Skip to content

Ko Ruwa Na Gama Ba Ki | Babi Na Ashirin Da Biyu

2
(1)

<< Previous

Motarsu Hajiya Mairo da Habeeb na sauka a tasha suka tari Napep.  Unguwarsu Habeeb ɗin suka nufa, suna cikin tafiya ne Hajiya Mairo ta ji ya kwanto a kan kafaɗarta, lokaci ɗaya kuma yana ta sauke numfashi, hankali a tashe ta ɗan duƙo da kanta tare da faɗin “Habeeb mene ne?”

Murya can ciki ya ce “Zuciyata nake jin kamar zata fashe, Umma.” Ajiyar zuciya ta sauke, ƙasan ranta kuma tana jin itama kamar tata zuciyar zata fashe, saboda tunda ta ga yanayinsa take jin wani irin tashin hankali, gani take kamar zata rasa shi.

Ido ta lumshe ta kuma buɗe, sannan ta yi magana cikin raunin murya, “Ko muje asibiti?”

Kai ya ɗaga mata alamar, “Eh.”

Duban mai napep ɗin ta yi tare da faɗa mashi su je wata private hospital da ke cikin gari. Juya akalar napep ɗin ya yi, cikin ƙanƙanin lokaci suka isa Asibitin.

Basu wani ɓata lokaci ba suka ga likita. Ganin yana jin jiki yasa likitan bashi gado, inda kuma ya nemi agajin likitoci biyu ƴan’uwansa suka haɗu a kan Habeeb, don yanayinsa akwai ban tsoro.

Ita kuwa Hajiya Mairo kan wani benci ta zauna, wanda daga inda take tana kallon ɗakin da Habeeb yake.

Wayarta ta fiddo a jaka, sannan ta danna number Alhaji Mainasara, bugu biyu ya ɗaga, saboda ya san zancen bai wuce na Habeeb.

Ko amsa sallamar da ya yi mata bata yi ba, ta ce, “Alhaji muna asibiti fa, ciwon Habeeb ya tashi”, kamar zata yi kuka ta ƙarashe maganar.

Daga can ya yi magana cikin tsananin tashin hankali ya ce, “Wa ce asibitin?”, faɗa mashi ta yi, ya ce “Ina zuwa.” Katse kiran ta yi sannan ta maida wayar a jaka.

Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tare da kafe ɗakin da Habeeb ke ciki da idanu, a zahiri ƙofar ɗakin take kallo, amma a baɗini duniyar tunani ta lula, wanda bai wuce na ɗaurin mintin da duniya ta yi musu ita da ɗanta ba.

Haka rayuwar duniya take dama kamar rawar ƴan mata, na gaba komin daɗewa sai ya koma baya, toh yanzu su Asabe ne gaba, da su ake ɗasawa, saɓanin baya da suke ƙasƙantacci kuma abin wulaƙantawa a wurinta. 

Tuna irin cin fuskar da ta yi musu lokacin da suka zo da maganar ciki ta yi, wanda wannan kaɗai ya isa ya hana su yafe mata ita da ɗanta, bare har su ɗauki ƴarsu su basu, ko da kuwa ba ta samu miji ba.  

“Allah gamu gare ka” ta faɗa a zahiri.

Nadamar data zame mata jiki ta shiga yi, “Allah wadaran ƙiyayya da gaba, Allah wadaran son zuciyata da na bi, yanzu gashi nan zan rasa ɗana”, wasu hawaye ne suka cika mata ido, domin ta sadaƙas Habeeb ba zai samu Jummai ba.

Tana cikin wannan tunani ne Alhaji Mainasara ya shigo, kallo ɗaya zaka yi mashi ka fahimci yana cikin tashin hankali.

Miƙewa ta yi tun kafin ya ƙaraso inda take.

Maganar farko da ya yi mata lokacin da ya iso ita ce, “Ina Habeeb ɗin yake?”

Nuna mashi ta yi, bai sake magana ba ya nufi ɗakin, bayanshi ta bi, kafin su isa kuma sai ga likitocin sun fito.

Wucewa sauran suka yi, shi kuma wanda ya karɓi Habeeb ɗin ya tsaya wurinsu.

Gaisawa suka yi, sannan Alhaji Mainasara ya ce, “Mahaifin Habeeb ne, don Allah wane hali yake ciki?”

Murmushi likitan ya yi, sannan ya ce, “Mu je ku ganshi.”

Cikin ɗakin suka shiga, faɗuwa gabansu ya yi don bai motsi, take Alhaji Mainasara ya fara tunanin ko irin wancan ciwon ne.

Hannunsa na kyarma ya riƙe hannun Habeeb da ke ɗaure da drip, Hajiya Mairo kuwa kuka ta fashe da shi,”Likita ya haka?” ta faɗa tare da riƙe ƙafafun Habeeb ɗin.

Ɗan motsin da hannunsa da ƙafarsa suka yi ne ya sanya suka ji ɗan sanyi a ransu.

Ganin sun firgice ya sa likitan fara magana ya ce,

“Allurar bacci aka yi mashi saboda ya ɗan samu sauƙi, nan da wasu awonni zai falka da ikon Allah.”

Kai Alhaji Mainasara ya gyaɗa sannan ya ce, “Toh ciwon fa, miye sila likita?”

Likitan ya ce “Zuciya ce Alhaji, ai kamar an taɓa yi mashi aiki ko?”

Kai Alhaji Mainasara ya sake ɗagawa “Ƙwarai an taɓa yi mashi.”

“Toh aikin ne ke son samun matsala, amma cikin ikon Allah an shawo kan matsalar, sai dai ba’a son ya falka da damuwa.”

Ita dai Hajiya Mairo hankalinta na wurin ɗanta, bata ma san me likitan ke cewa ba, addu’a kawai take mashi akan Allah ya dubi duminiyarsu.

Likitan na gama yi musu bayani ya fita.

Cike da tausayi Alhaji Mainasara ya kalli ɗansa, domin ya san sai dai Habeeb ya mutu don in ba tsananin rabo ba, toh ba zai samu Jummai ba.

Shafa kan Habeeb ɗin ya yi sannan ya ce, “Duk abin da yake alkhairi a gareka Allah ya tabbatar maka da shi.”

“Amiin” Hajiya Mairo ta ce, sannan ta fara magana cikin muryar kuka “Alhaji, Habeeb ya san yanzu Jummai ta samu miji, don Allah ko dai wurin wanda zai auri Jumman zamu mu nemi alfarma ya bar mashi, tunda ya fishi buƙatar ta.”

Ɗan shiru ya yi yana nazari, daga bisani ya girgiza kai. “A’a, in dai adalci zamu yi, toh kada mu je, kuma ni ban san ko waye ma zai aure ta ba.”

“Toh Alhaji baka ga halin da yake ciki ba, mutuwa fa zai yi.”

Ɗan gajeren murmushi ya yi don ya fahimci idonta ya rufe.” Shi wancan ɗin kina zaton ba zai mutu ba idan aka yi yunƙurin raba shi da ita tunda yana sonta, mu cire son zuciya sannan mu rungumi ƙaddara. Idan Habeeb na da rabon shan ruwa, Allah ya tashi kafaɗunsa, idan kuma kwanansa ya ƙare, toh Allah ya rahamshe sa.”

Kuka ta fashe da shi, gani take don yana da wani ɗan ne ya faɗi haka “Ba’a san inda ake dacewa ba Alhaji, wurin Asabe zan je da kaina in roƙi alfarma ta faɗa mani angon, idan ya so har can sai in je da kaina.”

Taɓ, abin da ya koro ɓera har ya shige cikin wuta, toh tabbas ya fi wutar zafi, ashe akwai ranar da Hajiya Mairo zata buɗi baki ta ce zata je wurin Asabe neman alfarma, lallai duniya ta gama da ita.

“Ba zan ce kada ki je ba, amma ina baki shawarar ki jinkirta.” Alhaji Mainasara ya faɗa yana kallonta.

Kasa cigaba da magana ta yi, sai dai kuka, shima ji yake kamar yayi kukan, musamman da ya ga Habeeb na ta yamutse fuska, alamar ciwo na cigar shi cikin baccin.

Sun kusa awa ɗaya a nan, daga bisani Alhaji Mainasara ya ce zai je gida ya dawo, miƙewa ta yi itama ta nemi ya rage mata hanya zata kai kayanta gida.

Tare suka fito, sai da suka biya wurin likitan suka yi magana sannan suka fito.

Kai tsaye Unguwar da Hajiya Mairo ke haya suka nufa, tun daga farkon unguwar zaka fahimci mazauna cikinta suna jin jiki.

Wani layi ta nuna mashi, wanda duk layin ba gida mai kyau bare ya sa ran nan take zaune.

Suna zuwa wurin wani gida mai karyayyen ƙyaure ta ce a tsaya.  Fitowa ta yi tare da kayanta, jakar Habeeb kuma ta bar mashi a mota.

sai da hankalinsa ya tashi da ya ga ta shiga gidan.

Tunawa da mugun halinta ne ya kawo ta gidan sai ya dena jin damuwa. Key ya yi ma motar tare da juyawa ya nufi gida.

Uwani na ganin yanayinsa ta san ba lafiya, cike da damuwa ta tambaye shi. “Alhaji lafiya?”.

Ya ce, “Habeeb ne ke asibiti.” Sallalami ta fara yi, tare da sake tambayar shi “Me ya faru kuma?”,

Ya ce, “Ciwon zuciyar dai.”

Shiru ta yi don ta san sila, a jiyar zuciya ta sauke ta ce, “Allah ka kawo mana mafita kan wannan lamari.” “Amiin” ya ce, suka shiga ciki.

Wanka ya yi, yana fitowa ya nufi masallaci don gabatar da sallar magrib. Da dawowarsa ko abinci bai ci ba suka tafi asibitin tare da uwani.

Can suka iske Hajiya Mairo har ta koma. Kuka Uwani ta shiga yi da taga Habeeb ɗin, Alhaji Mainasara ya ce, “Ashe da ku kuka yi jinyarsa a UK sai kun ƙarar da hawayenku saboda kuka.”

Ido Uwanin ta lumshe lokaci ɗaya kuma ta goge hawayen da ke fita a idonta. “Bawan Allah Habeeb, Allah ya baka lafiya.” Ta faɗa bayan ta buɗe idon.

Hajiya Mairo dake riƙe da hannun Salim ta ce “Amiin”, don tunda suka shigo ta jawo shi ta riƙe.

Shiru ɗakin ya yi kowa ya faɗa duniyar tunani.

Wayar Habeeb dake kan gadon ce ta fara ruri, Hajiya Mairo ta ɗaga kiran.

Muryar Nasir ta ji yana faɗin, “Kun dawo ne Habeeb.”

Idonta na kan “Habeeb ɗin ta ce, “Mun dawo, amma Habeeb ɗin na Asibiti.”

Sunan asibitin ta faɗa mashi sannan suka yi sallama, ba’a fi minti goma ba sai ga Nasir ya iso.

Idanunsa cike da ƙwalla ya ce, “Abba me ya samu Habeeb haka?” saboda bai san an masa aiki ba.

Alhaji Mainasara ya ce, “Ai Habeeb ya daɗe bai lafiya, har aiki aka yi masa a can.”

Wani irin tausayinsa ne ya kama shi, “Allah ya bashi lafiya.” Nasir ɗin ya faɗa.

Likita ne ya shigo ya ƙara dudduba shi, tare da tabbatar musu da sai cikin dare zai falka.

Shawarar wanda zai kwana aka yanke, Alhaji Mainasara da Nasir ne zasu kwana.

Gida aka maida su Uwani, sannan Nasir shima ya koma ya faɗa ma mahaifinsa.

Tare suka dawo da Babansa domin ya ga Habeeb, sosai ya jajanta ma Alhaji Mainasara.

A gida kuwa Hajiya Mairo kasa bacci ta yi, kusan raba dare ta yi tana sallah tare da nema ma ɗanta sassauci a wurin Allah.

Can wurin ɗayan dare Habeeb ya fara motsi tare da buɗe ido.

Nasir dake kansa ya ce, “Sannu Habeeb.”

Ɗan ɗaga kai Habeeb ɗin ya yi, Alhaji Mainasara na sallame Sallah ya taso, sannu ya yi mashi shima.

Ganin yana yunƙurin tashi suka kama shi ya zauna.

Tea mai kauri Nasir ya haɗa mashi, kuma cikin ikon Allah ya sha.

Washe gari bayan an yi Asuba Alhaji Mainasara ya koma gida.

Yanayin da ya samu Uwani ya nuna kwana ta yi kuka, domin idanunta sun ƙanƙance haɗe da kumburi.

Cike da damuwa ya zauna gefenta a kan gado, magana ya fara yi ƙasa-ƙasa cikin sigar lallashi, “Haba Gimbiya, da kuka na maganin damuwa da abin bai kawo haka ba, don Allah ku sanya ma zuciyarku salama, duk hukuncin da Allah ya yanke mai kyau ne.”

Idanunta cike da ƙwalla ta ce, “Alhaji na yi wani tunani, me zai hana a nemi shi wancan ya janye ya bar ma Habeeb neman auren.”

Kai ya girgiza ya ce, “Ku dai mata tunanin ku ɗaya ne, haka Mairo itama ta ce.”

“Toh Alhaji ai wannan ita ce mafita,” ya ce “A ganinku ba, gaskiya ba za’a yi ma kowa magana ba, rungumar ƙaddara ne kaɗai mafita.”

Kwatanta mata ya yi akan shima wancan ɗin zai iya faɗawa fin halin da Habeeb yake ciki, tunda dai so sunan shi so, don haka abar ma Allah lamarin.

Sosai ta fahimci maganarshi, addu’ar mafita suka nema a wurin Allah, sannan ita ta shige kitchen, shi kuma ya faɗa banɗaki ya yi wanka.

Tana gama haɗa breakfast din tayi wanka itama, sannan ta yi ma Salim, bayan ta shirya suka yi break, suna gamawa suka ɗunguma zuwa Asibitin. A kan hanya ne suka ga Nasir kan mashin zai koma gida, hakan ya tabbatar musu da Hajiya Mairo tana asibitin.

Zaune suka samu Habeeb, Hajiya Mairo kuma na shirin haɗa mashi tea.

Gaisawa suka yi da Hajiya Mairon, sannan suka dube shi tare da yi mashi sannu, kai ya ɗaga alamar yauwa.

Uwani ta ce, “Da sauƙi ko?”

“Eh da sauƙi.” Ya faɗa a hankali, tare da miƙa ma Salim hannu ya ce, “Zo”, Hajiya Mairo ce ta ɗora Salim ɗin a kan gado.

Aunty Uwani ta ce ma Salim ɗin, “Toh ka gaida Yaya.”

Cikin rashin iya magana ya ce “Yaya, ina nana,”  dariya su duka suka yi, Alhaji Mainasara ya ce “Bagwarin kawai.”

Breakfast ɗin da suka zo dashi Uwani ta buɗe, farfesun hanta ne ta zuba a cikin bowl sannan ta miƙa ma Hajiya Mairo ta ce, “A bashi.”

Hajiya Mairo na arba da wannan hanta yawunta ya tsinke, saboda ta ji haɗi.

Bayan ya gama ci ne ta ƙara mashi da tea, yana gamawa ya ɗan jingina kanshi da bango tare da lumshe idanu.

“Ka kwanta mana idan bacci zaka yi” Alhaji Mainasara ya faɗa yana kallon shi, buɗe idanun ya yi sannan ya ce “Ba bacci zan yi ba.”

Ɗan haɗe rai Alhaji Mainasara ya yi sannan ya ce, “Toh kuma bana son damuwa, yanzu a hakan kana iya lulawa duniyar tunani, daga nan kuma ciwo ya tashi ayi ta fama.”

Kai kawai ya ɗaga tare da lumshe idanun, don ba zai iya dena tunani ba.  Wani kallo Alhaji Mainasara ya yi mashi, sannan ya juya ya fita.

Tashi Hajiya Mairo ta yi akan kujerar da take, sannan ta tura ma Uwani ta zauna.

Kan darduma ta ja Salim suka zauna, wani irin son shi take, saboda yadda yake haka Habeeb yake sadda yana yaro.

Basket ɗin da breakfast ɗin yake ta jawo ta ce “Yunwa fa nake ji, Uwani taimaka mani da kwanon da kika zuba ma Habeeb.”

Ƴar dariya Uwani ta yi, sannan ta miƙa mata, hantar ta zuba, sannan ta zuba soyayyen dankali da kuma ƙwai a plate.

Rabon da ta ci abinci irin wannan har ta manta, don haka ne ta cika cikinta har ba wuri.

Alhaji Mainasara da likita ne suka shigo. Yadda Alhaji Mainasara ya barshi, haka kuma ya same shi, likitan yana gani ya ce, “Habeeb.”

A hankali ya buɗe idanun, “Banda damuwa fa.” ya faɗa lokaci ɗaya kuma yana ɗaura mashi wani drip ɗin.  

Gyaɗa kai Habeeb ya yi tare da faɗin, “Toh doctor.”  Abubuwan da ya kamata likitan yayi mashi, sannan suka fita shi da Alhaji Mainasara.

Kwanciya Habeeb ɗin ya yi, cikin lokaci bacci ya ɗauke shi.

Uwani da Hajiya Mairo kuwa hira suka riƙa yi, kai ka ce ba gaba a tsakaninsu, sosai Uwani ta yi mamakin yadda Hajiya Mairo ta canja, don tunda take basu taɓa hira irin wannan ba.

Ita kanta wannan fargaba da take ji idan ta ga Hajiya Mairo, ko ta ji an faɗi sunanta, toh ta dena ji, ta rasa dalilin haka.

Alhaji Mainasara ne ya sake dawowa, tare da faɗa musu zai je ya dawo, “Toh a dawo lafiya” suka ce, ya ce “Amiin”, zai fita kenan Salim kuma ya sanya kuka wai zai bi shi, da ƙyal aka yi mashi wayau sannan Alhaji Mainasara ya fita.

Fitarsa kenan sai ga Nasir ya shigo, da girmamawa ya gaida su, sannan ya wuce wurin Habeeb, cike da tausayi ya riƙa kallon fuskar Habeeb da ke bacci, tunanin irin ciwon da ya samu abokinsa ya riƙa yi.

Motsi Habeeb ɗin ya shiga yi alamar zai tashi.

“Habeeb” ya kira sunan shi, a hankali ya buɗe idanu sannan ya ce, “Nasir ka dawo.”

Kai Nasir ɗin ya ɗaga, sannan yayi mashi ya jiki.

Daga can su Hajiya Mairo suka taso, Uwani ta ƙara yi mashi sannu, Hajiya Mairo kuwa tana kallon shi ta ji kamar zata yi kuka.

Zaune Habeeb ya tashi tare da lumshe idanu, don wata irin faɗuwar gaba ce ya falka da ita.

Hajiya Mairo kuwa kasa control ɗin kanta ta yi, kamar zata yi kuka ta ce ma Uwani “Mu je waje, akwai inuwa a can.”

Uwani ta fahimci damuwarta, “Toh” ta ce suka fita, ƙarƙashin wata bishiyar zaintun suka zauna, wanda kuma ya kwantsama ƴaƴa, wasu ɗanyu wasu kuma sun nuna.

Yaran da ke wurin sai ciro ma mutanen da ke ƙarƙarshin bishiyar suke, da yake yana da girma, kusan duk a nan mutane ke shan inuwa.

Take ɗan dake cikin Uwani ya ce zaitun ɗinnan yake so. Hajiya Mairo ce ta yi ma yaran magana suka tsinko musu.

A can ɗaki wurin Habeeb kuwa, zama Nasir ya yi tare da kafe Habeeb da ido.

Habeeb ya san akwai tarin tambayoyi a bakin Nasir, don haka ne ma ya buɗe mashi hanyar tambayar.

“Nasir ka ga yadda na koma ko?”

Murmushi Nasir ya yi ya ce, “Na gani Habeeb, meye sila?”.

Sai da Habeeb ya ɗan lumshe idanu sannan ya ce “Fateema.”

“Kamar ya Fateema?” Nasir ya tambaye shi.

Mawiyacin halin da ya shiga tun bayan haɗuwarsa da ita a UK, da aikin da aka yi mashi, kawo ga dawowarta gida da kuma auren da zata yi, duk sai da ya ba Nasir Labari.

Daga Ƙarshe ya ce, “Nasir ina jin mutuwa zan yi, don Fateema ta fi ƙarfina a yanzu.”

Kai Nasir ya girgiza sannan ya ce, “Ba zaka mutu ba abokina, duka abubuwan da suka faru ƙaddara ce, ba mahani, idan ma laifi ne toh an samu sakamakonsa a yanzu, don haka babu wani abu da ya yi saura wanda zai cutar da wani a yanzu.”

Habeeb gani yake kamar Nasir bai fahimce shi ba,

 “Nasir yanzu ma kuwa cutar take ai.”

Nasir ya ce “Idan an so cuta zata cutar ko?”

Ɗan nisawa ya yi sannan ya ce “Habeeb, na san halin da kake ciki, don haka bana buƙatar ka faɗi mani idan na yi Magana.”

Ido kawai Habeeb ya lumshe.

Nasir ya ce “Shawara ce zan baka a matsayinka na musulmi wanda ya yadda da ƙaddara, a kan ka sanya ma rayuwarka haƙuri, ka ɗauki wannan a matsayin wata jarabawa, sannan ka nemi taimakon Allah a kanta, kada ka sake wahalar da zuciyarka ko ta iyayenka saboda Fateema.

Na san abu ne mai wahala ka dena sonta, amma abu ne mai sauƙi ka dena wahala a kanta.  kuma aure! idan Allah bai nufa ka aure ta ba ko duniya zata haɗu ba zaka aure ta ba, haka idan matarka ce ba mahani, don haka ka kwantar da hankalinka, kuma ka cigaba da addu’a.”

Sosai Nasir ya mashi Nasiha, ya kuma nuna mashi yanzu fa shi da mahaifansa ke cikin damuwa.

Ko mutuwa ya yi su ke da asara, don haka ya dena damuwa da wanda  bai san yana yi ba.

Habeeb ya gamsu da maganar Nasir, ya kuma ɗaukar ma ransa haƙura da Jummai, barin ma da ya tuna irin kyarar da ta yi mashi.

“Nasir na ji daɗin maganarka, da tuni an faɗa mani irinta, da abin bai kai haka ba.”

A take ya ji ƙarfi a zuciyarsa, hira sosai suka riƙa yi, Nasir kuma na ta ƙara tausar mashi da zuciya.

A can waje kuwa Alhaji Mainasara ne da abokansa suka shigo asibitin. Gaisawa suka yi da su Hajiya Mairo sannan suka nufo wurin Habeeb.

Su Hajiya Mairo sun yi mamakin ganin sauyin Habeeb, musamman Alhaji Mainasara da ke ta zullumin dawowa ya ganshi.

Ya jiki Mutanen suka yi mashi, da yake sun san komai suka ɗan yi mashi Nasiha.

Cike da jin daɗi Alhaji Mainasara ya dube shi “Ya dai Malam Habeeb.”

Murmushi Habeeb ɗin ya yi ya ce, “Da sauƙi Abba.” Duban Nasir ya yi ya ce, “Wai Nasir da sauki?”

Dariya Nasir ya yi, sannan ya ce “Sosai Abba.” 

Alhaji Mainasara ya san ƙoƙarin duk na Nasir ne, don haka ne ya ce, “Godiya nake Nasir.”

Hajiya Mairo kuwa daɗi ne ta ji, sai dai kuma mugun tausayinsa take.

Dangi ne suka yi ta zuwa na kusa dana nesa ganinsa, domin abin ya ba kowa tsoro.

Sai da ya ƙara kwana biyu sannan aka sallame shi. Kai tsaye gidan Ummanshi Alhaji Mainasara ya nufa da su. 

Tunda suka tsaya ƙofar gidan gaban Habeeb ke faɗuwa, tunanin me suka tsaya yi a wannan layin mai bola da kwatoci ya shiga yi.

“Mu je ko Habeeb” Hajiya Mairo ta faɗa lokacin da ta buɗe motar, jiki a sanyaye ya buɗe ya fito, ba abin da ke tashi sai warin bolar da ke jikin bangon gidan.

Alhaji Mainasara ya lura da sauyawar yanayin Habeeb, amma sai ya basar. Fitowa ya yi suka shigar da kayan tare, sannan ya ce zai je ya ɗauko Uwani.

Habeeb kuwa kasa zama ya yi a ɗakin, sosai yanayin gidan ya ɗaga mashi hankali, domin dai ko danginsu da ke ƙauye babu mai lalataccen gida irin wannan.

Rufin ɗakin ya shiga kallo wanda zallar kwano ne, ba abin da ke fitowa ta cikinsa sai hucin rana.

Duban shi Hajiya Mairo ta yi ta ce, “Ka zauna mana.” lokaci ɗaya kuma tana nuna mashi katifar da ke yashe a ƙasa, don baccin ita da ledar ƙasa babu wani abu da za’a zauna a kai.

Jiki ba ƙwari ya zauna gefen katifar, “Umma wai ina kuɗinki, kika kama wannan gidan haya.”

Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce “Kuɗi ai babu su Habeeb.”

Mamaki bayyane a fuskarsa ya ce, “Kamar ya ba kuɗi Umma”, don shi dai ya san kuɗin da ta mallaka har ta ƙare rayuwarta ba zasu ƙare ba.

Labarin yadda kuɗinta suka salwanta a wurin Hajiya Sa’a ta faɗa mashi.

Aikuwa take ya harzuƙa, don dama ba ƙaunar Hajiya Sa’a yake ba.  “Wallah ko mutuwa ta yi sai anbiya ki a kuɗin gado Umma.”

Ganin ranshi ya ɓaci kuma tana tsoron faɗawarshi damuwa ta ce, “A’a, na nabar mata, duniya ce ai.”

Halin ƙasƙancin da Hajiya Sa’a ta shiga ta faɗa mashi, baki ya taɓe ya ce, “Ai kaɗan ma ta gani, tunda zalunci ta sa ma kanta.”

Hajiya Mairo sai ta ji kamar da ita yake, domin ta yadda da duniya ce ke bi da ita itama.

Ɗan kishingiɗawa ya yi kan katifar, daga kishingiɗen suka riƙa hira shi da Ummanshi.

Suna cikin hirar ne su Uwani suka zo, girki mai rai da lafiya ta kawo musu.

Suka ci suna ta santi, Habeeb ya ce “Umma, har yanzu banga wanda ya kai ku iya girki ba ke da Aunty Uwani.”

Dariya Hajiya Mairo ta yi ta ce, “Ka cire ni nima, Uwani ta dabance a wurin girki.” suka kama dariya.

Warin bolar dake shigowa gidan ne ya riƙa tuƙar cikin Uwani, amai ta riƙa kwarawa, Hajiya Mairo ta ce “Ko dai warin bolar nan ne ya sa ki amai.”

Kai ta girgiza ta ce, “A’a, na daɗe ina yinshi.”

Hajiya Mairo ta ce “Allah ya sauƙe toh, ciki mai sanya amai bai da daɗi.”

Sun so kai dare a gidan, amma wannan amai ya sa dole Uwani ta yi ma Alhaji Mainasara waya cewar ya zo ya ɗauke su.

Ba’a jima ba sai gashi ya zo suka tafi. A hanya ne ta ke ce mashi “Alhaji yanayin Hajiya Mairo tausayi yake bani.”

Baki ya taɓe ya ce, “Toh ya dena baki tausayi ma, duk halin da ta shiga ita ta ja ma kanta, kuma kema shaida ce.”

Kai kawai ta gyaɗa, domin gaskiya ya faɗi.

Hira suka riƙa yi jefi-jefi, har suka isa gida.

Kwanan Habeeb uku a gidan mahaifiyarsa, wanda da ba ita ke cikin wannan gida ba ko zaman minti biyar ba zai iya ba.

A kwana na huɗun ne ya shirya komawa gidansu, Har gida Hajiya Mairo ta raka shi, sun daɗe suna hira sannan ta fito, part ɗinta ta kalla, sai kuma ta tuna gidan da take ciki.

Ajiyar zuciya ta sauke ta ce “Allah ka dafa mani” sannan Habeeb ya raka ta, ta samu abin hawa.

Yana dawowa daga rakiyarta ya wuce ɗakinsa, kan kujera ya zauna, tare da dafe kai domin abubuwa ne cunkushe a zuciyarsa.

“Yanzu haƙura zan yi da Fateema, me yasa ƙaddara kika shigo mani a fannin soyayya.”

Ido ya lumshe, tare da matse ƙwallan da suka cika mashi ido.

Anya zai iya jurar rayuwar maraici, domin tamkar maraya yake jin kansa, ba uwa a gida, kuma ba masoyiya.

Wasu hawayen ne suka cigaba da malala, “Tabbas ni na jefa kaina a wannan maraici, na cutar da kaina na cutar da wasu, Allah ka yafe mani.”

Tunanin halin da mahaifiyarsa take ciki ya shiga yi, ya zama dole ya san abin yi, amma kafin nan zai fara neman alfarma a wurin Abbansa, domin ba zai iya ɗaukar rashi biyu a lokaci ɗaya ba, fata ya riƙa yi Allah ya sa Abbansa ya saurare shi don abin mai girma ne.

Washe gari da asuba da suka je masallaci Abbanshi ya ce yana son ganinshi a ɗakin Uwani, domin shi ma yana da maganar da yake son yi da shi.

Suna shigowa Habeeb ya nufi ɗakinshi, bai jima ba ya fito ya shiga ɗakin Uwani.

Zaune ya samu Abbanshi da Uwani akan kujera three-seater.

Ƙasa ya zauna ya gaishe da su, bayan sun amsa ne wurin ya ɗan yi shiru.

Gyaran murya Alhaji Mainasara ya yi sannan ya ce, “Mun kira ka ne domin mu yi maka magana ta ƙarshe, wadda idan ka ji ta, toh zaka tsira da rayuwarka, idan ka yi watsi da ita, toh duk halin da lafiyarka ta samu kanta, kai ka sanya ta.

Na ji daɗin ganin yadda ka gyagije, hakan ya nuna ka fara rage damuwa a ranka, toh haka ake so, kuma dama shine sanadin kiran.”

Kan Habeeb na ƙasa yana sauraron sa, Uwani ma ta kasa kunne tana ji.

Cigaba ya yi da fa ɗin “Ka ɗauki wannan abu a matsayin ƙaddara, ka kuma cire duk wata damuwa, sannan ka nemi zaɓi a wurin Allah, idan ka yi haka, toh zaka samu mafita mai kyau a wurin Allah.”

Kai Uwani ta jinjina ta ce “Gaskiya ne.”

Tabbas Habeeb ya ji daɗin maganar Abbanshi, ga wadda kuma Nasir ya yi mashi, wadda tun da ya fara bin ta ya ji sauƙi, toh ina ga ya haɗa da ta Abbansa.

Ɗago kanshi ya yi sannan ya ce “Na gode Abba, kuma Insha Allah zan cire duk wata damuwa a raina, na haƙura, na bar ma Allah komai.”

Kamar zai yi kuka ya ƙarashe maganar, sosai suma suka tausaya mashi, musamman Uwani.

“Yauwa Habeeb, da ikon Allah mafita zata zo” Uwani ta faɗa tana kallon shi.

Alhaji Mainasara kuma ya sanya mashi albarka.

Shiru wurin ya yi, daga bisani Habeeb ya fara magana cike da fargaba, don ba lallai ne Abbanshi ya saurare shi ba, sannan haka Uwani ma.

“Abba don Allah wata alfarma nake nema a wurinku”

Alhaji Mainasara ya ce, “Alfarma Habeeb?”

Kai Habeeb ɗin ya ɗaga, sannan ya yi shiru.

“Ina jinka ka faɗa.” Alhaji Mainasara ya ce.

“Don Allah Abba, ka maido mahaifiyata a ɗakinta, tana cikin damuwa.”

Wata irin faɗuwa gaban Uwani ya yi, shi kuwa Alhaji Mainasara neman walwalarsa ya yi ya rasa.

Habeeb kuwa kasa ɗago kanshi ya yi don bai san da wane ido zai kallesu ba.

“Habeeb, Ka nemi wata alfarma, amma ba wannan ba, domin mahaifiyarka ba zata taɓa chanja hali ba.”

Alhaji Mainasara ya faɗi haka, yana rufe baki ya tashi ya nufi bedroom.

Ido Habeeb ya rumtse yana jin gabansa na cigaba da faɗuwa, tsoron abin da Uwani kuma zata ce ya shiga ransa.

Muryarta ya ji ƙasa-ƙasa, yana ɗago kai ya ga tana yi mashi kallon tausayi.

“Ka kwantar da hankalika, mahaifiyarka zata dawo da ikon Allah.”

Tana gama faɗin haka ta bi Alhaji Mainasara a ɗaki.

Zaune ta same shi saman gado, gefenshi ta zauna ta ce, “Haba Alhaji, so kake ya rasa ransa kenan, ba mata ba uwa, ka duba mashi mana.”

Fuska a murtuke ya ce, “Ke ba Uwarsa ba ce kenan.”

“Eh, Hajiya Mairo ce uwarsa, ita ce zai raɓa ya ji sanyi a ransa, ita ce motsinta zai sa ya manta da duk wani ƙunci, duk wata kulawa da zan yi mashi ba zata kai ta mahaifiyarsa ba, don haka ka duba mashi.”

Shiru ya yi tare da nazarin maganar ta, gaskiya ta faɗa, sai dai Hajiya Mairon ce da matsala.”

“Uwani kin san wacece Hajiya Mairo, kin san halinta fa.”

Katse mashi magana ta yi da “Halinta na da dana yanzu ba ɗaya ba, kai ko halinta na nan saboda ceton ran ɗanka zaka iya haƙura da shi.”

“Uwani kin dena so na ko, ke kike cewa na maido maki kishiya,” ya faɗa a marairaice.

Rungumo shi ta yi ta fashe da kuka, haƙiƙa ba don son ranta ba, sai don jihadin lafiyar Habeeb.

Cikin kukan ta ce “Ba ranar da zan dena sonka, kuma banƙi har a aljanna in zama ni kaɗai ba, amma dole mu ceci rayuwar Habeeb.”

Ido ya lumshe tare da ɗora haɓarsa a kanta, “Toh zan yi Nazari,” share mata hawayen ya yi sannan ya cigaba da sanya mata albarka, don shi gani yake har yanzu ba macen da ta kai ta kirki.

Habeeb kuwa yana komawa ɗakinsa ya zauna gaban gado tare da haɗe kai da gwiwa, a wannan yanayi kam ya fidda ran samun wani farinciki a sauran rayuwarsa.

Tunawa da ba’a son bawa ya riƙa yanke ƙauna da rahamar Allah ya sa shi kai kukanshi ga Allah “Allah ka dubi raunina, ka kawo mani mafita mai kyau, Allah ka share mani hawayena, sannan ka sanya mani dangana a zuciyata.” Sosai ya riƙa kai kukanshi ga Allah, domin shi kaɗai ya san azabar da yake sha a zuciyarsa, ko Jummai da ya ce ya haƙura da ita, faɗi ne kawai, amma a zuciyarsa yana jin ba daɗi. Sannan ga tsananin damuwar halin da mahaifiyarsa, wanda a yanzu ji yake ya shafe duk wata damuwa ta shi.

 Yana cikin wannan yanayi ne Nasir ya shigo, cike da damuwa Nasir ya duƙa tare da dafa shi ya ce, “Haba Habeeb, me yasa ka kasa koya ma zuciyarka haƙuri ne.”

Ɗagowa Habeeb ya yi da kansa, hawaye wasu na korar wasu ya ce, “Nasir ta ya zan iya ɗaukar haƙuri da rashin mahaifiyata a kusa dani, Allah zai iya chanja mani Fateema, amma mahaifiya fah, Nasir ba zan iya jurar ganin mahaifiyata cikin ƙasƙanci ba.”

A hankali ya Nasir ya rumtse idanu, cikin ransa kuma yana jin tausayin Habeeb, zama ya yi ƙasa suna fuskantar juna, sannan ya ce “Ka yi haƙuri Habeeb, komai yana da farko da kuma ƙarshe.”

Sosai ya lallashi Habeeb akan damuwarsa, bayan Habeeb ɗin ya bashi labarin yadda suka yi da Abbanshi.

A wurin Alhaji Mainasara kuwa, duk ba daɗi a ransa, ba wai Hajiya Mairo ce bai son maidowa ba, halinta yake gudu, wanda tsaf zata iya wargaza musu farincinkinsu da yayi saura.

Har ɗaki ya iske Habeeb, lokacin yana ɗaukar Online lesson a laptop ɗinsa.

Habeeb ɗin na ganinshi ya rufe laptop ɗin ya tashi tsaye, “Abba Sannu.”

“Yauwa Habeeb.” Ya faɗa tare da kallonshi cikin tausayi.

Kan gado ya zauna. Habeeb kuma ya zauna ƙasa.

Ƴar hira suka taɓa ta ɗaa da mahaifi, sannan Alhaji Mainasara ya yi mashi bayani akan yana son farinkinsa, sai dai yana tsoron Hajiya Mairo.

Marairaicewa Habeeb ya yi ya ce “Abba Insha Allah abin da ya faru a baya ba zai sake faruwa ba.”

Ɗanshiru Alhaji mainasara ya yi daga bisani ya ce, “Toh shikenan zata dawo, amma ka yi shiru da bakinka, ka bari sai mun kimtsa tukunna.”

Wani irin farinciki ne ya cika zuciyar Habeeb, godiya sosai ya yi ma mahaifinsa, domin ya zaftare mashi kaso mai yawa na damuwa.

*****

Yau ce asabar, kuma ranar da iyayen Ameer zasu zo nema masa auren Jummai.

A wannan rana zukatan mutane da yawa cike suke da farinciki, wasu kuma abin ba’a cewa komai, musamman Alhaji Mainasara wanda kowa ya san dalilin damuwarsa.

Asubar fari shi da Uwani suka fara shirin tafiya ƙauye. Wurin ƙarfe goma suka gama shiri sannan suka fito.

Magana Alhaji Mainasara ya yi ma Habeeb cewar zasu je ƙauye, fatan dawowa lafiya Habeeb ɗin ya yi musu, sannan suka shiga mota suka tafi.

A can kuwa ana ta shirin tarbar baƙi, an yi girki kala-kala masu rai da lafiya.

Su Uwani basu daɗe da isa ba, sai ga motocinsu Ameer sun iso.

Kai tsaye fadar Maigari suka sauka, domin shi da Alhaji Mainasara da kuma Kabiru ne iyayen Jummai.

Mamaki ne fal da zuciyar Alhaji Mainasara lokacin da ya ga Alhaji Aminu, wato yayan Ameer, kuma shine babban abokinsa a lokacin suna UK. 

Jindaɗi cike da fuskokiknsu suka miƙa ma juna hannu, Alhaji Mainasara ya ce “Ikon Allah, Alhaji ba dai ku ne angunan ba.”

“Aikuwa dai mune, ƙanena ne angon.” Alhaji Aminu ya bashi amsa.

Gaisuwar yaushe gamo suka yi, Alhaji Mainasara kuma ya faɗa mashi Jummai ɗiya ce a wurinshi, Alhaji Aminu ya ce, “Tuwona maina kenan” suka kama dariya.

Gaisawa suka yi da sauran mutane, anan aka nemi auren Jummai, kuma aka biya sadaki, wanda aka sanya nan da wata ɗaya za’a ɗaura aure.

Murna wurin Ameer bata faɗuwa, yana haɗuwa da Jummai ya ce “Saura ƙiris dai mafarkinmu ya zama gaskiya.”

Cike da kunya ta kama dariya, dariyar shima ya yi suka cigaba da hirarsu ta masoya.

Alhaji Mainasara da Alhaji Aminu kuwa suna baro wurin Maigari suka dasa hirarsu ta abokai, anan Alhaji Aminu ya shaida mashi Jummai ce yarinyar da yake bashi labarin bata da lafiya a gidanshi.

Shi kuma Alhaji Mainasara ya bashi labarin ita ce wadda Habeeb ke so ya aura.

Cike da jin daɗi suke hira, amma Alhaji Aminu na jin haka jikinsa ya yi sanyi, shi kaɗai ya san me yake saƙawa a ransa, domin zai iya rubutu litattafai a kan halin da ya ga Habeeb ya shiga saboda Jummai, kuma yanzu sai ace wani ne zai aure ta ba shi ba.

Alhaji Mainasara ya lura da sauyin yanayinsa, amma sai ya basar.

“Toh ya jikin Habeeb ɗin yanzu” Alhaji Aminu ya sake tambayar shi, duk da a gaisuwarsu ta farko sai da ya tambaye shi.

“Habeeb kam ya murmure Alhaji, yanzu haka shirin komawa UK yake da ikon Allah.”

Kai ya jinjina sannan ya ce, “Allah ya ƙaro lafiya.”

Alhaji Mainasara ya ce “Amiin ya Allah.”

Cikin gidansu Jummai suka shiga, da girmamawa su Asabe suka tarbe su, nan Alhaji Mainasara ke shaida musu alaƙarsa da Alhaji Aminu.

Kowa yayi farinciki da jin wannan, musamman Asabe.

Da yamma liƙis ne kowa ya kama hanyar garinsu, aka bar Asabe da Jummai sai su Basheer cikin gida, domin hada su Aisha aka tafi.

Sosai suka ji ba daɗi da tafiyarsu Aisha, Asabe ta ce, “Kai ni ban taɓa ganin mutanen kirki irin waɗannan ba.”

Dariya Jummai ta yi ta ce, “Wallahi kuwa Inna.” Labarin irin ɗawainiyar da su Aunty suka yi da ita a lokacin da su Alhaji Lawwali suka kusa kashe ta, ta faɗa mata. Asabe ta ce, “Allah Sarki, Allah ya saka musu da Alkhairi.”

Hira suka ɗaura, nan Jummai ta cigaba da bata labarin azabar da ta sha a wurin Alhaji Lawwali. Tsoro ne ya kama su Basheer. Asabe kuwa kamar zata yi kuka ta ce, “Allah ne zai saka maki.” Sai dai wani abu, har yanzu Asabe bata san Jummai ta yi zaman bariki ba, don an kwaɓi Jummai ko da wasa kada ta faɗa mata, kuma bata faɗi ba.

Bayan su Ameer sun ɗauki hanya ne kuma ya ke tambayar Alhaji Aminu inda ya san Alhaji mainasara.

Cewa ya yi “A UK, yana da kirki.” Labarin irin kyakyawar dangantakarsu a can ya bashi, sannan ya bashi labarin ɗansa Habeeb.

Ameer ya ce “Ai nasan Habeeb” hira sosai suka cigaba da yi, Alhaji Aminu kuma a ƙasan ransa yana ta saƙawa da kwancewa.

 Suna isa gida Aunty ta ga ya yi jugum.

Tambayar sa ta yi, “Lafiya?”

Sai da ya nisa sannan ya ce, “Na shiga rudani Hajiya, yarinyar nan akwai wanda yafi Ameer buƙatarta.”

 Haɗe fuska Aunty ta yi ta ce “Kamarya, dama ana yin haka?”

Ya ce “ƙwarai”, labarin mawuyacin halin da Habeeb ya shiga ya bata, daga ƙarshe ya ce, “Shi yafi dacewa da Ita ba Ameer ba, don haka zan ce Ameer ya janye ya bar masa.”

Kai tsaye Aunty ta ce, “Wannan ai ba magana ce Alhaji, shi Ameer ɗin kashe shi za’a yi a raya wani ke nan,” cikin fushi ta yi maganar, wanda tunda yake da ita bata taɓa yi mashi irin haka ba. Domin ita shaida ce a kan yadda Ameer ke son Jummai.

Fahimtar da ita ya shiga yi ya ce “Ba kashe shi za’a yi ba, jihadi zai yi, kuma Allah ba zai barshi haka ba.”

Ficewa ta yi daga ɗakin ba tare da ce komai ba, don wannan tsantsar rashin adalci ne.

Washe gari ta tashi kicin kicin da fuska, yara na gani suka fara tambayarta,”Umma lafiya.” Ta ce, “Ba komai.”

Kiranta Alhaji Aminu yayi tare da nuna mata yadda zuciyar Habeeb ta kusa dagargajewa, a zaton shi zata tausaya ma Habeeb, sai ji yayi ta ce “Shine fa ya jefa kanshi, don haka ba abin tausayi bane.”

Kwatanta mata ya shiga yi a karo na biyu, tare da tabbatar mata da shi zai samar ma Ameer mata da ta fi Jumma. Son Jummai ta kasance a cikinsu ya hana ta fahimtar maganarsa.

Ƙarshe ma ta samu Ameer ta ce “Kada ka yadda da duk abin da Alhaji ya zo maka da shi.”

Mamaki ne ya kama Ameer, karon farko kenan da ta fara zuga shi akan kada yayi ma ɗan’uwansa biyayya, saɓanin baya da take faɗa mashi bin ɗan’uwansa kamar bin iyayensa ne, domin shine kaɗai ya rage masa, kuma yake ji da duk wata buƙata tasa.

Gabansa ba faɗuwa ya ce “Aunty me ya faru toh”.

“Ka bari zaka ji.” Tana faɗin haka ta dafe kai, Ameer kuma bai matsa mata ba akan sai ya ji me yake gudana, don ya ga tana cikin damuwa.

Zuciyarsa cike da fargaba ya tashi ya fita, “Toh me ke faruwa ne?” ya tambayi kansa.

A wurin Alhaji Aminu ne kaɗai amsar take, don haka ne ya zaƙu ya ganshi domin jin abin da ke faruwa.

Inda suke aje motoci ya nufa, tare da jingina da ƙarfen rumfar, daga can cikin zuciyarsa kuwa sai bugawa take. Wayarsa dake aljihu ce ta yi ƙara, yana dubawa ya ga Habibty, murmushi ya yi sannan ya ɗaga wayar.

Duk yadda ya so binne damuwar da ke cikin zuciyarsa sai da Jummai ta gane, domin ta ji muryarsa ba kamar kullum ba.

Daga can ta ce, “Lafiya dai ko?”, sai da lumshe ido saboda matsananciyar faɗuwar da gabansa ya yi sakamakon fitowa da Alhaji Aminu ya yi. “Bana jin daɗi ne Habibty.”

Cike da damuwa ta ce, “Me ya faru?”

Alhaji Aminu na nufo shi, faɗuwar gabansa tana ƙaruwa “Wallahi ban sani ba, kisa ni a Addu’a.”

Ta ce, “Insha Allah.” Sallama suka yi, ya maida wayar Aljihu.

Alhaji Aminu ma faɗuwa ce gabansa ya shiga yi, domin shi kanshi ya san bai ma ƙanensa adalci ba.

Gaisawa suka yi, sannan Alhaji Aminu ya ce “Magana nake son yi da kai Ameer, ko kuma in ce alfarma nake nema a wurinka, idan ka ji zaka iya, toh ina godiya, idan kuma ba zaka iya ba, toh ba damuwa har ƙasan raina.”

Murmushi Ameer ya yi sannan ya ce, “Toh Yaya, Allah ya bani ikon iya yi maka wannan alfarma.”

“Amiin” Alhaji Aminu ya ce, sannan ya dasa da faɗin “Don Allah jihadi zaka yi, wanda tun kafin ka yi shi Allah ya musanya maka da mafi alkhairi, Fateema nake haɗa ka da Allah ka bar ma Habeeb, kai kuma zaka maye gurbinta da ɗaya daga cikin ƴaƴan abokaina.”

Tamkar aradu haka Ameer ya ji saukar wannan magana, domin bai taɓa kai ma ransa abin ya kai nan ba, ido ya rumtse tare da riƙe ƙarfen rumfar da suke tsaye da ƙarfi.

“Inna li Llahi Wa inna ilaihi raji’un” kawai ya ke furtawa a fili, domin ji yake kamar zuciyarsa zata tarwatse.

Dafa shi Alhaji Aminu ya yi, sannan ya cigaba da magana “Ka kwantar da hankalinka Ameer, idan har ba zaka iya ba, toh ba dole, amma kafin ka yanke hukuncin yadda da rashinta, toh ka yi shawara tukunna.”

Har a lokacin idanun Ameer a rufe suke, don haka bai san ma sadda Alhaji Aminu ya tafi ba, sai da ya buɗe sannan ya hange shi zai shige falo.

“Fateema zan rabu da ita, mafarkina, cikon burina, ba zan iya ba – ba zan iya ba.”  yana gama faɗin haka ya fashe da kuka mai tsuma zuciya, don gani yake kamar har an ƙwace mashi ita.

Cikin tashin hankali ya shigo gidan, bakinsa na kyarma ya dubi su Aisha, “Ina Aunty?”

Idanunsa ƙyam a kansa suka ce, “Tana kitchen.”

Da sauri ya nufi kitchen ɗin, Salma ta dubi Aisha ta ce, “Kuka yake.” Aisha ta ce “Na gani.”

Tashi suka yi suka bi bayansa, don jikinsu ya basu ba lafiya ba.

Yana shiga kitchen ya sake fashewa kuka, Tamkar Uwa Ameer ya ɗauke ta, don haka ne ya riƙo mata hannaye duka ya ce, “Aunty ba zan iya rabuwa da Fateema ba, mutuwa zan yi.”

Ido Aunty ta lumshe, wasu zafafan hawaye suka zubo mata, su Aisha da Salma ba basu san sadda suka fashe da kuka ba saboda tashin hankali.

Sun gama tsara yadda zasu yi rayuwa da Jummai idan ta shigo cikinsu, don haka akwai damuwa idan wannan mafarkin nasu bai zama gaskiya ba. Zare hannayenta ta yi ta ce, “Ameer, ba wanda zai raba ka da ita, ka rabu da batun Alhaji kawai.”

Tana gama faɗin haka ta juya ta nufi ɗaki, masifa shiga zazzaga ma Alhaji, ta ce “Wato rayuwar wani ta fi ta ƙanenka, wallahi wannan zalunci ne, kun shiga haƙƙin Ameer.”

Har ta ƙaraci sababinta bai tanka mata ba, domin gani yake bata fahimce shi ba.

Ameer kuwa ɗakinsa ya koma tare da rashewa ƙasan carpet, gani yake ƙarshensa ya zo, kuka ya riƙa yi kamar ransa zai fita, gabaɗaya ji yake duniyar ta masa ƙunci.

Kwatanta irin halin da zai shiga idan ya rasa Jummai ya riƙa yi, kawai sai ya ga mutuwa ce zai yi, don zuciyarsa ba zata iya ɗauka ba, cikin kukan ya ce “Allah kana gani ni mai rauni ne, kada ka jarabce ni da abin da ba zan iya dauka ba ya Allah.

kashe wayoyinsa ya yi, don a yanzu bai buƙatar komai.

Kiransa Dr.Misau ya riƙa yi yana son faɗa masa cewar ya kusa isowa,  domin dama zai zo wurin Aisha.

Ganin bai samu number shi ba ya ce ma Aisha ta kawo mashi waya.

A kulle ta samu ɗakin, tana bubbugawa ya taso, ta matukar kaɗu da ganin yanayinsa, domin idanunsa sun kaɗa sun yi ja.

Yana kar6ar wayar ya koma, tun kafin ya zauna Misau ya kira.

Cikin raunin murya Ameer ya amsa sallamar da ya yi mashi.

Kasantuwarsu abokai take misau ya fahimci halin da Ameer yake ciki, “Me ya faru ne?” Misau ya tambaye shi.

Ameer ya ce “Sai ka zo dai.”

katse kiran suka yi, sannan ya dora kansa a gado, yana jin kamar zuciyarsa zata tarwatse, pics din Jummai ya rika kallo, sai ya ji ya kara sonta.

Sai da ya gama kallon pics ɗin sannan ya yi wanka da ƙyal domin tarbar abokinsa, shirinsa ke da wuya sai ga Misau ya iso.

Ƙagare Misau yake ya ji halin da abokinsa ke ciki, don haka tun kafin ya ga Aisha ya fara tambayar Ameer damuwarsa.

Ameer ya ce “Bana son tarwatsa maka farincikin da ka zo da shi, ku fara ganawa da sahibarka tukunna.”

Haka kuma aka yi, sai da suka gama soyewarsu shi da Aisha, ya ci ya sha, sannan suka dawo ɗakin Ameer.

Buƙatar Yayanshi ya fada ma Misau cewar ya rabu da Fateema, zai nema mashi wata.

Tamkar almara Misau ya ji maganar don haka ne ma ya ce “Da gaske ne, ko kuma gwada ka dai yayi ya gani”, kai Ameer ya girgiza sannan ya ce “Wallahi ba wasa a ciki Dr., faɗa mani ina zan sanya kaina, ina son Fateema son da bana jin zan iya rayuwa ba tare da ita ba.”

“Tirƙashi,” Misau ya faɗa, domin abin bana wasa bane, gaba daya kansa ya kulle, haka kawai, rabuwa da masoyi ai bala’i ne mai zaman kansa.

“Toh wai a wane dalili ne za’a ce ka bar ma Habeeb,” Misau ya sake tambayar Ameer.

Cike da jin haushi ya bashi amsa da “Wai baban Habeeb abokinsa ne, kuma Habeeb ya fini buƙatarta, ji wata banzar hujja don Allah.”

Ko kusa Misau bai ji daɗi hakan ba, don ji yake kamar yayi kuka shima.

Ameer ya ce “Ya zanyi da rayuwata ne.”

Shiru Misau ya yi yana nazari, wannan lamari ba na wasa bane, don haka sai an yi nazari kafin a san yadda za’a yi.

“Ameer, na jiye maka tashin hankalin wannan abu, sai dai me ina baka shawarar daka nutsu ka yi nazari akan abin da yayanka yake so, ka san dai ba zai cutar da kai ba, kuma ba zai raba ka da abin da kake so ba faace ya baka wanda ya fishi, don haka kada ka bijire mashi.”

Shawara ya bashi a kan ya nutsu, kuma ya sassauta ma zuciyarshi kafin ya yanke hukunci.

shi Ameer bai ma san wane hukunci zai yanke ba don bai son ɓata ran dan’uwansa.

Shawara Misau ya sake bashi akan yaje ya fara ganin yarinyar, kafin ma ya yanke hukunci.

Bayan tafiyar Misau ɗin ne ya samu Aunty ya faɗa mata shawarar da ya yanke.

Zuciya ba daɗi ta ce “Toh Ameer, duk abinda Allah ya za6a mai kyau ne.”

Rana aka fidda domin Ameer ya je gidan abokan Alhaji Aminu domin fara ganin yaran kafin ma ya yanke hukunci.

Gidan wani Alhaji Musa suka fara zuwa, sai dai a yadda ya ga ɗiyar ba katsari, domin suturar jikinta kaɗai bata gamsar da shi ba.

Daga nan suka wuce gidan Alhaji Muhammad, da shigarsu gidan ya ji wata irin nutsuwa ta shige shi.

Falon Alhaji Muhammad suka sauka, inda aka yi musu tarba mai kyau, bayan sun ɗan huta ne Alhaji Aminu ya tambayi Alhaji Muhammad “Wai ina Meema ne, na daɗe ban ganta.”

“Makaranta ce ta ɓoye ta, amma yanzu tana gida,” Alhaji Muhammad ya bashi amsa.

“Meema” Ameer ya faɗa a ransa, domin jikinshi ya bashi ita ce wadda ake son haɗa shi da ita.

Waya Alhaji Muhammad ya ɗauka tare da danna number Meema, tana ɗagawa ya ce “Ki zo ga Abbanki ku gaisa.”

Ƙofa Ameer yayi ma zuru yana jiran ganin shigowar Meema, ba’a fi minti biyar kuwa ba sai gata ta shigo.

Sanye take cikin baƙar doguwar riga mai ado na golden ɗin zare, kanta kuma ta yafa gyalen rigar, wanda ya fito da dukkan kyanta.

Idanun Ameer a kanta yana kallon yadda take tafiya a natse, lokaci ɗaya kuma yana jin saurin bugun zuciyarsa na ƙaruwa.

Sai da ta durƙusa kanta na ƙasa sannan ya ɗauke kansa, amma duk da haka fuskarta yake kallo a cikin zuciyarsa.

 “Abba ina wuni” ta gaida Alhaji Aminu cikin muryarta mai sanyi, wadda kuma ta sanyaya zuciyar Ameer lokacin da ta shiga dodon kunnensa.

Amsawa Alhaji Aminu yayi, sannan ya tambaye ta “Ya karatu?” Ta ce “Alhamdulillah Abba.”

Juyowa ta yi wurin Ameer tare da gaida shi, cike da jin daɗin muryarta ya amsa.

Ita kuwa ta ji a jikinta Ameer na satar kallonta, don haka ba suna gama gaisawa ta miƙe ta fita.

“Meema ta girma” Alhaji Aminu ya faɗa yana kallon Alhaji Muhammad.

Dariya Alhaji Muhammad ya yi ya ce “Wallahi kuwa, girman ne ba wahala.”

Hirar yaushe gamo suka dasa, a nan Alhaji Aminu yake faɗa mashi sun haɗu da Isma’il a UK.

Ameer kuwa magana ya shiga yi da zuciyarsa, “Da so samu ne, da na haɗa biyu Fateema da Meema.” Domin cikin ɗan lokaci ya fara jin wani abu a kanta, sai dai ko kusa bai kai na Jummai ba.

Katse mashi tunani Alhaji Muhammad ya yi da faɗin, “Ameer ka ƙi dai samo mana suruka ko.”

Dariya kawai Ameer ya yi, suka cigaba da hira.

Wayar Ameer ce ta fara ruri, fitowa ya yi domin amsa kiran, bayan ya gama ne zai koma sai ga meema ta shigo gidan.

Ƙara faɗuwa gabansa ya yi, bai kuma san dalili ba, da zata wuce ne ta ce mashi, “Sannu.”

Ya ce “Yauwa.” Tare da raka ta da idanu har ta shige.

Ciki ya koma shima, ƴar hira suka ƙara daga bisani suka fito da nufin tafiya.

Suna kama hanyar gida ne Alhaji Aminu ya dube shi ya ce “Nafeesa sunanta, amma ana kiranta da Meema kamar yadda ka ji an ce, yarinya ce mai nutsuwa, wadda kuma kusan haka ƴan gidansu suke. Ka yi dogon nazari a kanta”.

 Kai kawai Ameer ya jinjina, lokaci ɗaya kuma idanunsa na kan titi, da yake shi ke driving ɗinsu.

Sosai Ameer ya shiga Nazarin rayuwa, kama daga son da yake ma Jummai, da kuma damuwar da ya shiga akan raba shi da ita da yayanshi yake shirin yi.

Magana ya shiga yi da zuciyarsa yana faɗin “Haka zafin rabuwa yake?, haka Habeeb ya samu kansa?, Lallai so ba wasa bane.”

Ɓangaren Meema ya dawo, kawai sai ya ji sanyi a ransa, hakan kuwa ya tabbatar mashi da zuciyarsa ta karɓe ta, idan kuwa hakane, toh ba zai yi haɗama ba, domin *Ciwon ɗa namiji na ɗa namiji ne*

Kuma gaskiya magani ya fi ciwo, Jummai ita ce ciwon, Meema kuma da ya yi ma gani ɗaya, ya fara ji a jikinshi ita ce maganin.

Don haka zai bar ma Habeeb, saboda mugun tausayinshi da ya fara ji a ransa. 

Sai da ya yi shawara da zuciyarsa da kuma Babban Amininsa Dr. Misau, sannan ya je ya samu yayansa ya faɗa mashi ya amince da ƙudirinshi.

Alhaji Aminu na ya yi murna, ya ce “Ameer na san ba zaka taɓa kunyata ni ba, Allah ya yi maka Albarka.”

Ameer ya ce “Amiin Yaya, na san nima ba zaka taɓa cutar da ni ba, ina roƙon Allah ya sa in zama mai yi mata biyayya a cikin duk abin da kake so.”

Aunty ma tuni ta yi Na’am, musamman da ta ji Meema ce, ita dama tsoronta kada ya samu wadda bata kai Jummai ba, kuma yanzu gashi ya samu wadda ta kusan fin ta ma.

Shawara Aunty ta bashi ta ce “Ka je ka ƙarayin Istikhara kafin a sanar da mahaifanta.”

“Toh” ya ce. A daren ranar yayi iskhara, son ta ne ya ji yayi babakere a ransa, wanda kuma yayi mamaki haka, “Ashe zan iya son wata mace bayan Fateema.” Tambayar da ya shiga yi ma kansa.

Amsar da ya samu ita ce “Muddin akwai tawakkali da haƙuri da biyayya, toh zaka iya son wata bayan wadda kake so, sai dai kuma akwai wahala.”

Shi dai bai ga wahala ba, domin Allah ne ya shiga lamarinsa.

Mahaifan Meema aka sanar mawa, cewar Ameer ya ganta yana so, sun yi na’am da abin. Itama ana faɗa mata ta yi na’am, ashe ita tun a kallon farko ta ji ta kamu da son shi.

Ranar da Ameer ya je wurin ta ya ga kulawa, duk da ranar ta farko ce amma ta nuna mashi ita wayayya ce, bata zaƙe ba, sannan kuma bata yi mugun kawaicinnan ba, ya ji daɗin haka, domin shi dama bai son mace mai rawar kan tsiya. 

A hankali kuma ya fara janye ma Jummai, kiran da yake mata a kullum ya rage, da ta yi mashi magana ya ce aiki ne ya yi yawa, ya yi haka ne domin ya samu sassauci a ransa, saboda kusancinsa da ita ƙara mashi sonta yake.

Shi kam ba don ƙaddara ba, da sai dai ya haɗa biyu.

Shirin sanar da Mahaifan Jummai aka yi, Alhaji Aminu ne ya kira Alhaji Mainasara cewar Ameer fa ya bar ma Habeeb, don haka zasu zo har gida a sanar da mahaifan Jummai.

Kada kaga murna wurin Alhaji Mainasara, godiya sosai ya yi ma Amininsa, ya ce “Kai kam ɗan aljanna ne.”

Alhaji Aminu ya ce, “Habawa Alhaji, ai tare zamu shige aljannar da ikon Allah.” Domin shi a ganinshi babu mutumin kirki kamar Alhaji Mainasara, shima a wurin Alhaji Mainasara ba kamar Alhaji Aminu.

Rana aka fidda domin Ameer ya damƙa ma Habeeb soyayyar Jummai a hannunshi. Ranar na zuwa suka ɗunguma ƙauye gabaɗayansu.

Jummai kuwa bata san wainar da ake toyawa ba, duk da Asabe ta sani, sai dai ta ga su Aunty Uwani da Alhaji Mainasara. Ba’a jima ba kuma sai ga su Ameer sun zo, hada Aunty.

Abin da ranta ya bata duk maganar auren ce ta kawo su, cike da jin daɗin zuwan su ta yi musu sann. 

Cike da tausayinta suka amsa, don a rana tsaka a ce ka rabu da wanda zaka aura akwai ciwo, fitowa su Alhaji Mainasara suka yi suka nufi fadar Maigari, Maigari ya gamsu da hukuncin da suka yanke, amma ya ce sai da Amincewar Jummai.

A can kuwa ɗaki aka kirata, gabanta na faɗuwa ta zauna.

Aunty ce ta fara magana cikin tattausar murya ta ce “Fateema, a matsayinki na mai ilimi kin san abin da Allah ya so, shi yake tabbata, sannan kin san matar mutum ƙabarinsa ko?”

Cike da ruɗanin maganar Aunty ta ɗaga kai, Aunty ta ce “Toh don Allah ki yi haƙuri da abin da Allah ya ƙaddara, ki karɓi Habeeb a matsayin mijin da zaki aura ba Ameer ba.”

A firgice ta ɗago kai ta kalle su, magana take son yi, amma tashin hankali ya hana ta, sai dai riƙa girgiza kai tare da fashewa da kuka.” Mugu azzalumin za’a ce in aura,” cikin ranta ta faɗi haka.

A zahiri kuma ta ce “Ko dai kun manta waye Habeeb, shi ne wanda ya tozarta rayuwata, shine wanda ya ji mani ciwon da sai a ranar da muka tsaya gaban zatin Allah nake sa ran zai warke,” tana wani irin kuka ta ƙarashe maganar.

Ido Asabe ta lumshe tana jin wani irin zafi a ranta, Habeeb kam arzikin Babanshi ya ci, amma wallahi da ba zata yadda da wannan ba.

Lallahin ta suka cigaba da yi, Uwani ta ce “Haba Jummai, Allah ma yana yafe mana, mu kuma yana son mu riƙa yafe ma junanmu, zaki ji daɗin Habeeb da yardar Allah, duk damuwar da ya shiga a kan ya rasa ki ne, kin san kuwa idan ya sake samunki zai kyautata maki.”

Magana mai tausasa zuciya suka riƙa faɗa mata, suka nuna mata matsayin Alhaji Mainasara, don haka ko don shi kada ta bijire musu, kuma sanin halinta na bin Iyaye ne ya sa har suka yanke wannan hukunci.

Wani irin kuka ta sake fashewa da shi, tana son gardama, amma tana gudun kunyata iyayenta.

Da gudu ta fito ɗakin aikuwa ta ga Ameer tsaye jikin bishiya.

Jan rigarshi ta yi suka nufi zaure, don gani take kamar ya dena son ta, “Haka zaka yi mani, kai ma ashe haka kake, maza baku da kirki.” Kukan da take yi ne ta ƙara ƙaimi.

Har cikin ransa yake jin kukan, lallashinta ya shiga yi, ya nuna mata Habeeb ta fi dacewa da shi, aikuwa ta ji zafin maganar.

Cikin fushi ta ce, “Haka ka ce” tana faɗin haka ta juyo cikin

gida, kai tsaye bukkarta ta nufa, domin an daɗe da gyara ta.

Jikin bango ta zauna tare da haɗe kai da gwiwa haɗe da faɗin, “Yaushe baƙincikina zai yaye?” Domin ta ɗauka ita da damuwa shikenan, ashe da saura, saboda bata san inda zata kai son Ameer da ya fara zamar mata iskar shaƙa ba.

Muryar Ameer ta ji a kanta yana faɗin, “Fateema, Habeeb shine wanda damuwarki zata yaye a tare da shi, shine gatan zuciyarki, shine masoyinki na farko, mai ƙaunarki, wanda yake gab da rasa ransa a dalilinki.

Durƙusawa ya yi daidai saitin ta lokacin da ta tsagaita kukan ya cigaba da faɗin, “Na san zaki yi tunanin ko bana sonki, toh ba haka bane, asali ke ce mafarkina, sai dai wanda ba zai zama gaskiya ba, ba don na so ba, ba don zuciyata zata iya haƙura dake ba, ba don kuma bana jin hucin zuciyarki a kusa da tawa ba, ina sonki, ina ƙaunarki, amma Habeeb ya fini ƙaunar ki.”

Shiru ya yi tare da sanya hannu ya share hawayen da suka gangaro mashi a kumatu.

Itakuwa tunaninta ya tsaya cak, ba abin da take sai kuka.

Cigaba da lallashinta ya yi ya ce, “Ki yi hakuri Fateema, wannan al’amarin rubutacce ne a wurin Allah, ki ɗauki wannan a matsayin ƙaddara, idan kika yi haka, zaki ji daɗin rayuwa da Habeeb.”

Basu san yadda take jin haushin Habeeb ba shiyasa suke mata ƙaryar zata ji daɗin zama da shi, ɗago da kanta ta yi, ta fara magana cikin kuka mai tsuma zuciya “Bana son Habeeb kai nake so, don Allah kada ka sake yi mani maganar shi, don ba zan taɓa jin daɗin rayuwa da shi ba.”

Kai Ameer ya girgiza sannan ya ce, “Ba gaskiya bane, son farko shi ne so, ki yi nazarin soyayyar ki da shi ta farko, idan baki ji wani abu ba toh tabbas baki son shi, zan baki minti goma ki yi nazarin rayuwarku ta baya, kada ki yi mani ƙarya idan na tambaye ki”.

Shiru ta yi, lokaci ɗaya kuma ta tsunduma tunanin rayuwarta da Habeeb, sai ta tuna shine wanda take kasa bacci idan bata ganshi ba, wanda take kuka idan yayi nisa da ita, wanda take samun kanta a nishaɗi idan suna tare.

 Shine wanda kullum take mafarkin samu, ta yi azumin nafila domin Allah ya bar mata shi.

 Son shi ne yasa ta guji Alhaji Lawwali, ganin ya rame ne ya sanya ta kuka cikin dare.

Take zuciya ta ƙaryata ta a kan ƙiyayyar da take masa.

Kallon Ameer ta yi tare da fashewa da kuka.

Ido Ameer ya lumshe na ƴan wasu daƙiƙi, tabbas ya fahimci amsar ta, don haka ne ma ya ce “Kada ki cutar da zuciyarki, ki nutsu, zaki dawwama a farinciki”, yana gama faɗin haka ya tashi ya fita.

A ƙofa ne yaga Ahamad, sai da ya sumbaci kansa, sannan ya tura mata shi a cikin bukkar.

Rungume shi ta yi tsam a jikinta tana kuka mai tsuma zuciya.

A fadar Maigari kuwa,  Alhaji Aminu ne ya ce a ɗaura auren Habeeb da Jummai kawai a wuce wurin, tunda ta amince, don dama amincewarta Ameer ya zo nema.  Haka aka yi, Maigari ya sake wakiltarta aka ɗaura aure.

Su Asabe na ɗaki sai dai suka ji buɗar mata, da hanzari suka fito, Asabe ta ce “Kai lafiya”.

Aminiyarta ta ce “Alƙawalin Allah ya cika, Jummai ta zama matar Habeebu, an ɗaura aure an biya sadaki lakadan”.

Aunty da Uwani sai murna suke, Asabe kuwa sai dai ta ce “Ikon Allah, toh Allah ya tabbatar musu da Alkhairi Amiin”

Jummai kuwa kukan da take ɗaukewa ya yi, tuni ta saduda, ta yadda akwai Habeeb a ranta, kuma ta yadda da hukuncin Allah bai chanjuwa, “Allah ka sa haka ne mafi Alkhair a gare mu, Allah ka sa ƙarshen baƙincikinmu ya zo.”

Habeeb kuwa bai san wainar da ake toyawa ba, ya san dai Abbanshi sun tafi ƙauye, amma bai san me suka je yi ba.

Sai da suka dawo, sannan Abbanshi ya kira shi a falon Uwani, abin da ransa ya bashi maganar komawarsa Uk ce, sai dai ganin suna ta fara’a ya sanya shi tunanin ko lafiya.

Fara’ar da suke ce ta sanya shi fara’ar shima, ƙasa ya zauna tare da yi musu sannu, bayan sun Amsa ne Alhaji Mainasara ya ce “Toh ka dai shigo mana da goron albishir ko.”

Dariya suka yi, sannan Habeeb ya ce “Goron Albishir kuma Abba?”,  Uwani ta ce “Kwarai kuwa, ka miƙo mu kuma mu faɗa maka”.

“Ai ban san da albishir ɗin ba Aunty, da sai goron ya rigani isowa ma,”  yana dariya ya ƙarashe maganar,.

Abbanshi ya ce “Hakane, Gimbiya toh faɗa mashi, amma fa sai ka biya.”.

Zuciyar Habeeb cike da son jin wannan albishir ya ce “Zan biya.”

Sai da Uwani ta ɗauki ƴan seconni sannan ta ce “An ɗaura aurenka da Fateema, sannan kuma Mahaifiyarka zata dawo ɗakinta, domin ta yi hidimar bikinka cikin walwala.”

Tamkar a mafarki Habeeb ke jin wannan magana, ido ya lumshe yana jin wani irin farincikin da bai misaltuwa, lokacin da ya buɗe ne wasu zafafan hawayen murna suka cika mashi ido.

“Ban san wa zan fara godemawa a cikinku ba, sannan ban san wane irin goro ne ya kamata in baku ba.” a kan gwiyoyinsa ya durƙusa, hannunsa duka akan na Abbansa, fuskarsa kuma tana kallon Uwani.

“Na gode muku sosai, Allah ya bani ikon biyanku da wannan alkhairi Amiin.”

Hannu Abbanshi yasa ya share mashi hawayen shi, sannan ya ce “Alhaji Aminu ma yana buƙatar ka gode mashi, don shi ya karɓi Fateema a wurin ƙanensa ya baka.”

Habeeb ya ce “Shima nagode mashi, kuma zan je har gida in ƙara gode mashi.”

Godiya ta musamman yayi ma Uwani akan dawowar mahaifiyarsa, don yana da yaƙinin da sanya hannunta.

“Bakomai” ta ce, don tana da yaƙinin yiwa kai ne.

Farinciki fal da zuciyarsa ya tashi ya fita, cike da azarɓaɓi ya kira Nasir ya faɗa mashi, sannan ya nufi gidan Hajiya Mairo.

Rawa ta kama yi saboda tsananin murna, shima ɗin rawar ya dunga yi suna dariya, da yake tana da ciwon ƙafa ta ce “Na gaji Habeeb,” suka kama dariya.

Murna wurinsu ba’a magana, godiya ta yi ma Allah domin ya ceci rayuwarsu ita da ɗanta.

Tare suka fito da Habeeb ɗin suka nufo gidansu.

A falo suka samu Uwani, bayan sun gaisa ta ce “Uwani ba abin da zan muku sai godiya, don Allah kuma ku yafe mani” idanunta cike da ƙwalla ta ƙarashe maganar.

Uwani ta ce “Don Allah ki bar faɗin haka ma, Allah ya yafe mana baki ɗaya Amiin.”

Washe gari kuma Hajiya Mairo ta nufi ƙauye, kai tsaye gidan Asabe ta nufa domin godiya da neman Afuwa.

Da kukanta ta riƙa faɗin, “Na cutar da ku cutarwa mai yawa, amma a haka kuka yadda muka haɗa iri, don Allah ku yafe mani Asabe.”

Asaben ma ai ta cutar da ita, don dai bai kai wanda ta yi musu ba, cewa ta yi “Hajiya mu duka ya kamata mu yafi juna, faɗa tun muna yara, gashi yanzu har jikokinmu ya cutar, yanzu da muna da kyakkwar alaƙa ai kai tsaye Habeeb zai zo neman aure Jummai, amma halinmu ya haifar musu da tsoro, daga nan ne kuma shaiɗan ya samu damar shiga a tsakaninsu.”

“Gaskiya ne” Hajiya Mairo ta faɗa, juna suka yafe mawa, tare da Alƙawalin babu sauran gaba.

Kiran Jummai aka yi, Hajiya Mairo ta ce mata “Ki yafe ma Habeeb kin ji, yana sonki, kuma zaki ji daɗinsa, jiya da bakina da nashi ya ce zai faranta maki fiye da zaton mai zato.”

“Uhm” kawai Jummai ta ce, kowa ƙaryarsa kenan wai Habeeb zai faranta mata “Toh Allah ya sanya ƙaryar ta zama gaskiya Amiin”.

Da Hajiya Mairo ta zata tafi ne ta ja hannun Ahamad da su Ali suka tafi a can gidansu, mutane sun yi mamaki, gulma aka fara yi ana faɗin ba dole su shirya ba, wasu kuma suka ce gaba ta yi musu hankali ai.

Gwaggo kuwa da tsufanta amma sai da ta kwaso shoki, ta ce “Kai ban taɓa jin abin farinciki irin wannan ba, uwar zata amarce, ɗaa ma zai angwance, kai abin yayi armashi wallahi.”

Cike da jin daɗi Hajiya Mairo ta ce, “Ni gwaggo hada zaulaya.” Dariya Gwaggo ta yi ta ce “Ba zaulaya bace Mairo, Allah dai ya tabbatar muku da alkhairi Amiin.

*****

Auren Hajiya Mairo da Alhaji Mainasara aka maida, inda ta koma ɗakinta mai cike da aminci.

A ɓangaren hidimar bikin Jummai da Habeeb kuwa, an yi shiri ba na wasa ba, dama akwai ginannanen gida na musamman, can aka zuba ma Jummai kayanta, wanda Alhaji Mainsara da su Aunty ne suka yi su.

Lefe kuwa sai da aka yi mata dozen na akwati, wanda ba abin da ba’a sanya ba.

Habeeb kuwa tuni ya je godiya wurin Ameer, har kuka yayi, Ameer kuwa ya ce “Haba abokina, ka wuce haka fa, ni dai fatana ka riƙe mani ƙanwa da kyau.”

Tsakaninsa da Jummai kuwa har yanzu bai sata a ido ba, kunya da kuma tsoron fuskantar ta ya hanashi zuwa, sai dai ya kira ta sau ɗaya a waya, shima tunda suka gaisa tayi shiru ta ƙyale shi, haka ya karaci surutunsa ya kashe wayar, mafarin tsoron ya shige shi a kanta.

Nasir ya samu ya ce mashi, “Gani nake kamar Fateema ba zata saki jiki da ni ba.”

“Nasir, kada ka damu, Insha Allah a hankali komai zai wuce, amma sai ka matuƙar jajirbe” don ya fahimci yana ɗan tsoronta.

*****

Gagarumin biki aka yi a birni da kuma kauye, sannan aka yi ma amarya nasiha akan ta zauna lafiya da mijinta, kuka sosai Jummai ta rika yi, wanda bai wuce na nisa da mahaifiyarta da zata yi ba, don wata irin shaƙuwa ce ta shiga tsakaninsu.

Asabe na kuka ta ce “Ba don aure ibada bane, da ban barki kika tafi ba Jummai, ki je ɗakinki, ki zama mai biyayya ga mijinki, ki rika kauda kai, sannan ki manta da baya, ki kuma fuskanci gaba.”

Ƙadaddabe ta Jummai ta yi tana kuka, da ƙyal aka janye ta, har waje Asabe ta raka ta, aka shigar da ita mota.

Katafaren gidanta aka nufa da ita, wanda ba abinda babu a ciki, na kayan ƙawa dai.

Washe gari aka yi walima, da yamma kowa ya watse, Uwani kaɗai aka bari da amarya, nasiha Uwani ta ƙara yi mata akan ko da wasa kada ta tuna abinda ya wuce, sannan ta ƙara mata da wasu dubaru na sace zuciyar ango.

Bayan anguna sun shigo ne Uwani ta tafi.

Su Nasir ne ja gaba wurin rakiyar angon, nasiha sosai suka yi musu, Nasir ya ce, “Ba abinda muka sani a kanku sai alkhairi, don haka ku rike alkhairin da aka sanku da shi.”

Sauran abokan ma suka ɗaura da nasu, sannan suka yi bankwana suka tafi.

Farincikin dake zuciyar Habeeb bai misaltuwa, da zumuɗi ya raka abokansa, sannan ya dawo, wata irin nutsuwa ya samu kansa da ita.

a bakin kofa ya tsaya yana kare mata kallo, sanyin ƙamshinta dana dakin suna ta dakar masa hanci. Sai da ya lumshe idanu sannan ya hau kan gadon ya zauna suna fuskantar juna.

Ƙuri ya yi ma kyakkyawar fuskarta ta yake hangowa a cikin mafayafin da ta rufe fuskarta. “Alhamdulillah, masha Allah.” ya faɗa, lokaci ɗaya kuma ya zura hannayensa tare da riko nata hannuwan dake cikin mayafi.

Tsarga su wani abu yayi, wanda dole suka lumshe idanu.

 “Fateemah” ya kira sunanta cikin murya mai kashe jiki.

Maimakon Jummai ta kalle shi, sai ta yi kasa da idanunta, cikin ranta kuma tana jin wata irin faduwar gaba, kamar a yau ne namiji ya fara zama kusa da ita.

“Don Allah ki kalle ni Teemah, Habeeb dinki ne, masoyinki ne, wanda ya shirya gazgata maki dukkan mafarkanki.”

Dan matse mata hannu yayi wanda ya sa ta rumtse idanu, “Fateemah na rasa wane aiki ne zanyi wanda zai nuna godiya ta ga Allah da ya sake bani ke, ina sonki, ina kaunarki, sannan ina neman afuwarki akan abinda na yi maki fateemah, sannan ba zan gamsu kin yafe mani ba har sai lokacin da kika saki jiki gareni.”

Maganganu masu tausasa zuciya ya rika faɗa mata, waɗanda su duka sai da suka yi kuka.

Sai dai har ya gama maganarsa idanunta na rufe, hakan ya sa ya yi zaton fushi take.

Zuciyar ba daɗi, ya yunƙunra zai tashi kenan ya ji ta riƙo mashi hannu, hakan ya sanya shi dawowa cike da farinciki.

Yaye mayafin dake kanta ya yi, sai kuwa ya yi arba da hawayen dake fuskarta, bai san sadda ya kafa baki a fuskar ba ya cigaba da lasarsu,  daganan ya gangaro ya zuwa bakinta, sai da ya yi mata tsotsar minti sannan ya janye bakinsa.

“Fateemah” ya amfaci sunanta, “Har yanzu kina so na? ” kai ta daga tare da magana cikin muryar kuka “Ina sonka mijina, na yafe maka”, daɗi ne ya kama shi, ai sadda ya sake rungumeta ba.

Shiru suka yi, zuciyoyinsu cike da farinciki. saukowa sukayi suka ciyar da kansu abinci, sannan suka yi wanka, suna fitowa suka shirya bacci mai cike da aminci.

Rayuwarsu tayi fari sal, suna cin amarcinsu gwanin birgewa, kamar wani abu bai taɓa faruwa ba.

Ahamad kuwa wurin Hajiya Mairo ya koma, inda ta haɗa da Salim duk ta riƙe, da yake Uwani cikin nata bata wahala.

Wata ɗaya da tarewar su Jummai aka fara shirin bikin Ameer da amaryarsa Nafeesa wato Meema.

Gaba ɗaya family ɗin su Jummai suka je wannan biki, Aunty ta yi murna ba kadan ba, tarba ta musamman aka yi musu.

Su Aisha kuwa santin Jummai suka riƙa yi, cike da zaulaya suka ce “Da kyau, lallai Habeeb ya iya kiwo,” Gaba ɗaya suka kama dariya.

Ameer ma ya ji daɗin ganin sauyi Jummai, haka yake mata fata dama.

A ranar Walima ne su Jummai suka tafi, saboda Uwani bata da lafiya.

Ameer kuwa a wannan dare ya ba amaryarsa kulawa ta musamman, washe gari yana ta ririta matarshi dan ta gaza komai sai kuka.

Tsam ya rungume ta a jikinshi ya fara magana mai tausasa murya “Haba green tea nah, wai miye ne don Allah.”

Ƙara shagwabewa ta yi ta ce “Toh ba kai ne ba.” Ido ya lumshe sannan ya kama kunnensa ɗaya, “Ni, toh tuba nake baby, ba zan sake ba.”

Shigewa ta yi jikinshi tare da ƙara narkewa.

Cike da ƙaunarta ya sumbaci goshinta sannan ya ce, “Kin yi hakuri ko”, tana ɗaga kai ya matse ta a jikinshi tsam.

Dr. Misau kuwa ya fara shirin angwancewa da Amaryarsa Aisha, inda kuma Salma ta haɗu da masoyinta Anas, wanda duk za’a ɗaura aurensu a rana ɗaya.

*Sai mu ce asha shagalin biki lafiyaaaa*😀

Rayuwa ta sauya, kowa cikin farinciki yake, Uwani ta haihu, Asabe kuwa ta sayi katafaren gida a birni.

Da dawowarta kuwa zawarawa suka fara zuwa, aikuwa ta ce “Ku yi ta kanku, fatana in tashi ni da Malam Amadu a aljanna.”

Habeeb kuwa tuni ya ɗauke Fateemarsa sun koma UK, inda suke rayuwarsu ta aljannar duniya.

A ranar da suka kai ma Dr. Umar ziyara ne. Jummai na ganinshi ta ce ta san shi.

Zainab matarshi ta ce, “A ina kika san mijina.”

“A FMC katsina, shekaru huɗu da suka wuce,” Bayani ta yi ma Dr. Umar akan itace ya taɓa yi ma ɗanta magani kyauta, da kuma taƙaddamar da suka yi akan za’a kwantar da ɗanta.

Mamaki bayyane a fuskarshi ya ce, “kai kai kai, na tuna, ina yaronki”

Hoton Ahamad ta nuna mashi, ya ce, “Allah Sarki, yaronnan ya sha wahala ai.”

Suna komawa gida Habeeb ya ce “Wace irin wahala ɗana ya sha?”.

Ɗan haɗe rai ta yi ta ce, “Ɗanka kaɗai kake tambayar irin wahalar da yasha, ka manta tare suke shan wahalar da mamanshi?”

“Sorry baby, me ya wahalar mani da ku ne.”

Labarin irin azabar da suka sha ita da Ahamad ta bashi, wanda shine sanadin ta fara yawon bariki.

Kuka ya kama yi ya ce, “Ku yafe mani baby, duk ni ne sila.”

Ko kusa bata so ya yi kuka ba, don haka ne ma ta sanya halshe ta lashe mashi hawaye, sannan ta ce “Ban faɗa maka don ka yi kuka ba, kuma mun yafe maka ai.”

Rungumeta ya yi a jikinshi ya ce “Dole in yi kuka baby, ina sonku, ina ƙaunarku, Allah ya bani damar faranta muku.”

Ta ce “Amiii ya Allah.”

Tunawa da Yakumbo tayi, labari ta bashi akan halin kirkin Yakumbo, cewa ya yi “Insha Allah, idan muka koma gida zamu kai musu ziyara.”

“Allah ya amince.” Ta faɗa, daga nan kuma suka koma bedroom domin sauke gajiyar da suka ɗebo.

Ni kuma na ce a fito lafiyaaaa

Tammat bi Hamdillah

*****

Godiya ta musamman ga Sis Hassab Suyudi, Ameer Sarki (Women Leader), My Son, (Abullahi Misau),  My Ummu (Ummu Mash) Mamana (Maman Rahama), Ƙawass Aminyass, maƙwafciyass (Maman Ilham kenan)

Ina yin ku Over wallahi

Sannan ina godiya ga sauran Fans, sannan ina yi muku sannu da jimirin bibiyar labarin nan tsawon wata huɗu cur, na fara shi a 1-1-2020 , In da a yau 22-4-2020 Allah ya nufa ya zo ƙarshe.

Na gode muku sosai.

Allah ya sa abin da ke ciki ya amfana Amiin. 

Sannan ina addu’ar Allah ya kawo mana ƙarshen wannan masifa ta Covid-19.

Allah ya sa mu yi azumi lfy, mu gama lfy, tare da dacewa da alkhairorinsa Ameen.

Na san wasu har yanzu basu fahimci ma’anar sunan labarin ba, don ana yawan tambaya ta, toh ku koma baya zaku fahimta Insha Allah

Wasu kuma zasu ce ina Alhaji Lawwali, toh tun a ranar gidan da suke asirin ya ƙone ƙurmus, kuma duk suna ciki, gidan abinci kuma gwamnati ta karɓe shi, bisa ga taimakon Ameer da Malam Ahamad.

Sai mun haɗu a wani novel ɗin Insha Allah.

Wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Maman Mu’azzam

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×