Skip to content
Part 16 of 22 in the Series Ko Ruwa Na Gama Ba Ki by Hadiza Isyaku

“Waye wancan da ahalina?”, Habeeb ya tambayi kansa, lokaci ɗaya kuma yana ta huci saboda azababben kishin da ke gab da tarwatsa masa zuciya. A fili ya cigaba da faɗin “Ya zama dole na san ko waye wancan, sannan kuma dole su rabu ko da kuwa mijinta ne, domin Fateema mallakina ce ni kaɗai”.

Yana gama faɗin haka ya bi bayansu da gudu, ɓangare ɗaya kuma yana ta sambatu kamar zararre. Sai da ya kusa cimmusu sannan ya tsaya cak! Kamar wanda aka sanya ma birki, a lokacin da ya ga sun shiga Taxi.

Tabbas Jummai ta hange shi tsaye yana ƙare musu kallo, amma sai ta ɗauke kai kamar bata ganshi ba.

Shima mutumin ya lura da Habeeb tun a train station, duban Jummai da ke kallon Ahamad ya yi tare da nuna mata Habeeb ya ce “Wancan matashin kamar mu yake bi fa”,

Kwantowa ta yi a jikinshi sannan ta saka idanunta a cikin na Habeeb, don karon farko ta gane damuwarsa a kanta, “Bana tunanin haka”, ta faɗa tare da girgiza kai.

Matse ta mutumin ya ƙara yi a jiki haɗe da sumbatar kanta. Murmushi suka jefi juna da shi sannan suka maida dubansu ga driver a lokacin da ya tada Taxi ɗin suka tafi.

Hakan kuwa ya yi daidai da fitar hawayen baƙinci a idanun Habeeb. Matarshi wadda yake fatan ƙare rayuwa da ita, yau ita ce kwance a jikin wani namiji. Bakinsa na kyarma ya ce “Allah ina neman tsarinka daga irin wannan mugun gani”, domin bai haɗa son Jummai da kowa ba.

Karkarwar da jikinsa ke yi ce ta sa shi zama akan wata kujera da ke bakin tatin saboda gudun faɗuwa. Dafe kansa ya yi da dukkan hannayensa, lokaci ɗaya kuma bakinsa na faɗin “Me ya sa Fateema za ki nemi wani namiji bayan ni, why Fateema why”.

Wani irin kukan baƙinciki ne ya fashe da shi, wanda wannan ba shi ne karon farko ba, ya daɗe yana kukan rasa Jummai.

Tabbas a rayuwarshi ba wanda yake muradin sake gani sai ita da ɗansa, amma kuma ba irin wannan ganin mai neman tafi mashi da rayuwa ba. Ya daɗe a wurin zaune, da yaga ba Sarki sai Allah, sai ya tashi tare da tarar taxi ta kai shi gida.

Ƙasa ya zauna a falo, gami da ɗora kansa a kan kujera yana sharɓar kuka, tausayin kansa ne cike da zuciyarsa, don shi kaɗai ya san irin azabar da yake ji a ransa, musamman idan ya tuna irin yadda mutumin ya matse mashi mata a jiki.

Yana cikin wannan hali ne sai ga abokinsa Isma’il, wanda kuma suka kama hayar gidan a tare. Cike da damuwa Isma’il ya duƙo tare da dafa Habeeb ya ce “Haba abokina, don Allah ka sanya ma rayuwarka haƙuri, komai da ka gani yana da ƙarshe, addu’a ce kaɗai zata bayyana maka matarka ba kuka ba”.

A hankali Habeeb ya ɗago jajayen idanunsa da suka koma kamar garwashin wuta, cikin raunin murya ya ce “Isma’il na ga Fateema da idona”.

“Kai don Allah, a ina ka ganta”, cike da farinciki Isma’il ya faɗi haka.

Cikin jin ɗacin yanayin da ya gan ta ya ce “A jirgin ƙasa, kuma ita da wani, wanda ba san ko waye ba”.

Dafe kai Isma’il ya yi “Ya Salam, toh ko ɗan’uwanta ne?”

Kai Habeeb ya girgiza tare da bashi labarin komai, tun daga cikin jirgin har zuwa shigarsu cikin taxi. Isma’il ya ji ba daɗi don shi shaida ne akan irin son da Habeeb ke yi ma Jummai.

Maganganu masu daɗi ya yi ta faɗa ma Habeeb, tare da yi mashi alƙawalin taya shi neman ta a duk inda take a cikin UK, da kuma yin bincike a kan alaƙarta da mutumin.

Dena kukan Habeeb ya yi, sai dai ajiyar zuciya.

Ciki Isma’il ya shiga ya yi wanka tare da chanja kaya, yana fitowa Habeeb ya tashi suka fita neman Jummai.

Jummai kuwa tunda ta ga Habeeb ta nemi dukkan walwalarta ta rasa, tana yin abubuwa ne kawai don bata son mutumin ya gane tana cikin damuwa.

Zaune take a kan gado tana ta kallon Ahamad da ke bacci, wanda a baɗini fuskar Habeeb take kallo ba ta Ahamad ba. Zuciyarta kuwa ba abin da take sai tafarfasa tare da fatan sake ganin Habeeb domin ta sauke masa kwandon wulaƙancin da ta iya ɗauka a sanadin yawon bariki. Gaba ɗaya ta manta da wani aurensa da ke kanta, don dama bata ɗauke da muhimmanci ba.

Shigowar da mutumin ya yi ce tasa ta ƙaƙaro murmushi tare da jifar sa da shi a lokacin da ya ja tunga ya tsaya a bakin ƙofa. Ƙuri suka yi ma juna da idanu, shi a ƙasan ransa yana jin wani masifar son ta, ita kuma tana jin kamar ta kashe shi saboda tsanarshi da ta yi.

Ɗauke idanunta ta yi daga cikin nashi tare da da ɗan cije leɓe sakamakon fushin da ke cike da ranta.

A hankali ya tako ya zauna a gefenta, tsagwayam ya ɗauke ta ya aza ta kan cinyarsa suna kallon juna.

Duƙo da kansa ya yi zai sumbaci bakinta, aikuwa ta janye kan tare da bayyanar da zahirin abin da ke cikin zuciyarta na fushi.

Sake maido kansa ya yi, a wannan karon itama ta sake janyewa.

Cikin kasalalliyar murya ya ce “Teemah lafiya?”.

Kalmar Teemah kuwa da ya faɗa ta zo ta tokare mata a wuya, don tana daga cikin abin da Habeeb ya yi amfani da su wurin yaudararta, kuma daga Habeeb har komai nasa ta tsane su iya tsana.

Shiru ta yi kamar bata ji me ya ce ba, ƙara shigar da ita ya yi a jiki “Teemah ikon Allah, me ya faru ne wai?”

Fizge jikinta ta yi ta tashi tsaye “Bana son wannan sunan please”.

Ko kusa bai damu da chanjawarta ba, asalima hakan birge shi ya yi don fushin ƙara mata kyau yake. Tsaye ya tashi shima, rungume ta ya yi sannan ya ce “Toh wane suna kike so na kira ki da shi?”

Zare jikinta ta sake yi ta ce a ɗan tsiwace “Ka kira ni da duk sunan da ka ga dama, amma banda Teemah”

Dariya ya yi “Toh shikenan, Jummala ai ya yi ko”.

Murmura ido kawai ta yi tare da juyawa ta nufi ƙofar falo, biyo tan da ya yi ne ya sa ta dakatawa tare da ɗaga mashi hannu “Kada ka biyo ni, zan dawo in same ka”,  bata jira jin me zai ce ba ta fice.

Shi kuwa da idanu ya raka ta, ƙasan ransa yana dariyar mugunta, don shi kaɗai ya san me ya aje a ransa, komawa ya yi kan gado ya zauna tare da yi ma Ahamad ƙuri, zumbur ya miƙe tsaye lokacin da yaga fuskar matashin nan cikin ta Ahamad “Me hakan ke nufi?” ya tambayi kansa, lokacin da ya tuna sadda Habeeb ke kiran Fateema, da kuma sadda ya isko su a lokacin da suka shiga taxi. “Lallai da wani abu anan, wanda ko miye masu shi sun makaro wallahi” yana gama faɗin haka ya koma ya zauna tare da ɗaukar wayarsa ya nemi fajiran abokansa da ke a nan UK.

Ita kuwa kan kujera ta kwanta tana ta saƙawa da kwancewa, tana cikin haka kuma bacci ya yi awon gaba ita.  kasantuwar daren jiya kwana suka yi a club, don haka ma bata san sadda mutumin ya fita ba.

*****

Bell ɗin da aka danna ce tasa Jummai tasowa ta buɗe don a zatonta mutumin ne.

Ras! Gabanta ya faɗi lokacin da ta ga Habeeb tsaye yana ta huci. Banko ƙofar ta yi da ƙarfi zata rufe saboda ta tsorata da yanayinsa.

Aikuwa ya riƙe ƙofar lokaci ɗaya kuma ya shiga ciki da ƙarfi. Cikin tsananin fushi ta ce “Me ya kawo inda nake?”

Habeeb ya ce “Ɗana na zo karɓa, don ba zan yadda ya yi rayuwa da ballagazar mace irinki ba”.

Ba ƙaramin fusata ta kalmar ballagaza ta yi ba, “Na rantse da Allah baka isa ka ɗaukar mani ɗa ba, kuma ai kai ne wanda ya buɗe ma uwar ɗanka hanyar ballagazanci, ko ka manta?” ta ƙarashe maganar cikin ƙaraji.

Hakan kuwa ya tada Ahamad daga baccin da yake ya kama kuka.

Habeeb na ji kuwa ya bi inda sautin kukan ke fitowa da gudu ya kutsa kai ciki.

Baya Jummai ta rufa masa tana faɗin “Wallahi kada ka taɓa mani ɗa”.

 Kamar ba da shi take ba ya ɗauke Ahamad tare da rungume shi tsam a jikinshi ya ce “Sorry my Son”

Tattaro ƙarfinta ta yi ta zo zata ƙwace shi, aikuwa ya bangajeta ta faɗi ƙasa, kafin ta miƙe har ya fice tare da sanya ma ɗakin key ya tafi da ɗanshi.

Wani irin kuka ta fashe da shi tare da miƙewa ta nufi ƙofa a lokacin da ta ji ana buɗe ɗakin daga waje.

Firgigit ta falka daga gajeren baccin da ta yi a yanzu, hannunta dafe da ƙirji, idonta kuma a kan ƙofar da ake shirin turowa a shigo.

Tana ganin wannan mutumin ta tashi da gudu ta maƙalƙale shi.

Da yake buƙatarta yake sai ya rungume ta ya ce “Kin huce daga fushin ko”.Numfashin da take ta saukewa ne yasa shi ƙara tambayarta “Me ya faru?”

Amsa ta bashi da “Wani mugun mafalki na yi yanzu”.

Tamayar ta ya sake akan kalar mafarkin, amma ta ƙi faɗa mashi, don bata fatan wani ya san alaƙarta da Habeeb.

Saɓarta ya yi suka shige ciki, wanda kuma har a wannan lokacin Ahamad bacci yake.

Romancing ɗinta ya shiga yi, da yake ba a cikin nutsuwarta take ba, sai ta kasa yi mashi komai.

Haƙuri ta bashi akan idan ta samu nutsuwa, zata jiyar da shi daɗin da bata taɓa jiyar da shi ba, da yake ya yadda da ita sai ya ƙyale ta.

Su Habeeb kuwa hotels suka riƙa bi suna neman Jummai, duk inda suka je babu ita ba alamarta. Da suka gaji Habeeb ya ce ma Isma’il “Mu koma gida kawai”.

Kai Isma’il ya girgiza “A’a mu ƙara bincikawa dai” duk da kuwa ya gajin. Ƙin bin maganar shi Habeeb ya yi, gidan suka koma, Isma’il ya yi ta bashi magana.

A wannan dare kuwa rutsum Habeeb da Jummai basu rumtsa ba. Shi dai tunani yake waye wannan mutumin, ita kuma tsoro ne cike da ranta na mafalkin da ta yi, don gani take kamar da gaske ne. Kuma a yadda take son Ahamad ba ta jin wani zai iya rabata da shi a zauna lafiya.

Washe gari Isma’il ya ja Habeeb suka nufi Soho Square Gardens duk don Habeeb ya rage damuwa, kasantuwar wurin akwai abubuwa masu ƙayatarwa da ɗebe kewar mai kallo.

Kan Kujera suka zauna suna kallon mutanen dake zaune a ƙasan grass, wasu da yara wasu babu.

Abin ya ƙayatar da Isma’il, don haka ne ma ya sa ido yana ta kallon wasu yara twins da mamansu.

Habeeb kuwa ganin wata mata da mijinta da kuma ɗansu guda ɗaya zaune ya sa shi jin ina ma ace shi ne da Jummai da Ahamad.

Jingina bayansa ya yi da kujera tare da lumshe ido ya faɗa duniyar tunanin da ya saba.

Ɗan taɓa shi Isma’il ya yi tare da faɗin “Habeeb kalli mutumin nan da nake baka labari na garinmu”.

A hankali Habeeb ya buɗe idanunsa ya ce “Wane mutum ne?” don shi ya manta da wani labari, ta Jummai kawai yake.

Isma’il ya ce “Wanda yake tara mata a gida yana masha’a da su”. “Eh na gane” Habeeb ya faɗa a taƙaice.

“Toh ka ganshi can zaune da wata, hada ma yaro, ko ina ya same su”.

Inda Isma’il ya nuna mashi ya bi da idanu, tare da miƙewa tsaye da sauri a lokacin da yaga Jummai zaune da wannan mutumin suna ta kwasar dariya.

“Fateema ce waccen yake tare da ita” Ya faɗa cikin tashin hankali.

Kafin Isma’il ya sake yin magana har ya nufi wurinsu Jummai da sauri.

Sunan “Habeeb” da Jummai ta ji Isma’il na kira ne ya sa ta waigowa a tsorace.

Zumbur ta miƙe tare da saɓar Ahamad, sanadin tunkaro su da ta ga Habeeb ya yi.

Babu abin da gabanta ke yi sai faɗuwa, don gani take ya zo ya raba ta da Ahamad.

Miƙewa mutumin ya yi bakinsa na faɗin “Fateema ina zaki je?”, don tuni ta yi gaba. Zai bi bayanta kenan ya ji an fizgo shi ta baya da ƙarfi. Ya buɗe baki zai yi magana kenan ya ji saukar naushi a fuska, hannu ya sa ya dafe wurin da Habeeb ya daka tare da ɗan lumshe ido lokacin da zafin dukan ke ratsa mashi kai.

Maganar Habeeb ce tasa shi buɗe idanun sadda ya ce “Uban me ya haɗa ka da waccen matar?”

Wani irin kallo mutumin ya yi mashi sannan ya ce,”Matar tawa kake tambaya ta alaƙa ta da ita”

“Ƙarya kake shege matsiyaci”. Habeeb ya faɗa tare da ƙara kai mashi duka.

Kaucewa mutumin ya yi sannan yace cikin fushi, “Ni shege, kai kuma Uban shege ko”, domin daɗin zama ya sa Jummai ta labarta mashi komai na rayuwarta, kuma da ya ga kamar Habeeb da Ahamad ya tabbatar da shine ubansa.

Duka Habeeb ya cigaba da kai mashi, wani ya samu, wani kuma mutumin ya kauce, gaba ɗaya Habeeb ya gigita shi.

Cikin ɗan ƙanƙanin lokaci wurin ya cika da Jama’a, ana haka sai ga police sun iso.

Su duka aka sanyama handcuffs aka nufi mota da su.

Idanu suka yi ta rabawa, Habeeb na duba Isma’il da tunda ya nuna mashi mutumin bai sake ganinshi ba. Shi kuma yana neman Jummai da ta yi mashi ɓatan dabo a wurin. Har aka tafi da su ba wanda ya ga wanda yake nema.

“Toh ina Isama’il ya shiga ne?” Habeeb ya yi tambayar kansa, tunawa da yawan mutanen da suka taru ne ya sa shi basar da tambayar, don zuciya ta hango mashi yana cikinsu.

Shi kuwa gogan Jummai ya san hotel ɗin da suka sauka ta koma, don tana tafiya ita kaɗai dama.

Da isarsu aka fara bincike, kai tsaye aka gane Habeeb ne ke da laifi, don haka aka saki mutumin.

Habeeb kuwa a cell aka tura shi aka ce za’a shigar da ƙara a kotu, bisa ga laifin farmaki da ya kawo ma mutumin.

Zuciyar Habeeb kamar zata fito saboda baƙinciki da takaici.  

Haka ya kwana a wannan wuri, ba Isma’il kuma ba dalilinsa, washe gari tunda farar safiya sai ga Isma’il ya zo.

Ko kallonshi Habeeb bai yi ba don ya hasala.

Haƙuri Isama’il ya bashi ya ce “Don Allah ka yi haƙuri, bayan Fateema na bi, na ga inda take, sadda na dawo kuma dare ya yi, na so shigowa aka hana ni”

Ganin inda Jummai take, tamkar ganinta ne a wurin Habeeb, don haka take ya dena fushin da yake. Yadda ake ciki ya faɗa ma Isma’il, akan za’a shigar da ƙara court.

Isma’il ya ce “Labari ne wannan, idan shi bai kai mu court ba, toh shi zamu kai shi”.

Tafiya ya yi yada sanar da sauran friends ɗinsu, cikin ƙanƙanin lokaci suka zo, tare da shiga da fita aka saki Habeeb.

 Jugum Habeeb da Isma’il suka yi bayan sun koma gida, kowa da abin da yake saƙawa a zuciya.

Daga bisani Isma’il ya yi magana cike da damuwa

“Habeeb na matuƙar tsorata da al-amarin Fateema, shin da auren naka ta yi wani auren, ko da auren take ke bin wani”

Saida Habeeb ya ɗauke hannunsa da ya dafe goshinsa da shi sannan ya ce “Nima abin ya ɗaure mani kai wallahi, amma ka san wani abu?”

Isma’il ya girgiza kai “A’a”,    Habeeb ya ce “Akwai saki a tsakanina da Fateema, sai dai kuma bani tunanin aure ne a tsakaninta da mutumin can, domin guduwa ta yi daga gida”.

Farkon abin da ya faru tsakaninsa da Jummai ya ba Isma’il labari, tun daga cikin da yayi mata, har kawo sakin da da yayi mata, wanda a can baya bai ba Isma’il irin wannan labarin ba, ya ce dai matarshi da ɗanshi sun ɓace.

Haɓa Isma’il ya riƙe, ƙasan ransa yana mamakin Habeeb, lallai duk abin da faru shine sila, don haka sakamakon kuskuren da ya aikata ne ya fara gani.

Kamar Habeeb ya san abin da ke ran Isma’il, magana ya yi kamar zai yi kuka “Isma’il

duk rayuwar da Fateema ta tsinci kanta a ciki nine sila, don haka dole in gyara kuskurena tun kafin in koma ga mahaliccina”.

“Kamar ya?” Isma’il ya tambaye shi, don ya san tunda Fateema ta haɗu da mutumin can sai wani ikon Allah kuma.

Habeeb ya ce “Ko ban sake mallakar ta ba, toh zan yi iya ƙoƙarina wurin ganin ta fita daga cikin halakar da take, idan na yi haka, toh ina sa ran samun tsira a wurin Allah”

Kai Isma’il ya jinjina “Wannan hakane, amma sai ka yi da gaske, domin mutumin can ya wuce yadda kake zato, duk matar da ƙaddara ta sa ta afka mashi, toh sai wani ikon Allah”.

Ko kusa Habeeb bai karaya da maganar Isma’il ba, sai ma tawakkali da ya ji cike da ransa “Allah ya fi shi, don haka duk abin da yake taƙama da shi na banza ne”.

Isma’il ya ce “Hakane”

“Ya sunan shi wai?”. Habeeb ya tambayi Isma’il. 

“Alhaji Lawwali” ya bashi amsa.

Habeeb ya ce “Toh ya ɗebo ruwan dafa kansa wallahi, ko auren Fateemah yake sai ya sake ta tunda ba mutumin arziki bane, bare kuma ba alamar aure”.

Isama’il ya ce “Toh me zai hana ka sanar gida, sai azo a tafi da ita”

Kai Habeeb ya girgiza don bai da wanda zai kira, Abbanshi ne, kuma rabon da ya ɗaga wayarshi har ya manta, Ummanshi kuma yadda bata son Jummai, ba zata yi murna da ganinta ba, bare har ta taimaka a maida ta gida.

Habeeb ya ce “Kafin wannan, mu samu mu raba ta da shi tukunna”

Tsara yadda zasu haɗu da Jummai ita kaɗai suka shiga yi. Washe gari tunda farar Safiya suka nufi Hotel ɗin da su Jumman suke.

Wuri suka samu suka tsaya tare da lura da shige da ficen mutanen da ke wurin.

Suna nan sai ga Alhaji Lawwali ya fito shi kaɗai.

Habeeb ya ce “Dubarshi  matsiyaci kawai”.

Ƴar dariya Isma’il ya yi “Ai wancan mutumin, sai dai addu’a, amma ko kusa babu Allah a zuciyarsa”

Gani suka yi wata mota ta faka ya shiga sun tafi.

Da sauri su Habeeb suka shiga ciki, kai tsaye reception suka nufa, tare da biyan kuɗin wuni ɗaya. 

Wata irin sa’a suka taka, domin ɗakinsu na kallon ɗakin su Jummai, hakan kuwa ba ƙaramin farinciki ya sa su ba, domin zasu gan ta cikin sauƙi.

Jummai kuwa tana ciki tana ta haɗa kaya don Alhaji Lawwali ya ce su bar ƙasar saboda Habeeb zai iya hana su walawa.

Tana cikin Haɗa kayan kenan Ahamad ya faɗo daga kan gado.

Da hanzari ta ɗauke shi ta yi ta rirrigawa.

Duk yadda ta so ya yi shiru, amma ya ƙi, saboda ya bugu sosai.

Ɗauko shi ta yi ta buɗe ɗakin zata fito, ba zato ba tsammani sai ta ga Habeeb tsaye a bakin ƙofar.

Gabanta na wata irin faɗuwa ta banko ƙofar da ƙarfi.

Shima ƙarfin ya sa ya tura ƙofar tare da shiga ciki, bayanshi ya jingina da ƙofar ta yadda ba zata iya buɗewa ba.

“Me ya kawo ka anan?”,  ta tambaye shi cikin fushi.

Kamar Habeeb zai yi kuka ya ce “Fateema ni kike tambaya me ya kawo ni a wurin ki?”

Ta ce “Kai waye da ba za’a ce maka haka ba”.

Ya ce “Ni a masoyinki kuma uban ɗanki”.

Wani mugun kallo ta jefe shi da shi “Uban ɗana? Kai baka ji kunyar faɗin haka ba. Ka manta daya daga cikin karnukan ƙauye ne uban ɗana”

ido Habeeb ya lumshe, lokaci ɗaya kuma ya tuna dalilinta na faɗin haka.

Sassauta murya ya yi “Don Allah to ki saurare ni, magana nake son yi dake”.

Ta ce “Maganar banza da wofi, mugun banza azzalumi”.

Ko kusa bai ji zafin abin da ta ce mashi ba, don ya san shine silar komai.

Haƙuri ya riƙa bata, tare da roƙon ta akan ta zauna.

Yadda ta yi da zaman, sai dai da sharaɗin zai sake ta.

Baki Habeeb ya buɗe yana kallon ta, “kaddai a ce bata san na sake ta ba” ya faɗa a ransa.

A fili kuma ya ce “Na ji zan aiwatar da abin da kike so”.

Hanya ta bashi a kan ya zauna, kafin ya wuce ya miƙa mata hannu da nufin karɓar Ahamad da tunda Habeeb ɗin ya shigo ya dena kuka.

Ƙin bashi Ahamad ɗin ta yi ta ce “Wato in baka shi ka gudu”,

Ɗan gajeren murmushi Habeeb ya yi sannan ya ce “Wa zan kai ma shi idan na gudar maki da ɗa”.

Miƙa mashi Ahamad ɗin ta yi, sannan ya zauna.

Ido ya lumshe tare da rungume ɗanshi tsam a ƙirji, cikin ranshi yana jin wata irin nutsuwa wadda a wurin Jumman ne kaɗai ya taɓa jin irinta.

Ya ɗauki ƴan mintuna a haka, daga bisani ya buɗe idanunsa, gani ya yi sai faman haɗa kaya take a akwati, wanda ko shakka babu shirin tafiya ne.

Cikin raunin murya ya ce “Ki zauna toh mu yi magana”.

Sai da ta gama haɗa kayanta sannan ta zauna a gefen gado, tare da ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya.

Wani irin mayen kallo ya cigaba da yi mata, don a yanzu ta fi da haɗuwa.

Ƙara tsuke fuska ta yi ta ce “Dama kallona ka shigo yi”.

Kai ya girgiza tare da lumshe ido ya kuma buɗe sannan ya ce”Waye wancan mutumin da kuke tare?”.

Kai tsaye Jummai ta dube shi ta ce “Dadirona ne”.

Ido Habeeb ya rumtse gam tare da cije leɓe, don maganar ta daki zuciyarsa, lallai Fateema ta matuƙar canja

Buɗe idanunsa da take suka kaɗa zuwa ja ya ce “Haba Fateema, kin san me kike faɗa”.

Ko kusa ita bata ga illar abin da ta faɗa ba, don haka ne ma ta ce “Tun da nake da kai na taba yi maka ƙarya?

Kai ya girgiza alamar “A’a”, ta ce “Toh ka yadda da maganata, hanyar da ka buɗa mani ce nake bi, ka ga ƙoƙarinka ko?”

Wasu zafafan hawaye ne suka cika ma Habeeb Idanu, sai da ya matse su sannan ya ce “Tabbas nine silar wargajewr rayuwarki, amma don Allah ki bani damar da zan gyara maki ita Fateema”

Dariy ta tuntsre da ita, sannan ta haɗe fuska “Ai ka makaro Habeeb, domin babu sauran abin da ya rage wanda zaka gyara a rayuwata”.

Zuciya iya wuya ta cigaba da faɗin “Zalunci ne Habeeb ka je ina neman sakayyarsa a wurin Allah, kai ne sanadin ɓacin rayuwata, kai ne sanadin mutuwar mahaifina, sannan kai ne sanadin sanyawa mahaifiyata ta tsangwame ni, ta azabtar da ni da yunwa da ƙishirwa, wanda a dalilinsa ne na bar ta domin neman ƴancina, komai kai ne sanadi Habeeb”.

Tana gama faɗin haka ta fashe da kukan baƙinciki.

Kukan shima ya cigaba da yi ya ce “Ki gafarce ni Fateema, tunin duniya na yadda nine sanadin komai, don haka ne ma na zo neman afuwarki”.

“Ba zan iya yafe maka ba Habeeb, don haka ka tashi ka fice mani daga ɗaki”

Kai ya girgiza yana kuka ya ce “Ba zan iya fita ba Fateema har sai kin yafe mani”

Ta ce “Ni zan fita” tana faɗin haka ta miƙe tare da nufar ƙofa.

Fizgo ta ya yi ta faɗo a jikinsu shi da Ahamad, tsam ya tattara su hada Ahamad ɗin ya rungume. 

Kacaniyar ƙwace kanta ta shiga yi, amma ta kasa. Haɗe musu fuskoki ya yi ita da shi suka shiga kallon Juna, bata ankare ba sai jin halshensa ta yi akan fuskarta yana lashe hawayen dake fita a idonta.

Nashi hawayen kuma tana jin sadda suke dira a jikin Ahamad.

Dakatar da lasar hawayen ya yi tare da fara magana cikin raɗa,

“Ki saurareni Fateema, nine Habeeb ɗinki, mamallakin farincikinki, yanzu rayuwarmu a haka bata fi daɗi ba, yanzu halattacen numfashin juna da muke shaƙa ba alkhairi bane”

Sadda dda kanta ta yi a ƙasa tana jin wani irin ɗaci a zuciyarta, don ita dai ta fidda rai daga samun farinciki.

Cigaba da magana ya yi “Wallahi bayan ke ban sake kusantar wata mace ba, kuma ba don bana buƙata ba, sai don ni ɗin mallakin ki ne ke kaɗai.

Don Allah kada ki bi wancan mutumin, ki biyo ni mu tafi, na maki alƙawalin nemo maki farincikinki da na ɓatar maki”.

Ɗan dakatawa ta yi da kukan ta ce “Zaka iya dawo mani da mahaifina”.

Ya ce “A’a” ta ce “Toh kamar haka ne a farincikina, ba zaka iya dawo mani da shi ba, don haka ka barni a kan rayuwar da ka ganni a yanzu, domin ita ce ta fi dacewa da ni”.

Zare jikinta ta yi daga riƙon da ya yi mata, sannan ta cigaba da faɗin “Ka furta mani sakin da muka yi sharaɗi da kai kafin ka zauna, sannan ka bani ɗana”.

A yadda take maganar ko kusa babu wasa a cikinta, don haka ne ma Habeeb ya ce “Zan barki a kan rayuwar da kike a kai Fateema, amma ki sani na sauke nauyin da ke kaina, kuma don Allah ki bani Ɗana, domin ba zan so ya tashi cikin lalatacciyar rayuwa ba”.

Hannu ta kai ta fizgi Ahamad da ƙarfi, wanda ya yi sanadin falkawarsa daga baccin da ya fara.

Kai Habeeb ya girgiza, tare da miƙewa ya ce “Allah ya shiryar da ke, sannan batun saki, tun washe garin ɗaurin auren na sake ki, ki je wurin Abbana ki karɓi divorce paper”.

Rufe bakinsa kenan wayarshi ta fara ringing, yana dubawa ya ga Isma’il, bai jira jin me zata ce ba ya fice, domin Isma’il ɗin na can waje yana gadin dawowar Alhaji Lawwali, kuma da alamun shine ɗin ya dawo.

Ido Jummai ta rumtse tana jin wani irin ɗaci a zuciyarta saboda sakin da Habeeb ya yi mata, domin hakan ya ƙara tabbatar mata da ba sonta yake ba, key ta sa ma ƙofar tare da durƙushewa a wurin tana kuka.

Takun tafiya ta ji, wanda jikinta ya bata Alhaji Lawwali ne, zaunar da Ahamad ta yi da sauri ta faɗa banɗaki.

Sadda ya shigo har ta fara kwarara ma kanta ruwa tana kuka, cike da baƙinciki ta yi wankan ta fito. Ƙuri Alhaji Lawwali ya yi mata, ganin haka ya sa ta fara murzar idanu tare da zaunawa akan cinyarsa ta ce “Hure mani idanuna, sabulu ya shigar mani”

Hure matan ya shiga yi, daga nan kuma ya fara neman abin da yake so, kasa hana shi ta yi, sai dai ƙasan ranta tana jin kamar ta mutu, kuka sosai ta riƙa yi.

Habeeb kuwa yana komawa ɗakinsu ya fashe da sabon kuka, Isma’il na shigowa ya gane Habeeb bai yi nasara ba, kamar Isma’il ɗin zai yi kuka ya ce “Ka yi haƙuri don Allah, tunda ta yi nisa, ka barta da Allah, shine kaɗai zai gyara mata rayuwa idan ya so”.

Cikin kukan Habeeb ya ce “Isma’il muddin ban sake mallakar Fateema ba, toh mutuwa zan yi”

“Ba zaka mutu ba akanta abokina” Lallashinsa Isma’il ya shiga yi, amma ya kasa yin shiru.

Sai da yayi kuka mai isarsa, sannan ya tashi ya yi wanka.

Daga su sai kayan jikinsu suka zo hotel ɗin, don haka Habeeb na kimtsawa suka fice.

Kusan a tare suka fita wajen hotel ɗin da su Jummai, Habeeb na ganin sadda Alhaji Lawwali ke riƙe da hannunta yana ɗan murzawa, ido ya rumtse yana jin kamar zuciyarsa zata fito waje.

Yana buɗewa ya ga zasu shiga mota, ya ɗaga ƙafa zai ruga wurinsu Isma’il ya riƙe shi gam, “Ka sake ni Isma’il, ba zan bari mutumin can ya tafi da Fateema ba” ya faɗa yana ƙoƙarin ƙwace kansa daga riƙon da Isma’il yayi mashi.

“Ba zan sake ka ba, ka rabu da su, duniya ce ta fi bagaruwa jima”.

Fasa bin su ya yi, akan idanunsu motarsu Jummai ta fice daga hotel ɗin.

Da baƙinciki suka koma gida. Isma’il ya ce “Toh wai me ya hana ka ƙwace ɗan, domin haɗari ne a bar mata shi”.

Kamar Habeeb zai yi kuka ya ce “Idan na ƙwace shi in kai mawa, kada ka manta

hanyar da aka samu yaron, ko kana ganin wani zai karɓe shi a hakan”

Isama’il ya ce “Gaskiya hakane kuma, Allah dai ya kawo muku mafita cikin Lamarin”.

“Amiin” ya ce, tare da kai ɗaukar wayarsa da ke ta ruri a ƙasan capet.

Number Nigeria ya gani, cikin zumuɗi ya ɗaga kiran don a zatonshi Ummanshi ce.

Muryar mace ya ji, wadda ko shakka babu Salma ce, amsa sallamar da ta yi mashi yayi, daga nan kuma yayi shiru.

Itama a nata ɓangaren shirun ta yi, da ya ji ta ƙi magana ya ce a fusace “Malama dama don ki ɓata ma mutane lokaci zaki kira su”.

Ɗan shagwaɓewa ta yi “Haba Habeeb, yanzu a haka zamu yi auren, duk wata kulawa da namiji ke ba mace baka bani, ba kira a waya, ba chat, sai dai duk idan na yi, yanzu ka duba WhatsApp, saƙona ya fi a ƙirga amma baka buɗa ba bare har in sanya ran reply, yanzu kuma na kira shine…”

Katse mata magana ya yi da faɗin “Dakata Malama, wai da wa kike shirin yin auren?”

Ta ce “Da kai mana, Haba Habeeb!”.

Wani ƙululun baƙinciki ne ya ƙara turnuƙe shi, don shi dai da ya auri Salma gwara ya ƙare rayuwarsa ba aure “Bari kiji Salma, ki yi gaugawar falkawa daga mafalkin da kike, domin ba zai zama gaskiya ba, ba zan ɓaye maki ba, babu ke a zuciyata, don haka ba zan aure ki ba, ki je ki nemi mai sonki”, yana gama faɗin haka ya katse kiran.

Isma’il da ke kallon ikon Allah ya ce “Kai da wa kuma?”,  Habeeb ya ce “Wata shegiyar yarinya ce, haka kawai uwarta ta ce ta bani ita”.

Dariya abin ya ba Isma’il ” Toh ka karɓe ta mana”. Habeeb ya ce “Allah ya kyauta, wallahi ba zan iya auren yarinyar ba”.

Dariya sosai lamarin ya ba Isma’il, shima Habeeb dariya ya riƙa yi, wadda iyakar ta baki, domin ji ya ke kamar gobara na ci a cikin zuciyarsa. 

Hira suka cigaba da yi akan batun Jummai, daga bisani suka samu mafita cewar Habeeb zai kira Nasir.

A taken ya kira Nasir ɗin tare da shaida mashi an ga Jummai a nan, ko da ta koma gida, toh a Katsina za’a same ta.

Nasir ɗin na jin haka, ya shaida zai faɗa ma Abbanshi komai, shi kuma ya samu Abban Habeeb sai a san abin yi.

Salma kuwa wurin uwarta nufa tare da faɗa  abin da Habeeb ya yi mata, aikuwa ta ce “Toh watan barin uwarsa a gidan nan ya tsaya” don dama sun gaji da zaman Hajiya Mairo a gidan.

Saboda son Habeeb da Salma ke yi ne yasa suke ta dannewa.

Rashin kunya Salma ta fara yi ma Hajiya Mairo a lokacin da ta ce ta ɗauko mata ruwa a fridge.

Shiru Salma ta yi kamar ba ji me ta ce ba.

“Da ke nake fa Salma” Hajiya Mairo ta faɗa cikin faɗa.

Baki Salma ta turo ta fara gunguni “Kawai mutumin na zamansa a riƙa takura mashi”

Miƙewa ta yi ta ɗauko ruwan tare da dungurar da shi a ƙasa.

Iya ƙuluwa Hajiya Mairo ta ƙulu, domin ta tsani yaro ya yi mata rashin kunya, “Zo ɗauke ruwanki bana so” ta faɗa lokacin da Salmar ta juya.

Aikuwa Salma ta juyo zata ɗauke ruwan, riƙe mata hannu Hajiya Mairo ta yi tare da fizgo ta ƙasa ta durƙushe.

“Yanzu don ubanki Salma ni kike ma rashin kunya”. Fizge Hannunta ta yi tare da faɗin ba dai ubana ba wallahi”

Duk wannan abu da ke faruwa akan idon Hajiya Sa’a.

Duban ta Hajiya Mairo ta yi tare da magana cikin jin haushi “Hajiya Sa’a kin ga ɗiyata, ni take ma rashin kunya”

Baki Hajiya Sa’a ta ɗan taɓe “Na gani mana, yara ne sai addu’a” tana gama faɗin haka ta miƙe ta nufi ciki, daga can ta ƙwala ma Salma da ke wurin fridge kira.

Da ido Hajiya Mairo ta raka Salma lokacin da ta bi bayan uwarta suka shige, “Lallai kema kin ce wani abu”

Kasa tashi ta yi daga inda take saboda takaici, Ɗaukar ma ranta ta yi duk ranar da Salma ta ƙara yi mata rashin kunya sai ta hukunta ta.

Sai dai kuma wannan ƙudiri ba ƙaramin takaici ya ja mata ba, domin Salma ba ta fasa yi mata rashin kunya ba, da abin ya kai Hajiya Mairo ƙarshe ta ɗaga hannu ta wanka mata mari.

Da yake Salmar ƴar iska ce ta ɗaga hannu zata rama, riƙe hannun Hajiya Mairo ta yi “Da kin raina kanki wallahi, a haka ɗana zai aure ki”.

Salma ta ce a tsiwace “Ɗan banza gareki” zagin Hajiya Mairo ta fara yi.

A wannan karon ma sai da Hajiya Mairo ta sake nuna ma Hajiya Sa’a abin da Salma ta yi mata.

Maimakon ta ɗauki mataki, sai cewa ta yi “Yoh kema Mairo, kamar baki san halin yaran zamani ba, ai ko ni da na haifi Salma ba zan mare ta ba”.

Hajiya Mairo ta ce “Haka kika ce?”.

Hajiya Sa’a ta ce “Ƙwarai kuwa”.

“Duk abin da aka yi ma shamuwa watan bakwai ne ya ja mata, ni nazo gidanku, don haka yau zan tafi.

Zagi da gori suka shiga yi mata, da yake ƴar tijara ce ta biye musu, ta ce “Tsinannu, dama wa zai iya haɗa iri daku”

Hajiya Sa’a ta ce “Talle dai bata yi ma audi gori, sanadin cikin shege da ɗanki yayi, aka sake ki, kin ga kuwa ku ne irin tsinannu”.

Maganganu masu zafi suka yi ta jifar juna da su,  sai da suka ci suka tsire da faɗan sannan ta tattara kayanta ta fito falo.

Duban Hajiya Sa’a ta yi “Kuɗaɗena na wurinki na ke son jin alert kafin in fita”, da yake sun haɗa jari suna kasuwanci, kuma Hajiya Sa’a ce ke jan ragamar kasuwancin, shi ya sa komai ke hannunta.

Hajiya Sa’a ta ce “Kuɗi an ci an cinye, ina jiran sammaci”.

Wani sabon faɗan suka dasa, a wannan karon yunƙurin dukan Hajiya Mairo suka yi, ba arziki ta bar musu gidansu, tare da tabbatar musu da ko da bala’i sai an biya ta kuɗinta.

Asabe kuwa tun ruwa na fita a idonta akan ɓatan Jummai har ta kai ga sun ƙafe. Kukan zuci ta dasa, wanda kullum take cikinsa ba dare ba rana.

Hakan ne kuwa ya haifar mata da matsanancin ciwon zuciya, wanda sai da ta yi wata biyu kwance a asibiti. Dr Ameer ne ya yi ta faman kula da ita tare da bata maganganu masu tausasa zuciya, domin shima ya yi iya ƙoƙarinsa wurin neman Jummai, amma bai ganta ba.

Aranar da aka sallame ta ne Dr. Ameer ya yi mata Nasihar da ta ɗaukar ma ranta cire damuwa, duk da ta san ba zata iya ba.

Ya ce “ki yi haƙuri, kowa yana ɗauke da ƙaddararsa, wadda kuma bata da makankara.

Muddin kika kasa haƙuri da ƙaddararki, toh a dalilin haka zaki iya rasa ranki, kin ga kin jefa sauran yaranki a damuwa. Gashi kuma basu da wani gata da ya wuce ke, ko kina fatan rayuwarsu ta shiga garari”

Kai ta girgiza tare da share hawayen da ke ta fita a idonta

ya ce “To ƴarki ba ita ce kaɗai ta fara barin gida ba, ansan irin wannan ba daɗi, amma ki yi haƙuri, duk abin da ta aikata kanta ta cutar.”

Sosai Asabe ta ɗaukar ma ranta cire Jummai a rai, tare da ba sauran yaranta kulawar da ta dace, domin rayuwarsu ta inganta.

A ɓangaren Jummai kuwa, suna komawa gida ta fara shirin barin gidan Alhaji Lawwali, a hankali ta yi ta ɗibar kayanta tana kai wa unguwar da suka fara zama da su Yakumbo ana aje mata, duk abin da ta ke shiryawa Alhaji Lawwali bai sani ba.

Sai da ta kwashe komai nata sannan ta bar gidan.

Alhaji Lawwali na dawowa ya ga bata nan, kiranta ya yi a waya, tana ɗagawa ya ce “Yallaɓoi kina ina ne?”

Daga can ta ce “Na kama gabana”, ko kusa bai fahimce ta ba “Kamar ya kin kama gabanki?” ya sake tambayar ta.

“Alhaji na gaji da hulɗa da kai, don haka zan je kuma in nemi wani” tana gama faɗin haka ta katse mashi kiran.

Wata irin ashar ya saki, tare da ɓaɓɓakewa da dariyar mugunta “Yarinya kin makaro wallahi, domin ba ke ce ta farko ba”.

Hotel Jummai ta kama, ta cigaba da rayuwarta a can, jefi-jefi ta kan yi hulɗa da mutane, domin ta rage ma kanta tsananin buƙata.

Alhaji Mainasara kuwa ya fara shirin zuwa Katsina, domin Nasir da Babanshi sun same shi har gida da labarin ganin Jummai. Wanda kuma suka tabbatar mashi daga wurinsu Habeeb labarin ya fito.

Hakan ne ya sa shi kiran Habeeb a karon farko tun bayan tafiyarsa.

Habeeb ya yi murna da jin muryar mahaifinsa. Shima Alhaji Mainasara ya ji daɗin jin muryar ɗansa, amma sai ya ɓoye.

Kai tsaye bayanai ya nema wurin Isma’il, yana samu ya yi mashi godiya tare da katsen kiran.

Habeeb ya son yin doguwar magana da mahaifinsa, amma dole ya haƙura, gaisuwar ma da suka yi ta gamsar da shi.

Washe gari tunda safe Alhaji Mainasara ya kama hanyar garin Katsina, cikin ransa yana ta jin daɗi, domin samun Jummai kamar yayewar mafi rinjaye a baƙincikinsu ne.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Ko Ruwa Na Gama Ba Ki 15Ko Ruwa Na Gama Ba Ki 17 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×