Skip to content
Part 2 of 22 in the Series Ko Ruwa Na Gama Ba Ki by Hadiza Isyaku

Da sauri Jummai ta ɗago kanta tare da tsagaita kukan da ta ke don a zatonta wurinta Asabe ta nufo, sai ta ga saɓanin haka, domin kuwa wurin da suke girki ta hange ta; ta buɗe tukunyar miya za ta kaɗa.

Malam Amadu kuma yana zaune a kan kujera ya na alwallar sallar Magariba.

Bayan hannu ta sa tare da goge majinar dake ta fita daga hancinta ta na shiga bakinta saboda tsananin kuka, kamar an ce ta kalla, sai ta ga jini, idonta lumshe ta sake kai hannu ga bakinta da ya kumbura, sai ta ji wani irin zugin da ɗazu ba ta ji shi ba saboda zafin da zuciyarta ke yi.

Ba tare da ta sake kallon hannun ba ta maida kanta a guiwa ta cigaba da a jiyar zuciya, ɓangare ɗaya kuma kunnenta na tsakar gida, ta na jin sadda mahaifinta ya gama alwalla ya fita masallaci.

Asabe kuwa daga inda ta ke sai sai sababi take tana faɗin “Wallahi shari’a ce zata raba ni da ɗan iskan da ya bata mani tarbiyyar ‘ya”

Zagi ta uwa ta uba ta yi ta ɓurmawa, kamar wanda take faɗan akan shi yana gabanta.

Haka ta yi ta kaɗa miya ta na wannan sababi, bayan ta gama ta yi alwalla itama ta shige ɗaki.

Jummai na jin shigewarta ta ɗago kanta da ya yi jingim ta taƙarƙara ta miƙe, duk da juwar da ke kwasarta ba ta tsaya ba sai da ta je tsakar gida inda suka kafe turmi ta zauna a kanshi, sai da ta juwar ta ɗan sake ta sannan ɗauki buta cike da ruwa ta nufi banɗaki, a can ma sai da yi kuka mai isarta sannan ta fito ta yi Alwalla ta nufi ɗaki.

Asabe za ta yi ruku’u kenan ta ga ta shigo, aikuwa ta fasa yin ruku’un ta shiga tafa hannu gami gyaran muryam “Ehem-ehem”, ɓangare ɗaya kuma hannunta na nuna ƙofa alamar ta fita.

Ido kawai ta lumshe tare da haɗe wani abu da yake ta taso mata a zuciya, sannan ta juya ta fita.

A daidai ƙofar ɗakin ta shimfida ɗankwalinta ta kabbara sallar a nan.

A masallaci kuwa duk yadda Malam Amadu ya so binne wannan damuwa a ranshi sai da ya kasa kasantuwar shi ne Limamin garin, da ƙyal ya iya jan mamu raka’ar farko, sauran raka’oin kuwa sai dai ya jawo ladan gaba shi kuma ya koma baya.

Ba abin da ke cikin zuciyarshi sai yadda akayi har cikin Jummai ya kai wannan lokaci ba tare da sun sani ba, da kuma yadda za su yi da shi ba tare da asirinsu ya tonu ba.

Sai da aka yi sallar Isha’i sannan ya koma gida, yana shiga ɗakinshi ya kishingiɗa ƙasan babbar dardumar da ke shimfiɗe a tsakar ɗakin, sannan tada kansa da matashin kai.

Asabe na ɗakinta tana ta saƙar zuci ta ji shigowarshi, tana fitowa ta nufi wurin da suke girki ba tare da ta kalli Jummai da ke zaune ƙofar ɗaki ta haɗe kai da gwiwa ta na ajiyar zuciya ba.

Tiren da ke cikin kwando ta ɗauka ta kife tuwon da ke cikin ɗan kwano a kai, sannan ta ɗora kwanon miya ta ɗauka ta nufi ɗakinshi, bayan ta aje ta ɗan russuna saitin fuskarshi ta ce “Ga tuwon nnan Malam”

Idanunshi da ke rufe ya buɗe ya kalleta “Ba zan iya cin tuwonnan ba Asabe.”

Cike da damuwa ta zauna gabanshi, lokaci ɗaya kuma tana kallon abincin ta ce cikin sigar lallashi, “Toh idan baka ci tuwon ba me zaka ci Malam, dan Allah ka daure ka ci ko kaɗan ne.”

Muryarshi Kamar zai yi kuka ya ce, “Wallahi bana iya ci Asabe, ki ɗauke shi kawai.”

Shiru ta yi haɗe da tagumi idanunta na ta fitar da ƙwalla.

Zuciyarshi cike da damuwa ya tashi daga kishingiɗen ya jingina bayanshi da bango ya ce, “Ba cikin yarinyar nan ne abin mamaki ba Asabe, yadda aka yi har ta kai wannan lokacin ba tare da wani ya lura da shi ba, shine abin mamaki.”

Ta ce bayan da share hawayen da suka gangaro mata a kumatu, “Malam yaran yanzu ne fa, duk wayon iyayensu wani lokaci nuna masu suke sun fi su”, Ya ce “Hakane.”

Shawarar yadda za’a boye wannan lamari kada wani ya sani suka shiga yi, aka ce a kai ta birni gidan Yayar Malam Amadu, toh mutanen unguwar duk sun san ba ta yi aure ba, dan haka za’a gane.

Asabe ta ce “Toh ko gidan Uwani zamu tura ta wadda ita kuma ƙanwa ce a wurinta da itama ta ke aure a birni.”

Ya ce “Ba tana da kishiya ba?”, ta ce “Eh”, ya ce “Toh ba zamu kai ta can ba.”

Ya ce “Toh ya zamu yi Asabe, ƙaddara ce tunda ta same mu dole mu ɗauke ta.”

Ai sai ta ida fiddo kukan da ke maƙale a zuciyarta, har cikin ransa ya riƙa jin kukan, sai yake jin shima da yana da ikon yin kukan da ya yi.

Cikin raunanniyar murya ya riƙa lallashinta, ya ce “Ki dena kuka Asabe, idan kuma kina da wata hanyar da zamu bi ba tare da asirinmu ya tonu ba sai ki faɗi, ni dai tsorona Allah, tsorona mutanen gari su ji wannan labari”.

Ko da jin haka sai ta tsagaita kukan ta ce “Asabitin birni zamu a cire mata shi, ita ce kaɗai hanyar da asirinmu ba zai tonu ba,” ya girgiza kai tare da ƙin Amincewa, da yake kamar ta fi ƙarfinshi ta shiga matsa mashi har dole ya amince.

Cike da zumuɗin zuwa asibitin ta fito daga ɗakin hannunta ɗauke da tiren tuwon, dan ya kasa ci sai fura da itama ya sha daƙyal.

Inda ta bar Jummai nan ta same ta, yunwa ta sa hawayen da ke fita a idanunta sun ƙafe sai dai kukan zuci, dan ko lashe Asabe bata abinci ba, tana jin yadda ɗan cikinta ke billayi alamar shima yana buƙatar Abinci.

Ba tare da ta ce mata komai ba ta wuce ta kimtsa wurin, sannan ta rufo gidan ta dawo ɗaki ta kwanta.

Sai da kusan awa biyu da shigarta ɗakin Jummai itama shiga, har ta yunƙura za ta kore ta wata zuciyar ta ce ta ƙyale ta.

Haka wannan dare ya shuɗe ba tare da wani daga cikinsu ya rumtsa ba, asali ma duk ƙagara suka yi gari ya waye, Musamman Asabe da ta zaƙu su je asibiti a zubar da cikin.

Suna tashi da Asuba ta dubi Jummai cike da tsana ta ce, “Sai ki shirya zamu je asibitin birni a zubar da wannan shegen da ke jikinki.”

Ras! Gabanta ya faɗi, dan ta ji an ce mutuwa ake, wani ɓangare na zuciyarta ya ce “Ai gwara ma ki mutu, da dai wannan rayuwar mara amfani.”

Ta na kuka ta je ta jawo ruwa a rijiya, ba tare da ta dafa ruwan ba ta yi wanka da su, duk da kuwa jin sanyin da ke gare ta, ko da yake yanzu duk wani abu na jin daɗi zuciyarta bata muradinsa.

Haka ta fito ta na ta rawar ɗari ta shige ɗaki ta shirya.

Asabe ma ruwan da zata dama koko ta ɗiba ta yi wanka, tana fitowa ta dama kokon ta sallami kowa in banda Jummai, duk da kuwa ta zuba mata nata.

Jummai na gani kowa na kalaci banda ita, sai dai ta sa hannu ta goge hawayen da ke ta malala a fuskarta.

Ƙanenta Bashir na gani ya miƙo ma ta nashi, kamar ya san kukan me ta ke “Ga nawa kisha Yaya Jummai.”

Adaidai lokacin kuma Asabe ta shigo, aikuwa ta daka mashi wata irin tsawa da sai da ya kusa ɓarar da kokon.

Haka duk suka yi kalaci banda Jummai, ba yan sun gama suka fito tsaf cikin shirin tafiya Asibiti.

Malam Amadu da shima ya shirya ya dubi Asabe ya ce “Duk kun yi kalaci dai ko?,” ba tare da ta bashi amsa ba ta shige ɗaki dan ta san Jummai bata yi ba.

Ya maida tambayar ga Jummai, ta girgiza kai “A’a.”

Sai da ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce “Je ki yi kalaci”, ta sake girgiza kai “Na ƙoshi.”

Ba tare da ya sake yi mata magana ba ya je ya ɗauko kokon haɗe da Breadi ya bata, dan ya ga alamar yunwa a tare da ita, ba musu ta karɓa, tunda ta kafa kai bata janye ba sai da ta shanye kokon, breadin kuma ta miƙa ma Bashir, aikuwa ɗan da ke cikinta ya yi ta juyi alamar ya samu abinci. 

Asabe na fitowa ta wurga mata harara ta ce “Munafukar banza”, sai dai ta sadda kanta ƙasa.

Yaran gidan aka tura su makarantar boko da yake ƙauyen suna da makaranta.

Su kuma suka kama hanyar tasha, su na isa mota ta tashi sai birni.

Mota na aje su suka nufi General hospital, da shigarsu Asabe ta ga wata nurse cikin fararen kaya ta tsaida ta “Dan Allah Likita wane ɓangare ne ake zubar da ciki?”

Wani mugun kallo da ta watsa mata sai da su duka suka sha jinin jikinsu hada Malam Amadu.

“Aka ce maki ana zubar da ciki ne anan da zaku zo”, Asabe ta ce “Toh wace Asibitin ce ake zubarwa,” ta ce “Ban sani ba”, ta na faɗin haka ta yi gaba ta bar su nan.

Malam Amadu ya ce “Ki riƙa bin komai a sannu Asabe,” ta yi shiru dan ta tsorata da da nurse ɗinnan.

Cikin Asibitin suka ƙarasa, duk wanda suka gani da fararen kaya sai sun tambaye shi dan a zatonsu duk mai farar riga likita ne, haka suka baro asibitinnan ba tare da sun samu abinda ya kai su ba, asali ma sai ɓacin rai da suka fito da shi, dan kusan duk wanda suka tambaya ba wanda ya gaya masu magana mai daɗi.

Haka suka yi ta bi asibitocin da ke cikin birni, har Allah ya sa suka iske wani matashin likita mai hankali, ya tambayesu “Me ke tafe da ku?”

Asabe da duk inda suka je ita ke magana ta nuna Jummai “Wannan yarinyar ce ta yi ciki ba tare da aure ba likita, shine mu ka zo a zubar da shi.”

Malam Amadu ya ce bayan ya ja tsaki “Ke kam Asabe baki iya magana ba wallahi.”

Murmushi kawai likitan ya yi, ya maida dubanshi ga Jummai da ke ta sussunne kai alamar kunya, sai da ya ƙare mata kallo ya fahimci ta na cikin damuwa, musamman da ya ga bakinta kumbure wanda ko shakka babu dukanta aka yi.

Ya Juyo ga Malam Amadu ya ce mashi “Malam kuna son ɗiyarku kuwa?” Malam Amadu ya ce “Ƙwarai kuwa likita, muna son ta.”

Ya ce “Toh ba zan boye maku ba, a yadda cikin ƴarku ya girma akwai matsala babba idan aka ce za’a cire shi, domin za ta iya rasa ranta.

Asabe ta yi charaf ta ce “Ai ko zata mutu ba wani abu bane Likita.”

Gaba ɗaya suka kalle ta hada Jummai, ƙasan ranta tana tunanin anya ma Asabe ce ta haife ta.

Likitan kuwa sai dai ya yi murmushi dan ya fahimci Jahilci da ƙauyanci ne suka dabaibaye ta.

Maganar Fahimta ya yi masu, ya nuna masu illar da ke cikin zubda ciki ya ce “Ko da ba matsala ta ɓangaren lafiya, toh zunubin da zaku ɗauka a wurin Allah fa? 

Kuma ba’a zuwa kai tsaye a ce za’a zubar da ciki sai an samu izni daga wani likitan, wanda shima sai idan ya ga matsalar da za’a iya rasa uwar ko ɗan sai ya ce a cire, ko kun zo da takardar shaida ne?”

Asabe ta ce “A’a Likita.”

Ya ce “Toh a dokance sai an zo da takardar shaida tukunna.”

Gabaɗayansu basu so jin wannan bayani ba, musamman Jummai da ta ke jin ba ta muradin komai a rayuwarta sai mutuwa.

Godiya Malam Amadu ya yi mashi suka tashi, har sun kai bakin ƙofa Likitan ya tsaida shi “Malam”

Su duka suka tsaya, ya ce ma Asabe da Jummai “Ku je ku”.

Bayan fitarsu ya shiga yi ma Malam Amadu magana mai tausasa zuciya.

“Wato sai mai ƙarfin tawakkali ne zai iya cinye jarabawar da kuka samu kanku a cikinta Malam, dan haka ku yi haƙuri gami da maida komai ga Allah.

Sannan ita yarinyar ku bi ta a sannu, kyara da tsangwamar da kuke nuna mata ku dena, dan su kaɗai suna iya sawa ta rasa rayuwarta, mai ciki ba abinda ta ke buƙata sai kulawa.”

Godiya ya ƙara yi ma likitan, likitan yace “Ba komai.”

Malam Amadu ya ce “Idan ba damuwa dan Allah ya sunanka?” dan ya ji daɗin abinda ya yi mashi, Likitan na murmushi ya ce “Ameer Sarkee.”

Ya ce “Masha Allah, na gode Malam Ameer, ni sunana Amadu.”

Bankwana suka ƙara yi, ya fita daga office din.

Ya ce ma Asabe “Sai mu koma gida,”  ta nuna ita a ƙara zuwa wani asibitin, ya kamo hannun Jummai ya ce “Toh sai ki je, mu dai mun yi gida”,  da ta ga da gaske ya ke, ta bishi suka tafi, a hanya suka sayi Awara da kunun Aya, suka ci a cikin mota, Jummai kuwa kasa ci ta yi sai dai ta riƙe nata.

Mota na aje su tasha Malam Amadu ya tsaya yi masu cefane, su kuma suka nufi gida.

Jummai za ta shiga ɗaki kenan Asabe da ke ciki ta tsaida ta, ba ta ankare ba sai ta ga tana ta watso mata kaya waje.

Wata irin ƙara Jummai ta fasa ta ruga cikin ɗakin ta ƙadaddabe ta “Dan Allah Inna ki tausaya mani kada ki kore ni”, dan a zatonta korarta zata yi.

Ba tare da sauurari abinda ta ke cewa ba ta ingijeta, aikuwa ta ɗurƙushe kan gwiwoyinta tare da riƙe mata ƙafa tana kuka.

Ganin haka sai ta tsagaita jefa kayan ta ce “Toh wa ya yi maki ciki?” dan yanzu ba abinda ta fi son sani sai shi.

Tambayar da Jummai ta tsana kenan, dan duk sadda aka yi mata ita sai ta tuna lokacin da ya sa mata wuƙa a wuya tare da iƙrarin kashe ta idan ta ce shine.

Ganin bata da niyyar faɗa mata ta fizge ƙafarta, Jummai ta faɗi zaune.

Malam Amadu na shigowa ya ga kaya warwatse, ga kuma sautin kukan Jummai a ɗaki, da hanzari ya ƙaraso ya ce “Wai me ke damunki ne Asabe, dan Allah ki bar yarinyar nan ta huta”.

Ta ce cikin sababi “Ka ga na yi mata wani abu ne?” ya ce “Toh kukan me take idan har ba wani abu kika yi mata ba”

Ta ce ”Ɗakina zata bar min, daga yau ba ni ba ita wallahi.”

Ya ce “Idan ta bar maki ɗaki ta tafi ina?”

Ta fito tare da nuna mashi bukkar da suke aje duk wani tarkacen shara ta ce “Can zata koma wallahi, ƙeyarta bana son sake gani a inda nake.”

Duk yadda ya so ta ƙyale ta amma fafur ta ƙiya, ya dubi Jummai da ke rashe tsakar ɗaki tana kuka kamar ranta zai fita ya ce “Ke ki ka ja ma kanki Jummai.”

Yana faɗin haka ya a je ledar cefanen tare da shigewa ɗakinshi ya na ta goge hawaye.

Haka ta jawo Jummai ƙeee! duk da tirjewar da take sai da ta fiddo ta waje.

Wani irin kuka Jumman ta riƙayi, tun muryarta na fita har ta kai ga ta disashe.

Asabe na fitowa ta daka mata tsawa, ta ce ta kwashi kayanta ta koma cikin bukkar sai ta yi kukan a can.

Haka ta tattara komai nata ta nufi cikin bukkar da ba komai cikinta sai shara.

<< Ko Ruwa Na Gama Ba Ki 1Ko Ruwa Na Gama Ba Ki 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×