Skip to content
Part 10 of 16 in the Series Ko Wace Kwarya by Sadik Abubakar

Waye Alhaji Saminu?

Alhaji Saminu Lawan Shanono shi ne cikakken sunansa, haifaffen garin Shanono ne da ke jahar Kano. A can ya girma har ya yi auren fari, bayan shekara ɗaya kuma ya komo birinin Kano. Sana’ar sayar da gwanjo ya fara kafin daga bisani ya haɗu da wani maigida ɗan siyasa. Sai ya bar sayar da gwanjon ya riƙa bin sa duk inda zai je. Ana haka idan aka samu wata ‘yar kwangila ta sayen kayayyaki a gwamnatin ƙaramar hukuma, shi ake a ba wa. Tafi-tafi har ya samu ɗaukaka yanzu ba irin kwangilar da ba ya yi. Shi ne Mamallakin kamfanin kwangila na SHANONO CONSTRUCTION NIGERIA LIMITED.

A yanzu haka yana zaune a unguwar Tudun Yola. Yana da matan aure huɗu, kodayake ya rabu da ɗaya, dalilin da ya sa zai cike gurbinta da Zaliha ke nan. ‘Ya’yansa tara, guda biyun ƙarshe ne kawai Zaliha ta girmewa.

Uwargidan sunanta Hajiya Lami, mai bi mata kuma tana amsa suna Hajiya Sabuwa, sai ta ukun ana kiran ta Suwaiba. Babban ɗansa namiji ne wanda uwargidan ta haifa masa, sunansa Anas. Sai mata uku da suka biyo bayansa, Nusaiba da Habiba da Fa’iza, biyu tuni suna ɗakin mazajensu.

Ita ma Hajiya Sabuwa tana da yara uku mace ɗaya, Zuwaira wacce ita ma an yi mata aure sai maza biyu Aminu da Isma’il ƙannenta.

Suwaiba kuma tana da yara biyu ƙanana sune Aliyu da Sadiya. Wacce ta fita ba ta haifa masa komai ba.

Har kawo yanzu cikin ahalin nasa babu wanda ya samu labarin yin auren, walau matan ko kuma ‘ya’yan, bai sanar da su ba gudun kada su maimaita masa makamancin abin da suka yi masa lokacin da zai aure wacce ta fita.

Babu shakka Haliya Lami da Hajiya sabuwa suna taka muhimmiyar rawa wajen daƙile ƙudurinsa na ƙara aure. Kai hasalima su suka fitar da ita, domin auren bai ci Talata ba bare Laraba ya mutu mut!

Ta fuskar kula da iyali ba shi da matsala, dukkan buƙatun yau da kullum kama daga kan abinci da sutura da sauran abubuwa, wanda ransu yake muradi shi suke yi.

Matsalarsa ɗaya dai ita ce, ba ya iya tsawatarwa. Sai abin da uwargidan ta tsara, haka ma ‘ya’yan abin da suka yi niyya shi suke aiwatarwa. Hajiya Lami da Hajiya Sabuwa sun haɗe kansu suna gasa wa Suwaiba aya a hannu, baya ga shiga tsakaninta da Alhajin da suka yi. Ba ta da sakewa sam haka ma yaranta, zaman dai Ibada kawai take.

Marainiya ce gaba da baya, iyayenta sun rasu, a hannun kakarta ya aure ta, kakar kuma ta rasu, sai dangin iyayen nata ba ta cika kai musu ƙorafi ba kasancewar ta marar son magana.

To wannan ke nan a takaice game da tarihin Alhaji Saminu da iyalansa.

To, tsawon mako biyu aka kwashe ana rubuta jarabawar WAEC, ranar ƙarshe aka shirya liyafar yaye ɗalibai kamar yadda aka saba.

An ba da kyautuka da karrama wasu daga cikin malamai da ɗaliban har ma da sauran jama’ar da ke ba da gudummawa wajen ciyar da ilimi gaba a makarantar.

Bikin na bana ya zo wa yaya Abdul cikin wani yanayi na rashin walwala, sam bai yi wani farinciki ba duk kasancewar shi ne wanda ya samu lambar yabo ta malami mafi ƙwazo da kula da aiki.

Ita ma Zaliha haka abin ya kasance mata, masu iya magana na cewa, ‘Abin da ya ci doma ba ya barin awai.’ Ita ce ɗaliba mafi tsafta da ɗa’a.

A ɗaya ɓangaren kuma shirye-shiryen bikinta da Alhaji Saminu sun yi nisa sosai, kawo yanzu dai babu abin ake dakon illa zuwan ranar da aka tsayar. Duk wani abu na aure da ake yi a bisa al’ada, Alhaji Saminu sai da ya riɓanya shi.

Ba wai kaya na jigari-jigari ba, kaya ne irin na wanda suka ci suka tayar da kai da naira. Umma ta samu abin da take buri, ta tatsi madarar naira sosai. Ko yanzu kasuwa ta watse ɗankoli ya ci riba.

Zaliha kuwa ta ƙara ramewa ta ƙarjale tamkar mai cutar ƙanjamau. Tunanin ya zame mata guda biyu, baya ga tunanin wanda ta yiwa tanadin ƙare rayuwarta da shi akwai kuma tunanin rayuwar da take shirin faɗawa ciki.

Gidan mai mata uku ita ta huɗu, kuma matan ba yara ba manya sa’annin mahaifiyarta. Shin ya ya za ta yi a cikinsu? Me ta sani game da irin wannan zama?

Shi ma yaya Abdul kusan yanayin da ya tsinci kansa ke nan, Inna ke ɗawainiyar rarrashin sa safe da yamma. Idan ya zauna ya yi shiru sai a yi ta magana bai sani ba. Hakan ya sa Inna ta ƙara ƙaimi a kansa, har tsayuwar dare ta riƙa yi domin Allah Ya sassauta masa yanayin da yake ciki. Ta yi ƙoƙarin maye masa gurbin Zaliha da wata ‘yar aminiyarta mai suna Aisha da ke karatu a makarantar ‘yammata ta Jogana.

Ita ma ta kammala lokaci guda da su Zalihar. Sai dai ya ƙi amincewa, don ko kama mata zancen ba ya yi. Babu wacce zuciyarsa ke ambato face Zaliha. Addu’a ta ci gaba da yi masa kawai. Babu shakka ita ce mafita, duk abin da ya yi wa bawa tsanani to ya rungumi haƙuri da addu’a, su ne matakan nasara.
*****
Rana ba ta ƙarya sai dai uwar ɗiya ta ji kunya! Ta faru ta ƙare an yi wa mai dami ɗaya sata. Komai nisan gari akwai na gabansa. Wannan zantuka haka suke, ba kokwanto.

An ɗaura auren Zaliha da Alhaji Saminu Shanono, an yi shagalin biki ƙasaitacce. Duk auren da ya yi a baya babu wanda ya buɗe bakin lalitarsa naira ta riƙa ambaliya kamar wannan.

A ranar ɗaya aka haɗa ɗaurin auren da yini, aka gama aka kai amarya gidanta bayan an yi dukkan abubuwan al’ada, wanda suka haɗa da fada fa nasihohi da jan kunne ga ango da amarya.

Sai da bikin ya rage saura awanni arba’in da takwas sannan ya sanar da matansa, kodayake sun yi hasashen hakan lokacin da suka ga an sake gyare gidan gabaɗaya tare da sauya dukkan kayan da ke ɓangaren wacce ta fita, wanda kuma nan ne inda aka kai Zaliha. To su a tunaninsu ba yanzu zai yi auren ba. Wannan mamaya da ya yi musu ta ba su mamaki sosai.

Amma sun lashi takobin babu shi babu zaman lafiya, sun ga ta yadda zai ji daɗin auren.

Gidan nasa tamfatsetse ne, ɓangare-ɓangare ne da yawa wanda ko zai auri mata huɗu sau huɗu to gidan zai ishe su da duk ‘ya’yan da za su haifa.

Ɓangaren da aka kai Zaliha ya fi kowanne sashe haɗuwa da kayan alatu na ƙasar waje, abin da aka kai ta da shi shi ne kayan jikinta kawai.

Tunda aka fita da ita take tuttular da hawaye har aka kai ta, ‘yan kai amarya suka gama ‘yan nasihohinsu suka bar ta nan. Abokanan ango ma suka rako shi, su ma suka yi duk surutan da ake yi suka watse, Zaliha ba ta numfasa da kwaranyar da hawaye ba. Babu shakka da a ce hawaye na ƙarewa to tuni da nata sun ƙare.

Rarrashin ta ya shiga yi da faɗin, “Ina so ki fahimci wani abu, wannan ba lokaci ba ne na kuka. Duk abin da kike tunani ba haka ba ne, nan gidan aminci ne kika zo. Duk wata kulawar da kike buƙata za ki same ta a wajena. Duk ‘ya mace da kike gani irin wannan rana tana jiran ta komai daren daɗewa. Na yi alƙawari ba za ki taɓa yin kukan rashin kulawa ba, ki kwantar da hankalinki, nan ne sashenki.”

Ya jima yana ta magana shi kaɗai, ita kuwa sai ɓarin hawayen take, da kyar ya samu ta daina kukan sannan ya miƙe ya cire manyan kayan jikinsa, ya janyo kazar sayen baki ya zauna bakin gado kusa da ita sosai. Ya gutsiro ya kai mata baki, sai ta sake fashewa da kuka.

“Zaliha ya kamata ki daina kukan nan haka, kada ya janyo miki ciwo. Ba cutar da ke zan yi ba.” Ya faɗa yana ƙara matsawa jikinta, cikin kukan ta ce, “Ba na ci.”

Ya buga ya raya ta ci, amma fur ta ƙi, haka nan ya haƙura ya ƙyale ta. Ya ci wacce zai iya ya bar mata sauran. Yana gamawa ya wanke bakinsa ya haye gadon sannan ya ce, “To ki tashi ki sanya kayan barci.”

Tamkar dutse yake yiwa maganar, daga kwance ya matso kusa da ita, ta saki kuka mai sauti tare da miƙewa daga kan gadon. To ganin yadda ta ƙi sakin jiki a daren, sai ya ƙyake ta ya yi kwanciyarsa har barci ya kwashe shi.

Tsakar ɗakin ta zauna ta ci gaba da sharɓar kukanta har barci ya yi awon gaba da ita. Kiran sallar farko ta farka, me masarrafar sautinta za ta jiyo mata? Munshari ne ya cika ɗakin, irin mai gurnanin nan.

Banɗaki ta shiga ta yo alwala ta zo ta fara salla. Sai da aka yi kiran Assalatu sannan ya farka, ganin ta tana salla ya ba shi mamaki sosai. A tunaninsa ba ta yi barci ba ke nan? Miƙewa ya yi ya shiga banɗaki ya yi alwala ya fita ya tashi sauran iyalansa sannan ya wuce Masallaci.

Gari na ƙarasa wayewa bayan an yi karin kumallo, ya tattara dukkan ahalin nasa ya gabatar musu da Zaliha, sannan ya gabatar mata da su ɗaya bayan ɗaya. Ya ja kunnensu da su yi zaman lafiya da juna. Harara kawai Hajiya Lami da Hajiya Sabuwa suke aika wa Zaliha.

Suwaiba kuma a ranta take cewa, “Wannan yarinya da a ce kin san yadda gidan nan yake da ba ki yarda kin shigo shi ba koda wasa, babu abin da za ki tsinta face baƙin ciki da takaici.”

Anas kuwa kallon Zaliha yake sosai yana jinjina yadda mahaifin nasu ya zaluƙo wannan kyakkyawar halitta haka. A ransa shi ma ya ce, “Gaskiya Alhaji wannan ba kalarka ba ce ba fa!”

Bayan ya gama yi musu nasihar kowacce ta ja zugarta ta koma ɓangarenta, shi ma ya ja amaryarsa suka yi sashenta.

A can ɗin ya ci gaba da jan hankalinta yana dannar ƙirjinta akan ta saki ranta. Ta sani yanzu ta shigo wata sabuwar rayuwa ce wacce ta bambanta da wacce ta kammala a gaban iyayenta, wannan zango da ta shiga zango ne na Ibada tsantsa, zango ne mafi muhimmanci a rayuwar kowanne mahaluki.

Sauraren sa kawai take da kunne amma sam ba fahimtar mai yake cewa take ba, sam zuciyarta ba ta tare da shi. Turnuƙun baƙin ciki ne maƙare a ranta. Wannan ke nan.

Duk da addu’ar da Inna ta duƙufa yi wa yaya Abdul sai da ya kwanta ciwo bayan an ɗaura wa Zaliha aure. Cuta kashirɓan, ya ƙi ci ya ƙi sha, ya rame sosai ba inda yake fita. Har sai da ta haɗa da karɓo masa rubutun dangana ya riƙa sha kana ya fara samun kansa. Duk da cewa Inna ta ɓoye wa jama’a musabbabin cutar tasa amma makusanta sun san dalili, da yawa sun ga rashin darajar Umma sosai.
*****
Kimanin mako guda ke nan da kai Zaliha gidan Alhaji Saminu, har kawo yanzu ta ƙi sakin jiki, kullum cikin abu ɗaya take, watau kuka. Ya yi rarrashin har ya gaji.

Sati ɗayan matansa suka ba shi ya ci amarci shi da amaryarsa, sai dai ga shi satin ya ƙare amarcin ya ƙi ciyuwa. Bayan cikar mako gudan ne ya fara fita ofis.

To tun ranar da ya tara su ya yi musu jan kunne, matan nasa ba su sake yin tozali da Zaliha ba, tana can sashenta komai Alhajin ne ke kai mata. Fitarsa ke da wuya, Hajiya Lami ta nufo ɓangaren Zalihar, kai tsaye ta shiga har cikin ɗaki. Iske ta ta yi tana kuka, sai mamaki ya kama ta, “To kukan me kike yi kuma? Ke da kika zo cin daula”.

A ranta ta yi wannan maganar kafin ta matsa kusa da ita. Zaliha ta ɗago kai ta dube ta tare da tsayar da kukan take yi, ganin ta kai sa’ar Umma sai ta yi tunanin ko za ta taushe ta, ta ɗan ƙarfafa mata gwiwa. Amma sai ta ji saɓanin haka, “Yo kukan me za ki yi kuma ‘yar nan? Ba dukiya kika zaɓa ba? Don haka kuka ba ki fara komai ba tukunna, da ganin ki ba za ki rasa saurayi daidai aurenki ba, amma shi ne kika biye wa kwaɗayi da son abin duniya. Ke sai kin auri mai kuɗi ko? To za ki ci kuɗi kuma za ki ci takaicin da sai kin yi nadamar shigowa wannan gidan, da ke da dukkan kwaɗayayyun iyayen naki. Allah Ya ba ku samari waɗanda suke son ku amma kuna hange, to za ki ji kuma za ki gani, mu je zuwa.” Tana gama maganar ta juya ta fice.

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI’UN!” Cikin wani sabon kukan Zaliha ta faɗi wannan addu’a sannan ta ɗora da faɗin, “Ya Allah ka tsare ni daga sharrin wannan gida, Allah ka san abin da ba mu sani ba, ka zama gatana kai kaɗai ne ka san ciwona, ina roƙon ka ka kawo mini waraka Ya Hayyu Ya Ƙayyum!”

Tana gama addu’ar sai ta ji kukan ya ɗauke mata tamkar an yi ruwa an ɗauke, haka nan sai ta ji zuciyarta ta ɗan kwarara.

Jim kaɗan da fitar Hajiya Lami, sai ga Hajiya Sabuwa nan ita ma ta shiga da faɗin, “Amarsu ta ango, amarya ba kya laifi koda kin taɓa ɗan samu gida. Har yau ba a gama cin amarcin ba ne, bare a fito a gaisa da ‘yan gida? To mu ga mu muna zo da kanmu.” Ta ɗan tsahirta da surutan nata, Zaliha ba ta ce mata uffan ba, illa kallon ta da ta yi kawai. Ita ɗin ma kusan sa’ar Umma ce, a ranta ta ce, “In Sha Allah duk kaidinku da makircinku kanku zai tsaya, ba na nufin kowa da mugun sharri duk wanda ya nufe ni da shi Allah ka mayar masa kansa.

Walahaula Walaƙuwwata illa Billah!”

“Kin yi shiru ana magana kina jin mutane, ko haka aka faɗa miki idan kin zo kada ka yi wa waɗanda kika tarar magana? To ki saurare ni, idan kin ƙi magana, na tabbata ba za ki hana kunnenki jin abin da za a faɗa ba. Hajiya sabuwa ta zo yanzu ta fada miki yadda zaman gidan nan yake ko? Cin wannan dukiya ba ya yi yuwa cikin sauƙi, idan har kika dage sai kin ci, to ki yi shirin cin ɓangare biyu. Ki ci kuɗi kuma ki ci baƙar wahala idan ma ta zo miki da kyau ke nan, ko kuma ki ci tsagwaron wahalar.”

Shiru Zaliha ta yi tana sauraren ta, a zuciyarta kuma tana cewa, “In Sha Allahu ba zan ga wahala ba, ke dai da kike ambaton ta ke za ki gan ta da yardar Allah!”

Ta juya za ta fita ke nan sai Zaliha ta yi gyaran murya ta ce, “Na ce ba!”
Da sauri Hajiya Sabuwa ta juyo cike da mamaki ta kalle ta, kamar ta yi magana sai kuma ta ji ta gaza.

Zaliha ta ci gaba da cewa, “Abin mamaki, ke da uwar ɗakin taki kun tako takanas ta kano har nan kun faɗi maganganun da kuke buƙatar amsarsu, amma kun gaza haƙurin ‘yan ɗakikun da zan ba ku amsa. Hakan ya nuna kuna shakkar abin da zai fito daga bakina ke nan, to Alhamdu Lillahi! Allah na gode maKa da wannan baiwa da ka yi mini. Ina so ki buɗe kunnuwanki ki saurari abin da zan faɗa miki sannan ki isar wa da ita shugabar taki.”

Ta ɗan ja numfashi ta ɗora cewa, “Da ke da ita dukkanku kun haife ni, ba zan yi kishi da ku ba, ba kuma zan taɓa faɗa muku maganar rashin tarbiyya ba. Amma ku sani duk yadda kuka ma’amalance ni haka za a ma’amalanci ‘ya’yan da kuka haifa a cikinku, na tabbatar duk kalaman da kuka zo kuna yi mini babu wacce za ta so ‘yarta ta tsinci kanta a gidan mata masu irin halinku. Amma daɗin abin lamarin ba a hannunku yake ba, don haka abin da kuka shuka shi za ku girba. Sannan na ji duk kumfar bakin da kuke yi akan wannan ƙazantar ce da ba ku san ta wace hanya ya tara muku ita ba, to ku kuka damu da ita. Ni ba ta gabana, aurena da wannan mutumin umarnin mahaifiyata na bi. Da za ku yi mini alfarma ɗaya da kun sa Alhaji ya sake ni, kuma da kun cika mararsa son kishiya da ko auren ma ba za ku bari ya yi ba.”

<< Ko Wace Kwarya 9Ko Wace Kwarya 11 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×