Matar na tuba bata rasa mijin aure.
Tunda motarsu Jummai ta ɗauki hanyar ƙauyensu gabanta ya soma faɗuwa, ba komai ya jawo haka ba sai tsoron mahaifiyarta, da kuma mutanen gari da bata san da wace fuska ce zata kalle su ba.
Addu'a ta shiga yi ƙasan ranta tana faɗin "Allah ka sa mahaifiya ta yi farinciki da komawa ta", domin gani take har yanzu Asabe na riƙe da ita.
Aisha da ke gefenta ce ta lura da shirun da ta yi, ɗan taɓo ta ta yi ta. . .