Ko da bacci yake da ƙaurin suna a wurin sata, toh a wannan lokaci bai samu sa’ar sace Jummai ba, domin yadda ta ga rana, haka ta ga dare.
Sanyin da ke fitowa daga ƙasan simintin yana shiga jikinta, da kuma rashin sabo da kwanciya ƙasa ne suka fi takura mata, uwa uba kuma ga tsohon ciki, wanda duk kyawun muhallinka ba zai bari kayi bacci cikin jin daɗi ba.
Haka ta yi ta juye-juye a ƙasa, idan ta gaji da kwanciya sai ta tashi zaune ta haɗe kai da gwiwa.
Gabaɗaya ta rasa me ke mata daɗi, saboda duk illahirin gaɓoɓin jikinta ciwo suke, cikin ƙanƙanin lokaci kuma matsananciyar mura da zazzaɓi suka rufe ta.
Jikinta na karkarwa ta jawo jakar kayanta, lokaci ɗaya kuma bakinta na faɗin “Wai Allah”
Lulluɓe jikinta ta yi gabaɗaya da zannuwan da ta fiddo daga cikin jakar, kan ka ce me hucin zazzaɓin ya game cikin Zannuwan, hakan ne ya ƙara galaibaitar da ita, ta shiga sanbatu.
“Ka cuce ni, ka ɓata mani rayuwa kuma ka guje ni, da na san haka zaka yi mani, da ban amince da kai ba, azzalumi kawai”.
Wani irin kuka mai ƙarfi ne ya ƙwace mata, wanda shima bata san tana yin sa ba.
Haka ta kasance cikin wannan dare, ko da Asuba ta doso sanyinta ya dake ta, sai ta fara dawowa daidai.
Kiraye-kirayen sallar da ta ji ana yi ne ya sa ta ida wartsakewa. Duk da sauran zazzaɓin da ke jikinta bai hana ta fita waje ta yi alwalla ba.
Sanin bata iya jumirin tsayuwa ya sa ta yi sallar daga zaune, tana gamawa ta cigaba da neman gafarar mahaliccinta, domin tana da yaƙinin kuskuren da ta aikata ne, take gani a cikin ƙwaryar shanta.
Tana cikin addu’ar ne ta ji idanunta sun yi nauyi, alamar bacci ya zo, da yake tana da buƙatar sa sai ta yi sauri ta shafa addu’ar. Lokaci ɗaya kuma ta matso jikin bago, tare da jingina da shi ta makure a cikin hijabi.
Cikin ƙanƙanin lokaci bacci mai cike da nutsuwa ya yi awon gaba da ita.
Ba ita ta farka ba sai da gari ya yi haske, shi ma cikin baccin ne ta ji kamar ana kiran sunanta.
“Yaya Jummai,” ƙin buɗe idanunta ta yi, don a zatonta mafarki take.
Sai da aka ɗan bubbuga jikinta “Yaya Jummai ki tashi”, sannan ta ɗan buɗe idanun a hankali tare da fitowa daga cikin hijabin.
Bashir ne tsaye a gabanta, hannunsa ɗauke da cup ɗin koko, sama kuma plate ne na soyayyen dankalin hausa.
A ɓangare ɗaya kuma idanunsa na kan tulin sharar da ke gafenta, kallo ɗaya zaka yi mashi ka tabbatar da ransa bai so ganin yayarsa cikin wannan yanayi ba.
Cikin muryarta da bata fita ta ce “Bashir”.
A hankali ya maido dubanshi gare ta, tare da duƙawa ya aje cup ɗin ƙasa, kamar zai yi kuka ya ce “Ga kalaci”.
Tambayar shi ta yi “Inna ce ta ce ka kawo mani?”
Ya girgiza kai “A’a”
Take zuciyarta ta kare, idanunta kuma suka cigaba da ɓuɓɓugar da ƙwalla, don ko shakka babu nashi ne ya kawo mata.
Ganin tana kuka, ya yi magana cike da damuwa “Ba ki da lafiya Yaya Jummai? ” Shi a tashi yarintar duk wanda ke kuka toh bai da lafiya.
Kai kawai ta ɗaga mashi, don bata son kukan da ke maƙale a zuciyarta ya fito.
Ya ce “Toh bari in ɗauko maki magani”, yana faɗin haka ya fita, da yake gidan basu rabuwa da magani, sai gashi ya dawo da ledar magunguna a hannu.
Miƙa mata ledar ya yi, “Ki ɗauki wanda za ki sha, sai in maida sauran”.
Ba tare da ta yi magana ba ta karɓa, maganin zazzaɓi da mura ta ɗauka, sannan ta ƙulle ledar ta miƙa mashi.
Yana karɓa ya fita, sai gashi kuma ya dawo da ƙaton cup cike da ruwa “Ga ruwa”.
Cike da soyayyar ƙanenta ta karɓi ruwan, ta ce “Na gode ƙanena.”
Murmushi kawai ya yi, sannan ya juya ya fita, don bai son Asabe ta san cewa ya zo wurin Jummai.
Yana fita ta ɗauki kokon ta kai baki, tamkar magani ta riƙa jin shi, tana gama sha ta ɓalli magani shima ta sha, dankalin kuma sai dai ta rufe shi da ɗankwali don ta bata iya ci. Komawa ta yi ta kwanta, domin biyan bashin baccin da ta ɗauka a daren jiya.
Bashir kuma yana komawa ɗaki ya zuba wani kokon da dankali.
Ali, wanda ƙanenshi ne da ke bi mashi ya ce “Laa! sai na faɗa ma Inna”.
Ɗan langaɓe kai Bashir ya yi, ya ce “Toh idan mun je makaranta, ba zan ba ka irin alewar jiya ba”.
Cike da son alewar, Ali ya ce “Toh bazan faɗa ba, zaka ba ni ko?”
Bashir ya ɗaga mashi kai alamar “Eh”
Tsawon kwana uku Jummai na cikin wannan bukka, wadda ta fi dacewa da a kira ta da kurkuku. Ba tare da ta samu wata kulawa daga wurin mahaifiyarta ba.
Kamar ma babu ita a gidan, don tunda ta dawo cikin wannan bukka Asabe bata sake neman ta ba.
Ko abinci da hannunta bata sake cewa ga shi a kai ma Jummai ba, sai dai Bashir ya fakaici idonta ya ɗiba ya kai mata
Tun abin na damun Jummai har ta kai ga ya zame mata jiki, idan Bashir na nan ta na da abinci, idan kuma bai nan ta haƙura, don a gidan ba mai tunawa da ita sai shi.
A rana ta huɗu ne tana zaune ta yi tagumi sai ga Bashir, hannunsa ɗauke da tsintsiya ya ce, “Yaya Jummai, ki fito in share maki ɗakin kafin Inna ta dawo”
Janye tagumin ta yi ta ce, “Toh Bashir.”
Da hanzari ta taƙarƙara ta miƙe, suka shiga gyaran ɗakin a tare.
Cikin ƙanƙanin lokaci suka gyara wurin, tare da toshe duk wata ƙofa da ɓeraye ke fitowa. Sannan Bashir ya ɗauko wata tsohuwar tabarma ya shimfiɗa.
Ba ƙaramin kyau wurin ya yi ba idan aka haɗa shi da can baya.
Godiya Jummai ta yi ma ɗan ƙanenta ta da take jin ta fi so, saboda kulawar da yake nuna mata.
Suna daga wajen bukkar suka jiyo muryar Asabe da wata maƙwabciyarsu, za su shigo.
Da sauri Jummai ta shige ciki, shi kuma ya nufi ƙofa suka haɗe a zaure.
Suna shigowa Asabe ta ja matar suka nufi ɗakinta, don ba ta son a san da zaman Jummai a cikin gidan, sun daɗe suna hira, sannan matar ta fito da nufin tafiya.
“Ina Jummai, kwana biyu na dena ganinta?”
Tambayar da matar ta yi lokacin da bata ga Jummai a tsakar gida ba,
Asabe ta ce “Ai tana birni”, matar ta ce “Ita dai ta zama ƴar birni, ƙila ma ta samo mana suruki a can.
“Uhmm” kawai Asabe ta ce, ta yi mata rakiya har bakin ƙofa ta tafi.
Baki Jummai da ke kwance tana saurararsu itama ta taɓe, don a yanzu ba inda ta fi tsana irin birni, saboda can ne sanadin shigar ta wannan hali.
***** *****
Yanzu kuma damuwar Asabe da Malam Amadu ita ce, rashin sanin wanda ya yi ma Jummai ciki, duk wasu hanyoyi da suke ganin za ta faɗa musu sun bi, amma ta ƙi faɗa.
Zaune su ke tsakar gida suna shan hantsi, Asabe ta dubi Malam Amadu da ya fara ramewa saboda zullumi ta ce, “Malam! Ko dai Kabiru za’a kira ya tambayi yarinyar can, tunda mu ta ƙi faɗa mana.”
Shiru ya yi kamar bai ji me ta ce ba, ƙasan ranshi kuma yana tunanin abin da zai faru idan har Kabiru ya zo.
Katse mashi tunani ta yi da faɗin, “Malam na ce ko a kira Kabiru?”
Sai da ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce “Kabiru kuma?”
Ta ce “Eh Malam”
Ya ce “Maganar nan fa har yanzu ba wanda ya san da ita, ba kya gani asirinmu zai iya tonuwa idan har muka sa wani.”
Ta ce “Kabiru fa ɗan’uwana ne Malam, kuma abin da ya same mu ai ya same shi.”
Ba don ranshi ya so ba, ya ce “Toh shikenan, idan kina ganin ba matsala ki kirawo shi.”
Ta ce “Ba wata matsala Malam.” Ya ce “Toh shikenan.”
Hira suka cigaba da yi, wadda kaso mai yawa na cikinta a kan Jummai ne.
Bayan sun gama hirar, Asabe ta shirya ta nufi gidan Kabiru.
Zuciyar Malam Amadu cike da fargabar zuwan Kabiru, ya tashi ya nufi bukkar da Jummai ke ciki, tare da fatan Allah ya sa ta faɗa mashi tun kafin Kabiru ya zo.
Zaune ya same ta, ta yi zurfi a cikin tunani, har ta kai ga bata sanin mai shiga da mai fita.
Cike da tausayin ta ya riƙa kallon ta, Yarinyar da ya ɗauki burin duniya ya ɗaura a kanta, ya sha alwashin sai ta yi karatun boko mai zurfi duk don ta taimaki al-ummar ƙauyensu, amma ƙaddara ta kasa cika mashi wannan buri.
“Jummai,” ya kira sunanta a hankali.
A tsorace ta waigo, don bata san lokacin da ya shigo ba, kasa sanya idonta ta yi cikin nashi, saboda tsananin kunyar da take mashi.
Bai wani ɓata lokaci ba ya ce, “Jummai so nake ki faɗa mani wanda ya yi musabbabin shigarki cikin wannan hali, domin mu ɗauki matakin karɓo maki haƙƙinki, saboda ya zalunce ki.”
Tunda ta sadda kanta ƙasa bata ɗago ba, sai ma hawaye da ta riƙa ɗigarwa.
Duk yadda ya so ta yi magana amma ta ƙi, kamar zuciyarshi za ta fashe ya fito daga ɗakin.
Asabe kuwa a zaure ta haɗu da Kabiru ya turo mashin zai fita.
Yana ganinta ya dakatar da tura mashin ɗin, ganin fuskarta ba walwala ya sa shima ya ɓoye tashi walwalar.
A tsayen suka gaisa, ya ce “Bari in shigar da mashin ɗin”, Asabe ta dakatar da shi “Ai ba zama zan yi ba Kabiru.”
Abin da ke tafe da ita ta shiga zayyana mashi, cewar Jummai ta yi ciki, kuma ta ƙi faɗin wanda ya yi mata.
Tamkar a cikin mafarki yake jin maganar Asabe, mafarin ya saki mashin ɗin ba tare da ya sani ba.
Ƙarar faɗuwar mashin ɗin ce ta tabbatar mashi da ba mafarki yake ba, ido ya bi mashin ɗin da shi, ɓangare ɗaya kuma yana jin wani irin tashin hankali a cikin zuciyarshi.
“Ciki?” ya faɗa cikin murya mai ɗauke da zallar mamaki.
Asabe ta ce, “Ciki fa har ya fara girma.”
Hannunsa dafe da kai ya ce “Ya Salam, tamu ta same mu, Allah ka iya mana.”
Shiru suka yi, kowa na jin kamar zuciyarshi zata fito, musamman Kabiru da abin yake sabo a gunsa.
Ɗago mashin ɗin ya yi, ya fidda shi waje, sannan Asabe ta hau suka tafi.
A Ƙofar gida suka haɗu da Malam Amadu, bayan sun gaisa suka shiga ciki a tare.
Jummai na zaune cikin bukka, sai ga Ali ya shigo, “Yaya Jummai ki zo in ji baba Kabilu” cikin maganarshi ta yara ya ce haka.
Wata irin faɗuwa da gabanta ya yi, sai da ɗan cikinta ya juya, saboda mugun tsoronsa suke.
Hijabinta ta sanya ta fito, ganin tsakar gidan ba kowa, ta tambayi Ali “Yana ina?”
Ya ce, “Ɗakin Inna”, can ɗin ta nufa, a daidai ƙofa suka ci karo da Asabe, jinkinta na kyarma ta dawo baya, Asaben ta fita, ita kuma ta shiga.
Zaune ta same shi saman kujera, Malam Amadu kuma zaune a bakin gado.
Kabiru na ganin ta ya rumtse idanu tare da dafe kai, karo na farko kenan da ya samu kansa cikin tashin hankalin da bai taɓa samun kansa a baya ba.
Ƙasa ta zauna tare da kai gaisuwa gare shi, amma ya ƙi amsawa, bata wani damu ba tunda ta san laifin da ta yi.
Tsit ɗakin ya yi, kowa na zancen zuci, sai da aka ɗauki lokaci a haka, sannan Kabiru ya ɗago da Jajayen Idanunsa ya ce,
“Jummai yanzu abin da kika jawo mana kenan, duk tarbiyyar da kika samu a wurin mahaifanki ta tafi a banza, sakayar da zaki yi musu kenan!”
Tunda ya fara maganar kanta ke ƙasa, ba abin da ke ranta sai kunya da nadama.
“Tambayarki zanyi, wa ya yi maki ciki?”
Daga duƙen ta rumtse idanunta, lokaci ɗaya kuma ta tuna lokacin da azzalumin nan ya wanka mata mari tare da faɗin “kashedin ki da cewa ni ne, don kashe ki zan yi”.
Shiru ta yi, kai ka ce ba da ita Kabiru yake ba.
Ai kuwa ya daka mata tsawa, don ba abin da ya tsana irin a yi watsi da shi idan ya yi tambaya.
A gigice ta ɗago tare da fashewa da kuka, “Dan Allah ku dena yi mun wannan tambayar”, tana faɗin haka ta shi da sauri zata fita.
Asabe dake bakin ƙofa ta fizgo ta, ai kuwa ta durƙushe a kan gwiwoyinta.
Lokaci ɗaya kuma Asaben na faɗin “Gidan Ubanwa zaki je.” Kusan a tare Kabiru da Malam Amadu suka yo kan Jummai ta da fasa wata irin ƙara “Wayyo Allah, Inna zan mutu.”
Cikin tsananin fushi Malam Amadu ya dubi Asabe, “Ke kam baki da hankali wallahi, kashe ta zaki yi?”
Ita kuwa Asabe ko a jikinta, don gani take wannan ce kaɗai hanyar da Jummai zata faɗa musu wanda ya yi mata ciki.
Kuka sosai Jummai ta riƙa yi, saboda ba ƙaramar buguwa gwiwoyinta suka yi ba.
Malam Amadu da ke jin zafin kukanta ya nufi ƙofa, kafin ya fita ya juyo ya ce ma Kabiru, “Banda duka Kabiru, a ƙyale ta idan ta ƙi faɗa”, bai jira jin me Kabiru zai ce ba ya yi tafiyarsa.
Ido Kabiru ya raka shi da shi, don shima zuciyarshi ta kare, tausayin Jummai ya shiga ranshi, don haka ba zai iya taɓa mata lafiyar jiki ba.
Fitowa shima ya yi, don ba zai iya jurar jin kukan Jummai ba.
Hakan ba ƙaramin ƙule Asabe ya yi ba, duban Jummai da ke ta rizgar kuka ta yi “Tunda kin zaɓi tona mana asiri, ki je, wallahi ba ni, ba ke, kuma KO RUWA NA GAMA BA KI a gidannan, azaba ce kin ɗaura aure da ita”, tana gama faɗin haka ta bankaɗo ta waje.
A wannan lokaci sai da Jummai ta zaɓi mutuwa a kan rayuwa, kuka ta riƙa yi kamar ranta zai fita, sai da ta yi mai isarta a wajen, sannan ta tashi da ƙyal ta koma cikin bukkarta.
Abu kuma kamar wasa, wunin ranar ko ruwa Bashir bai kawo mata ba.
Dalili da Asabe ta kwashe komai ta ɓoye, saboda ta daɗe da sanin yana ɗibar mata abinci yana kai ma Jummai.
Jummai kuwa kamar yunwa zata kashe ta, Allah ya taimake ta akwai ɗan sauran kokon da ta rage da safe, hannunta na kyarma ta ɗauka ta shanye.
Amma ba abin da yayi mata, sai ma ƙulle mata ciki da ya yi, haka ta kwana tana juye-juye har asuba.
Da safe ta yi ta zuba ido tana jiran Bashir ya kawo mata kalaci, amma shiru, sai can wurin shabiyun rana ta ji an jefo mata wani abu a baƙar leda, tana dubawa ta ga dankali ne.
Da hanzari ta ɗauki dankalin ta yi ta ci, aikuwa ya shaƙare ta ta yi ta shaƙuwa.
Kamar Bashir ya san tana buƙatar ruwa, sai gashi da ruwa cike da jug ya aje mata a bakin ƙofa, cike da tausayin kanta ta ɗauki ruwan ta sha.
Ƙulle sauran dankalin da ta rage ta yi, don ta san zata neme shi anjima.
Tsawon kwana ukku kenan tana cikin wannan hali, gabaɗaya yunwa ta sauya mata kamannu, duk ta yi baƙi da muni, Ɗan cikinta kuwa tun tana jin motsinsa har ta dena ji, hakan ne ya ƙara mata damuwa.
Zaune take tsakar gida ta haɗe kai da gwiwa, ba abin da cikinta ke yi sai juyawa, saboda duk wunin yau ruwa kaɗai ta sha.
Malam Amadu na shigowa, ya ga duhun mutum, da yake farin wata ya shiga duhu.
Da fitila ya hasko ta, “me kike yi yanzu a cikin wannan sanyin?”
A hankali ta ɗago kanta da take jin kamar zai tsage “Yunwa nake ji.”
Sanin an yi girki a gidan, ya ce “Toh zaman me kike yi, da har yanzu baki ci abinci ba?”
Ta ce “Ai Inna ta dena bani abinci.”
Take ranshi ya ɓaci, tunani ya shiga yi, anya Asabe Mutum ce, wane irin hauka ke damun ta da zata riƙa hana ‘yar cikinta abinci.
Cike da tausayin Jummai ya ce “Taso.”
Daƙyal ta iya miƙewa ta bi bayanshi, ƙofar ɗakin shi ta tsaya, shi kuma ya shiga ciki, abincinsa ya ɗauko ya miƙa mata, tana kyarma ta karɓa.
Ya ce “Zauna nan ki ci.”
Hannu baka hannu ƙwarya Jummai ta riƙa cin abincin, wani irin tausayinta ya kamshi, bai san sadda hawaye suka riƙa fita a idanunsa ba.
Duka ta cinye abincin saboda ba ƙaramar yunwa take ji ba.
Ya ce “Ya ishe ki?” Ta ɗaga kai.
Ruwa ya miƙo mata tasha, sannan ta tashi ta nufi ɗakinta.
Kwanciyarta kenan, sai gashi da ƙaton bargo, lulluɓa mata ya yi, sannan ya kunna mata maganin sauro.
Yana fitowa kuma sai ya ɗauko wani karyayyen ƙyaure ya gitta mata a bakin ƙofa.
Tana jin duk sadda ya yi mata wannan gatan, kukan zuci ta shiga yi tare da yi ma kanta Allah wadai.
Tun daga wannan rana Jummai ta samu sauƙi a gidan, don Malam Amadu bai fita sai ya tabbatar da ta yi kalaci, haka da rana, daddare ma sai ya tabbatar da ci abinci, kafin ya ci nashi.
Jummai na kwance cikin bukkar ta, wani tunani ya fara zo mata a zuciya, ba na komai bane sai na son ta faɗa ma iyayenta wanda ya yi mata ciki, don ta fahimci abin da suke son sani kenan.
Wani sashe na zuciyarta ya tambaye ta, “Mutuwa ki ke son yi ko?”
Watsi ta yi da maganar zuciyarta ta ce a fili “Indai hakan zai rage ma iyayena damuwa, toh na zaɓi in mutu.” Cike da ƙwarin gwiwa ta tashi, ba inda ta tsaya sai ƙofar ɗakin babansu.