Skip to content
Part 12 of 16 in the Series Ko Wace Kwarya by Sadik Abubakar

Dariyar ƙeta da kisisina Hajiya Lami ta yi sannan ta ce, “Ƙarya kasa ɗan duba ya gano ranar mutuwarsa. Ni da girmana na rasa wacce zan yi wa wannan ƙetar sai yarinyar da na ɗauke ta tamkar ‘yata!”

Ta ɗan tsagaita da maganar ta matsa kusa da Zaliha ta rungume ta sannan ta ci gaba da cewa, “Ai ni wannan yarinya tamkar ni na haife ta a cikina haka nake jin ta, yaushe ne ma na shigo na ga tana kuka, rarrashin ta na yi da nasihohi. Ina nuna mata ai nan ba gidan kishi ta shigo ba, ta kwantar da hankalinta matuƙar ina gidan nan ba zan taɓa bari a musguna mata ba. Saboda haka ni ban san komai ba Alhaji.”

Ya nisa ya ce, “Ni na san da haka ai, marar son zaman lafiya da ma ita ce.”
Ya ɗan numfasa sannan ya sake mayar da akalar maganar kan Hajiya Sabuwa ya ce, “To ki saurare ni da kyau, kafin ki cutar da ‘yar mutane zan yi wa tufkar hanci. Ki je na sake ki saki ɗaya.”

Ihu haɗe da kuka ta saki, cikin sautin kukan ta riƙa cewa, “Hajiya Lami Allah Ya isa tsakanina da ke macuciya azzaluma, duk ke ce kika sani aikata wannan abin. Kuma wallahi ka yi bincike a kanta duk abin da take faɗa ƙarya ne, ko Madina ma ita ce ta fitar da ita daga gidan nan. Wannan ɗin ma kuma za ka gani.”

Cikin dariyar makirci Hajiya Lami ta ce, “A’a Alhaji bai kamata ka yanke hukunci cikin fishi ba, jan kunne ya kamata ka fara yi mata, idan har ba ta bari ba, so sai a ɗauki wannan matakin.”

“Ai wannan ɗin ma jan kunne ne, kanta rawa yake, gara ta je can gida ta yi musu rawar kan ni na gaji.”
“Haƙuri za a yi Alhaji, a bar ta ta ci albarkacin ‘ya’ya. Da girmanta bai kamata ta koma gida da sunan zawarcin saki ba. Ina roƙon ka don Allah ka janye wannan sakin, idan mai ji ce wannan sai ya zame mata izna nan gaba.”

Alhaji ya ja numfashi sannan ya ce, “To wallahi don kin sa baki ne zan ƙyale ta amma da zamanta ya ƙare a gidan nan, ba na son sakarcin banza.”

“A dai yi haƙurin Alhaji, mai haƙuri ke da nasara, na gode sosai Allah Ya ƙara girma. Mu bari mu koma. Sai ki taso mu tafi ai.”

Alhaji ya dakawa Hajiya Sabuwa tsawa da cewa, “Ki tashi ki ɓace mini da gani. Miƙewar ta yi ta bar wajen salalo-salalo.

Zaliha ta koma cikin ɗakinta tana kuka, bin ta ciki ya yi domin ya rarrashe ta. “Wallahi sai na tafi gidanmu, ni ba zan zauna a nan ba a haukata ni ko a saka mini wani ciwon da zai fi ƙarfin iyayena. Ka ƙyale ni na tafi kawai!”

Rarrashin dai ya ci gaba da yi tare da alƙawarin cewa zai ɗauki tsattsauran mataki akan lamarin, idan akwai yi yuwar ya sauya mata gida ma to zai ware ta daga cikinsu. Nan dai ya samu ta daina kukan sannan ya koma can sashen da yake, watau ɓangaren Suwaiba. Ita duk wannan hayaniya da ake ba ta sani ba, illa dai ta ji kiran da Alhajin ya kwaɗa wa uwargidan. Ba ta cika shiga sabgar da ba a kasa da ita ba.

Yau dai Hajiya Sabuwa ta ga tsantsar makircin Hajiya Lami, ta haɗa mata gadar zare ta rufta da ita. Ranta a ɓace yake, saulin abin ma duk yaran gidan ba sa nan, suna can bikin murnar zagayowar ranar haihuwa ta ‘yar maƙwabtansu.

Waje ta nema ta zauna tana tunanin yadda za ta rama wannan kunyatarwar da uwargidan ta yi mata, ta lashi takobin ba za ta bari abin ya wuce haka nan ba, sai ta ɗauki fansa ko ta halin ƙaƙa. Yadda ta sa ta ji kunya ta zubar da hawaye, to lallai ita ma sai ta ga faruwar hakan a kanta. Gabaɗaya daren nan gaza barci ta yi, tsananin baƙin ciki da takaici ne suka hana ta sakat!

To ita ma Zaliha kusan hakan ce ta kasance da ita, ba ta yi wani barcin arziki ba. Gari na wayewa ta kira Umma, lokacin kuwa Abba bai kai ga fita ba. Mamaki ne ya kama Umma na ganin kiran, domin tunda aka kai ta wannan ne kiran farko da ta yo mata, “Allah dai Ya sa lafiya.” Ta faɗa a ranta kafin ta ɗaga wayar.

“Ina kwana Umma?” Zaliha ta faɗa cikin rarraunar murya.

“Wa alaikums salam.” Umma ta amsa.
Bayan sun gama gaisawar, sai ta gaza yin ƙorafin da ke ranta, “Ina Abba, ko ya fita ne?”

“A’a, bai fita ba tukunna, bari a ba shi.”
Miƙa masa wayar ta yi, ya kara a kunne tare da cewa, “Assalama Alaikum!”

Wani irin sanyi Zaliha ta ji ya ratsa mata zuciya, ta amsa, “Wa alaikums salam! Abba ina kwana?”

“Lafiya ƙalau Zaliha, ya kwanan gidan?”

“Alhamdulillah Abba! Ya ya aiki?”
“Aiki mun gode Allah!”

Shiru ta yi Abba ci gaba da tambayar, “Lafiya dai babu wata matsala ko?”
Kamar ta faɗa masa abin da ke ranta, amma sai ta ji shi ma ba za a ta iya faɗa masa ba, “Ba komai Abba.”

“To madalla! Allah Ya yi miki albarka.”
“Amin Abba!”

Ya miƙa wa Umma wayar, ta karɓa da cewa babu wata damuwa ko?”

“E.” Ta amsa a gajarce cike da jin haushinta.

“To shike nan nan ki gai da maigidan. Sai an kwana biyu zan zo ai.”

Zaliha ba ta yi wani farinciki da albishir ɗin zuwan ba, domin ta san zuwan ba na komai ba ne face don ta ƙara wa jakarta nauyi. “Koda ma a ce na faɗa mata matsalar ba fahimta za ta yi ba, ƙarshe ta zama kamar waɗannan mararsa imanin, ta ce bari ita ma ta je wajen bokan ta karɓo mini maganin tsarin jiki.” A ranta ta yi wannan maganar.

Ta ci gaba da saƙe-saƙenta, zuwa can sai ta yanke shawarar kiran wata ƙanwar Umman ana kiran ta Anty Maryam. Ita ce ‘yar auta a ɗakinsu.
Cikin sa’a bugu ɗaya ta shiga, ta ɗaga da sallama, “Assalama Alaikum! Amare manyan gari.”

Cikin murmushin jin kunya ta ce, “Anty ina kwana?”

“Lafiya ƙalau, ya kike ya gidan?”
“Lafiya ƙalau!”

“To Ma Sha Allah! Ya ya abokan zaman naki? Da fatan dai babu matsala ko?”
Ƙwalla ta ciko maƙil a idonta, dandanan muryarta ta sauya zuwa yanayin kuka, ta ƙwarara ta da kyar ta ce, “Anty don Allah ki tambayi Abban Ilham, gobe ki zo.”

“Akwai damuwa ke nan, me ke faruwa? Ke da shi ne ko kuwa?”
Kukan da take tattalin kada ya bayyana ya kufce mata, cikin kukan ta ce, “Anty kawai ki zo don Allah ke kaɗai ce za ki fahimce ni…” Kukan ya ci ƙarfinta alatilas ta yi shiru.

Hankalin Anty Maryam ya tashi matuƙa, cikin ƙarfafa muryar gwiwa ta ce, “Daina kukan kin ji, In Sha Allah zan zo. Yanzu ma abin da ya sa aikin kwana ya yi har yanzu bai dawo ba, amma ina tafe goben ki kwantar da hankalinki kuma ki ci gaba da addu’a.”

Rarrashin ta ta yi sosai kafin ta kashe wayar. Hakan ya ɗan sanyaya mata zuciya, ba shakka tana da yakinin Anty Maryam ɗin za ta taimaka mata fiye da Umma.

Washegari da wurwuri Anty Maryam ta shirya ta diro gidan, kai tsaye ta wuce sashen Zaliha. Iske ta ta yi tana zaune a falo ta yi jugun. Sallamar Antyn ta ji, ta miƙe da sauri cike da murna ta rungume ta kafin ta ƙarasa isowa tana faɗin, “Sannu da zuwa Anty!”

Suka suka ƙarasa ta sake ta nufi kicin ta dauko abincin da yi don ƙarin safe amma ta gaza ci, ta haɗo da lemo ta kawo ta ajiye.

“SubhanAllah! Me ke damun ki haka duk kin zuge cikin ‘yan kwanaki ƙalilan?” Anty Maryam ta faɗa bayan ta ƙare mata kallo, cikin alhinin damuwa take maganar. Zaliha ta kwantar da kanta akan cinyar Anty Maryam, hawaye tuni sun fara ambaliya daga idanuwanta.

“Anty tunda kuka kawo ni gidan ban ga ranar da za ta fito ta koma ga Mahaliccinta ba face na zubar da hawaye ba adadi, kullum rayuwata cikin baraza take ƙara shiga. Gori suke yi mini wai na zo cin dukiya, to zan ci kuma zan ci wahala. Manyan matansa biyu sun sha alwashin babu wacce za ta zauna lafiya matuƙar suna nan.”

Ta ɗan dakata sannan ta ɗora da cewa, “Yanzu jiya da Magariba Allah Ya tona asirinsu, Ya kare ni daga wani mugun abu da suka shirya mini. Na leƙo zan kulle ƙofata na ga matarsa ta biyun tana zuba mini magani a wajen da zan taka, da na gan ta shi ne ta rikice tana sambatu wai uwargidan ce ta ce ta zuba mini. Ana cikin hakan sai ya zo, daga ƙarshe dai ta sake ta, amma uwargidan ta kafe sai da ya mayar da ita. Wallahi Anty bakinsu ɗaya, ba ki ga wulaƙancin da suke yi mini ba. Ta ukun ce kawai take da kirki, ita ma haka suke azbatar da ita har ‘ya’yanta. Don Allah ki taimaka mini, na rabu da wannan gidan kafin su illata ni.” Ta ƙarasa maganar da shasshekar kuka mai taɓa zuciya.

Anty Maryam ta jinjina kai tare da cizon leɓe ta ce, “Ki daina kuka, na lura yaya Saratu ta fifita dukiya sama da farincikinki. Tun lokacin da na ji an ce mutumin mata ne da shi har uku, na ji ban gamsu da abin ba. Kuma ta ɓoye mana abubuwa da yawa game da shi saboda ta san ba ta taki gaskiya ba. To idan ita ta gaji da ke, mu muna son ki kuma ba za mu zauna mu zuba mata ido don taƙamar ita haife ki ba, ta kai ki wajen da za a sabauta miki rayuwa saboda biyan buƙatarta. Sam wannan ba gidan zamanki ba ne, In Sha Allah za a san yadda za a yi. Kodai ya ware miki gidanki can wata unguwar daban ko kuma ya san abin yi.”

“Anty don Allah ni ba na son sa ma wallahi!”

Shiru suka yi cikin yanayin damuwa kimanin mintuna biyu, Anty Maryam ɗin ta katse shirun ta faɗin, “Ni na yi mamakin yadda abin ya taso gadan-gadan lokaci ɗaya kuma aka daina maganar Abdullahi.”

“Wallahi duk Umma ce, ba ki ga ma irin cin fuskar da ta yi masa ba.”
Cike da mamaki ta ce, “Ikon Allah! To wai ni me ya samu yaya ne? Yanzu yaron nan ko bai ci darajar komai ba, ai ya ci ta ɗawainiyar karatunki da yake ba dare ba raba tun ba ki san kanki ba, wani abin ma sai ya hana kanwarsa ya yi miki. Amma shi ne za ta rufe ido? Shin arziki ba na Allah ba ne? Ba ka rena mutum domin ba ka san ya ya gobensa za ta kasance ba. Ki yi haƙuri indai har da rabon zama tsakaninku sai kun zauna.”

“Wallahi Anty abin da Umma ta yi akan auren nan ta saɓa wa Allah sosai, har wajen boka fa ta je karɓo maganin da za ta raba ni da yaya Abdul.”

Anty Maryam ta zaro idanu haɗe da yin salati, “INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI’UN! Wai ni duk yaushe yaya ta sauya haka ban sani ba? Babu shakka ba da tunaninta kawai take aiki ba. To shi Abban naki duk bai san wainar da ake toyawa ba ne? Kuma me ya sa tun a wancan lokacin ba ki faɗa mini ba?”

“Shi Abba ya san wani abin kuma ya yi faɗa amma ta ƙi ji, ta ƙi fahimtar sa, ni kuma ta ja kunnena akan lallai kada na sake na faɗa wa kowa, idan ba haka ba sai ta saɓa mini.”

“To shike nan, bar ta daga nan wajenta zan nufa, ba za ta cutar da ke ba. Ba a bori da sanyin jiki. Na san ba ki da wasa wajen kula da Ibada, ki ci gaba da addu’a da karatun Ƙur’ani. Duk lokacin da za ki fita can ki yi addu’a, Allah zai tsare ki daga dukkan cutarwarsu. Su boka ne gatansu, ke kuma kina Allah wanda ran bokan yake hannunSa.”

“To shike nan Anty na gode! Ga abinci nan.”

“A’a na ƙoshi! Hala ma ba ki karya ba ko?”

Ta yi murmushi tare da sunkuyar da kai ba ta ce komai ba. Anty Maryam ta ce, “To maza ki ɗauka ki ci, ki daina zama da yunwa. Ina ba ki tabbacin zan yi duk mai yi yuwa na ga kin fita daga wannan kuncin rayuwar.”

Nan dai ta tsare ta sai da ta ci abincin sosai, tana mata ‘yan nasihohin kwantar da hankali. Daga ƙarshe ta ce, “Bari na tafi sai zuwa jibi zan sake dawowa.”

“To Anty na gode sosai Allah Ya saka da alkairi, ki gai da gida, ki gai da mini da Ilham.”

Tana fitowa ba ta zame ko’ina ba sai wajen Umma kamar yadda ta yi niyya, fuskarta a murtike babu fara’a ta shiga da sallama. Umman na tsakar gida ta amsa mata da, “Maraba da baƙin hantsi, daga ina haka? Shiga mu je.”
“A’a ba sai na shiga ba, bar ni daga wajen ma.”

“Ban gane daga waje ba? Ina za ki? Sauri kike ne?”

“Babu inda za ni nan na zo kuma ba sauri nake ba.”

“To fa! Ikon Allah! Ya na ga ranki a ɓace? Ina fatan dai lafiya?”

Anty Maryam ta yi ajiyar zuciya sannan ta ce, “Yaya mene ne ribar abin da kika yi yanzu? Kin ɗauki ‘yar fulillikar yarinya ƙarama kin jefa ta cikin miyagun kuraye azzalumai, suna yunƙurin haukatar da ita ko ma su fantsama ta uwa duniya ke kina nan hankalinki kwance babu abin da ya dame ki. Idan kin gaji da ita ne, ai mu ba mu gaji da ita ba, mu ma muna da hakki a kanta sai ki bar mana ita, mu nema mata farincikin da take nema.”
Murmushi Umma ta yi tare da faɗin, “Magana kike mini a baibai, fito fili ki faɗa mini me ke faruwa?”

“Babu wata magana da zan faɗa miki da ba ki sani ba, tunda kin shirya komai don biyan buƙatarki. Ba ki duba halin da za ta shiga ba, shin TA ZAMA HAJA ne? Haba yaya! To gaskiya abin da na ji ba zan iya barin ‘yata a wannan hali ba matuƙar ina raye.

Gabaɗaya babu wanda yake son abin sai ke, ke ɗin ma don ki karɓi kuɗinsa ne kika tilasta mata ba don ranta yana so ba. Ko a da ba a yi auren dole an ga da kyau ba bare yanzu. Baya ga haka a ɗauki yarinya an kai cikin mushirikan mata, wanda sun yi jika da ita ba ma ‘ya ba, babu wacce ba ta girme ni ba a cikinsu.”

Ta ɗan tsahirta sannan ta ɗora da cewa, “Jiya da safe ta kira ni take faɗa mini abin cutarwar da suka shirya mata, Allah Ya kuɓutar da ita. Don haka tunda Ubangiji Ya nuna mana, to dole mu san abin yi, mu janye ta daga cutarwarsu.”

“To yanzu na fahinta, watau ƙara ta ta kai wajenki ke nan! Ba ki san Zaliha ba ne, duk abin da za ta faɗa miki yanzu ƙarya ne. Wancan yaron ne yake ci gaba da hure mata kunne, shi ya sa za ta riƙa bijiro da abubuwa kala-kala. Kin manta da kawai iskancinta ne, za ta yi ta bari.”

<< Ko Wace Kwarya 11Ko Wace Kwarya 13 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.