A ɗaki kuwa Malam Amadu ji yake tamkar ya tsige zuciyarshi daga ƙirjinshi, saboda azabar zafin da take mashi. Babbar damuwarshi ita ce, yadda zai fuskanci mutanen gari yayin da suka gane ɗiyarshi na ɗauke da cikin da ta same shi a hanyar banza, a matsayinshi na wanda ake gani da ƙima, anya kuwa zasu cigaba da ba shi girma idan suka gane haka?
A hankali ya furta “Ina ma mafarki nake”, tare da dafe kanshi da yake jin kamar ana sara mashi wani abu a ciki, don ya san abu ne mai wahala su cigaba da ba shi girma.
Take zuciya ta fara son hana shi bin shawarar da likita ya ba su, ba don komai ba sai don ƙimarshi ta dawwama a idanun mutanen gari.
Wani ɓangare na zuciyarshi ya ce “Da ɗa ya ji kunya, gwara lahira ta yi baƙo, ku kai ta wani asibitin kawai, idan ya so ta mutu ma”
Wani sashen kuma ya dakatar da shi da faɗin “Wato da kunyar duniya, gwara ta lahira ko? Domin idan har ta mutu to alhaki na kansu, tunda likita ya faɗa musu gaskiya”.
Ido ya lumshe tare da matse wasu zafafan hawayen da bai san da fitar su ba, gaba ɗaya dabarar shi ta kwance, duk hanyoyin da suke ganin ita ce mafita sun bi, amma ba wadda ta yi daidai da abin da suke nema na rufin asiri sai guda ɗaya kawai, ita kuma ko shakka babu sai ta ja musu fushin Allah, shi kuma a yadda yake tsoron mahaliccinsa bai fatan aikata abin da zai ja mashi fushinsa.
Wani Iska mai zafi ya furzar gami da maida lamarishi ga Allah ya ce, “Allah kai ka ɗora mana wannan waƙaddara, ka bamu ƙarfin ɗaukarta ba tare da gazawa ba Ya Allah”.
Yana cikin wannan yanayi ne Asabe ta kunno kai cikin ɗakin, ƙasan da yake zaune ita ma nan ta zauna, tare da kafe shi da idanu tana son gane idan kuka ya yi.
Kallon ta shi ma ya yi da jajayen idanunsa masu ɗauke da siffar abin da ke cikin zuciyarsa na raɗaɗi.
Hakan ya ba ta damar gane abin da take nema, cike da mamaki ta ce “Wai kuka ka ke Malam? “
Ba tare da ya ba ta amsa ba ya ɗauke kansa ya cigaba da kallon gefe.
Sai da ta ɗan taɓe baki sannan ta ƙara magana “Kai kenan kana kuka, mu kuma mu yi me toh? “
Zuciyarsa a dagule ya juyo tare da bata amsa, “Me fa zaku yi Asabe, bayan zuciyar taku a ƙeƙashe take”
Cikin rashin jin daɗin amsar da ya ba ta, ta sassauta murya ta ce”Kamar ya zuciyarmu a ƙeƙashe Malam, ka kuwa san yadda na ke ji dangane da wannan al’amari, da har zaka gaya mani ƙeƙashewar zuciya”.
Tabbas ya san ta fi shi ma damuwa tunda ita ta haifi Jummai, toh amma abin da take yi mata ne bata kyautawa.
Ya ce “Na sani mana”. Ta ce, “To me yasa ka ce haka?”
Ya ce “Abubuwan da kike ne basu kamata ba, tun daga jiya zuwa yau baki bar yarinyar nan ta huta ba, kuma na san har nan gaba ma ba zaki barta ta huta ba.
Kalli yanzu inda kika maida ta da zama, wuri ne da ko dabbarki ba zaki ɗaure ba, bare kuma ‘yarki, wai duk da sunan nuna mata kuskurenta”.
Tunda ya fara magana har ya kai ƙarshe ta ke kallon shi fuska a murtuke, don bata yadda abin da take ma Jummai ba daidai ne ba, ya buɗe baki zai cigaba da magana ta katse shi a hasale
“Toh ai can ne yafi dacewa da ita, kasan dai gidannan bai rabuwa da jama’a, muddin kuma tana ɗakina toh ga asirinmu can ya tonu, idan kuma haka ka ke so sai ta dawo, ni dai ina cikin gida, kai da ke fita kai zaka fi kwasar abin kunya ba ni ba”
Shiru ya yi yana nazarin maganarta, lallai ta faɗi gaskiya, zaman Jummai a waccan bukkar wani rufin asirin ne a garesu.
Ya ce “Kuma haka ne Asabe, sai dai zan gaya maki wani abu da shima zai iya tona asirinmu, kwakwazon da kike ki dena don Allah, sannan tsana da tsangwama da kike nuna mata ita ma ki dena, don za ta iya haifar da abin da ba ki yi tsammani ba”
Ta ce “Toh na ji”, a ƙasan zuciyarta kuma ta na jin ba ranar da za ta bar Jummai ta huta, tunda har ta jawo masu abin kunya.
Haka suka yi ta magana, wata cikin lalama, wata kuma cikin faɗa duk don su samu mafita.
Ɓangaren Jummai kuwa kasa shiga cikin bukkar ta yi, ta tsaya daga bakin ƙofa ta na ƙare ma cikinta kallo, a ɓangare ɗaya kuma tana tunanin yadda za ta iya rayuwa a wannan wurin mai cike da tsummuna da sharar kayan gona da suka fi dacewa da a kai su bola a zubar.
Inda ta fi tsoro a gidansu kenan, shine kuma ƙaddara ta ware mata da sunan rayuwa a ciki, idonta lumshe ta tambayi kanta “Yanzu ni zan zauna anan?”, sanin amsar ita ce “Eh” ta sa ta fashewa da wani sabon kuka, wanda ba na komai bane sai na fargabar abin da zata tarar a ciki na ƙwari da ƙanan dabbobi, irinsu ɓera da tsaka, waɗanda su ne ta fi tsoro a rayuwarta.
Ta daɗe tsaye bakin ƙofar tana kuka, da ta ga dai bai da amfani sai ta shiga ta ɗan ture sharar gefe da ƙafa, sannan ta aje tarkacen kayanta a ƙasan sumuntin.
Zuciyarta cike da ƙuna ta raɓa inda ta share ta zauna , don ƙafarta har ta fara kumburi saboda tsayuwa.
Haka ta yi ta raba ido cikin bukkar, duk inda ta ji wani motsi sai ta kai duban a wurin, ɓangare ɗaya kuma tsikar jikinta na ta tashi, don ji take kamar wani abu zai hau mata jiki.
Hankalinta bai gama tashi da wurin ba sai da ta ga duhu ya fara, tsoronta Allah, tsoronta ɓerayen da ke cikin ɗakin, wanda tunda sauran haske take jin motsinsu.
Kukan da ya zame mata jiki ta dasa, aikuwa kanta ya yi ta sarawa, ga yunwa na ta murɗar mata ciki, don tun kokon da ta sha da safe bata sake cin komai ba.
Tana jin sadda Asabe ke rabon Abinci amma ba’a ba ta ba, a kan kunnenta ta ji Bashir na faɗin “Inna ina abincin Yaya Jummai in kai mata”.
Aikuwa ta daka mashi tsawa “Ban sani ba dan ubanka, ɓace mani a gani ko in ɓaɓɓala ka”.
Jummai na jin haka ta girgiza kanta tare da cije leɓe ta cigaba da sharɓar kuka.
Tana jin sadda Asabe ta ja sauran yaran suka shige ɗaki, Malam Amadu ma akan idonta ya shigo gidan ya nufi ɗakinshi, saboda ƙofar bukkar na kallon ƙofarsu ta shigowa.
Take tsoron da ke zuciyarta ya ƙaru, idonta na ƙofa ta ji faɗowar wani abu tim! A ƙasa, wanda ko shakka babu ɓera ne, a gigice ta miƙe tsaye ta nufi ƙofa a guje, aikuwa wannan ɓera ya bi ta cikin ƙafafunta suka fita tare.
Wani irin haki ta riƙa yi tare da dafe ƙirji ta bi ɓeran da kallo, da yake akwai hasken farin wata , lokaci ɗaya kuma ta ji juwa ta kwashe ta, ganin zata faɗi ta yi maza ta isa jikin iccen bedin da ke nesa kaɗan da bukkar ta jingina bayanta tana ta maida numfashi.
Can kuma ta ji mararta ta murɗa, “Wash Allah” ta furta tare da cije leɓe ta sulale ƙasa zaune.
Hannunta na dafe da marar ta yi ta nishi, ɓangare ɗaya kuma idanunta na ta fitar da hawaye.
Ta daɗe cikin wannan yanayi tana ta nishi, ko da marar ta saki sai ta miƙe a daddafe ta nufi ɗakin Asabe da zummar kwana a can.
A hankali ta tura ƙofar ta shiga, fitilar ɗakin da ke kunne ne ya sa ta ganin Asabe zaune saman gado ta yi tagumi.
Wani mugun kallo da Asabe ta jefe ta dashi, sai da hantar cikinta ta kaɗa.
“Me ya kawo ki ɗakina”, Asabe ta tamayeta cikin kaushin murya tare da shiɗowa daga saman gadon.
Jummai na kuka ta ce “Dan Allah Inna ki banni in kwana a nan”.
“In bar ki anan ki kwana na?”
Jummai ta ɗaga kai, “Toh wa yayi maki ciki”, Asabe ta sake tambayar ta lokacin da ta ƙaraso gabanta.
Ras! gaban Jummai ya faɗi, ta kasa cewa komai sai sharɓar kuka.
Asabe tace “Baki da Amsa?”, Jummai ta yi shiru.
Ta kuwa ja mata hannu ta yi waje da ita, “Ka da in sake jin motsinki a nan”, tana faɗin haka ta sakar mata hannu, tare da shigewa ɗakinta ta sa kuba.
Cak! Jummai ta tsaya da kukan da ta ke, don ta fahimci ba shine magani ba, Iyayenta ne magani, kuma tunda sun gaza, ba zata sake wahalar da kanta da kuka ba.
Magana ta shiga yi da zuciyarta akan ta yi haƙuri ta koma ɗakin.
“Ɓeran fa?”, ta tambayi kanta, maimakon amsa sai ta sake jefo ma kanta wata tambayar, “Ɓera maciji ne?”, ta girgiza kai kamar zuciyarta na tsaye gabanta.
Bata tare da ta sake magana da zuciyarta ba ta sa kai, ba inda ta tsaya sai cikin bukkar, tare da ɗaukar ma ranta duk abin da zata ji ko gani ba zata sake fitowa ba, ko da kuwa zai zama ajalinta.
Cikin duhun tasa ƙafa ta ƙara matsar da sharar gefe, har sai da ta share inda zai ishe ta kwanciya, ta jawo jikkar kayanta zata fiddo zane ta ji ta tirje wani abu, tana ɗaga jikkar ta laluba, ashe awararta ce wadda suka saya asibiti.
Tana kyarma ta fasa ledar ta cigaba da ci ba tare da tunanin ta lalace ba.
Zuciyarta a dake ta fito tasha ruwa, ta kuma shiga ban ɗaki ta fito
Tana komawa ta shimfiɗa zane ta kwanta, tare da makurewa cikin hijabi, ba tare da ta damu da sanyi da kuma sauron da ke ta yi mata kuwwa a kunne ba.
Bata fi minti biyar da kwanciya ba ɓeran nan ya dawo, “Wayooo Allah na” ta furta tare da rumtse idanu lokacin da yabi ta kanta ya wuce.
Wata irin karkarwa jikinta ya shiga yi, har ta yunƙura zata tashi, zuciya ta maida ta “Ki koyi haƙuri da rayuwa Jummai”, nasihar da ta cigaba da yi ma kanta kenan, har dai ta dake.
Haka ɓeraye suka yi ta safa da marwa a jikinta, amma ko gyazau.
Sai ma ta lula duniyar tunanin azzalumin da shine sanadin shigarta wannan hali, duk da itama ta bada guddumuwa, amma ya fi ta tunda shi ya fara bijiro mata da abin.
“Allah ka yi mani sakayya, sannan ka yafe mani kuskuren da na yi” ta furta a hankali.
Wasu zafafan hawaye suka cigaba da fita a idanunta, duk da ta so hana su, amma zafin da zuciyarta ke yi yasa ta kasa tsaida su.