Skip to content
Part 19 of 22 in the Series Ko Ruwa Na Gama Ba Ki by Hadiza Isyaku

Ƙuri Alhaji Mainasara ya yi ma jikin Habeeb yana son gane idan ya na motsi, lokaci ɗaya kuma idanunsa na fitar ƙwallan tsoro da firgincin rasa ɗansa, domin ba inda jikin Habeeb ke motsawa, sai a medical monitor ne kaɗai zaka iya fahimtar yana da rai.

“Allah ka tashi kafaɗun ɗana” ya faɗa, tare saka hannunsa cikin na Habeeb dake ɗaure da drip.

Tunanin lalurar da ta jefa Habeeb cikin wannan  hali ya shiga yi, wanda har aka turo ƙofar ɗakin aka shigo bai sani ba.

Sai da wanda ya shigo ɗin ya zagaya tare da gyara ma Habeeb Oxygen ɗin dake maƙale a hancinsa sannan ya lura da mutumin.

Kallon mutumin Alhaji Mainasara shiga yi, sanye yake cikin lab coat, idanunsa kuma na cikin siririn farin glass wanda ko da mutumin bai taɓa Habeeb ba, toh zaka iya kiran sa da Doctor, don komai na jikinsa ya nuna.

Gyara ma Habeeb kwanciya mutumin ya yi, wanda har a lokacin idon Alhaji Mainasara na kansa.

Da fara’a ya zagayo wurin Alhaji Mainasara tare da yin sallama.

Amsa sallamar Alhaji Mainasara ya yi, a lokacin da hannayensu ke cikin na juna.

Ƙara faɗaɗa fara’arsa ya yi domin yana ji a jikinsa Alhaji Mainasara ne mahaifin Habeeb, cewa ya yi,

“Sunana Umar Mahamud, ni ne kuma Doctor ɗin da ya ke kula da Habeeb.”

Mamakin hausar da ya yi ce ta kama Alhaji Mainasara, domin ko kusa bai kama da hausawa, sannan kuma ba bature bane domin bai kama da su, zaka iya kiran sa Balarabe, shima irin na Sudan ɗin nan masu sirki da baƙi.

Murmushi Alhaji Mainasara ya ƙaƙaro tare da faɗin “Masha Allah Dr, Allah ya yi jagora.”

“Amiin” Doctor ɗin ya faɗa, lokaci ɗaya kuma idanunsa na kan medical monitor yana duba yadda bugun zuciyar Habeeb ke tafiya.

Ƙagare Alhaji Mainasara yake ya ji me ye sanadin shigar Habeeb cikin wannan hali, don haka ne ma ya katse ma Doctor nazarin halin da Habeeb yake ciki da faɗin.

“Doctor, don Allah wane irin ciwo ne ya samu ɗana?”

Ajiyar zuciya Doctor Umar ya sauke, don a yanzu haka numfashin Habeeb duk da Oxygen amma bai tafiya daidai, sakamon jikinsa yaƙi karɓar maganin da aka ɗora shi a kai.

“Ciwon zuciya ne mai tsanani ya kama shi, wanda sakamonsa za’a a yi masa aiki a zuciyar, muddin dai bai falka ba, domin a yanzu yana akan magani”.

Ido Alhaji Mainasara ya lumshe, tare da matse ƙwallan da suka cika masa ido, “Yaushe ake sa ran yi mashi aikin?”

“Nan da one week Insha Allah” Doctor ɗin ya faɗa.

Alhaji Mainasara ya ce “Allah ya sa ayi a sa’a, sannan kuma ya bashi lafiya”

Wurin Habeeb ɗin su duka suka juya, Alhaji Mainasara na masa addu’a, shi kuma Doctor Umar yana ƙara duba shi.

Doctor ɗin na gamawa suka fito tare, anan yake shaida ma Alhaji Mainasara shi ɗan Katsina ne, ƙarin karatu ya zo yi anan, sai kuma ya ga an kawo Habeeb, kasantuwar sa ƙwararre a nan, sai ya karɓe shi domin bashi kulawa ta musamman.

Fatan Alkhairi Alhaji Mainasara ya yi mashi, tare da roƙonsa a kan don Allah kada ya yi ƙasa a gwiwa wurin ganin Habeeb ya samu lafiya.

Tabbatar mashi ya yi da zai jajirce, su kuma su taya shi da addu’ar samun nasara a wurin Allah.

“Insha Allah” Alhaji Mainasara ya faɗa, sannan suka yi sallama, da zimmar anjima zasu haɗu domin tattauna yadda aikin zai kasance.

Tafiya Doctor ɗin ya yi, shi kuma Alhaji Mainasara ya samu wuri ya zauna, zuciyarsa a dagule ya fiddo waya ya kira Uwani.

Bugu biyu ta ɗaga wayar tare da yin sallama, idanunsa a rumtse ya amsa sallamar, sannan ya yi shiru.

Hakan ne ya ƙara jefa Uwani cikin fargaba, don burinta bai wuce ta ji sun isa lafiya ba, sannan ya lafiyar Habeeb, cikin tsananin damuwa ta ce “Kun isa ko Alhaji?” Kai ɗaga har a lokacin kuma idanunsa na rufe ya ce “Mun isa.”

Da sauri ta ce “Toh ya jikin Habeeb ɗin.”

Saida ya sauke ajiyar zuciya don ji yake kamar zuciyar zata fito sannan ya ce “Habeeb na cikin mawiyacin hali Gimbiya, yanzu haka yana ICU, bai san me ke wakana a wannan duniyar ba”, kamar zai yi kuka ya ƙarasa maganar.

Hankali a tashe ta ce ina ne ICU Alhaji?”  Ya ce “Intensive Care Unit kenan, shashe ne da ake aje waɗanɗa rashin lafiyarsu ya tsananta, domin basu kulawa ta musamman, kuma a wannan sashe duk wanda ya shiga ba lallai ne ya fito da rayuwa ba, don haka ku sanya Habeeb cikin addu’a.”

Daga can ta fashe da kukan da ya ƙara karya ma Alhaji Mainasara zuciya, wanda yasa maƙalallun hawayen dake idonsa malalowa.

“Wayyo Habeeb, Insha Allah ma zai fito da ransa da lafiyarsa, Allah ya bashi lafiya mai ɗorewa”.

“Amiin” Alhaji Mainasara ya faɗa, sannan suka ɗan yi shiru kowa na share hawaye.

Katse musu shirun ya yi ta hanyar faɗin “Kun tafi gidan ko?” Domin sun yi da ita zata tafi ƙauye har ranar da Allah ya sa ya dawo, don ba zata iya zama gidan ita kaɗai ba, saboda tsoron da aka tsiri bata tun bayan sakin Hajiya Mairo.

Ta ce “Sai anjima Insha Allah, bari na yi dama ku isa tukunna”

Ya ce “Allah ya yarda, ki tabbatar da kin kulle ko ina, sannan a kashe wutar cikin gidan baki ɗaya”, ƙasan ransa kuma yana ƙara yaba halin kirkin Uwani, tana son tafiya, amma ta haƙura har sai mijinta ya isa inda ya tafi, wanda da Mairo ce, toh ƙila har rigan shi fita sai ta yi, tunda kowa da tafiyarsa.

Tabbatar mashi ta yi da za’a kashe wutar, sannan suka yi bankwana, ya katse kiran.

Yana nan zaune ya hango wani matashi ya nufo shi, wanda ko shakka babu shine Isama’l ɗin da suke waya.

Isama’l ɗin na isowa ya yi mashi sallama tare da ɗan duƙar da kai alamar girmamawa.

Hannu Alhaji Mainasara ya miƙa mashi sannan ya amsa sallamar, gaisawa suka yi, sannan Isma’il ɗin ya tabbatar mashi da shine wanda suke waya.

Faɗaɗa fuskarshi ya yi, don bai manta kara da karamcin da mahaifin Isma’il ɗin ya yi mashi a lokacin da ya je gidansu ba.

Ɗan matsawa ya yi akan kujerar da yake zaune, don zata iya ɗaukar mutum biyu ya ce “Bismilla ka zauna”.

Cike da jin kunya Isma’il ya zauna. Jajanta ma juna rashin lafiyar Habeeb suka yi, sannan Alhaji Mainasara ya nemi jin farkon ciwon Habeeb a wirin Isama’l, domin shine wanda yafi kusa da shi.”

Isma’il ya ce “Tunda Habeeb ya zo nan yake cikin damuwa, wadda mun so ya faɗa mana ita amma ya ƙi, saboda ciwon zuciyar da damuwar ke haifar mashi, toh daga baya abin ya yi sauƙi, sai da wannan Fateema ta zo nan, da kuma jin har a Katsina ba’a ganta ba, bayan ta koma abin ya tsananta, wanda ya riƙa aman jini”.

Haɓar da Alhaji Mainasara ya riƙe ya saki, tare da sauke ajiyar zuciya, domin ya fara fahimtar silar ciwon Habeeb, “Toh Allah ya yaye masa” ya faɗa, sannan suka cigaba da magana.

Sai da suka kusan awa ɗaya anan har Alhaji Mainasara ya tada mashi labarin gidansu Isma’il ɗin da yaje, sosai ya ƙara yaba ma Mahaifin Isma’il bisa ga halin kirkinsa, sannan ya yi ma Isma’il ɗin nasiha akan kullum su kasance masu yi ma mahaifansu biyayya, kada su biye ma ruɗin duniya su saɓa ma haifansu.

Saboda ya tabbatar da abin da Habeeb ya shuka ne yake girba, duk da bai faɗi hakan a cikin nasihar ba.

Isma’il ya ji daɗin hakan, ta shi suka yi suka koma wurin Habeeb, ta glass suka leƙa shi, har yanzu yana nan a yadda yake.

Sosai suka tausaya mashi, tare da yi mashi fatan samun lafiya sannan suka fito daga asibitin.

Shi Isma’il gida ya wuce, Alhaji Mainasara kuma ya wuce hotel ɗin dake kusa da asibitin ɗin, don ba zai iya nisa da Habeeb ba.

Ɗaki ya kama, sannan ya yi wanka ya fito, magana ya yi aka kawo masa abinci, don rabonsa da abinci tun a cikin jirgi da ya sha coffe.

Da ƙyal ya iya cin abin da aka kawo mashi, don ko kusa baya sha’awar komai.

Lokaci ya duba yaga an isa yin sallar azuhur, tashi ya yi don dama da alwallarsa, abin sallarshi ya fiddo a jaka tare da shimfiɗa wa ya gabatar da sallar azuhur, yana gamawa ya ɗora da nafila raka’a huɗu.

Bayan ya gama nafilar ya ɗaga hannu tare da yi ma Allah kirari da Salatin Annabi S.W.A, sannan ya cigaba da roƙa ma Habeeb lafiya a wurin Allah.

Bai fito daga hotel ɗin ba sai da ya yi sallar la’asar. Kai tsaye asibitin ya koma domin ganawa da Dr. Umar.

A irin wannan lokacin ne itama Uwani ta fito da shirin tafiya ƙauye. Drivern gidan ne ya ɗauke ta suka kama hanya garin.

Suna cikin tafiya direban ya fara kawo mata gulmar Hajiya Mairo, da yake mugun surutu gare shi.

 “Wai Hajiya yaushe rabon da kiga Umman Habeeb ne.”

Ɗan yamutse fuska Uwani ta yi, don a rayuwarta ba macen da ta tsana irin Hajiya Mairo, ce wa ta yi “Ni fa rabon da in sanya ta a ido ai tun ranar da ta bar gidan.”

Dariya ya yi “Toh wallahi yanzu idan kika ganta ba zaki gane ta ba.”

Uwani ta tambaye shi “Saboda me?”

Ya ce “Yoh duk ta lalace, wannan isa da izzar duk babu su, saboda ba abin hannu.”

Taɓe baki ta yi ta ce “Toh Allah ya kyauta,”  sannan ta cigaba da yi ma ɗanta wasa, don idan ta biye mashi har hirar da bata kamata ba sai ya kawo mata. 

Da ya fahimci bata son hirar sai ya ja bakinshi yayi shiru, ba wanda ya sake magana har suka isa garin.

Asabe na cikin ba dabbobinsu ruwa sai ga Bashir ya shigo da gudu har yana tuntuɓe. 

Da hanzari ta ɗago tare da faɗin “Kai lafiya” don a zatonta wani ya biyo shi.

Cikin shesshekar gudun da ya yi ya ce “Inna, Aunty Uwani ce ta zo”.

 “Uwani dai” Asaben ta faɗa tare washe baki.

 Kafin ya bata amsa sai ga yara sun shigo da ƙaton akwati suna ja.

“Uwani da wannan ƙaton akwatin” ta faɗa a ranta, tare da baro wurin dabbobin. Zuciya ce ta fara ruwaita mata wani abu marar daɗi, domin Uwani bata taɓa zuwa da akwati mai girman wannan ba

Sallamar Uwanin ce katse mata tunanin. Tashin farko mood ɗin Uwanin ta kalla, ganin ba alamar damuwa a ranta yasa ta faɗaɗa fuskarta haɗe da dariya ta ce “Kai maraba da baƙi – maraba da baƙi”.

Cikin farinciki suka tarbi Juna, Asabe ta karɓi Salim dake ta miƙo hannu yana son ta ɗauke shi.

Yaran gidanma hada na maƙwabta ba abin da suke sai murna, don duk sadda ta zo, toh sai ta yi musu tsaraba.

Cikin ɗaki aka shiga da akwati da kuma tsarabar da ta yo musu, aikuwa yaran suka ƙi fita.

Tsawa Asabe ta daka musu “Toh ayi waje, ba damar baƙo ya zo, sai ku zo ku yi cirko-cirko kamar zakaru.”

Dariya Uwani ta yi ta ce “Kai Yaya Asabe, wai kamar zakaru,” dariya Asaben ta yi ta ce “Toh idan ba iya shege ba sai yara su zo su cika ɗaki.”

Uwani da ta san me ya kawo su ta jawo jakar da tsarabar take, ledar sweet ta fiddo tare da fasawa, duk yaron da ke wurin sai da ta bashi sweet, aikuwa suna fita zuka jawo yara, kan kace me gida ya cika da yaran gari, wai ana sadakalle gidan Malam Amadu.

Sai kusan kowa ya samu, sannan Asabe ta kora sauran da basu samu ba, ya rage gidan daga Asabe da ƴaƴanta sai Uwani.

Gaisuwar yaushe gamo suka yi, sannan Uwani ta miƙa ma Asabe Jaka ɗaya ta tsarabar, ɗayar kuma ta ce ta gidan Kabiru ce.

Tayi murna sosai tare da gode ma Uwani da kuma Alhaji Mainasara, wanda da ba don su ba da kuma su Ameer, toh da Allah kaɗai ya san halin da zasu shiga, tunda Kabiru ba wani abu gare shi ba.  

Ƙagare Asabe take ta ji dalilin zuwan Uwani da waɗannan uwayen kayan, mafarin ta tambaye ta “Waɗannan uwayen kayan kamar kin yo hijira fa”.

Dariya Uwani ta yi, sannan ta ce “Alhajin ne ya yi tafiya, shine na taho nan har sai ya dawo”

“Wace irin tafiya ce haka ya yi?” ta yi gaugawar tambayarta.  

Faɗa mata ta yi cewar Habeeb ne bai da lafiya, ya tafi wurinsa.

Baki Asaben ta taɓe ta ce “Allah ya sauƙe” amma ba don addu’ar ta kai zuci ba, saboda a duniya idan akwai wanda ta tsana toh Habeeb ne, domin shi ne sanadin faɗawar ɗiyarta a damuwa.

Ɗan shiru suka yi, daga bisani Asabe ta yi magana cikin raunin murya “Yanzu da Jummai na nan ai da ba sai kin zo nan ba.” A bin da bata sani ba shine, da Jumman na nan, ƙila da Habeeb ɗin bai yi rashin lafiya ba, bare har Alhajin ya tafi wurinsa.

“Hakane” Uwanin ta ce, cikin ranta kuma bata so a ja maganar, gudun a fama tsohon ciwo, don abu ne mai sauƙi Asabe ta kama rizgar kuka.

Hirar Hajiya Mairo suka dasa, Asabe ta ce “Na ganta kwanaki a motar haya, wai haka ta lalace ne?”.

Uwani ta ce “Ai ƙaryarta ta ƙare fa, yanzu ba kuɗin, ba kuma ƙaryar sai tsiya”.

Cikin jin daɗin halin da Hajiya Mairo ta faɗa Asabe ta ce, “Ahaf, ai kaɗan dai ta gani, kuma wallahi alhakin Jummai ba zai barsu ba, domin ɗanta ne silar wargajewar farincikinmu.”

Uwani ta ce “Shine fa wallahi, yanzu dai yana can rai hannun Allah, ko ya tashi, ko kuma ya mutu.”

Asabe ta ce “Wallahi ba don mutuncin Alhaji Mainasara ba, da sai na roƙi Allah ya kashe Habeeb, itama ta ji abin da muka ji.”

Kai Uwani ta girgiza sannan ta ce, “Ko bai mutu ba duniya ta hora su ai.” Hira sosai suka cigaba da yi, har daɗin hirar ya sa Uwani ta faɗa mata cewar an ga Jummai a Katsina, amma da aka je sai aka taras bata nan.

Uwani bata taɓa zaton abin zai damu Asabe ba, aikuwa sai ta ga Asabe ta rikice sai sababi take, wai har aji labarin Jummai amma aƙi faɗa mata, abu kamar wasa sai Asabe ta kama kuka tana faɗin “Idan an gaji da neman ta, ni a bar ni in nemi ɗiyata, kullum sai ƙaryar za’a nemo ta ake, amma kuma shiru”, gaba ɗaya ta manta irin ƙoƙarin da kowa ke mata.

Haƙuri Uwani ta bata ta ce, “Ba da wata manufa aka ƙi faɗa maki ba, duk don kada a sanya maki rai, kuma a ƙi ganinta, ƙarshe ki shiga wani ƙuncin”.

Da yake hali na nan ko kusa bata saurari Uwani ba, ta cigaba da sababin da sai da Uwani ta ji dama bata faɗa mata ba.

Da Uwanin ta ga abin ya ƙi ƙarewa sai ta ɗauki Salim ta goya, su Basheer suka raka ta gidan Kabiru.

Tana fita Asabe ta dasa sabon kuka tare da addu’ar duk inda Jummai take, Allah ya sa tana cikin aminci, wanda kullum ita ce addu’ar da take mata.

Kuma tabbas addu’arta ta karɓu, tunda gashi Allah ya jefa ta Hannun su Aunty, wanda da ba a hannusu take ba, ƙila da tuni su Alhaji Lawwali sun samu galaba a kanta.

Don yanzu haka cikin fafutukar ganin ta samu suke, sai dai kuma abin ya ci tura, saboda da abin da ke tare da ita sun ƙi magana idan ana yi mata  ruƙiyya, bare kuma har ayi maganinsu, sai dai ihun dake yi ne ya yi sauƙi duk sadda ake karatun, da zaran malamin ya tafi kuma, sai ta cigaba.

Ba komai ne ya jawo haka ba, sai mugun wayon su Alhaji Lawwali da kuma shaiɗanunsu.

Da zaran sun ga mai karatu ya zo, toh sai su yi nisa da ita, nisan da ba za su san me ake ba, bare har ya cutar da su, da kuma an gama, sai su dawo su cigaba da azabtar da ita.

Azabar da suka fi yi mata ita ce ta wuta, bayan sun ɗaure ta a jikin wani iccen tsamiya, wanda a kansa ba komai sai baƙaƙen Aljannu,  kuma tana ganin su da idanunta suna bata tsoro.

Sannan a riƙa sanya wani ƙarfe a wuta ana nana mata a jiki, da zaran zafin ya shige ta sai ta fasa ƙara, wadda wannan ƙara take firgita duk mutanen gidan.

Gaba ɗaya duk sun fita hayyacinsu, duk sun fara ramewa saboda zullumin halin da take ciki, barin ma Ameer, da yake jin mugun tausayin ta, wani lokaci har hawaye yake idan tana kukan.

Ahamad kuwa Allah ya taimaka akwai Ammu, mafarin da ya fara kuka sai Ameer ya fita da su.

Yauma kamar kullum tana kwance a falo, har yanzu kuma babu sauyi a jikinta, domin bata san wake kanta ba. Aunty ce zaune a gefenta, hannunta ɗauke da cup ɗin salala wadda aka dama ruwan magani.

Kira Aunty ta kwaɗa ma Altine, da sauri ta fito daga kitchen ta zo “Hajiya ga ni”.

Idon Aunty na kan Jummai ta ce “Ki kama mani ita a bata wannan salalar”.

“Toh” Altine ta ce, sannan suka tada Jummai zaune tare da jingina mata baya da kujera.

A yadda take kallon mutane, sai ka yi tunanin tana da hankali, sai ka yi mata magana ne zaka gane bata da lafiya, domin ko kallon inda kake ba zata yi ba, bare ta baka amsa.

A hankali Aunty ta riƙa bata salalar tana sha, Altine kuma tana riƙe da ita, lokaci ɗaya kuma tana zancen zuci.

Sai da Aunty ta gama bata salalar, sannan Altine ta nisa ta ce.

“Ni kuwa Hajiya akwai wani mai magani a kusa da garinmu, duk irin ciwon da ke damun mutum, toh idan aka kai shi sai ya warke”.

Aunty da burinta kenan ta ce “Ke Altine, da gaske”.

Altine ta ce “Wallahi kuwa Hajiya, kin ga yana bada maganin mayu, da baƙaƙen iska, sannan ko asiri aka yi maka, toh idan ka je wurinshi sai ya karya shi, me zai hana kai ta can”.

Sai da Aunty ta kalli Jummai, sannan ta juya ga Altine ta ce “Bari Ameer ya dawo, sai mu shirya tunda gobe Asabar sai ya kaimu can, lamarin yarinyar nan yana bani tsoro wallahi, musamman idan tana cewa gasu nan, abu dai kamar mayu”.

Altine ta ce “Ai mayun ne ma Hajiya, su ne ke yin haka”, da yake Mayya ce ta kashe mata ɗiya, shi ya sa ta gane su ne ke bibiyar Jummai.

Suna cikin wannan magana ne Ameer ya shigo falon, ba inda idanunsa suka dira sai cikin idanun Jummai,

Sauri Jumman ta yi ta rumtse idanunta, saboda shaiɗanun dake jikinta tsoronsa suke.

Da tunanin abin da ya sa bata son haɗa ido da shi ya zauna a kan kujera, domin ba yau ne ta fara haka ba idan suka haɗa ido.

Tambayar Aunty jikin Jummai ya yi, lokacin da Altine ta tashi ta koma kitchen.

Aunty ta ce “Wannan jiki kam ba’a cewa komai Ameer, sauƙin ma tana ɗan cin abinci, da ba’a sa yadda abin zai kasance ba”.

Yunƙurin tashi Jumman ta shiga yi, Ameer ya ce, “Ina zaki?”  ba da faɗa ya yi maganar ba, amma sai da ta zabura.

Duban Aunty ya yi sannan ya ce “Aunty na lura yarinyar nan tsoro na take, kalli yadda take ta kyarma, ko dama tun ɗazu haka take?”

Kai Aunty ta girgiza sannan ta ce “A’a, shigowarka ne ta fara wannan abin.”

Maida dubansu suka yi ga gare ta lokacin da ta fara gyangyaɗi, zamar da ita Aunty ta yi a kan pillow, cikin ɗan lokaci da bacci ya ɗauke ta.

Maganar mai maganin Aunty ta yi ma Ameer wanda Altine ta bata labari.

Da farko ƙin amincewa ya yi, wai masu maganin cikin ƙauyukan nan duk bokaye ne da matsafa.

Aunty ta ce “Ba duka ba fa Ameer, kuma shi magani ai dace ne, ko haka zamu sanya mata ido”.

Shiru ya yi, don ko kusa bai gamsu ba, sai da Aunty ta yi mashi bayani sosai sannan ya ɗan yadda, shima don bai son yi mata gardama ne.

A taken Aunty ta buga ma maigidanta dake Uk waya, batun wurin mai maganin ta bashi labari, da yake ya san komai, fatan samun nasara ya yi musu, sannan suka yi Sallama.

Tana gama wayar ta juyo kan Ameer da ya kafe Jummai da idanu, kyakkyawar fuskata da ta ƙara kyau saboda rama yake kallo, a hankali ya ɗauke idonsa tare da maida shi wurin Aunty lokacin da ta ce “Gobe Insha Allah sai ka kai mu ko”.

“Allah ya kai mu goben lafiya” ya faɗa tare da miƙewa ya fita, itama Auntyn ɗaki ta koma ta ɗan kwanta, don basu samun wani isashen bacci.

Washegari tunda safe suka shirya sai ƙauyen da mai maganin yake, Altine ce gaban mota don ita ta san hanya, Aunty da Jummai kuma suna bayan mota.

Ammu da Ahamad kuwa gidan ƙanwar Aunty aka kai su.

Tafiya ce mai ɗan nisa, don sai da aka kusa zuwa kano sannan suka yanki hanyar wani ƙauye, wanda ko kaɗan hanyar bata da kyau, sau biyu motarsu na kafewa cikin rami, sai sun yi da ƙyal kafin su fita.

Ameer kuwa ba abin da yake sai tsaki, ƙasan ransa yana jin kamar ya shaƙaro Altine, don ita ta ja musu wannan wahalar.

Aunty itama duk ta gaji, ba don lafiya za’a nema ba, toh da tun a ramin farko da suka kafe ta ce a juya, don bata da zuriyar zaman mota ko da kuwa hanya na da kyau, bare kuma irin wannan wadda ba kwalta sai ramuka.

Tambayar Altine ta yi “Wai har yanzu ba’a kai ba?”

Altine ta ce “Saura kaɗan Hajiya”. 

ƴar tafiya kaɗan suka ƙara, sai gashi sun isa cikin ƙauyen da mutanen cikinsa duk fulani ne sai ƴan kaɗan.

Sai da suka yi ƴar tafiya sannan suka isa gidan mai maganin, wanda tun a ƙofar gida zaka san gidan na mai magani ne, don ga mutane nan birkij, hada marassa lafiya duk a kwance.

Fitowa suka yi a motar, Aunty ta riƙe hannun Jummai suka shiga ciki su duka.

Gida ne madaidaici mai ɗakuna huɗu, wuri su Aunty suka samu tare da zama, Ameer kuma ya ce fitowa zai yi, don mata sun fi yawa a ciki.

Anan suka ga marassa lafiya daban-daban, wanda sai da Aunty ta zubar ma wasu da hawaye saboda mawiyacin halin da suke ciki.

Suna nan zaune har layi ya zo kansu, tashi suka yi tare da shiga ɗakin mai bada maganin.

Zasu zauna kenan Jummai ta ƙwace daga hannun Aunty tana shirin rugawa.

Cikin tsawa malamin ya ce “Maza dawo”, ai kuwa jikin Jummai na ɓari ta dawo ta zauna.

Gaishe da Mai ganin Aunty da Altine suka yi, amsawa ya yi sannan ya ɗora musu da bayanan da Aunty bata tambaye shi ba “Matsafa ne suka kama ta, kuma suna wahalar da ita, don ta ƙi shiga ƙungiyarsu, yanzu haka kurwarta tana a hannunsu suna azabtar da ita”.

Har ya kai Aya Aunty na kallon shi, cikin ranta tana mamakin yadda aka yi ya san haka “Anya wannan ba malamin ɗan duba bane?” tambar da ta jefo ma kanta, lokaci ɗaya kuma idonta na kan Altine da ke ta jinjina kai alamar da gamsu da aikin Malamin.

Maganar malamin ce ta katse mata tunani a lokacin da ya ce “Yanzu zaku fara bada sadaka kafin a fara yi mata aiki”.

Aunty ta ce “Kamar nawa Malam”,  ya ce duk abin da Allah ya hore muku”.

Hannu ta miƙa wurin Altine ta karɓi jaka, dubu biyar ta zaro ta aje a gabanshi.

Sai da ya watsa ma kuɗin wani baƙin ruwa sannan ya ɗauke su ya saka cikin sabon ƙoƙo.

Minti ɗaya bai yi da saka kuɗin a ƙoƙon ba Jummai ta kama wata irin ƙara wadda ta firgita su Aunty, alama ya yi musu da su nutsu.

Magani baƙi ya haɗa da ruwa, ya miƙa ma Aunty ya ce “A’a bata”, lokaci ɗaya kuma ya dakatar da Jummai daga ƙarar da take.

Ruwan maganin Aunty ta bata, tana cikin sha Amai ya tuƙo ta.

Wani bokiti ya miƙa ma Aunty, Jumman ta riƙa Aman a aciki, kalar aman sai da ta ɗaga masu hankali.

Domin shi ba jini ba, gashi nan dai wani iri.  bayan ta gama ya bada ruwa aka bata, aikuwa sai ta ɓingire nan tana bacci.

Ya ce ma Aunty, “Wannan gubar da take shaƙa ce a wurinsu ta fara fidda wa,  yanzu zan baki wani hayaƙi da kuma laya, idan kun je gida a samu baƙaƙen ka ji a yanka gab da magariba, sai a turbuɗe layun da zan baki a inda aka yi yankan”.

Ido kawai Aunty tabi shi da shi, don ta tabbata boka ne, idan ba haka ba na me a ce sai an yi yanka.

Wasu ƙullin magunguna haɗe da layu da kuma wani man shafawa ya bata, tare da yi mata bayanin yadda za’a yi amfani dasu.

Godiya Aunty ta yi mashi, amma ba don ta gamsu da shi ba.

Gani ta yi ya ce ma Jummai “Ke tashi”,  aikuwa sai ga Jummai ta tashi sai waige-waige ta ke alamun tana son sanin inda take.

Kiran sunanta Aunty ta yi, sai ji ta yi ta amsa.  Tambayar Jummai mutumin ya yi “Ina mutanen da suka ɗaure ki?”.

Kusurwar ɗakin riƙa kallo, daga bisani ta nuna wurin sannan ta ce “Gasu can suna ta gudu.”

Mutumin ya ce “Toh sun tafi kenan ba zasu sake dawowa ba”

Mamaki ne ya kama Aunty, yadda cikin ɗan lokaci ta samu sauƙi, dubu goma ta fiddo ta ƙara mashi, don ta ji daɗin samun lafiyar Jummai.

Shi kuwa ya ji daɗin kuɗinnan, godiya ya shiga yi ma Aunty, ta ce “Ai ka fi haka Malam”

Fitowa suka yi, Altine ta ce “Kin gani ko Hajiya, ai malamin nan ya iya aiki”

Murna fal da zuciyar Aunty ta ce “Nagani Altine, aiki kamar dai yankan wuƙa”.

Fuskokinsu cike da jin daɗi suka zo wurin motarsu, lokacin Ameer kuma yana masallaci don gabatar da sallar azuhur.

Aunty ta dubi Jummai da ke jingine da mota ta ce “Fateema, yanzu me ke maki ciwo”.

Murya can ciki ta ce “Kai na”.

Altine ta yi sauri ta ce “Shima zai dena idan Allah ya so”.

Kallon ta Aunty ta riƙa yi, ƙasan ranta tana jin wani irin tausayinta.

Shi kuwa Ameer tun daga nesa mamaki ya kama shi, don da alamu Jummai ta samu lafiya sakamon maganar da ya ga tana yi.

Yana ƙarasowa ya ƙara faɗaɗa fuskarta ya ce “Ba dai ta warke ba”.

Aunty ta ce “Aikuwa dai ka gani”, Altine kuwa sai sai washe baki take akan ta yi sanadin samuwar lafiyar Jummai.

Kallon Jumman ya yi, sai ya ji wani irin daɗi a ransa wanda bai misaltuwa.

Motar suka shiga, farinciki fal da zukatansu suka nufi gida.

Sai da suka huta, sannan Aunty ta yi ma Ameer bayanin yadda malamin ya ce ayi da layun da ya bada.

Aikuwa fafur ya ce ba za’a yi yanka ba, wannan ai shirka ne, Aunty ta ce “Toh baka ga ta samu sauƙi ba”.

Ya ce “Aunty da haram zamu nema mata lafiya, dama na ce maki wallahi bokaye sun fi yawa a ƙauyen nan.”

Sosai ya nuna ma Aunty illar yin yanka don wanin Allah, ya nuna mata shirka ce wadda zata ita kai mutum wuta, da yake Auntyn tana da ilimi da tsoron Allah sai ta gamsu da maganarshi, ta ce “Toh ai shikenan tunda ta samu lafiya”, a haka dai aka bar maganar. 

Cikin ikon Allah Jummai ta fara murmurewa, sai dai jikinta ba kuzari sosai, ko magana ma bata cika yi ba.

Su kuwa basu damu da rashin maganarta ba, tunda dai ta samu lafiya, Ameer kuwa koda yaushe yana cikin gidan, burinshi bai wuce ya ga Jummai ba, domin wata irin nutsuwa yake samu idan yana ganinta.

Da zaran ya shigo bai ganta ba, toh sai ya tambayi Aunty.

A nan ne Aunty ta gane son da taɓa faɗa mata yana ma Jummai ba na wasa bane, domin ko kusa halin barikin da Jummai ta shiga bai sa ya dena sonta ba, sai ma kamar ƙaruwa da ya yi.

Kuma tunanin da Aunty ta yi hakane, son da yake ma Jummai ƙaruwa ya yi, sakamon kyawunta na asali da ya fito, saɓanin sadda tana ƙauye. 

Bayan sati biyu da zuwansu wurin mai magani ne ciwo ya dawo sabo. 

Su Aunty na zaune a falo suna hira sai ga Jummai ta fito da gudu daga ɗaki tana faɗin “Wayyo Aunty, gasu nan, zasu kama ni”.

A firgice Aunty ta ce “Su wa kuma, kai mun shiga uku”.

Jummai na kuka ta ce “Waɗannan mutanen ne Aunty, Alhaji Lawwali ne, ya ce kashe ni zai yi, don Allah kada ki bari ya kama ni Aunty”, jikin Aunty ta faɗa tare da ƙadaddabe ta tana kuka.

Gani Aunty ta yi kamar an fizge ta daga jikinta, ƙasa ta faɗi tana ta billayi, daga nan kuma bata sake sanin inda kanta yake ba.

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’una Aunty ta shiga faɗi, lokaci ɗaya kuma tana kallon Jummai da ta koma kamar gawa.

Ameer ma take idanunsa suka kaɗa zuwa launin ja saboda tsananin fushi.

Wanda a ransa yake jin da Allah zai bayyana mashi abin da ke cutar da Jummai, toh da sai ya yaƙe shi da iya ƙarfinsa, saboda cutar da suke mata ta yi yawa.

Kasa kallon Jumman ya yi saboda suturar da ke jikinta, sai dai ya dubi Aunty da ke ta kuka.

Kafin yayi magana ta riga shi da faɗin “Ameer ko dai don ba’a ƙarasa maganin ne ba”.

Kai ya girgiza, “A’a Aunty, irin wannan ciwon yana yin waiwaye dama”.

Shiru Aunty ta yi, don ita abin duk ya tsorata ta, ciwo yaƙi ci ya ƙi cinyewa, sake magana ta yi “Ameer ko dai mu maida yarinyar nan a wurin iyayenta, a ganina zai fi dacewa.”

“Mu ƙara haƙuri Aunty, komawarta da lafiya ya fi, akan ta koma da lalura”.

Aunty ta ce “Toh Ameer yanzu ina kuma zamu nema mata magani, ka ga dai an yi mata ruƙiyya, kuma dai har wani gari an je.”

Shiru ya yi, don bai san inda za’a neman magani ba, kasantuwar shi baƙo ne a Katsina.

Itama Auntyn shiru ta yi tare da kafe Jummai da ta fara motsi, ta hanyar jujjuya kai, alamar tana jin raɗaɗi a jikinta.

Wasu zafafan hawaye ne suka zubo ma Ameer, bai sake magana ba ya fice daga falon, tare da ƙudirin duk inda mai magani yake sai ya nemo shi kafin ya dawo, tunda Katsina ba ƙaramin gari bane, akwai masu bada magani kala-kala, sai dai idan ba’a neme su ba.

A ɓangaren Hajiya Mairo ma, duk ta rame saboda fargabar halin da ɗanta yake ciki, duk inda take sa ran zata samu kuɗi amma bata samu ba, kuma ƙaddarar da take da ita, ko da ta saida, toh ba zata ishe ta yin tafiya ba.

Abin da ranta ke bata shine Corona Virus ce ta kama Habeeb, saboda ance ta fara game ƙasashen turai.

Yes! Corona virus ɗin son Jummai ce ta kama zuciyar Habeeb, sai a sa shi da addu’a, duk dai irin su sis Hassab sun ce ko kusa basu tausayin shi

Gidan Hajiya Sa’a ta je da nufin idan ta na nan ta karɓi kuɗinta.

Ta yi sa’ar ganin Hajiya Sa’a, sai dai cikin mawuyacin halin da yafi nata, domin kwance take bata da lafiya.

Da nufin faɗa ta je gidan, amma ganin yanayin Hajiya Sa’a ya sa jikinta yin sanyi.

Zaune take, amma bakinta ya karkace, alamar ciwon ɓarin jiki take.

Cikin yanayin damuwa ta ce “Hajiya Sa’a me ya faru haka?”.

Hajiya Sa’a sai dai kallo, don bata iya yin magana, duk da tana son yin maganar.

Wata mata dake kula da Hajiya Sa’ar ta ce “Wallahi damfarar ta aka yi, kuɗaɗenta sama da billion aka kwashe a banki, tun da ta faɗi sai ɓarin jikinta ya shanye, sannan ga Salma ta bi wani saurayi sun gudu, wai ita ba zata iya wahalar kashi da fitsari ba.”

Sallallami Hajiya Mairo ta shiga yi, don ta san kuɗinta sun lume, waɗanda dama tuni Hajiya Sa’ar ta cinye.

Matar ta kasa kunne ta ji Hajiya Mairo ta jajanta musu, sai kawai ta ji ta ce “Ai kaɗan kika gani Hajiya Sa’a, kuɗin haram ko, toh ga makomarsu nan, ɗiya kuma ban ga laifinta ba, tunda kema haka kika yi ma Uwarki”.

Matar ta ce “Haba ke kuwa, maimakon ki jajanta mata, sai ki kama faɗin wasu maganganu”.

Mugun kallo Hajiya Mairo ta watsa ma matar, “Ke da alamun hayarki aka ɗauka ki kula da ita, da kin san halin wannan fajirar matar, toh da kin batta cikin kashi da fitsarin da take ciki”

Bata jira jin me matar zata ce ta fito, cikin ranta tana tunanin inda zata faɗa kuma, ganin babu wurin zuwa yasa ta komawa gida da nufin shirin tafiya ƙauye don a saida gonar da ta rage musu.

Tana gama shirin ta ɗauki ƴan sauran kuɗinta da waya ta nufi tashar mota, cikin sa’a kuwa mota ta rage mutum ɗaya, tana shiga mota ta tashi suka nufi ƙauye.

Duk bata san an sace mata waya ba sai da ta isa gidansu, ta laluluba waya da nufin kiran Alhaji Mainasara, duk da ba ɗauka yake ba, kuma ko ya ɗaga ma bata da isassun ƙuɗin da zata yi magana da shi tunda bai ƙasar.

Ɓacewar wayar nan ba ƙaramin tashin hankali ya ƙara mata ba, gululun dake maƙale a zuciyarta ne ya fashe, wasu zafafan hawaye ne suka zubo mata, “Wai wannan wane irin bala’i ne ke bibiyata, ɗana bai da lafiya, ina son ganin sa amma abu ya gagara, ƴar wayar da nake sa ran jin muryarsa ma an sace”,  cikin kuka ta faɗi wannan magana.

Matar babansu da suka gana ma azaba ita da ƴan’uwanta ce ta shiga bata haƙuri, ta ce “Tunda dai Alhajin na can wurinshi, ki kwantar da hankalinki, Insha Allah da sauƙi”.

“Haba gwaggo, ana fama da cutar Corona virus ɗin zan kwantar da hankalina, yanzu haka fa an ce ta fara yawa a ƙasashen turai”.

Sosai hankalin Gwaggon ya tashi, don jikanta ya bata labarin yadda cutar Corona take da kuma irin illar da take da ita.

Faɗa mata ta yi Uwani na gari, don haka ta je wurinta ko Allah zai sa ta samu jin halin da Habeeb yake ciki.

Da farko girman kai ya hana, daga baya taga ƙunci na shirin kashe ta, ta shirya sai gidan Asabe, wanda tunda take bata taɓa shiga gidan ba saboda mugun abu.

Su Asabe na cikin ɗaki kenan suka ji ana ta rafka sallama, tashin farko Uwani ta gane muryar Hajiya Mairo, sai dai ta kasa gazgatawa saboda babu dalilin da zai kawo Hajiya Mairo a wannan gida.

Ita ke bakin ƙofa don haka ta fito da nufin ganin mai Sallama.

Faɗuwa gabanta ya yi, cewa ta yi “Yaya Asabe fito ki ga mai sallama”.

Da sauri Asaben ta fito, itama sai da gaban nata ya faɗi.

Cikin tsananin Fushi ta nufi Hajiya Mairo da ta ja tunga a bakin ƙofa ta ce “Ke matsiyaciya, me ya kawo ki gidana”. Don a zatonta tsiya ta kawo ta.

Maimakon Hajiya Mairo ta maido mata mai zafi, sai ta sassauta murya ta ce “Abin da kike zato ba shi ya kawo ni ba Asabe, kuma ba wurinki na zo ba, wurin Uwani na zo don in ji halin da ɗana yake ciki.”

“Toh ai da ni da Uwanin duk ɗaya ne, don haka ki kama gabanki tun muna shaida juna.”

Ƙin biye ma Asabe ta yi, sai ma ta juya wurin Uwani ta ce “Don Allah Uwani ya jikin Habeeb, har yanzu ban san halin da yake ciki ba.”

Tausayinta ne ya kama Uwani, don abin da zai sa Mairo ta yi sanyi ba ƙarami bane.

“Jikinsa da sauƙi, amma yanzu haka yana ɗakin thiyater, ana yi masa aiki a zuciya”.

Asabe ta ce “Ubanwa yasa kika bata amsa, ai da kin batta ta ji abin da muka ji, tsinanna mai baƙin hali, abin da kuka shuka ne kuka fara girba.”

“Na gode Uwani” Hajiya Mairo ta faɗa, tare da juyawa tana kukan tashin hankali, aiki a zuciya ba abu bane mai sauƙin da za’a iya kwantar da hankali a kansa.

Da zagin wulaƙanta Asabe ta raka ta, amma ko a jikinta, don ciwon ɗanta shine babban tashin hankalinta a yanzu.

*Ya Allah, ka yi mana tsari da wannan cuta ta Covid 19, waɗan da ka ɗora mawa ka yaye musu, mu kuma da abin bai zo mawa ba, ka kiyaye mu kada ya zo mana Ya Allah*

Maman Mu’azzam

<< Ko ruwa Na Gama Ba Ki 18Ko Ruwa Na Gama Ba Ki 20 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×