Kan doguwar kujera Habeeb ya kwanta yana mai fuskantar rufin ɗakin. Fuskar Jummai da ke ta yi mashi gizo a idanu ce ta disashe mashi ɓacin ran da ya fito da shi daga ɗakin Uwani.
Tambayar kansa ya yi, "Wace ce waccan?"
Nazarin kyakkyawar fuskarta ya shiga yi, yana mai son gane da wanda ta ke kama.
Wani dogon tsaki ya ja lokacin da ya gano da Asabe take kama, ƙoƙarin yakice ta a zuciya ya fara yi, don a rayuwarshi ba wadda ya tsana irin Asabe, saboda Ummanshi ta bashi labarin irin kitimullin da suka yi da ita. . .