Zare hannunta ta yi daga riƙon da ya yi mata ta ce “Wai lafiya ya Habeeb?”
Idanunsa da suka fara kaɗawa izuwa launin ja ya buɗe a hankali, tare da jifar ta da wani mayen kallo, wanda sai da jikinta ya ɗan yi sanyi.
“Fateema” ya kira sunanta cikin kasalalliyar murya.
Idanunta na na cikin nashi ta amsa “Na’am”
ya ce “Bana son ki tafi”, lokaci ɗaya kuma ya riƙo duka hannayenta biyu ya fara murzawa a hankali.
Take tsikar jikinta ta tashi, cikin sanyin murya ta ce “Nima wlh bana so Yaya Habeeb, amma ba yadda zamu yi, tunda an koma school”,
Tana gama faɗin haka ta janye hannayenta don ba zata iya jurar abin da take ji ba.
Shiru ya yi, cikin ranshi kuma yana amsa umarnin da zuciya ke ba shi na ya taɓa jikin Jummai.
Daga bisani ya ce “Hakane, toh me zaki yi mani wanda zan riƙa tuna ki ina jin daɗi a raina?”.
Cikin rashin fahimtar zancensa ta ce “Kamar me kenan?”
Ya ce “Kamar komai ma Teemah.”
Murmushi ta yi tare da maida hankalinta ga titi, don bata san me zata yi mashi ba.
Ya ce “Kin yi shiru”, sai da ta kalle shi sannan ta ce “Wallahi ban san me zan maka ba.”
Kai tsaye ya ce “Toh ni na san me zaki yi mani.”
Tambayar shi ta yi “Toh miye?”
Har ya buɗe baki zai yi magana sai kuma ya yi shiru, ta ce “Ka yi shiru.”
Ya ce “Nauyin faɗa nake.”
Ta ce “Kada ka ji komai, ni taka ce”
Ido ya lumshe na wasu ‘yan daƙiƙu, saboda faɗuwar da gabansa ke yi.
Bayan ya buɗe idanun ya dube ta “Uhm, so nake daman….”
Ta ce “Oh Yaya Habeeb, ka tafi kai tsaye da maganarka, duk abin da kake so ka faɗa zan maka Insha Allah.”
Ya ce “Toh ai kunyar ki nake ji Teemah.”
Dariya maganarshi ta bata, ta ce “Yau ka fara jin kunyar tawa ko?”
Ya ce “Eh wallahi.”
Ta ce “Toh kada ka damu, faɗi duk abin da kake so in maka wanda ba zaka manta da ni ba.”
Matsowa ya yi dab da ita, tare da rungume ta a jikinshi, lokaci ɗaya kuma ya kanga bakinshi a kunnenta, “So nake kiyi mani haka, tare da ɗan kissing ɗina a baki”.
Ido ta zaro, gabanta na na wata irin faɗuwa ta ce “Subhanallahi, miye haka Yaya Habeeb?” Lokaci ɗaya kuma ta shiga kacaniyar ƙwace kanta.
Ƙin sakinta ya yi, sai ma ƙoƙarin saka bakinshi cikin nata da yake.
Janye kanta ta yi ta ce “Amma ka bani kunya wallahi”. Tana faɗin haka ta fizge jikinta, tare da ɓalle murfin mota zata fita.
“Ina zaki je” ya faɗa lokacin da ya riƙo mata hannu.
“Wata motar zan samu, don ba zan iya tafiya tare da kai ba”, ficewa ta yi daga motar tare da banko murfin da ƙarfi.
Ido Habeeb ya lumshe yana jin wani irin ɗaci a ransa, a yadda yake buƙatarta ko kusa bai ganin laifinsa, sai ma nata laifin.
Fitowa ya yi shima, tare da zagayowa inda take. Tana ganinshi ta ƙara haɗe rai.
“Ki shiga mu tafi” ya ce cikin faɗa.
“Ba zan shiga ba, ka buɗe mani ma in fito da Kayana.”
Ya ce “An ƙi a buɗe maki”
Wani mugun kallo ta jefe shi da shi.
“Toh ni kuma ba zan shiga ba, haka kawai ka kai ni ka baro”.
Ɗan shiru ya yi, daga baya ya sassauta murya don ya ga faɗan bai yi “Ni ba zan kai ki in baro ba, amma ki shiga don Allah mu tafi.”
Ta ce “Toh bana son abin da kake mani.”
Kai ya ɗaga “Ba zan sake ba.”
Yana rufe baki ya buɗe mata ta shiga.
Bayan ya koma ciki ya ce mata “Wallahi nima kin ban mamaki Fateemah, ace yadda muke son juna har zan iya neman wani abu a gunki in rasa, don Allah ki taimaka mani in rage zafin da nake ji a tare da ke.”
Ranta a ɓace ta ce “Ni fa ba ƴar iska bace, don haka ka dena mun wannan maganar”.
Kamar zai yi kuka ya ce “Nima ɗin ai ba shi bane.”
“Toh kada ka sake taɓa mani jiki, kuma in dai don haka ne kake so na, toh zan iya haƙura da kai wallahi.”
Lallashin ta ya riƙa yi akan ta amince ya ɗan taɓa jikinta, amma ta ƙi, hakan ne kuwa ya harzuƙa shi ya ce cikin kaushin murya “Dama shi ɗan ƙauye, duk inda ya ke sai an gane.”
Ta ji haushin maganar, amma ta ƙi yin magana, sai dai ta kalle shi.
Ya sake cewa, “Son dama da ake iƙrari duk na ƙarya ne.”
Cewa ta yi “Duk abin da zaka faɗa ba damuwata ba ne, ni dai ba zan bari ka illata mani rayuwa ba.”
Tada motar ya yi, suna tafiya yana faɗa mata baƙaƙen maganganu, wasu ta maida, wasu kuma ta yi shiru.
Da isarsu tashar mota ya tsaya “Toh a fitarmun a mota.”
Baki ta taɓe ta ce “Toh na gode”, tana gama faɗin haka ta buɗe motar ta fito.
Baya ta buɗe ta kwaso dukkanin kayanta, in banda tsarabar da ya siyo mata.
“Tunda Soyayyar ƙarya nake maka, ga tsiyatakun kayanka nan.”
Juyowa ya yi “Kada ki bar mani komai a nan, idan baki so ki, sai ki zubar.”
Bata bashi amsa ba ta rufe motar, tare da ta jan akwatinta ta tafi.
Bayanta ya bi da kallo har ta ɗan yi nisa.
Sai ya ji duk bai kyauta ba, fitowa ya yi tare da fiddo ledar, wani almajiri ya samu ya ce “Don Allah ka kai ma waccan mai akwatin a hannu,”
Karɓa almajirin ya yi, ya nufi Jummai.
Yana isa ya ce “Wai wancan mai motar ya ce a baki.”
Tana ɗaga kai ta hangi Habeeb har ya juya da motar ya tafi.
“Nagode”ta ce bayan ta karɓa.
Har ya juya ta kira shi, tare da fiddo biscuit ta bashi, godiya ya yi mata, ya juya yana murna.
Bata daɗe ba ta samu motar garinsu.
Tana isa gida aka yi ta murna da dawowarta, musamman ƴan ƙannenta da ta yi ma tsarabar kayan wasa.
Kowa na murna ita kuwa abin duniya duk ya ishe ta, “Dama haka Habeeb ya ke, shin zan iya cigaba da tarayya da shi?”, tambayoyin da ta shiga jera ma kanta kenan.
Kafin ta samu Amsa Asabe ta ce “Wai ko baki da lafiya ne Jummai?”
Ta ce “Wallahi Iskan mota ne ya sa mani ciwon kai,” Asabe ta ce “Ayya, toh ki sha magani”.
“Toh” ta ce, ta ɗauki maganin ta sha.
Zama ta yi don samar ma kanta mafita akan lamarin Habeeb.
A yadda take son shi kam ba zata iya haƙura da shi ba, amma zata yi nesa da shi don gudun kada ya sake taɓa ta.
Shima abin da ya ɗaukar ma ransa kenan, cewa ba zai sake neman Jummai ba, duk da hakan ba ƙaramar baraza bace a gare shi.
Wayar da ya ɗaukar mata alƙawali zai riƙa kiranta kullum, bai taɓa kira ba. Wani lokaci sai ya ji kamar ya kira, amma girman kai sai ya hana shi.
Idan kuwa abin ya ci ƙarfinsa, sai ya buɗe pics ɗinta ya yi ta sumbata.
Ita kuwa tamkar marar lafiya ta koma, tunanin Habeeb ya hana ta saƙat.
Suna komawa school ƙawarta mai suna Halima ta tambaye ta meke damunta, don ta lura da sauyawarta, cike da damuwa Jummai ta labarta mata dukkan abin da ya faru tsakaninta da Habeeb.
Halima ta ce “Hmm! Samarin yanzu duk haka suke fa, da kin haɗu da saurayi, toh abin da zai fara nema a wurinki shine ya taɓa ki, da kin yi gangacin bashi dama, toh zai kai ki ya baro, don haka ko da wasa kada ki bari ya sake taɓa ki”.
Jummai ta ce “Insha Allah ba zan sake ba, wancan ma ba da sani ba”.
Ce wa Halima ta yi “Toh Allah ya kyauta”, “Amiin” Jummai ta ce, suka cigaba da tattauna matsalar.
Jummai ta ce “Toh yanzu ya zan yi da son shi a raina, kin ga tunda na dawo bai neme ni ba, kuma mun yi da shi zai kira ni”.
Saida Halima ta yi nazari sannan ta ce “Toh ki kira shi mana, idan bai ɗaga ba ki ƙyale shi, tana yiyuwa ma dama ba son ki yake ba”.
Jummai ta ce “Nifa ba zan iya kiranshi ba”
Matsa mata Halima ta yi akan ta kira shi.
Fiddo wayar Jummai ta yi, har ta yi dialing numbersa, kafin ta fara tafiya ta yanke kiran, “Halima ni dai ba zan iya ba.”
Halima ta ce “Toh shikenan, kisa mashi ido, idan yana son ki, da kanshi zai neme ki.”
Abin da Jummai bata sani ba shi ne, kiran da ta yi ma Habeeb ya shiga kafin ta katse.
Yana zaune ɗakinshi ya hangi wayarshi na haske, yana dubawa ya ga “Teeman-Habeeb”
Wani irin daɗi ne ya ratsa shi, dama yana son kiranta kunya ta hana shi
Da sauri ya yi dialing Numberta. Jummai na cikin magana da Halima ta ga kiran Habeeb.
“Duba ki gani Halima, shine ya kira.”
Halima ta ce “Toh ko kiranki ya shiga ne?”
Jummai ta ce “A’a”
Alamu Halima ta yi mata da ta ɗaga wayar kafin ta tsinke.
Ɗagawa ta yi tare sa wayar a handsfree don Halima ta ji.
Daga can ya yi Sallama, bayan ta amsa ya ce “An tuna da mu kenan.”
Koda ya ce haka, sai ta gane kiran ya shiga, baki ta taɓe ta ce “Toh tunda ku bakwa son ladar zumunci ai shikenan.”
Sassauta murya ya yi “Ki gafarce ni Teemah, ban san me zan ce maki bane idan na kira.”
“Hmm, ai ba dai damuwa, tunda haka ka zaɓa ba wani abu,” Jummai ta faɗa idanunta na kan Halima.
Magana mai tausasa zuciya ya faɗa mata, tare da tabbatar mata shima bai da wani sukuni, tunaninta duk ya hana shi komai.
Bayan sun gama wayar Halima ta ce “Toh kin gani, kunya ce ke hana shi kiran ki.”
Murmushi Jummai ta yi, tare da yi mata godiya. Tun daga wannan rana Jummai da Habeeb suka dasa Soyayyar su a waya.
Duk abinnan Asabe bata sani ba, da yake Jumman ba a gidan take kwana ba, tunda Uwani ta yi aure, ta koma taya kakarsu kwana.
Da dare ya yi sai Habeeb ya kira ta, sai su kusa raba dare suna waya.
Wata irin hira mai kashe jiki suke yi, wanda duk masifarka ba zaka ji me suke cewa ba idan suna waya.
Hakan yasa kullum suna manne da juna a waya, Habeeb ya ce “Ban san me ya sa bana iya komai ba idan sautin muryarki na shiga a kunnena.”
Murmushi mai sauti kawai ta yi suka cigaba da hirarsu ta masoya.
Kakarsu ta ce “Ni dai na banu da wannan ƙus-ƙus a waya, Uwani ta tafi, ke kuma kin dasa daga inda ta tsaya”, Dariya Jummai ta yi “Toh Gwaggo ki liƙe kunnuwanki kawai” suka kama dariya.
Wata rana da suna waya ya tambaye ta “Yaushe zaki zo?”
Ta ce Sai bayan ka zo”
Ya ce “Toh kuwa kin kusa ganina.”
Bayan Hajiya Mairo ta huta daga tafiyar da ta yi, Alhaji Mai Nasara ya kwashe su gaba ɗaya suka nufo ƙauye.
Kowa ya yi murna da ganin Danginsa, Musamman Uwani da ta daɗe bata ga danginta ba.
Jummai kuwa bata san Uwani sun zo ba, sai da ta dawo makaranta ake gaya mata.
Tana cire Unifoam ta nufi gidan Kakarsu inda Uwani ta sauka.
Tana cikin sauri ta ji an ce “Ke ji mana.”
“Yaya Habeeb”
Ta faɗa a ranta, don duk inda ta ji muryarshi zata iya gane ta, kuma wannan ita ce sararshi idan ya haɗu da ita a waje, lokacin da ta je gidansu.
Juyowa ta yi zuciyarta cike da farinciki ta ce “Kai ne?”
“Ni ne da kai na” ya faɗa, yana ƙarasowa inda ta ke.
Zuciyoyinsu cike da farincikin ganin juna suka gaisa, ta ce “Na yi fushi ma.”
Ya ce “Da na yi me?”
“Me ya sa baka faɗamun zaka zo ba, kuma ko ɗazu sai da muka yi waya da kai.”
Ya ce “So nake in baki mamaki ai”, ta ce “Ka kuwa bani”. Dariya suka yi, ya tambaye ta inda zata je.
Wurin Uwani ta faɗa mashi zata, da yake ya san gidan ya ce toh zai iske ta a can.
Da farinciki Jummai ta isa wurin Uwani, murna kamar zasu haɗiye juna.
Ashe ƴan gulma sun ga lokacin da Habeeb ke Magana Jummai, har sun faɗo ma Hajiya Mairo.
Habeeb na komawa gidan kakanninsa Hajiya Mairo ta ce “Uban me ya haɗa ka magana da ƴar gidan Asabe”.
Ya ce “Wacece haka Umma?”, duk da ya san wadda take nufi.
Masifa ta shiga yi mashi, don ta fahimci rainin wayonsa ne ya motsa.
Bai ji faɗan da Ummansa ta yi mashi ba, Da yamma ya kira Jummai a waya cewa su haɗu, ta ce tana Islamiyya, amma da dare su yi mahaɗa idan ta dawo.
Habeeb ya ce “Toh ki samar mana wurin da ba mutane sosai, na ga ƴan garinnan naku sun cika sa ido”.
Inda kuwa mutane basu cika wucewa ba Jummai ta samo musu, domin gabatar da hirarsu ta yaushe gamo.
Habeeb ya ce “Wai haka kika ƙara kyau Fateemah” ta ce “A hakan?” ya ce “Ƙwarai kuwa,” ta ce “Bayan rashin ganin ka duk ya ramar da ni.”
Ya ce “Toh ai yanzu gani ko,” Murmushi ta yi suka cigaba da hira.
Rashin yawan mutane a wurin ya sa shaiɗanin dake zuga Habeeb sake zuwa a wurinsu.
A wannan karon wurin Jummai ya fara tsayawa, tare sa mata jin daɗin gugar jikinta da Habeeb ke yi a hankali, wanda daɗin kalaman da yake faɗa mata ya hana ta janye jikinta.
Sannan ya ƙarasa wurin Habeeb ya buɗe mashi baki, “Fateemah” ya kira sunanta.
Cikin wata irin murya ta amsa.
“Ki bani dama in taɓa jikinki.”
Gabanta na wata irin faɗuwa ta ce “Tsoro nake ji”, ya ce “Na me?”
Ta ce “Inna ta hanani, ta ce ciki ake samu idan namiji na taɓa mace.”
Sassauta murya ya yi, “Ai abin bai kai nan ba, kawai zamu ɗan rage kewa ne, wancan ai sai kin zama mallakina ko.”
Yana faɗin haka ya jawo ta a jikinshi.
Karkarwa jikinta ya shiga yi, tana son hana shi, tana tsoron kada ya yi fushi irin na rannan.
“Ki saki jikinki” ya faɗa cikin raɗa, wasu irin abubuwa ya cigaba da yi mata, tare da nuna mata yadda shima yake so ta yi mashi.
A tsorace Jummai ta riƙa yi mashi yadda duk yake so.
Godiya ya riƙa yi mata, don burinshi ya gama cika.
Ta ce “Tafiya zan yi, dare ya fara”. Ya ce “Toh ina zaki ce kin tsaya?”
“Ai gidan kakarmu nake kwana, zan ce Inna ce ta tsaida ni”.
Ya ce “Yauwa baby, to sai gobe ko,” ta ɗaga kai.
Sallama suka yi, ta nufi gidan kakarsu, Uwani ta ce “Ke bakya gudun dare ko”.
“Aiki na ƙarasa ma Inna,” ta ba Uwani amsa.
Gaba ɗaya ta tsargu da kanta, bata bari suka yi hira ba, ta haye gadon ƙarfe ta kwanta.
Tun daga wannan rana Habeeb ke zuwa wurin Jummai suna sheƙe ayarsu, tun tana jin tsoro har ta saba.
Ko da ya koma gida sai suka dasa da sex chat, da yake ƴar ƙaramar wayarta na facebook.
Kullum zumuɗin sake haɗuwa suke. Da Habeeb ya ga sun daɗe basu haɗu ba, sai ya haɗa Kaya ya ce wurin iyayen Hajiya Mairo zai je.
Hajiya Mairo ta yi mamaki, don rabon da ya ce zai je ƙauye da kansa tun yana yaro.
Da zai tafi ya biya wurin Uwani ya ce idan tana saƙo ta bada.
Ta ce “Ka gaida mani kowa, amma bani da saƙo.”
Kayan daɗi Jummai ta haɗa ma Habeeb, zauren kakarsu aka yi zancen.
Aikuwa kamar su cinye Juna, ita kakar bata san wainar da ake toyawa ba, a zatonta kwashe-kwashen samarin Jummai ne.
Duk abin da suke Habeeb bai taɓa kusantarta ba, sai lokacin da zai tafi. Mahaɗa suka yi a wajen gari, bayan an taso daga makaranta.
Suna cikin romancing juna wasa ya chanja salo.
Jummai ta ce “Wallahi tsoron ciki nake.”
Ya ce “Ai na sha ƙwayoyin hana ɗaukar ciki.”
Ta ce “Dama maza na sha?” Ya ce “Eh”
Ta ce “Toh kada a samu matsala maganin yaƙi yi, ya ce “Ba za’a samu ba.”
Kalallame ta ya yi da magana, har ta amince.
Bayan mota suka koma, suka cigaba da abin da suke so,
Bata taɓa tunanin haka ake ji ba, don sai da zafi ya sa ta yi nadamar ba shi kanta.
Kuka ta riƙa yi akan zafin da take ji, ya ce “Kada ki damu, da kin zauna ruwan zafi zaki dena ji.”
Yana gama faɗin haka ya rungumo ta tare da goge mata hawaye “Sai nake jin dama matata ce ke, amma ba komai, mun kusa yin aure ai.”
Ita kuwa wani baƙinciki ne ya taso mata, da ta tuna zina ce fa suka yi.
Astagfirullah” ta faɗa a fili, tare da zare jikinta ta tashi.
“Me ya faru?” ya tambaye ta.
Ta ce “Zina ce fa muka yi yanzu.”
Shiru ya yi tare da sosa kai.
Tare suka fito a motar, ta maida Hijabinta.
Zuciyarta cike da tsanar kanta ta ɗauki jaka da takalmanta ta sa.
Bankwana suka yi, ta tafi tana ɗingishi.
Kallon da wasu mutane ke mata ne ya sa ta ga kamar sun gane abin da ya faru.
Daidaita tafiyar ta yi, har ta samu ta isa gida.
Asabe na ganin yanayin tafiyarta ta tambaye ta, “Lafiya?”
Jummai ta ce “Tsallen kwaɗi aka samu a makaranta”.
Asabe ta ce “Ai maganinku kenan”.
Ruwan zafi ta dafa da sunan zata gasa ƙafafaunta, tana shiga banɗaki ta gasa jikinta.
Toh faruwar wannan abu ta ƙeƙashe ma Habeeb zuciya, burinshi kawai su sake haɗuwa.
Kiran Jummai ya yi a waya tare da bijiro mata da buƙatarshi.
Da ta nuna ƙin amincewa sai ya shiga yi mata romon baka, cewar da ya gama degree zai aure ta, kuma Masters ma zasu tafi ƙasar waje a tare, daga can sai ta yi karatunta itama.
Ta ce “Toh kana ganin iyayenmu zasu yadda mu yi aure?”
Ya ce “Zasu yadda mana, abin da har Umma na faɗa mawa ina sonki”
Jummai ta ce “Toh ya ta ce.”
“Ce wa ta yi ta amince,” kuma duk da ƙarya ya ke, asali ma ko maganar budurwa Ummansa bata so, burinta kawai ya yi karatu.
Jummai ta ce “Wallahi ban yadda ba”, dariya ya yi “Toh shikenan, kin san dai dole ma in aure ki, ko don in cigaba da samun ƙaunar da kike nuna mani.”
Amincewa ta yi da buƙatarshi, ta ce “Toh da Aunty Uwani ta haihu zan zo.”
Marairaicewa ya yi “Har sai ta haihu?”
Ta ce “Ai ta kusa.”
Matsawa ya yi akan zai zo ƙauye, ta ce “A’a”
Tun kafin Uwani ta haihu Jummai ke jin ba daɗi a jikinta, amma sai ta ƙi faɗi don gudun a hana ta zuwa.
Uwanin na haihuwa ta kwashi kayanta sai birni, da yake ya kama lokacin hutu. Kwananta biyu da zuwa ta fara zazzaɓi.
Kuɗi Uwani ta bata akan ta je wata clinic da ke cikin unguwarsu. Tana cikin tafiya ta ga Habeeb a mota, tsaida shi ta yi.
Cike da jin daɗi ya tsaya, don tunda ta zo basu haɗu ba.
Tambayarta ya yi ina zata je.
Ta ce “Clinic”
Ganin yadda take magana a kasalance ya tabbatar mashi da bata da lafiya.
“Mu je in kai ki Asibiti, a rufe wurin yake.”
Shiga ta yi suka nufi asibiti.
Kafin su je ta kira Uwani cewar ta wuce Asibiti, saboda Clinic ɗin a rufe take.
“Toh” Uwani ta ce, saboda sun taɓa zuwa asibitin a tare.
Da zuwa ta yi sa’ar ganin likita, bayan ya mata ƴan tambayoyi, sai ya bata awon fitsari.
Ras! gabanta ya faɗi, tunani ta shiga akan wane dalili zata yi awon fitsari?.
Zaune ta samu Habeeb a waje, yana ta saƙa yadda zai kusanci kusance ta kafin su koma gida.
“Kin gama?”, ya tambaye ta.
“A’a, awon fitsari zan yo.”
Mamaki bayyane a fuskarsa ya ce “Awon fitsari kuma?” ta ce “Eh wai.”
Kai ya gyaɗa “Toh je ki yo.”
Fitsarin ta yo ta kawo ma likita ya auna.
Bayan wasu daƙiƙu ya ce “Madam kina da juna biyu.”
Wata irin faɗuwa gabanta ya yi, Ido ta zaro tamkar mayya ta ce “Juna biyu fa ka ce likita”
Ya ce “Ƙwarai Hajiya.”
Take zufa ta rufe ta, bakinta na sallallami ta fito, wurin Habeeb ta nufa tare da zama jagwab a gefenshi, don juwa ta fara kwasarta har ba ta ganin gabanta.
Magana take son yi amma tashin hankali yasa ta kasa.
“Ke lafiya?” Habeeb ya tambaye ta.
“Ciki, wai ciki gare ni Habeeb” ta faɗa tana sheshshekar kuka.
“What!” Ya faɗa tare da miƙewa tsaye.
Tsayen itama ta tashi, bin bayanshi ta yi don har ya nufi wurin likita.
Da shigarshi likita ya tabbatar mashi da cewa ciki ne gare ta.
Habeeb ya ce a sake gwadawa, aka gwada, nan ma sakamako ɗaya ne.
Clinic ɗin da ya yi mata ƙaryar a rufe take suka nufa nan ma maganar ɗaya ce.
Wani irin kuka Jummai ta riƙa yi, tamkar ranta zai fita, shima ɗin duk ya kiɗime tunda ya taɓa kusantarta, toh amma bai ba ransa daga wannan zata samu ciki ba.
Dafa kafaɗarta ya yi, “Don Allah Fateema ki dena kuka”, ƙasan ransa kuma yana saƙa yadda zai taimaka mata a cire cikin tun kafin a gane.
Cikin kukan ta ce “Toh idan ban yi kuka ba in yi me, ai duk kai ne ka ja mani, sai da na ce maka ciki ake samu, amma ka matsa dole.”
Wani mugun kallo ya yi mata “Wace irin magana ki ke faɗi; kina nufin ni na yi maki ciki?”
Ta ce “Toh waye idan ba kai ba.”
Cikin tsananin fushi ya ce “Ƙarya kike wlh,kin san dai inda kika samu abinki, ni da sau ɗaya na taɓa kusantarki?”
Gardama suka riƙayi, ita ta ce bayan shi ko hannunta wani bai taɓa riƙewa ba.
Shi kuma ya ce ƙarya ta ke, kusanci ɗaya kuma na farko bai isa ace ciki ya shiga ba, don haka ta je can ta nemi wanda ya yi mata ciki.
Haka suka yi ta gardama, ƙarshe Habeeb ya ce ta fitar mashi daga mota ko ya ɓaɓɓala ta.
Ce wa ta yi “Wallahi ba zan fita ba.”
Aikuwa ya buɗe motar tare da fidda ta da ƙarfi, ya ja motarsa ya bar ta nan.