke idonta sannan ta ce “Tsoro nake ji kada ya mutu Yakumbo.”

Cike da tausayawa Yakumbo ta ce “Insha Allah ba zai mutu ba.”

Karɓar shi ta yi, sannan ta fito da shi tsakar gida, ruwa ta yi ta shafa mashi a jiki, a hankali kuwa zafin jikin ya yi ta raguwa.

Ɗaki ta dawo dashi, tare da miƙa mata shi ta ce;

“Ki bashi ya sha.”

Karɓarshi ta yi, sai dai kuma ya ƙi karɓa don bakinsa cike yake da ƙuraje, kuma dama dai ba komai a cikin maman, don rabonta da abinci tun jiya da rana, saboda ba abinci a gidan.

Haka ya wuni bai ci komai ba sai ruwa da kuma zumar da Yakumbo ta ke lasa mashi a baki.

Dadaddare tana rungume da shi ta yi tagumi taga ya fasa ƙara,  cikin ƙanƙanin lokaci kuma idanunsa su ka birkice.

Kuka ta fashe da shi tare da miƙa ma Yakumbo da tayo kansu da sauri, ruwan dake kusa da ita ta yayyafa mashi, ajiyar zuciya ya sauke, amma kuma idanunsa da numfashinsa a birkice suke.

Kuka sosai ta riƙa yi don ta ba ranta mutuwa zai yi, Yakumbo ma kanta ta tsorata da yanayinsa.

“Allah ga bayinka masu rauni, ka kawo mana agaji.” Kamar Yakumbo zata yi kuka ta faɗi haka.

A zaune suka kwana suna kallon yadda yake ta numfashi a sarƙe.

Aikuwa tunda farar safiya Yakumbo ta koma gidan wannan Alhaji, ta yi sa’ar ganinshi, buƙatarta ta faɗa mashi cewar jikanta ne bai da lafiya.

Abin mamaki sai ta ga ya zaro duɓu ɗaya ya bata, har ga Allah ta raina kuɗin a ƙasan ranta, amma a zahiri karɓa ta yi tare da godiya.

Tana zuwa suka nufi Asibiti ita da Jummai, aikuwa da isarsu aka tura su Emmergency.

Bayan an masa komai aka miƙo mata takardar magungunan da ake buƙata.

Kai Jummai ta dafe lokaci ɗaya kuma idanunta suka ciko da ƙwalla, don bata san inda zata samu kuɗin maganin ba.

Lallashin ta Yakumbo ta fara yi ta ce “Ki yi haƙuri, Allah da ya ɗora mana, shi zai kawo mana mafita.”

Share hawayen da suka zubo mata ta yi “Toh yanzu Yakumbo ina zamu samu waɗannan kuɗaɗen.”

Shiru Yakumbo ta yi tana nazari, duk inda take tunanin zasu samu, sai ta ga ba wurin zuwa bane, ajiyar zuciya ta sauke tare da duban Jummai “Wallahi kai na ya kulle Jikata.”

Suna cikin wannan hali ne suka ji ana kiran iyayen Ahamad Habeeb, da hanzari suka shiga, don a zatonsu mutuwa ya yi.

Wata nurse ce ta ce musu “Ku ake jira ku kawo allurai da magunguna.”

Cikin raunin murya Yakumbo ta ce mata “Malama wallahi bamu da komai, ku taimaka mana don Allah.”

Wani mugun kallo nurse ɗin ta jefe su da shi “Toh ya za’a yi kenan tunda baku da komai.”

A yadda Nurse ɗin ta yi magana a wulaƙance ne ya ƙona ma Jummai rai.

Cikin kaushin murya ta ce “Duk abin da ake buƙata za’a kawo Insha Allah.”

Kallon ta Yakumbo ta yi tana son Tambayar ta inda zasu samu kuɗin, da sauri ta fita don bata son sake wata magana a gaban Nurse ɗin.

Bayanta Yakumbo ta bi tare da Tambayar ta wanda zai bada kuɗin maganin.

“Cikin gari zan shiga, ko da roƙo ne sai na neman ma ɗana lafiya.”

Tausayin ta ne ya kama Yakumbo, yarinya ƙarama, amma sai fama take da rayuwa, fatan samun nasara ta yi mata,

Fitowa Jummai tayi bakin titi, cikin ranta tana tunanin wurin da zata.

Gidajen da ke kusa da Asibitin ta fara shiga tana neman taimako, amma ko asi ba wanda ya ba ta.

Wani gidan ma baƙar magana aka faɗa mata.

Da hawaye ta fita daga unguwar ta nufi titi.

Tana isa titin ta yi tsaye, don bata san inda zata je ba, ƙasan ranta kuma tana fargabar rasa ɗanta tunda shi kaɗai ya rage mata a yanzu.

“Dole in rasa Ahamad muddin ban samu kuɗin magani ba.” Abin da bakinta ke ta faɗi a fili.

Kai ta girgiza tare da neman tsarin Allah bisa ga wani abu da zuciya ta fara saƙa mata a take.

“Yanzu idan ba can ɗin ba ina zaki samu kuɗin da za’a yi ma ɗanki magani” wani shaiɗanin sashe na zuciyarta ya tambaye ta.

Ido ta lumshe tare da yadda da zuciyarta don bata son rasa ɗanta

Napep ta tara da naira ɗari ɗin da ke hannunta.

Ba inda Napep ta aje ta sai gidan abinci. Cikin sa’a kuwa ta hangi wanda ta zo wurin domin sa zaune yana danna waya.

Zuciyarta cike da ƙuna ta isa inda yake, tare da jawo wata kujera ta zauna suna fuskatantar juna.

Tabbas ya gane ta duk da sauyawar da ta yi, amma sai ya basar ya ce “Malama lafiya?”

“Na zo karɓar aikin da na ce bana so, idan kuma an ba wani, toh zan je wani wuri in nema.”

Shiru ya yi yana kallon ta, duk yadda ya so ɓoye farincikinsa, amma sai da ya kasa.

Murmushi mai sauti ya yi “Tana nan ba’a ba kowa ba domin mallakinki ce ke ɗai.”

Wani irin kallo ta yi mashi tana son sanin dalilinsa na cewar mallakinta ne.

Ya fahimci hakan, ya ce “Na san zaki so jin dalilin da ya sa na aje maki ita ko?”

Ajiyar zuciya ta sauke tare da ɗaga kai alamar “Eh”

“Dalilin na farko shine soyayyarki, na biyu kuma,  yarinya mace kamarki, muddin ta yi gangancin nisa da ahalinta ba tare da wani dalili ba, toh dole ta nemi irin wannan aikin, ko dai don biyan buƙatarta ta sha’awa, ko kuma don ta samu abin da zata ciyar da kanta.”

Shiru Jummai ta yi tare da lumshe ido, Lallai ya yi gaskiya, nadamar barin gida ce ta taso mata, a lokacin da nadamar bata da amfani, domin shaiɗan da zuciyarta sun yi galaba a kanta, a yadda take ji a yanzu, ba don maganin ɗanta kaɗai ba, hadda biyan buƙarta, don ta kai maƙura a wurin buƙatuwa.

A hankali ta buɗe idanunta tare da magana ƙasa-ƙasa, “Yaushe za’a fara aikin.”

“Duk sadda kika shirya.” Ya bata amsa a taƙaice.

Kai tsaye ta ce”Yanzu haka a shirye nake.”

Tausayin yadda ta miƙa wuya ne ya kama shi, amma tunda yana da baƙin duduri a kanta dole ya aiwatar da abin da yake so da ita.

Tashi ya yi tsaye, ganin haka itama ta miƙe, magana da hajiya ya ce zai yi, ta ce “Kada ka sanya ta a cikin zancena, domin ba a ƙarƙashinta zan yi aikin ba.”

“An gama” ya ce, ƴan maganganu ya je suka yi da Hajiyar, ba’a daɗe ba sai gashi ya dawo.

Kai tsaye motarshi suka nufa, da shigarsu ya tada suka tafi.

Shiru su duka suka yi, kowa da irin abin da yake saƙawa a ransa, har suka shiga Unguwar GRA ba wanda ya yi ma wani magan. Wani katafaren gida suka tsaya, tun kafin ya yi horn maigadi ya buɗe musu gate ɗin.

Wurin da ake aje motoci suka nufa, duban ta ya yi lokacin da ya kashe motar, “Madam bisimillah”

Buɗewa ta yi ta fito, gida ne ƙayataccen, wanda tun daga waje ta gane haka.

Cikin wani ƙayataccen falo suka shiga.

Faɗuwa gabanta ya yi lokacin da ta ga wata mata zaune a kan kujera, a zatonta matarshi ce.

Gani ta yi matar ta taso da girmamawa ta yi mashi sannu da zuwa, amsawa ya yi haɗe da faɗin “Ga baƙuwa nan, a gyara ta sannan a kawo mani ita a ɗaki”, Yana gama faɗin haka ya haura sama.

Hakan da ya faɗi ne ya tabbatar ma Jummai da ba matarshi ba ce.

Wani irin kallo matar ta yi ma Jummai, sai da ta ga ya shige sannan ta sassauta murya ta ce “Ke kuwa me ya ja maki bin wannan mutumin?”

“Buƙata” Jummai ta bata amsa a taƙaice.

“Wace irin buƙata ce haka don Allah, kin kuwa san halin shi?”

Tunawa ta yi da ɗanta na can rai a hannun Allah, kuma halin mutumin ko ba’a faɗa mata ba ta san ɗan iska ne.

Ce mata ta yi “Malama a matse nake, don haka ki yi abin da aka sanya ki.”

Abin da Jummai ke nufi da maganarta daban, abin da matar ta fahimta daban.

Baki matar ta taɓe “Okay, toh ki biyo ni.”

Bin bayanta Jummai ta yi, wani bedroom ne suka shiga, wanda tsayawa faɗin haɗuwarshi ɓata lokaci ne.

Ban ɗaki suka shiga, matar ta nuna mata yadda zata yi amfani da kayan ciki, domin komai na zamani ne.

Da yake tana da kai, cikin ɗan lokaci ta wanke kwantaccen gashinta, sannan ta yi wanka da wasu sabulai masu ƙamshi, tana gamawa ta ɗaura towel ta fito.

Gaban dressing mirror ta zauna, matar ta taya ta wurin kwalliya, aikuwa sai gata ta yi kyau.

Wato doguwar riga da ke kan gado matar ta miƙa mata.

Karɓa ta yi ta sanya, sosai rigar ta fito da duk wata komaɗa ta jikinta.

Turarukta mashi ƙamshi ta feshe jikinta da su, waɗada da ta san da me aka yi su, da bata fesa ba, takalma ta zura suka fito.

Sama suka haura, matar na knockin ya buɗe.

Cikin wata irin murya ya ce ma matar “Kin gama aikinki, na gode.”

Lokaci ɗaya kuma ya jawo Jummai a jikinshi tare da rufe ƙofar.

Wata irin faɗuwa Jummai ta samu kanta, domin wannan shine karo na biyu a wurinta.

Janta ya yi suka nufi gado, daga nan kuma mai aukuwa ta auku.

Tunda yake tarayya da mata, bai taɓa samun kamarta ba, don haka kuɗaɗe ya bata masu yawa, tare da sake neman ta a gobe.

Cike da baƙincki ta yi wanka tare da maida kayan da ta zo dasu a jikinta.

Ɗaukar ta yayi suka koma gidan abincin, daga nan ita ta koma gida ta chanja kaya, don suna fitar da wani ƙamshi, wanda bata son Yakumbo ta ji shi.

Can ƙasan jakarta ta tura kayan, sannan ta fito.

Asabiti ta nufa, ta biya dukkanin kuɗin da aka lissafa.

Wurin Yakumbo ta dawo, don dama ita tabar ma Ahamad.

Ƙarya ta shirga mata akan wani bawan Allah ne ta nemi taimako wurinshi, Yakumbo ta ce “Allah Sarki, na Allah basu ƙarewa.” 

Shi kuwa Ahamad cikin ikon Allah ya fara samun sauƙi, kafin a sallame shi kuma Jikan Yakumbo yazo da nufin su koma.

Yakumbo ta so su tafi da Jummai, toh rashin lafiyar Ahamad ta hana, sai dai suka yi mata kwatance tare da bata Number waya.

Bankwana suka yi, har jikan Yakumbo ya mata Alkhairi mai yawa.

Bayan cikar Ahamad da sati biyu aka sallame su, aikuwa tana komawa gidan mai gidan ya ce ta fita, saboda an gaya mashi tana zuwa gidan abinci aiki, shi kuma ba zai ba karuwa mafaka ba, a can baya ma arzikin su Yakumbo ta ci.

Hakan kuwa ya ƙara tunzura ta tare da faɗin “A can baya ni ba karuwa ba ce, amma a yanzu na shirya zama, domin samun farincikina, tunda babu sauran masu tausayi a duniya.”

Gaba ɗaya ta kwase kayanta daga gidan ta nufi GRA gidan wannan mutumin.

Sadda ta je mutumin bai nan, sai dai wannan mata.

Ba’a daɗe ba kuwa sai gashi ya dawo, tamkar wanda aka yi ma bushara saboda murnar ganin Jummai.

Kwantar da Ahamad ta yi wirin wannan mata, sannan suka nufi sama, haƙuri ta bashi akan rashin dawowarta, ya ce ai ba komai.

Alaƙa ce mai ƙarfi ta ƙullu a tsakanisu, a yadda yake jin daɗin hulɗa da ita ne yake sakar mata kuɗaɗe.

Cikin ɗan ƙanƙanin lokaci gyagije a gidanshi, don ya ɗauke ta tamkar mata. Ahamad ma yayi ɓul-ɓul abin sa. Gida kuwa tuni ta manta da shi, saboda ta san ko ta koma baƙinciki ne, nan kuwa rayuwa take mai cike da ƴanci.

Idan kaga yadda Jummai ta zabure sai ka riƙe baki, domin da bakinta take gazgata waɗannan mata da ta haɗu da su a wurin neman aiki.

Cikar Ahamad da shekara ɗaya ne suka fara fita ƙasar waje, domin taya shi murna

Uk suka je in da suke ta shan yawon su a can.

Suna cikin tafiya a cikin jirgin ƙasa ne ta ji wata irin faɗuwar gaba, wadda ta samo asali ne daga shaƙar turaren Habeeb da ta yi.

Take damuwa ta bayyana a fuskart ɗan kwantowa ta yi ajikin mutumin, “Mene ne” ya tambaye ta.

“Bana jin daɗi ne” ta faɗa tare da shige mashi, a yadda yake lallaɓa ta kai kace matar shi ce.

Shi kuwa Habeeb yana duƙe da kansa, a seat na gaba, ƙasan ransa yana jin ƙaruwar faɗuwar gaba.

Ƴar tafiya kaɗan jirgin ya ƙara suka isa tashar jirgin, Habeeb na zaune don ya kasa tashi daga inda yake, yaro mai kama dashi ya gani saɓe a hannun wata, wadda idan ka tambayeshi wacece, toh zai ce Jummai ce.

Faɗuwa gabanshi ya cigaba da yi, kamar wanda aka tsikara ya bi bayansu, duk da zuciya na faɗa mashi ba Fatima bace, saboda bata yi wayewar wannan ba.

Juwa ce ta kwashe shi lokacin da suka yi ido huɗu da Jummai, sadda mutumin ya riƙo mata hannu.

Itama ta matuƙar firgita da ganinshi, amma sai ta ɗauke kai mutumin ya ja ta suka tafi.

“Fateemah!” Habeeb ya faɗa da ƙarfi, don ƙafarshi ma bata ɗaukarshi.

Ƙin juyowar da ta yi ne ya sa shi bin Ahamad dake kafaɗarta da ido.

<< Ko Ruwa Na Gama Ba Ki 14Ko Ruwa Na Gama Ba Ki 16 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.