Cikin sigar mamaki ta ce, "Yaya kin ga halin da take ciki kuwa? Yanzun nan fa daga wajenta nata nake, yarinya ta rame ta lalace ta firgice duk ta sauya kamar ba ita ba, ana aure a samu kwanciyar hankali, yaro ya murje ya gyagije amma ita sai dai akasin haka. To ina amfanin auren ke nan? Kuma na tambaye ta sarai ta ce ita ba ta son sa ko kaɗan biyayya ta yi akan tilastawar da kika yi mata. To idan so kike sai an kawo miki ita a gadon asibiti ciwon zuciya ya kama ta ko kuma. . .