A fusace Hajiya Sabuwa ta ce, "Lallai yarinyar nan ba ki da mutumci, tunda haka kika ce, za ki ga makircinmu. Sai kin yi nadamar faɗa mini wannan maganganun."
"Ki gafarce baiwar Allah! Ni fa ban faɗa miki wani abu na zafi ba, abubuwan da ya kamata ki sani ne, domin tafiya ba tare da ka san halin abokin tafiyar ba da wahala. Sai a yi ta samun cikas da saɓani, amma yanzu aƙalla kin fara sanin ko ni wace ce? Don haka nan gaba idan kin ji na faɗi wata magana ko na yi. . .