Skip to content
Part 17 of 22 in the Series Ko Ruwa Na Gama Ba Ki by Hadiza Isyaku

Cikin amincin Allah Alhaji Mainasara ya isa a garin Katsina. Inda tun a Welcome to Katsina ya samu tarbar ɗaya daga cikin yaran Alhaji Muhammad, wato mahaifin Isma’il, domin Alhaji Mainasara bai san garin Katsina sosai ba, asalima wannan shi ne zuwansa na biyu a garin.

Kai tsaye Unguwar GRA suka nufa, a gidansu Isma’il ɗin.

Da isar su katafaren gidan aka nufi babban falon da ake tarbar baƙi da shi, wanda kayan alatun da aka ƙawata falon da shi za su fahimtar da kai cewa mutanen gidan na da alaƙar jini da sarauta, domin manyan hotunan sarakuna ne manne a kowace kusurwa ta bangon falon.

Alhaji Mainasara ya shaida halin Katsinawa na kara da karamci, domin ya samu kyakkyawar tarba a wurin Alhaji Muhammad da iyalansa, kai ka ce dama sun daɗe da sanin juna.

Saboda ɗaya bayan ɗaya yaran gidan suka riƙa kawo mashi gaisuwa, shi kuma yana amsawa tare da sanya musu albarka.

Yawan yaran da kuma tarbiyyarsu ce ta birge Alhaji Mainasara, kasantuwar sa mutum mai son ƴaƴa, bayan yaran duk sun fita ya dubi Alhaji Muhammad da suke zaune tare a kan three-seater ya ce “Masha Allah, Allah ya albarkaci Zuri’a Alhaji”.

Sai da Alhaji Muhammad ya yi ƴar dariya sannan ya ce “Amiin ya Allah”, domin yana jin daɗin irin wannan addu’a.

Wata gaisuwar suka sake yi, sannan Alhaji Muhammad ya jajanta mashi lamarin hanya, kasantuwar kowa ya san yadda tsaro ya taɓarɓare a yanzu, tafiya idan ba dole ba, babu mai son yin ta.

Da wannan nake cewa Allah ka kawo mana ƙarshen waɗannan masifun Amiin

Suna cikin maganar hanyar ne aka fara kiran sallar Azuhur a masallacin gidan. Fitowa suka yi tare da yin alwalla suka nufi cikin masallacin domin gabatar da sallah.

Sadda suka dawo daga masallacin har an kawo lafiyayyen abinci a dining.

Iso Alhaji Muhammad ya yi mashi a dining area, ko kusa Alhaji Mainasara bai yi fulako da wannan abinci ba, don ya ci ya ƙoshi, tare da yaba ma waɗanda suka yi girkin.

Alhaji Muhammad kuwa ya ji daɗin hakan.

Bayan sun gama cin abincin suka koma falo tare da tattauna abin da ke tafe da Alhaji Mainasara.

Alhaji Muhammad ya dube shi cike da damuwa ya ce “Alhaji ban ji daɗin  labarin ƴarku da na ji a wurin Isma’il ba, musamman da aka ce tare take da wancan shaiɗanin mutumin”.

Alhaji Mainasara ya ce”Toh ya za’a yi, yaran zamani ne sun faye son zukatansu, addu’a ce kaɗai zata gyara mana su”.

“Toh Allah ya shirya mana zuri’a” Alhaji Muhammad ya faɗa, domin shi ma yana da tabon yara har biyu, mace da namiji.

Bayanin waye Alhaji Lawwali, Alhaji Mainasara ya nema a wurin shi.

Alhaji Muhammad ya ce “Kafin ka sani yana da kyau, mu fara samun tabbacin idan da gaske suna tare tukunna, kada mu zarge shi akan abin da ta yiwu ba shi ne ba, duk da zai iya aikata fin abin da ake zarginsa”

Faɗuwa gaban Alhaji Mainasara ya fara yi domin akwai alamun ban tsoro a tare da Alhaji Lawwali. Tabbas ya san zai iya zama dole ga  Jummai ta kauce hanya tunda har tabar gida.

Toh amma bai yi tsammanin abin ya kai haka ba, “Ok ba damuwa Alhaji, a bincika tukunna” In ji Alhaji Mainasara.

Tambayar Alhaji Muhammad ya yi “Toh ta ya zamu bincika Alhaji, ni dai ka ga ban san ko ina a garinnan ba”

Alhaji Muhammad ya ce “Kada ka damu, Insha Allah zamu taimaka har Allah ya sa ku samu ƴarku, yanzu zan sanya a kira Alhaji Lawwalin anan”.

Godiya Alhaji Mainasara ya yi mashi akan taimaka mashi da ya ce zasu yi.

Waya Alhaji Muhammad ya ɗauka tare da kiran ɗaya daga cikin yaran gidansa, cewar a samo mashi number Alhaji Lawwali yanzu.

Ba da daɗewa ba kuwa sai ga wanda aka kira ya shigo falon, da alamun ya samo number, cikin girmamawa ya gaishe su tare da bada number ga Alhaji Muhammad, sannan ya fita.

Number Alhaji Lawwali, Alhaji Muhammad ya sanya a wayarsa tare da kira, sai da ta kusa tsinkewa sannan ya ɗaga kiran tare da tambayar wanene.

“Alhaji Muhammad ne maƙwanbcinku” Alhaji Muhammad ya ba shi amsa.

Sanin a kusa da su ba wani Alhaji Muhammad sai shi ya ce cikin girmamawa “Ranka ya daɗe kai ne da kira na?”.

Alhaji Muhammad ya ce “Ƙwarai ni ne, don Allah idan ba damuwa ina neman ka a gidana”.

Daga can ya ce “Ok Insha Allah yanzu zan shigo” kasantuwar yana cikin unguwar.

Alhaji Muhammad ya ce “Ok toh sai ka shigo”

Katse kiran ya yi tare da duban Alhaji Muhammad da ya yi zugum alamar ya faɗa duniyar tunani, ce masa ya yi “Ka ji muryarshi kamar mutumin kirki, amma da an bincika halinsa kare ba ya ci”.

Murmushi Alhaji Mainasara ya yi tare da faɗin “Ai da yawan mutane zahirinsu ya sha banban da baɗininsu, shi yasa sai su yi ta cuta a bayan ƙasa, ba tare da an gane sune ba”.

Alhaji Muhammad ya buɗe baki zai yi magana sallamar yaronsa ta katse shi, dubansa ya yi tare da tambayar sa “Lafiya?”.

Kansa na ƙasa ya ce “Ranka ya daɗe Alhaji Lawwali ne ya iso”.

Kai ya jinjina tare da faɗin “A shigo da shi”.

Ƙofar shigowa falon Alhaji Muhammad ya kafe da ido, cikin ransa kuwa ƙagare ya ke ya ga Alhaji Lawwali.

Faɗuwa gaban Alhaji Mainasara ya yi a lokacin da Alhaji Lawwalin ya shigo falon da sallama, domin ko kusa bai da siffar mutanen kirki.

Alhaji Lawwali, ma sai da gabansa ya faɗi lokacin da suka haɗa ido da Alhaji Mainasara, cike da girmamawa ya miƙa musu hannu suka gaisa, daga bisani ya zauna ƙasa tare da sadda da kansa ƙasa, cikin ransa yana tunanin inda ya san Alhaji Mainasara.

Muryar Alhaji Muhammad ce ta katse mashi tunani tare sa shi ɗago kai ya dube shi a lokacin da yake faɗin “Na san dai ka yi mamakin kiran ko?”.

Alhaji Lawwali ya ce “Eh gaskiya ranka ya daɗe” don tunda yake bai taɓa doguwar magana da shi ba.

Alhaji Muhammad ya ce “Na san da haka dama, magana ce muke son yi da kai, da fatan zaka bamu haɗin kai”.

Alhaji Lawwali ya ce “Insha Allahu Ranka ya daɗe”.

Sai da Alhaji Muhammad ya kafe shi da idanu sannan ya ce “Ka san dai kowa ya san kai waye a garin nan, da kuma halinka, don haka ne na kira ka domin jin ina yarinyarmu da aka ce an ganku tare”.

Ƙuri su duka suka yi mashi, tare da kasa kunne don jin me zai ce.

Ɗan shiru Alhaji Lawwali ya yi, daga bisani ya ɗago idonsa ba ko kunya ya ce “Wace a ciki ranka ya daɗe, don suna da yawa yaran”.

Amsar da ya bada ta ba Alhaji Mainasara mamaki, don a zatonsa zai yi musun abin da ake zarginsa, amma sai ya ji saɓanin haka.

“Sunanta” Alhaji Muhammad ya tambayi Alhaji Mainasara.

Cike da ƙunar zuciya ya ce “Jummai ne sunanta”.

Da hanzari Alhaji Lawwali ya ɗago kansa tare da duban Alhaji Mainasara, lallai ba wannan mutumin ne ya sani ba, Habeeb ne da kuma Ahamad ya sani, wanda tsananin kamarsu da shi ne yasa shi tunanin ya sanshi, kuma ko shakka babu akwai dangantaka mai ƙarfi a tsananisu.

Maida dubanshi ya yi ga Alhaji Muhammad “Fateema kenan Ranka ya daɗe”.

Alhaji Mainasara ya karɓe da “Eh ita fa, tana goyon yaro ma”.

“Toh wallahi yanzu bama tare, tun satin da muka dawo daga UK ta gudu daga gidana, yanzu haka nemanta nake, don ko wayarta ma bata shiga”.

Ido Alhaji Mainasara ya rumtse, ƙasan ransa yana jin wata irin ƙuna “Yanzu rayuwar da Jummai ta zaɓa kenan, wadda kuma ɗana ne sanadi” gwauron numfashi ya sauke tare da duban Alhaji Muhammad lokacin da ya ke ƙarya ta Lawwali akan suna tare da Jummai, kawai dai ya ɓoye ne.

Rantsuwa Lawwali ya riƙa yi tare da faɗin “Wallahi iya gaskiyar da na faɗa maka kenan Ranka ya daɗe, wallahi bama tare, nima na sanya a nemo mani ita”.

A yadda yake ta rantsuwa ne ya sanya su ɗan yadda da shi, asalin in da suka fara haɗuwa shi da Jummai aka tambayeshi.

Ya faɗa musu a gidan abinci ne, sai kuma gidansu na ƴan gudun hijira.

“Kamar ya gidansu na ƴan gudun hijira”? Alhaji Mainasara ya tambaye shi.

Ya ce “Toh ta dai ce itama ƴar gudun hijira ce, iya abin da na sani kenan”.

Kamar Alhaji Mainasara zai yi kuka ya ce “Ok”, tunanin halin babu gaira babu dalilin da Jummai ta sanya kanta ya shiga yi, ko da yake uwarta ta ja mata, domin da ta yi haƙuri da ƙaddara da ƴarta bata shiga garari ba.

Alhaji Muhammad ne ya ce mashi “Toh yanzu ya za’a yi Alhaji ko kana da wata tambaya da zaka yi mashi, ka ji dai yadda ya ce”, ya ce “Eh toh akwai, kuma dai bai wuce ya yi mana kwatancen gidan gudun hijirar ba”.

Kwatancen ya yi musu, duk da ya san bata can ɗin, amma tunda sun nema zai basu.

“Toh mun gode, kana iya tafiya Alhaji”.

Miƙewa ya yi tare da miƙa musu hannu da nufin yin sallamar bankwana. Hannunsa Alhaji Muhammad ya riƙe tare da faɗin “Nasan zaka nemi Fateema kai ma, toh kashedin ka da yi mata wani abu, domin mun san ɓoyayyen halinka wanda baka tunanin mun sani”.

Wani irin mugun kallo suka yi ma juna, mai ɗauke da fassarori daban-daban.

Bai ce komai ba ya zare hannunsa tare da miƙa ma Alhaji Mainasara suka yi sallama, “Na wuce” ya faɗa cikin kaushin murya, domin zuciyarsa ta taɓu akan abinda Alhaji Muhammad ya ce mashi, kuma wallahi ko duniya zata tashi ba wanda isa ya hana shi aiwatar da abin da yayi niyya akan Jummai.

Da ido suka raka shi har ya fice falon, Alhaji Muhammad ya ce ma Alhaji Mainasara “Wancan da kake gani mugu ne, zargin tsafi ake yi mashi, duk yarinyar da ya fara hulɗa da ita, toh ko dai ya bada ta ga matsafa, ko kuma ta zama ƴar ƙungiyarsa”.

“Inna li Llahi wa inna ilaihi raji’un” bakin Alhaji Mainasara ta shiga furtawa, domin yaga alama, hankali tashe ya cigaba da magana “Yanzu ɗayan biyu kenan akan Fateema, ko dai ta zama ƴar ƙungiyarsu, ko kuma tana akan tarkonsa, idan har zargin da ake masa ya zama gaskiya”.

Alhaji Muhammad ya ce “Haƙƙun, amma tunda basa tare bani tunanin zata zama ƴar ƙungiyarsu, sai dai su kafa mata tarkon bayar da ita”.

Hannu Alhaji Mainasara ya dafe kai dashi tare da lumshe ido saboda tsabar tashin hankali. Alhaji Muhammad ya lura da yanayinsa, cewa yayi “Insha Allahu wannan ma ba zai yiyu ba, nemanta za’a yi tun kafin su cutar da ita”.

Tsara yadda za’a neme ta suka yi, gidan ƴan gudun hijirar aka fara zuwa, maƙwabtan suka ce tunda ta kawo kaya bata sake dawowa ba, Alhaji Mainasara ya ce “Toh don Allah idan ta dawo ku ce ta je gida ana nemanta”.

Toh suka ce, ya zaro kuɗi ya basu.

Bincike aka shiga yi gidajen masu zaman kansu da aka sani, hadda hotels duk an je, amma ba’a same ta ba, numberta ma da Alhaji Lawwali ya basu bata shiga. 

Sai da Alhaji Mainasara yayi sati a katsina, amma ba Jummai ba alamarta.

Shirin tafiya ya yi.

Alhaji Muhammad ya bashi magana akan damuwar da ya gani ƙarara a tare da shi, tabbatar mashi da zasu cigaba da neman ta suka yi. Godiya ya yi musu bisa ga karamcin da suka yi mashi, sannan ya hau motarsa ya nufi garinsu.

Da baƙinciki  ya koma gida.Tuni Uwani ta san ba’a ga Jummai ba don suna waya, amma bata san hatsarin da take ciki ba, sai bayan dawowarsa.

Kuka sosai ta shiga yi, ta ce “Duk Yaya Asabe ce ta ja mata, da ta yi haƙuri da ƙaddara, da Jummai bata shiga wannan hali ba”.

Alhaji Mainasara ya ce “Kafin ita Habeeb ne, don haka Allah ba zai bar shi ba shima”.

Uwani ta ce “Ka dena faɗin haka Alhaji, duka ƙaddara ce, Allah kuma ya kawo mana ƙarshen ta”, “Amiin” ya ce tare da ja mata kunne akan kada ta faɗa ma Asabe halin da ake ciki, don dama ko zuwa Katsinan ba’a faɗa mata ba, saboda gudun wannan, ƙarshe kuma damuwar ta zame mata sabuwa.

Shi kuwa Alhaji Lawwali tuni sun fara shirin shiga meeting shi da sauran matsafa ƴan uwansa, babban gidan da suke tsafin.

Gida ne da aka gina a wajen gari, wanda idanun mutane baya gani saboda tsafance shi da suka yi.

Zaune suke a cikin wani wani baƙin daji ƙarƙashin wata itaciya mai ƙayoyi, a ɓangare ɗaya kuma suna sanye da jajayen kaya su duka mazansu da matan, fuskokinsu kuma shafe da wani farin abu, wanda ya fito da zahirin idonsu da ke shafe da wani baƙin kwalli.

Wannan kwalli shine ke bayyana musu abin da ido bai gani, asalima ba daji bane suke

ciki, ɗaki ne, wanda da zaka shiga ba abin da zaka gani sai jeren kayan ɗaki.

Hajiya mai gidan abinci ce zaune akan wata kujera mai siffar jemage, wadda kuma ita ce shugabarsu.

Su kuma suna zaune a ƙasa suna fuskantar ta, tsakiyarsu kuma wuta ce, sai kuma ƙoƙuna cike da jini.

Wata irin tsawa ta daka tare da karanto wasu ɗalasimai na tsafi, suma sauran cigaba da karanto abin da take karantawa suka yi.

Sai da suka ɗauki mintuna suna wannan karatu, wanda su kaɗai suka san ma’anarsa, daga bisani suka fara meeting ɗin.

Farkon abin da suka fara tattaunawa shine, yadda aka yi aka san abin da suke aikatawa, tare da toshe duk wata kafa da za’a sake gane musu.

Bayan sun gama wannan kuma, Hajiya mai gidan abinci ta ce “Abu na biyu da ya kawo mu nan shi ne, yaran da muke son sawa a ƙungiya, ɗaya ta gudu, ɗayar kuma ta yadda, har ma ta bada ƙanenta, yanzu wadda ta gudun za’a nemo don mun fi buƙatar ta”.

Nuna Alhaji Lawwali ta yi ta ce “Lawwali kai ne kurwarta ke kusa da kai,  don haka ka haska mana yanzu mu ga inda take”.

Jinin dake kusa da ita ta ɗiba tare da watsawa a cikin wutar, take wata tsuwwa ta fara fita a ciki, tare da game illahirin wurin.

Jinin shima Alhaji Lawwali ya ɗiba ya watsa, sannan ya saki wani baƙin abu da ke hannunsa na hagu a cikin wutar.

Jummai ce ta bayyana a cikin wutar, tare da wani matashi suna tafiya a cikin mota.

Wani irin kishi ne ya turnuƙe Alhaji Lawwali, musamman yadda ya ga tana kwasar tariya, wanda tunda yake bata taɓa yi mashi irin ta ba.

Ido ya ƙwalalo tare da fasa ihu, lokaci ɗaya kuma ya sanya hannu a wutar zai birkice motar.

Dakatar da shi ɗaya cikinsu ya yi “A raye muke buƙatar ta”.

Huci Alhaji Lawwali ya kama yi, ƙasan ransa yana jin kamar ya kashe kansa don baƙinciki

Hajiya mai gidan abinci ta ce masa “Ka yi gaugawar kawo mana ita, tun kafin ta fara bamu matsala.”

Cikin tsananin fushi ya ce”Za’a nemo ta ba da daɗewa ba shugaba”.

Cigaba da aiwatar da abin da ya tara su suka yi, basu tashi ba sai da suka kashe mutane goma, wasu ta hanyar sanya su hatsarin mota, wasu kuma ta hanyar rashin lafiya.

*Shi ya sa ake son duk sadda mutum zai hau abin hawa ya yi addu’a, don akwai sheɗanun da aikin su ne sanya hatsari a hanya, domin muguwar manufa ta iyayen gidansu bokaye da matsafa, da fatan Allah ya kare mu da kariyarsa Amiin*

Zuciyar Alhaji Lawwali kamar zata buga lokacin da suka gama meeting ɗin. 

Kai tsaye Hotel ɗin da Jummai ta ke ya nufa, don yana ganin duk wani motsi na ta

Ita kuwa mota na aje ta nufi cikin hotel ɗin da sauri, Muryar Alhaji Lawwali ta ji a bayanta yana faɗin “Ranki shi daɗe Jummala.”

Wata irin faɗuwa gabanta ya yi, don kwana biyu tana mafalkin yana bin ta da gudu a cikin wani daji, hakan ne ya ƙara mata tsanar sa a ranta.

Fuska kici-kicin ta juyo tare da saka idanunta masu ɗauke da tsoro a cikin nasa.

Murmushi ya yi wanda iyakar sa fuska ya ce “Na yi kewar kyakkyawar fuskar nan ta ki Jummy.”

Kasa magana ta yi, don gabanta ta ke jin yana wata irin faɗuwa, sai dai ta jefe shi da mugun kallo.

Matsowa ya yi kamar mai shirin shiga jikinta ya ce “Ke kuwa fushi kyau yake miki, ki zo mu koma yadda muke, ko fushin ne ki riƙa yi mani ina jin daɗi.”

Baya ta ja tare da yin magana a fusace “Ka fita idona Alhaji, wallahi yadda na bar cikin uwata, haka na barka.”

Ahamad kuwa ƙara ya fasa, tamkar wanda ke ganin baɗinin Alhaji Lawwali.

“Don Allah laifin me na yi maki Jummy”, ya tambaye ta kamar zai yi kuka, don har a ƙasan ransa yana sonta, sai dai kuma buƙatar tsafinsa ta fi son da yake mata.

Ce wa ta yi “Baka yi mani komai ba”. 

Magiya ya kama yi mata, amma ta ƙiya, ƙarshe ta juya ta shige cikin Hotel ɗin, ƙasan ranta kuma tana ta zagin shi.

Wani mugun kallo ya bi bayanta da shi, tare da fara baƙin aikinsa a take.

Domin kuwa tana shiga ta faɗa banɗaki, da ga can ciki ta ji kamar motsin mutum a ɗakinta, da hanzari ta fito don a zaton ta wani ne ya shigo. Sai dai tana dubawa ta ga ba kowa, Ahamad ma har ya yi bacci, baki ta taɓe tare da komawa cikin banɗakin ta yi wanka.

Da ddare kuwa dama tana da sarar raba dare tana kallo. Yau ma kamar kullum sai da dare ya raba sannan ta kwanta, aikuwa bacci ya fara fizgarta kenan ta ji mutum kwance a bayanta ya ƙadaddabe ta.

Firgigit ta falka tare da tashi zaune, gabanta na wata irin faɗuwa ta shiga dube-dube, don dama a kunne take barin fitila.

Lallai abin da ta ji da gaske be ba mafalki ba, amma kuma babu kowa a saman gadon sai Ahamad.

Zuciyarta cike tsoro ta fara karanta addu’oi kwanciya bacci, wanda rabon da ta yi su har ta mance, ƴar nutsuwa ce ta shige ta a lokacin da zuciya ta ruwaita mata da mafalki ne ta yi, kuma tunda ta yi addu’a shikenan.

Can kuma gab da Asuba ta ji a cikin bacci kamar ana kiran sunanta, a hankali ta fara buɗe idanunta tare da duban mutumin da ke tsaye a kanta, wanda ko kusa bata ganin fuskarsa saboda ya lulluɓata da wani baƙin ƙyalle.

Gaba ɗaya ta buɗe idanun don tabbatar da abin da take gani idan mafalki ne. Ɓat mutumin ya ɓace ma ganinta, a gigice ta tashi zaune tare da dafe gaba, cikin ƙanƙanin lokaci zufa ta rufe ta, duk kuwa da sanyin AC ɗin dake akwai.

“Wai me ke faruwa dani ne?” ta tambayi kanta, don ta fara ƙaryata mafalki ne abin da take gani.

Kiran assalatun da aka fara ne ya fara rage mata tsoro, don yanzu mutane za su fara fitowa.

Taƙarƙarawa ta yi zata shiɗo daga kan gadon da nufin yin alwalla ta ji kamar an riƙe ta, bacci ne a take ya cika mata ido, da yake ba damuwa da sallah ta yi ba, sai ta koma ta kwanta.

Bacci mai daɗin gaske ne ya yi awon gaba da ita, ba ita ta falka ba sai bakwai na safiya, shima Ahamad ne ya tada ta da kuka. Ko kusa bata damu da makarar da ta yi ba, saukowa suka yi ita da Ahamad suka nufi banɗaki.

Wanka ta yi mashi sannan ta fiddo shi, komawa ta yi tare da wanka da alwalla ta fito.

Mamaki ne ya kama ta aokacin da hancinta ya shaƙi ƙamshin turaren da ta taɓa fesawa a gidan Alhaji Lawwali.

“Oh, ko wa ke da irin wannan tureren” ta faɗa a ranta, don a zatonta daga waje ne ƙamshin ya shigo.

Sallah ta gabatar, sannan ta shirya musu ita da Ahamad, breakfast ta yi magana aka kawo, suna gamawa ta ɗa ɗauki waya ta shiga facebook a sabon account ɗinta mai suna Ummu Ahamad, wanda kuma Habeeb na cikin friends ɗinta, ba tare da ya san ita ce ba.

Wall ɗinsa ta shiga, aikuwa ta ci karo da sabon cover photo ɗin da ya chanja, ƙuri ta yi ma photon tare da sakin wani shu’umin murmushi.

Domin heartbroken logo ne a jikin photon, a ɓangaren dama an sanya harafin *F*, a na hagun kuma an sanya harafin *H*, sai ƙasa kuma an rubuta “World seems depopulated”.

Reacting photon ta yi da sign na Wow saboda photon ya ɗan birge ta.

Ta je zata yi comment kenan ta ji kanta ya sara, fasa comment ɗin ta yi, sai ma ta fito daga facebook ɗin gaba ɗaya ta aje wayar.

A hankali wannan ciwon kai ya yi ta shigar ta. Cikin ɗan lokaci ta ji kamar ana sara mata wani abu a cikin kan.

Zamewa ta yi ta kwanta akan sofa, tare da dafe kan, zazzaɓi ne mai zafi kuma ya rufe ta, kan kace me ta fara rawar ɗari.

Kan gado ta koma tare shigewa cikin bargo saboda haƙoranta har gugar juna suke yi.

Ahamad kuma ta bar shi nan a tsakar ɗaki yana ta wasa.

Wayarta ce ta fara ruri, da ƙyal ta iya fiddo kanta cikin bargon tare da duba wayar ta ga mai kira.

Ganin Faisal ne ya sa ta ɗaga wayar, don shi ne ke ɗawainiya da dukkan buƙatunta, ita kuma tana biyansa da kanta, duk kuwa da milliyoyin kuɗin da Alhaji Lawwali ya zaƙire mata account da su.

Daga can ya ce “Hajjaju yau nake son komawa, kin shirya na zo mu yi bankwana”

Muryarta ƙasa-ƙasa ta ce “A’a”,  tambayarta ya yi “Saboda me?”

“Bani da lafiya” ta bashi amsa a shagwaɓe.

Cike da damuwa ya ce “Oh sorry, bari in zo mu tafi asibiti”.

“Toh” ta ce tare da katse kiran.

Ba’a daɗe ba sai gashi ya zo, har a lokacin kuma tana kwance a kan gado.

Kan gadon ya hau tare da yaye bargon a hankali, ba ƙaramar firgita ya yi da irin ƙyarmar ɗarin da take ba, hannunta ya kama ta tashi zaune tare da jingina baya da kan gadon.

“Sannu” ya ce, ta ɗan buɗe ido alamar yauwa.

“Asibiti zamu je, don baki da lafiya sosai”. 

Yana faɗin haka ya taimaka mata ta shiɗo a kan gadon.

Hijabinta da takalma ya miƙo mata, sannan ya ɗauki Ahamad suka fita.

Wata private clinic dake cikin gari suka je, cikin ikon Allah ta samu ganin likita.

Ƴan gwaje-gwaje aka yi mata, aka ce bayan kwana biyu ta zo ta karɓi result.

Saida suka yi ɗan yawo a gari sannan suka dawo.

Godiya ta yi ma Faisal, don yana da kirki sosai.  Sai dai matsalarsa bin mata, wanda kuma matsala ce mai girma.

Ya ce “Ba komai, ai ke ta daban ce, bana jin zan iya biyan ki irin daɗin da kike jiyar da ni”.

Murmushi kawai ta yi, ya sake cewa “Na ma fasa tafiyar yau, anan zan kwana, gobe sai in tafi”., da yake aiki ya kawo shi a Katsina, duk ranar Jumu’a da yamma yake komawa garinsu.

Jummai bata cika son maza na kwana a wurinta ba, amma a yau murna ta yi da

kwanan Faisal, don abin da ta gani a daren jiya ya yi mata tsaye a rai.

Anan ɗin ya kwana, duk irin kulawar da ta dace aba mace, sai da ya bata, kai ka ce matarsa ce.  washe gari kuwa ta samu sauƙi sosai.

Hakan ne ya bashi damar karɓar Allah ya kiyaye a wurinta sannan ya tafi.

Asabe kuwa hakanan sai ta ji gabanta na faɗuwa.

Abin da ranta ya bata ciwonta ne ke son motsawa, don haka tana ganin abin nata gaba-gaba ta yi saurin zuwa Asibitin birni, don Dr. Ameer ya ce da ta ji ba daidai ba ta koma.

Da kansa ya duba ta, sai dai bai ga komai ba, ko hawan jinin ma lafiya lau bai hau ba.

Sosai ya tausaya mata akan halin da take ciki, domin kullum ƙara lalacewa take.

Tambayar ta ya yi “Kina jin juwa idan faɗuwar gaban ta zo”.

Ta ce “A’a”.

Wasu magunguna ya ɗora ta a kai, sannan ya haɗa ta da Dr. Misau, domin shi an yi mashi transfer, kuma yau ne yake shirin komawa can ɗin.

Ya ce “Duk abin da na iya, toh Dr Misau zai yi maki mafiyin sa”.

Asabe ta ji ba daɗin tafiyar Dr Ameer, domin ganin sa kaɗai yana rage mata damuwa, saboda kyawawan halayensa, musamman a kulawar da yake basu tun daga abinci da magani, sauƙinta ma ga Alhaji Mainasara da ke ta ƙoƙari shima.

Musayan number suka yi ita da Dr. Misau.

Da zata fito Dr. Ameer ya zaro dubu goma ya bata, tayi farinciki da kuma godiya.

Kai tsaye gidan Uwani ta dosa, da yake duk a gari ɗaya ne, sai dai akwai ɗan nisa a tsakaninsu da asibitin.

Da murna Uwani ta tare ta. Tunda suka gaisa Asabe ta yi Jugum.

Cike da damuwa Uwani ta ce “Menene kuma Yaya Asabe?” duk da kuwa ta san damuwar bata wuce a kan Jummai. 

Idanunta cike da ƙwalla ta ce “Uwani faɗuwar gaba ke damuna, ina ji a jikina duk inda Jummai take, toh tana cikin hatsari”. Da kuka ta ƙarasa maganar

Itama Uwanin kukan ta fashe da shi, ƙasan ranta tana jin wani irin tausayin ƴar’uwarta.

Haƙuri ta riƙa bata, tare da tabbatar mata da Jummai ba abin da zai same ta da yardar Allah.

Magana sosai ta riƙa bata, har ta yi shiru.

Hira suka yi tayi jefi-jefi, bayan lokaci kaɗan ta ce tafiya zata yi, saboda yara.

Kayan abincin da Alhaji Mainasara ya bada ne Uwani ta kwaso mata, Godiya ta ce ayi mashi, sannan ta kira mai napep ya kwashe su ita da kayan zuwa tashar mota. A cikin motar da ta shiga ne tayi kiciɓus da Hajiya Mairo a kusa da seat ɗin da zata zauna, kasa yadda da Hajiya Mairon ce ta yi har sai da ƙara kallonta. “Yo ina kuɗin ake zaune a motar haya”

Asaben ta faɗa a ranta, tare wucewa seat ɗin baya ta zauna

Hajiya Mairo kuwa duk kunya ce ta kama ta, hira suke da wata mata, amma tunda ta ga Asabe bakinta ya mutu, don abin kunya ne a ganta a motar haya.

Tunanin yadda Asabe ta lalace haka itama ta shiga yi, ƙasan ranta ta ce “Baƙin halinta ne ta fara girba”, gaba ɗaya ta manta da nata baƙin halin.

Haka suka yi ta sukar junansu a zuciya, har motarsu ta isa garinsu.

Cika da batsewa suka yi tayi tare da hararar juna a lokacin da suka fito motar, Hajiya Mairo da har yanzu fitinarta na rai ta ce “Aras can dai, a wannan karon ko da cikinwa kuma ƴar zata dawo?”

Asabe ta ji zafin maganar, amma da yake ta yi sanyi, sai ta juya mata ƙeya tare nuna kamar bata ji me ta ce ba.

A ɓangaren Jummai kuwa, kwana biyu na cika ta koma asibiti domin karɓar result tare da ganin likita.

Abin da likita ya faɗa mata ne ya ɗaure mata kai, domin ya ce ko Malayria bata ita, gashi ita kuma a yanzu ji take kamar ana jan ruwan jikinta.

A kan wani benci ta zauna tare da yi ma takardun ƙuri tana kallo, hakan ya ba Ahamad damar tafiya wurin wani yaro da zai kai shekara bakwai a duniya.

Ta ɗago da niyyar kiran Ahamad ɗin kenan, ta ga yaron ya kama hannunsa sun nufi wurin wata mata dake ta danna waya,

“Umma ga ƙane na samo, yanzu ba sai kin haifa mani wani ba”, yaron ya faɗa tare da tura mata Ahamad a gabanta.

Dariya mutanen wurin suka kama yi, matar na ɗagowa Jummai ta ga ai ma ta san fuskarta, sai dai ta manta inda ta santa.

Dariyar mata itama ta yi sannan ta ce “Da kyau Ammuna, Lallai ka hutar da ni”

Jummai na jin ta ce “Ammu” ta tuna a motar haya ne ta san ta, tasowa ta yi ta zo kusa da ita ta zauna

Cikin girmamawa ta gaida matar da ke ta dariya, bayan ta amsa ta ce “Amma Aunty baki gane ni ba ko”.

Yalwatacciyar fuskarta ta sa a cikin ta Jummai, tare da nazarin ko ta san Jummai.

kai matar ta girgiza tare da faɗin “Gaskiya ban gane ba”. 

Bayani Jummai ta yi mata a farkon inda suka fara haɗuwa a mota. Baki matar ta buɗe tana kallon su ita da Ahamad, cikin ranta kuma tana mamakin sauyawar su.

Jumman dake ƴar ƙauye, wadda a lokacin ba abin da ke fita a jikinta sai ƙarnin jego, amma ita ce yanzu da tunda ta zauna wurin ƙamshin turarenta ya baɗe ko’ina

“Kin chanja” matar ta faɗa tare da jawo hannun Ahamad, wanda a can baya yake kamar skeleton.

Murmushi Jummai ta yi, matar ta ce “Kun dawo nan da zama kenan”,  Jummai ta ce “Ai tunda na zo dama ina nan”.

 “Allah Sarki, toh ya maigidan”, don a zatonta Jummai na da aure.

Ɗan shiru Jummai ta yi, daga bisani ta ce “Ai bani da aure”.

Mamaki cike da matar ta ce “Ayya”.

Hira suka cigaba da yi, anan Jummai ta faɗa mata abin da ke damunta, da kuma yadda likita ya ce. Sosai matar ta jajanta mata.

Sannan ta ce “Akwai ƙanin mijina, babban likita ne, zan haɗa ki da shi sai ya ƙara duba ki”

Godiya Jummai ta yi mata, tare da karɓar address ɗin gidanta, da nufin gobe za ta shigo.

Shirin tafiya ta fara, aikuwa Ahamad da Ammu suka kafe akan basu rabuwa, da ƙyal aka samu aka raba su, ta hanyar yi musu alƙawalin gobe za’a kawo Ahamad a gidansu Ammu.

Washe gari wurin ƙarfe goma Jummai ta shirya, ta nufi gidan wannan matar a Layout, sai da ta shiga unguwar ma ta ga ashe ta san wurin. Lokacin da ta je neman aiki har ta ƙofar gidan ta wuce, amma Allah bai sa ta shiga ba.

Da fara’a matar ta tarbe ta, Ammu da Ahamad kuwa sai murna suke.

Falo suka zauna suka gaisa, sannan ta kawo mata ruwa da lemu.

“Ya jikin toh” matar ta sake tambayarta, ta ce “Toh ba’a cewa komai dai, don ko jiya ban yi bacci ba, sai in ji kamar ana shirin tashi da ni sama”.

Damuwa bayyane a fuskar matar ta ce “SubhanaLlah, Allah ya kawo sauƙi”.

Jummai ta ce “Amiin”.

“Na yi ma likitan da zan haɗa ki da shi magana, yanzu haka yana gidan, bari a kirawo shi”.

Ammu ta kira ta ce “Je ka wurin Uncle ka ce ina kiran sa”.

Hannun Ahamad ya ja suka tafi, ko minti biyu ba’a yi ba sai gashi ya shigo.

Ras! Gaban Likitan da kuma na Jummai suka faɗi, domin sun shaida Juna, cak ya tsaya a inda yake a lokacin da ita kuma ta miƙe tsaye. 

“Jummai” ya faɗa tare da nuna ta da yatsa.

“Dr. Ameer” ta faɗa a ranta, ɓangare ɗaya kuma jikinta na ta kyarma.

 Gaba ɗaya sun sanya matar a duhu, miƙewa ta yi tare da faɗin “Kun san juna ne?”

Kai Ameer ya ɗaga sannan ya yi magana cikin fushi, domin suturar dake jikin Jummai kaɗai ta tabbatar mashi da zaman kanta take “Ita ce yarinyar da nake baki labari Aunty, kin ganta nan ta zaɓi farincikinta fiye da na mahaifanta”

Wani irin kallo matar ta jefi Jummai da shi domin ta san komai a kan ta,  wanda kuma wannan kallo sai da yasa hantar cikin Jummai kaɗawa.

Kyarma ta kamayi tare juyawa tana shirin ficewa a falon.

Tsawa Ameer ya daka mata tare da faɗin “Gidan ubanwa kuma zaki” ba arzki ta tsaya don ta tsorata da yanayin Ameer, ashe dama yana da fushi irin haka…?

Maman Mu’azzam

<< Ko Ruwa Na Gama Ba Ki 16Ko ruwa Na Gama Ba Ki 18 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.