Skip to content
Part 7 of 16 in the Series Ko Wace Kwarya by Sadik Abubakar

Ta ɗan turo ƙaramin bakin nan gaba ta ce, “Ba za ka bari ba ko yaya Abdul? Ni lafiyata ƙalau kawai na gaji da zuwa makarantar ne.”

Cikin dariyar ya ce, “Ikon Allah! Watau mun gaji da zuwa makarantar boko amma ba mu gaji da zuwa Islamiyya ba.”

Ta sake zumɓurar baki ta ce, ‘Yaya Abdul! Yaya Abdul! Shike nan bari na tafi kawai tunda yau sai dariya kake yi mini idan na yi magana.”

“To ai idan mutum ya ji abin yin dariya ba ya sanin lokacin da take kufce masa, amma a yi mini afuwa ba zan sake ba. Yanzu faɗa mini gaskiya dai, idan ba haka ba kuma zan ci gaba da yin dariyar.”

“To shike nan zan faɗa maka. Da ma ba komai ba ne da ma Abba ne. Ka ga wata makarantar kawai nake so a sake mini.”

Dariya ce ta sake suɓuce masa, ya yi ta tulluƙa abarsa har sai da ta fara fusata sannan ya ɗan numfasa ya ce, “Gaskiya kyanki shirin drama irin mai ban ban dariyar nan. Daga rashin lafiya sai gajiya, yanzu kuma canja makaranta ma za a yi gabaɗaya.”

Ta gama ƙulewa sosai ta miƙe baki a zumɓure za ta tafi. Cikin sigar rarrashi da tarairaya haɗi da sakin wani ƙayataccen murmushi ya ce, “Koma ki zauna ƙanwata ta kaina, abar alfaharina mai sa ni farinciki da nishaɗi.”

Zaman ta yi ya riƙa bin ta da wani irin mai cike da kulawa har sai da ta magantu da cewa, “Ya dai?”
Ya ɗan kauda kai tare da haɗiyar yawu sannan ya ce, “Abban ne ya ce za a canja miki makaranta ko kuwa?”
Kanta a ƙasa ta ce, “A’a ba shi ba ne, kawai dai shi yanzu ba…”

Ya yi saurin katse ta da cewa, “Ya isa haka gobe ki shirya ki tafi makaranta.”
Ta rasa inda za ta sa kanta saboda jin kunya, ta fuskanci ya gane dalilin ƙin zuwan nata. Sun jima suna hira, yana zolayar ta ita kuma tana masa shagwaɓa tamkar ƙaramar yarinya.
Washegari da safe ta shiga kici-kicin shirin makaranta, Umma na kallon ta ba ta ce mata uffan ba, sai da suka gama karin kumallo ta ce, “Umma zan tafi makaranta, jiya da yaya Abdul ya zo ya ce yau na shirya na je.”

“Don me za ki faɗa masa? Shi ma yana fama da ƙanwarsa da mahaifiyarsa duk nauyinsu na kansa.” Abba ne ya yi wannan maganar cikin sigar faɗa.

Umma ta karɓe zancen da cewa, “To ai ba komai ba ne idan ya biya mata indai ba tambayar sa ta yi ba. Ko tambayar sa kika yi ne?”

Kafin Zaliha ta buɗa baki Abban ya sake karɓe akalar zancen da fadin, “Ba haka ba ne, yaron nan yana yi daidai gwargwado. Bai kamata a siƙe shi ba.”

Cikin tsantsar biyayya da bayyana dukkan gaskiya, Zaliha ta ce, “Abba wallahi ba roƙon sa na yi ba, da ya tambaye ni ma me yasa ba na zuwa ce masa na yi ba ni da lafiya. Shi ne ya ce to ai yanzu na warke na tafi kawai.”
“To shike nan ba komai, Allah Ya yi miki albarka, Allah Ya sa a biya mu albashi sai na biya miki na shekara ɗaya ma na huta.”

“Amin Abba!”

Ta faɗa sannan ta juya tana kallon Umma, “Yanzu fa sai ki ce sai na ba ki kuɗin tara ko?” Dariya ta yi tare da sunkuyar da kai. Umma ta ci gaba da faɗin, “Ai ni na san kwanan zancen, wannan kallon da biyu ake mini shi. Yau sai dai Abbanki ya fanshe ni, hutawa zan yi.”

Naira ɗari Abban ya zaro ya ce, “To ga shi ko, a yi karatu sosai kuma a kula, Allah Ya tsare.”

Da ta zo makaranta ba su haɗu da yaya Abdul ba sai da aka tashi, ta tsaya jiran sa kamar kullum. Mintuna kamar biyar bayan an ragu ya fito, “Mu tafi ko? Ya faɗa kafin ya iso kusa da ita.
Jerewa suka yi suna tafiya, ya sa hannu cikin aljihunsa ya zaro rasitin biyan kuɗin maaranta mai dauke da sunanta ya miƙa mata tare da cewa, “Ki saka wannan a cikin jaka.”

Ta karɓa cikin jin kunya ta ce, “Yaya Abdul na gode sosai Allah Ya saka da…”
Ya dakatar da ita da cewa, “Ya isa haka, ba na son ki ce kin gode. Mene ne abin godiya don mutum ya yi wa ƙanwarsa abu, da ma ai haƙƙinsa ne na ya yi mata.

“Hmm! Ai wallahi godiya ta zama tilas! Kuma kada fa ka manta kai ne kake karanta mana haɗisin da ke cewa, ‘Wanda duk ba ya gode wa mutane, to ba zai gode wa Ubangiji ba.”

Murmushi ya yi kawai, ba shi da ta cewa, domin ta kai kat! Idan aka ce Annabi ya ce, to bi ake a sunkuyar da kai haɗe da mika wuya don neman dace da sa’a a ranar tsayuwa.

Jin ya yi shiru bai ce komai ba sai ta ce, “Ko da gyara a maganata?” Murmushi ne ɗauke a fuskarsa ya ce, “Wane mutum in ji mutuwa! Ni na isa na yi gyara a wannan maganar? Abu ɗaya dai nake so ki yi mini alƙawari!”
Martanin murmushin ta mayar masa sannan ta ce, “Ina jin ka yayana!”

“Yawwa ina son duk lokacin da makamanciyar wannan buƙata ta taso ki riƙa sanar da ni, kin ga yanzu a dalilin ba ki sanar da ni ba ne har kika yi asarar karatun kwana biyu. Koda ba za ki faɗa mini baki da baki ba, to ki riƙa rubutawa kina ajiyewa wajen da zan gani, don na san ki da jin kunya da zurfin ciki. Wannan ne alƙawarin da nake so ki yi mini.”

Shiru ta yi, kallo ɗaya za ka yi mata ka fahimci kunya ce ta yi sansani a fuskarta. “Kin yi shiru ba ki amsa mini ba.” Ya sake faɗa.

Shirun dai shi ne abin da za ta iya yi a wannan yanayi. A haka har suka zo daidai wajen da suke rabuwa. Da ta iso gida take nuna wa Umma takardar biyan kuɗin, farinciki ta nuna sosai da fatan alkairi. Shi kuwa Abba sam bai ji daɗin hakan ba za ganinsa kamar Zalihar ce ta tambaye shi ya biya mata. Sannan kuma hakan kamar zubar da ƙima ne. Daga ƙarshe dai ya ce da Zalihar ta faɗa wa yaya Abdul ɗin yana son ganin sa.

Washegari kuwa da dare yaya Abdul ya zo daidai lokacin da ya san zai samu Abban, bayan ya gaishe shi cikin ladabi da girmamawa. Abban ya ɗora da faɗin, “Jiya Zaliha take nuna mini abin arziki, kai da kake fama da kanka, ga hidimar su Inna, ai da ka bari wataƙila karshen watan nan a sakar mana kuɗaɗen gabaɗaya. Da ma wani ɗan bincike ake gudanarwa, abin da ya kawo cikas ke nan.”

Kansa sunkuye cikin matuƙar risinawa ya ce, “Abba ai ba komai, tun farko ma ban sani ba da ko fashin kwana ɗaya ba za ta yi ba. Kuma ina roƙon ka don Allah ka bar mini wannan ɓangaren na karatunta.”

“A’a kai haba! Sam ba zai yi yu ba. Idan amarya ba ta hau doki ba, ai ko ba za a ɗora mata kaya ba. Wannan ma da na san za ka yi wallahi ba zan bari ba. Wannan ɗin da ka yi na gode sosai Allah Ya saka da alkairi.”

Cikin jin kunya ya ce, “Abba ai ba wahala ba ce, duk abin da na yi wa Zaliha kaina na yi wa, ƙanwata ce.”
Haka dai suka rabu Abba na cewa ba zai ɗora masa wahala ba, shi kuma yana cewa ya ji ya gani zai iya.

Ranar wata Asabar ɗin tsakiyar wata, Umma ta shirya ta tafi kasuwar Kurmi don yin wasu saye-saye. Ta je ta sayo abubuwan da take buƙata, a kan hanyarsu ta dawowa wani mai mota ƙirar A-kori-kura ya lafto kaya, burki ya shanye masa. Ya cacimi Adaidaitar da Umma take ciki da wasu masu tafiyar ƙasa ya haɗa da motocin da ke gabansu ya matse, abin babu kyan gani. Mutane biyu suka karye nan take har da direban Adaidaitar, hatsarin ya yi muni sosai, Umma ba ta samu karaya ba sai raunuka da bugawa, a sume aka kwashe su zuwa aisibitin Murtala sashen ba da kulawar gaggawa (Emergency).

Wayoyin majinyatan aka bincika da nufin ko za a iya gano danginsu, cikin sa’a kuwa ana duba wayar Umma, lambar Abba ce kiran ƙarshe da ya shiga. Kiran sa aka yi, yana ɗagawa ya ji muryar namiji yana faɗin, “Barka da war haka, mai wannan wayar ce suka yi hatsari suna nan asibitin Murtala sashen gaggawa, amma da sauƙi.”
A razane Abba ya riƙa faɗin, “SubhanAllah! To gani nan zuwa In Sha Allah!”

“Abba lafiya dai?” Zaliha ce ta tambaya cike zaƙuwar jin dalilin tashin hankalin Abban nata.

“A’a ba komai, wai su Ummarki ne suka yi hatsari, bari na je na gani. Ki zauna.”

Bai gama rufe bakinsa ta zube ƙasa sumammiya, “INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI’UN Zaliha!” Ya faɗa tare kama ta yana girgiza ta.

Ɗaukar ta ya yi ya kwantar bisa kujera ya fara yi mata firfita, tana kwance shame-shame kimanin mintuna biyar ba ta motsa ba, tashin hankalinsa sai ya ƙara daɗuwa ainin.

Tashin hankali ba a sa maka rana. Ana bikin duniya ake na kiyama. Ana wata sai ga wata. Abba ya ga ta-kansa, ga mata can ta yi hatsari bai san a halin da take ciki ba, nan kuma ‘ya ta suma. Allah ke nan! Mai yin yadda Ya so, a lokacin da Ya so, kuma ga wanda Ya so. Yakan jarrabi bawa da masifu kala-kala ba don Ya tagayyara bawan ba, sai don Ya auna ƙarfin imaninsa.

Ganin Zaliha ba ta farka ba kuma can ana jiran sa hankalinsa zai rabu gida biyu, sai ya miƙe da sauri ya nemo Mai Adaidaita. Ya saɓi Zaliha ya saka a ciki ya ce ya kai shi asibitin Murtala.

Tunda ita ma suma ta yi zai fi kyau ya kai ta asibitin don ya tara hankalinsa waje guda.

Yana isa aka shiga da Zaliha sashen kulawar gaggawa ita ma. Sai da aka duba ta aka sa mata ruwa sannan ya nemi ɓangaren ‘yan hatsari inda aka kwantar da Umma. Ita ma ɗin tuni likitoci sun hau kanta ana ta ba ta kulawar gaggawa, sai dai har kawo wannan lokaci ba ta motsa ba. Ta bugu a ƙirjinta kuma ta zubar da jini sosai, lamarin da ya sa ake buƙatar yi mata ƙarin jini.

“INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI’UN!” Ita ce kalmar da ke ta maimaituwa a bakin Abba. Ba shakka wannan jarabarawa ce mai girman gaske daga Allah, tilas ta girgiza duk wanda aka aiko masa ita.

Babban ƙalubalen da zai fuskanta a wannan jinya da zai yi ita ce rashin kuɗi, har yanzu ba a sakar masa albashinsa ba ga shi an shiga wata na biyar. A halin da ake ciki kuɗin hannunsa dududu ba su wuce naira dubu biyu ba.

Jadawalin abubuwan da ake buƙata za a yi wa Umma aka gabatar masa ciki har da jini lita ɗaya, abin da ya fi ɗugunzuma masa hankali ke nan.

To, a Islamiyya yaya Abdul bai ga Zaliha ba har lokacin ya ƙure, har ma aka tashi. Bayan Magariba ya yi salla sai ya biyo ta gidan ya ji ko lafiya? Iske ƙofar gidan ya yi a garƙame da kwaɗo, mamaki ya ɗan kama shi kaɗan haɗe da tunanin, ‘to ina suka tafi haka har da kulle gida kuma ba ta faɗa mini ba?’

Yana tsaye a wajen sai ga wata ‘yar maƙwabtan su Zalihar ta fito, sai ya tambaye ta, “Waɗannan unguwa suka tafi ne?”

Ta ce, “A’a Zaliha ce ba ta da lafiya sun tafi asibiti tun da rana.”

Hankalinsa ya tashi nan take har wani gumi ne ya fara tsattsafo masa. Bai tsaya tambayar ta ko wane asibiti suka tafi ba, da sauri ya bazamo bakin titi ya kira lambar Abba bugu ɗaya ta shiga Abba na ɗagawa bai jira ya fara yin magana ba ya ce, “Abba barka dai, kuna wane asibitin ne?”

“Muna nan Murtala ɓangaren gaggawa.”

Jin Abba ya ambaci ɓangaren gaggawa hankalinsa ya ƙara tashi, bugun zuciyarsa ya ƙaru, babu shakka shi ma da za a gwada jininsa a wannan lokaci to za a samu ya hau.

A kiɗime ya tari Mai Adaidaita ya ce, “Mu je!”

“Ina za mu je?” Mai Adaidaita Sahu ya tambaya.

“Malam mu je da sauri ka kai ni asibitin Murtala.”

Mai Adaidaita ya ja yana faɗin, “Allah Ya sawwaƙe!”

Suna isa ya zaro kuɗi kafin Mai Adaidaitar ya gama tsayawa tuni har ya dire ya kutsa kai cikin asibitin yana kiran lambar Abba, tare da tambayar inda suke. Zuwa lokacin Zaliha ta farfaɗo, ruwan da aka sa mata bai ƙarasa ƙarewa ba. Abban yana kusa da ita yana kwantar mata da hankali game da mahaifiyar tata.

Fitowa ya yi ya shiga da yaya Abdul, idonsa a kan Zaliha tana kwance, kusan minti ɗaya suna kallon juna, hawaye ya ciko a idonsa. Cikin dabara ya share shi duk da haka ta gani, matsawa ya yi daf da gadon ya ce, “Sannu ya ya jikin naki?”

“Jiki da sauƙi” Ta amsa.

Ya juyo ga Abba ya ce, “Mene ne yake damun ta?”

Cikin yanayin alhini Abba ya ce, “Wallahi lafiyarta ƙalau muna tare da ita a gida sai aka yi mini wayar uwar sun yi hatsari shi ne ita kuma ta faɗi a sume!”

“INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI’UN! Umma ce ta yi hatsari, tana ina yanzu?” A matukar firgice yaya Abdul ya riƙa yin maganar wadda ta janyo dukkan hankulan majinyatan kansu.

Cikin murya marar kuzari Abba ya ce, “Tana can sashen…” Sai ya dakata da maganar gudun kada Zaliha ta sake rikicewa.

Miƙewa ya yi ya fito daga ɗakin, yaya Abdul ma ya biyo bayansa.

Suna fitowa sai ga jami’ar da ke kula da Umma ta taho ta sanar masa lallai fa ana buƙatar jinin da za a ƙara wa Umman da gaggawa. “Ya jikin yarinyar?” Ta tambaya.

Ya amsa mata da cewa, “Alhamdu Lillah! Ta warware saura kaɗan ruwan ya ƙare.”

“To madalla, Allah Ya rufa asiri. Da ma batun jinin ne, ya kamata a samo wanda za su bayar a yau domin idan an ɗauka sai an tantance kafin a ƙara mata, ga shi lokaci sai ƙara ja yake.”

“Wai Umman ce za a ƙarawa jini?”

Yaya Abdul ya tambaya.

Abba ya girgiza kai kafin ya yi magana ya yaya Abdul ya dubi jami’ar ya ce, “Za a iya ɗibar nawa?”

“Me zai hana, gwadawa za a yi tukunna.”

Gwajin aka fara yi sai dai bai yi daidai ba, amma za a ɗiba sai a yi musaya a wajen masu sayarwa. Sai sun ba da wani abin ihsani. Yaya Abdul ya ce, indai sai sun ba da kuɗi ne kawai a bar shi. Nawa ne lita ɗayar? Aka faɗa masa, nan take ya tinkari wajen da ake sayar da jinin ya sayo ya kawo aka tantance aka jona wa Umma.

Ruwan da aka sa wa Zaliha kuwa tuni ya ƙare har an cire mata, ta miƙe garau da ita. Ta matsa sai ta ga Umma amma Abba ya hana.

Yaya Abdul ya dubi Abba ya ce, “Bari na ɗan je gida yanzu zan dawo.”

<< Ko Wace Kwarya 6Ko Wace Kwarya 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×