Daren nan gabaɗaya ba ta rintsa ba, gari na wayewa ta kira Anty Maryam ta ce, don Allah ta zo yanzu-yanzu.
Nan da nan Anty Maryam ta zari hijabi ta saka, da ma ta gama shiri za ta kai Ilham maƙaranta. Tana ajiye ta, sai ta nufi gidan hankalinta a tashe, ko gaisuwa ba su tsaya ba, ta tambaya lafiya? Zaliha ta kwashe duk abin da ya faru ta faɗa mata, har da yadda suka fara magana da Anas ɗin, babu abin da ta ɓoye mata, daga ƙarshe ta ce, “bari na kira su Suwaiba ki ji daga bakinsu.”
Tana miƙewa sai ga Alhajin nan ya shigo, “me kuma kike yi a gidan nan har yanzu? Wallahi ba don na ga mahaifinki marar son hayaniya ba ne da har ke zan sa a adana mini, munafuka ki riƙa wani simi-simi da ke kamar ta Allah.”
“Duk abin da za ka faɗa a kaina ka faɗa, ni dai ba zan furta wata kalmar rashin ɗa’a da, domin ka yi sa’an mahaifina. Saboda haka ko ba ka ci albarkacin komai ba ka ci na furfura, kuma daɗin abin dai ba a titi aka tsinto ni ba, ka fi kowa sanin hakan. Sannan ina son ka ba ni shaidar cewa ka rabu da ni kamar yadda shari’a ta tsara.”
A gaban Anty Maryam suka yi wannan musayar yawun, ranta ya yi matuƙar ɓaci. Yadda bai ji kunyarta ba ita ma sai ta mayar masa da fusataccen martani kamar haka, “malam kada ka sake siffanta ta munafuka, ga munafukai nan ka tara gindima-gindima a gida. Kai da ma banda ƙaddarar ina kai ina wannan yarinyar!”
Nan da nan waje ya cuɗe kowa ya fito, daga ƙarshe Anty Maryam ta ja hannun Zaliha suka fice. Gidanta suka nufa kai tsaye, nan ta shiga tausar Zalihar da fararen kalmomi da cewa, ta kwantar da hankalinta, kada ta ji tsoron komai. Ita za ta gyara duk lamarin, za ta samu Umma su yi magana ta fahimta tukunna.
Dare ya yi mijin Anty Maryam ya dawo ya ga Zaliha yake tambayar me ya faru? Anty Maryam ta zayyane masa komai, ya nuna rashin jin daɗi tare da fatan Allah Ya sa haka ne ya fi alkairi.
Kwanan Zaliha biyu a gidan, a rana ta biyun ne da dare ta tisa ƙeyarta suka taho gidansu. Cikin dace kuwa Abba na nan, sallama suka yi suka shiga. Bayan an gaisa a gaggauce Umma ta ɗora da tambayar, “Lafiya na gan ku tare?”
Anty Maryam ta mayar da kallon ta ga Abba, cike da nutsuwa ta ce, “Watau duk wani abu tsararre ne a wajen Ubangiji, Ya riga Ya gama tsara wa bayinSa komai da zai faru da su tun gabanin ƙirƙirar duniyar da bayin ke rayuwa a cikinta. Bawa bai isa ya sauya ko kuma ya ƙetare ƙaddararsa ba.”
Sai da ta gama tattaro duk wasu zantuka da ke sa zuciya ta yarda ta aminta da Allah ne Mai sarrafa al’amura sannan ta ce, “Allah Ya kawo ƙarshen zaman Zaliha da mijinta.”
Ta juya ga Umma ta labarta mata duk abin da Zaliha ta fuskanta wanda ya yi sanadiyar mutuwar auren. Jikinta ya yi sanyi sosai, a yanzu har tausayin Zalihar ne ya fara kama ta, cewa ta yi, “To Allah Ya sa haka ne ya fi alkairi.”
Anty Maryam ta ji daɗin yadda ta fahimci maganar ba tare da an kai ruwa rana da ita ba. Daga ƙarshe ta roƙe su da su bar Zaliha a wajenta tukunna.
Washegari da safe Umma ta kira Alhaji Saminu, yana ji yana kallo wayar ta yi ruri har ta yanke bai amsa ba. Ta sake kira a karo na biyu, nan ma dai bai amsa. Ba ta gajiya ba ta sake jarabawa, sai ya ɗaga murya a cunkushe ya ce, “Salama alaikun!”
Ta amsa masa, “Wa alaikums salam! Ashe haka abu ya faru? Ka san sha’anin ƙuruciya ta ɗan yau, ka haife shi ne amma ba ka haifi halinsa ba. Sai an riƙa haƙuri ana kauda kai.”
Kafin ta gama rufe bakinta ya ce, “Ai haƙurin na yi yanzu, na kauda kan ne shi yasa na sallame ta. Da ma cuta ta kika yi, kin san yarinyarki lalatacciya ce shi ne kika yaudare ni, to na bar ki da Allah!”
Yana faɗa ya kashe wayar. Ji ta yi kamar ya watsa mata garwashin wuta a zuciya, nan take hau huci tana jin haushin kanta haɗe da nadamar abubuwan da suka faru. Takaici goma da ashirin, ga abin da take hange bai samu ba, ga yarinya ta zama ƙaramar bazawara. “Na shiga uku ni Saratu! Ya Allah na tuba ka yafe mini duk laifukan da na yi maka. Kaicona! Na yi nadamar mayar da kyautar da ka yi mini hajata ta samun abin duniya, na fifita buƙatata akan kwanciyar hankalinta. Allah ka karkato da hankalin yaron can kanta, da ma shi ne mijinta amma sai da na san yadda na yi na raba su. Yanzu da wane idon zan kalli mahaifiyarsa?” Tunanin da ya game zuciyarta ke nan ta gaza samun sukuni.
Bayan kwana biyu ta wanki ƙafa ta nufi gidan Anty Maryam domin su tattauna yadda za ta ba wa Inna haƙuri. Anty Maryam ɗin ce kawai za ta iya lalubo yadda za a warware bakin zaren. Da isa gidan bayan an yi gaishe-gaishe, ta dubi Zaliha ta ce, “Zaliha na cutar da ke, na cutar da rayuwarki akan dauɗar duniya. Ki yafe mini.”
Ƙwalla ce ta ciko sosai a idon Zaliha, kwantar da kanta ta yi a kan cinyar uwar cikin rarraunar murya take faɗin, “Umma ki daina faɗar haka, ba ki cutar da ni ba ko kaɗan. Ai uwa ba ta taɓa cutar da ɗanta, abin da ya faru ƙaddarata ce, ba laifinki ba ne. Allah za mu yi wa godiya da Ya jarrabe mu da wannan jarabawa kuma In Sha Allah mun ci ta!”
“Alhamdulillah! Allah Kai ne abin godiya, Allah Ya ƙara mana rufin asiri da fahimtar juna.” Anty Maryam ce ta furzo wannan maganar cikin fara’a da sakin fuska.
Umma ta ce, “Na yi wa Abdullahi cin mutuncin da ba na jin zai sake kallon Zaliha, na rasa da wane idon zan kalli mahaifiyarsa?”
Anty Maryam ta ce, “Babu shakka ransu ya ɓaci matuƙa, amma yanzu ki bar komai a hannuna In Sha Allah zan gyara lamarin. Dalilin da yasa ma na ce ki bar mini ita ke nan a wajena, amma yanzu ba za mu yi magana ba sai bayan ta yi idda, zan kira shi kafin lokacin. Sannan Inna mai fahimta ce, tana da sauƙin kai in dai ba shi ba ne ya ce ya haƙura to ita ba za ta ƙi amincewa ba.”
“To shike nan, Allah Ya sa.”
Yini suka yi a gidan suna ta hira gwanin ban sha’awa, sai yammaci Zaliha ta rako Umma ta har titi ta tafi gida.
*****
Magana ba ta ɓuya in ji masu iya zance, tun kafin cikar Zaliha kwanaki bakwai da barin gidan Alhaji Saminu, maganar ta fantsama gari. Labari ya iske kunnuwan su Inna. Masu tsegumi sai yi suke, wasu na cewa ai alhakin yaya Abdul ma ba zai bar auren ya yi ƙarko ba. Wasu kuwa na ganin da ma ai ƙarshen alewa ƙasa, kowa dai da irin albarkacin bakin da ya tofa.
Ita kuwa Inna ba ta ce wani abu, illa nuna alhinin mutuwar auren. Jamila ce ta riƙa cewa, “Allah Ya ƙara, da ma tunda suka zalinci yaya Abdul sai Allah Ya saka masa.”
Kwaɓar ta Inna ta yi da cewa, “Bai kamata ki riƙa yin haka ba, idan mutum ya jefe ka da dutse, kai ka jefe shi da gayan fura. Sai Allah Ya ganar da shi kuskurensa, ya ji kunya ya gyara.”
Shi ma gogan (Yaya Abdul) bai nuna farincikinsa a fili dangane da mutuwar auren ba, amma cikin zuciyarsa maƙare take da murna, domin ya fara jiyo ƙamshin sahibar tasa za ta dawo masa. A ransa yake cewa, ai lallai addu’arsa ce ta karɓu abin ya zo ta wannan fuskar.” Sai dai ya tabbata ba zai yi tozali da ita ba, sai ta gama Idda.
Ƙalubale ɗaya da yake tinkara shi ne yadda zai koma mata, yana tsoron kada Inna ta ce ba shi da zuciya. Har ya manta cin mutuncin da aka yi masa. An aurar da ita ga mai kuɗi, sai yanzu kuma da ya sake ta ta zama bazawara shi zai aura? Wannan ita ce damuwarsa a yanzu.
Duk abin da ya faru ya wuce shi a wajensa ba wai ransa ba ne bai ɓaci ba ko rashin zuciya, amma tunda an yi walƙiya, kowa maitarsa ta fito fili. Ita Umma ta gane ashe ba kowacce dukiya ba ce take zama farinciki ga mutum ba, wani mai dukiyar da za a karɓe ta a saka masa farinciki a ransa da gudu zai rabu da kuɗin. Don haka wataƙila za ta sauya ra’ayinta ta gane kowanne bawa da irin arzikin da Allah Ya ba shi.
Bayan Sati Biyo.
Bayan sati biyu, Anty Maryam ta shirya ta yo wa gidan su yaya Abdul tsinke, daga Inna sai Jamila ta iske, shi ba ya nan. Bayan sun gaisa, Inna ta jajanta mata da cewa, “Ashe Zaliha kuma haka abu ya faru? To Ubangiji Allah Ya kiyaye gaba, Allah Ya rufa asiri.”
Cike da murmushin kunya Anty Maryam ta ce, “Amin Ya Allah! Da ma na ɗan jima ina son na zo, abin ne dai sai a hankali, uzuri yawa yake yi.”
“Allah Sarki! Ai kam fitar sai an rufe ido.” Inna ta faɗa.
Shiru suka yi ‘yan daƙiƙu, Anty Maryam ta nisa da cewa, “Abubuwa da dama sun faru a baya, idan har na ce ban sani ba to ƙarya nake yi. Inna ke babba ce, don Allah ina son mu yafi juna, komai ya wuce. An ɓata muku matuƙa; an yi muku butulci. Amma ku yi haƙuri, a ɗauki hakan a matsayin kuskuren da makamancinsa ma ba zai sake faruwa ba, al’amarin ne ya zama na ƙaddara. Duk ya mutum ya so ya hana bai isa ba, mu kanmu ba ta daɗin ranmu yaran suka farraƙu ba, ƙaddararsu ce ta zo a haka. Ina mai bayar da haƙuri a madadin kowa daga iyayen Zaliha, wacce ta hassasa abin ta nuna nadamarta.”
Inna ta ja numfashi tare da gyara zama sannan ta ce, “To Alhamdu Lillah! Da ma haka ake da buƙatar bawa ya kasance, idan ya aikata kuskure to sai ya tuba ya gyara. Mu kam dai duk abin da ya faru ta ɓangarenmu ya wuce tun a lokacin, mun manta da shi. Allah Ya yafe mana gabaɗaya. Sai dai ni yanzu ba ni da ta cewa game da batun za su ci gaba da tarayya ko akasin haka, idan bai sauya ra’ayinsa ba to falillahil hamdihi. Ba na tilastawa yaro akan ya bi abin da ransa ba ya so, idan ya zo mini da abin da yake so; dubawa nake idan akwai matsala sai na nusar da shi ta cikin hikima ba tare da da tashin hankali ba. Idan har Allah Ya ƙaddara matarsa ce, ni zan fi kowa farinciki domin abin da yake so ke nan, ina da yaƙinin ba zai ba ni kunya ba, za su yi zaman lafiya.”
Cikin risinawa Anty Maryam ta ce, “To shike nan ba komai, Allah Ya tabbatar mana da alkairi. Na gode sosai Allah Ya ƙara girma da arziki.”
Nan suka yi sallama ta miƙe ta fito. Tunda suka fara tattaunawar Jamila sai yatsina fuska take, ita kam sam ba ta bukatar wannan sulhun, ba ta maraba da shi, don haka Anty Maryam na fita ta dubi Inna ta ce, “Cabɗijan! Lallai waɗannan mutanen ba su da tunani, ai wallahi yaya Abdul ya fi ƙarfin ya auri bazawara. Sai da suka zaɓi mai kuɗin sun ga ba su samu ba za su dawo wajen talaka?”
“Ke Jamila ba na son iyashege da shiga cikin abin da ba a kasa da ke ba, idan yana son ta sai a hana shi? Kuma tunda har suka karya bullensu suka nemi afuwa sai a yi musu. Babu wanda ya san me Ubangiji Ya ɓoye a tsakaninsu, yanzu ita Saratun da ta yi uwa ta yi makarɓiya ta hana, ai ga ishara nan tun ba a je ko’ina ba. Sannan abin da za ki duba ba da son yarinyar aka yi auren ba, ba ita ce ta ƙi shi ba; don haka ki yi musu fatan alkairi kawai.”
“To Inna yanzu ya ya batun Aisha ke nan?”
“Yo ya ma saurare ni ne,? Ba ki ga ya ƙi kama zancen ba bare har a sa rai. Shi ya sa ban zurfafa ba akan maganar, ganin yadda hankalinsa bai bar kan Zaliha ba.”
Ita dai Jamila ba ta ji daɗin wannan komayyar ba, da za a bi ra’ayinta da Inna ba ta amsa musu ba. Tunda suka rufe idanu a baya, suka nuna ƙyamarsu ga yaya Abdul ɗin saboda sun samu mai dattin aljihu, don haka yanzu abin nasu ya zama rashin ta ido ke nan.
Da yammaci Inna take sanar da yaya Abdul cewa, Anty Maryam ta zo ta ba da haƙuri tare da neman yafiya. Bai yi mamaki da jin wacce ta zo ɗin ba, kasancewar halinta da na Umma akwai bambanci mai yawa. Ya san tana da fahimta; mai halin dattako ce. Farinciki ya yi sannan ya ce, “Allah Ya yafe mana gabaɗaya.”
Inna ta ce, “Ni yanzu tausayin yarinyar ne ma yake kama ni.”
Ya yi shiru yana murmushi bai ce komai ba.
Ta ci gaba da cewa, “Abin da nake so da kai shi ne, ni ba zan hana ka sake komawa wajenta ba, idan har kana son ta to addu’a zan ci gaba da yi maka. Kuma na tabbata yanzu uwar ta gane kuɗi ba su ne farinciki ba. A cewar ‘yar uwar tata ta yi nadama sosai kuma ta ce a ba ka haƙuri.”
Murmushin ne dai yalwace a fuskarsa bai iya furta komai ba. Inna ta ƙarasa da faɗin, “Idan ta kammala iddarta sai ka je ku gaisa.”
Ya ƙara sakin wani murmushin tare da sunkuyar da kai.
***
To a ɓangaren Anty Maryam ɗin ta ji daɗin yadda Inna ta nuna fahimta, amma duk da haka hankalinta bai kwanta sosai ba, tana buƙatar ta yi magana da yaya Abdul. Don haka bayan sati ɗaya da zuwanta gidansu sai ta kira shi a waya a safiyar ranar Juma’a. Dayake ba shi da lambarta, da kamar ba zai amsa ba, amma sai ya ɗaga da sallama. Ta amsa masa, jin muryar babba ce ya sa ya zarce da gaisuwa, “In kwana ya gida ya yara?”
“Lafiya ƙalau wallahi, ya aiki ya su Inna? Ai ranar nan na zo gidan ba ka nan.”
Sai yanzu ya gane ta; ya ƙara risinawa tamkar a gabanta yake, “Anty ce ke nan, ya ya Ilham?”
“Tana nan ƙalau tana makaranta.”
Shiru suka yi na ɗan takaitaccen lokaci, zuwa can ta katse shirun da cewa, “Idan kana da lokaci yau ko gobe ina son ganin ka.”
Gabansa ne ya faɗi, shin farinciki ne ya sa shi hakan ko kuwa? “To Anty ba damuwa zan zo yau da yamma In Sha Allah!”
A hankali sai ya ji yana tsintar kansa cikin wani daddaɗan yanayi wanda rabon sa da kasancewa a ciki tun kafin Alhaji Saminu ya yi kutse cikin rayuwarsu. Saboda haka tun da safen ya kulla niyya zuwa gidan nata.