Misalin ƙarfe biyar na yammaci, bayan la’asar sakaliya, Zaliha ta faɗa kicin domin ta girka musu abincin dare.
Da ma haka suka tsara aikace-aikacen gidan, watau girkin safe da na rana Umma ke yi, yayin da ita kuma ke kula da na dare. Kamar yadda ta ambata tuwon shinkafar ta yi da miyar kuɓewa ɗanya, wacce ta ji kayan ɗanɗano da busasshen kifin banda. Tana gamawa ta shiga bayi ta sulla wankanta gwanin sha’awa.
Umma na can ɗakinta tana wani abin, jira take yi Zalihar ta gama girkin ta san dabarar da za ta yi ta zuba mata garin maganin a ruwan wanka.
Kiran ta ta yi domin ta ji kusa gamawar? Me idonta zai yi tozali da shi idan ba yarinya ba cikin ɗaurin ƙirji da tsalli-tsallin ruwan wanka a jikinta. Wani sabon mamaki haɗe da turnuƙun baƙin ciki ya sake taso wa Umma lokaci guda, mazewa ta yi ta ce, “A’a me zan gani haka? Yanzu ba ki gama aikin ba kika shiga wanka?”
Dariya ta yi ta ce,”Umma ke nan, ai tuni na gama komai, shi ne na yi wankana da wuri.”
“Shi ke nan, da ma na ji shiru ne ba motsin shi ne na kira ki, ashe wanka kika shiga.”
Murmushi ta yi ta fito zuwa ɗakinta ta zauna gaban madubi ta fara kwalliya, ba wata doguwar kwalliya ta yi ba, irin kadaran kadahan din nan ce, saboda zafin da ake yi. Amma fa duk da haka ba ƙaramin kyau ta yi, domin ita yarinyar ko babu kwalliya a fuskarta kyanta bayyana yake. Irin kyawawan yaran nan ne ajin farko. Baƙa ce amma ba can ba, ba ta shiga kanti ba, tana alfahari da baƙinta. Hoda mai karɓar fatarta take shafawa kawai.
Takaici da baƙin ciki suka sake turnuƙe Umma, “Wannan wace irin ‘ya ce haka? Anya kuwa maganin nan zai yi aiki a jikinta? Ta wace hanya zan ɓullo mata ne?” A ranta take waɗannan tambayoyin, ta jima sosai tana tunani har aka kira sallar Magariba, wanda hakan ne ya tilasata mata miƙewa ƙafafunta a nauyaye ta nufi bayi ta kama ruwa sannan ta yi alwala.
Ita kuwa Zaliha zamanta ta yi a falo kasancewar tana cikin kwanakin fashin sallar.
Misalin ƙarfe takwas da ‘yan mintuna, yaya Abdul ya iso ƙofar gidansu a bisa mashin dinsa ƙirar Lifan. Wayarta ya kira, dayake da ma abin da take tsammanin ke nan, farinciki ne da nishaɗi suka bayyana ƙarara a fuskarta.
Ɗaga wayar ta yi tare da karawa a bangaren kunnenta na dama, “Amincin Allah Ya tabbata a gare ki gimbiya sarautar mata!”
“Tare da kai!” Ta faɗa cikin yalwataccen murmushin da ya sanya dukkan nutsuwa a jikinta.
“Ina ƙofar gida.” Yaya Abdul ya faɗa yana faɗaɗa fara’arsa tamkar tana kallon sa.
“Ayya ga shi kuma ba na nan!” Cikin sigar zolaya ta faɗi wannan maganar. Kasancewar ta faɗa masa duk lokacin da ya zo kada ya sake tsayawa, ya shiga kawai tunda gidan ba baƙonsa ba ne.
Murmushi mai ɗan sauti ya yi tare da cewa, “To ba komai, bari na jira ki ko?”
“A ina za ka jira ni? Ba na gari fa! Na yi tafiya ne, kawai ka koma sai wani lokacin.” Ta ƙarasa maganar da dariya.
Dariyar shi ma ya yi tare da cewa, “Ba ki da dama wallahi! Da ma mutum ya taɓa yin tafiya ba tare da izinin yayansa ba?”
Cikin muryar shugaɓa ta ce, “Yaya Abdul na faɗa maka fa tun ba yau ba idan ka zo ka riƙa shigowa, kunyar ce ba ka daina ji ba?”
Cikin lallausan murmushi ya ce, “Ai neman izini kafin mutum ya shiga gidan mutane wajibi ne.”
“To ai ba gidan wasu ba ne, gidanku ne. Ni daga yau kawai idan ka zo ka riƙa shigowa.”
Ta kashe wayar tare da miƙewa ta nufo wajen Umma da ke zaune a falo, sai ta ji wata ‘yar fargaba ta kama ta ganin yadda ta ƙara matsin lamba akan yaya Abdul ɗin. Haka nan ta daure cikin kalar tausayi da sanyin murya ta ce, “Umma yaya Abdul ne ya zo.”
Shiru ta yi ta murtike fuska ba tare da ta kalle ta ba. Ta ci gaba da cewa, “Umma don Allah ki yi haƙuri da maganar Alhaji Saminu, ki ba wa yaya Abdul dama. Ya fi kowa sanin ƙimata da darajata. Umma Alhaji Saminu fa matansa uku ni a ta huɗu zan je kuma duk ba sa’annina ba ne.” A yanayin kalar tausayi matuƙa take maganar, amma ko gizau Umma ba ta yi ba, illa ma wani mugun haushinta da take ji.
Matsawa Zalihar ta ƙara yi kusa da ita ta durƙusa tare da kwantar da kanta bisa gwiwoyinta ta ce, “Ba na son na kasance cikin jerin yaran da ke nuna rashin biyayya ga zaɓin iyayensu, zan iya yarda na auri Alhaji Saminu. Amma akwai abin da zai riƙa bibiyar mu wanda hatta al’umma sai sun yi mana hukuncin da rashin adalci ga yaya Abdul. Umma yaya Abdul ba shi da matsala, a unguwar nan ba ni kaɗai ba ce yarinya a makarantar da yake koyarwa, amma ya zaɓe ni yake ba ni kulawa ta musamman.” Kuka ne yake neman suɓuce mata, alatilas ta gimtse bakinta ta yi gum.
“Ki yi kukan mana, ko ba kuka ba? Kin daɗe ba ki daina ba. Ki buɗe kunnuwanki ki saurare ni, idan har kina son ki ci gaba da ganin fara’ata, na ba ki watanni biyu ki cire wannan yaron daga ranki kuma ki saurari Alhaji Saminu sosai. Mutane da kike iƙirarin za su yi mana hukunci, ina ruwanki da su? A wannan zamanin idan har za ki tsaya duba me jama’a za su faɗa a kanki sannan ki yi ko ki ƙi yi, to babu abin da za ki taɓa yi a yaba miki. Kuma idan kika auri wancan ɗin kika shiga wahala babu wanda zai fara farinciki sama da su ɗin, mutum ba shi da gadonka amma yana da gadon maganarka.”
Shiru suka yi kowannesu yana ɗanɗanar ƙunar zuci, zuwa can Umma ta katse shirun da cewa, “Ki tashi ki san yadda za ki yi da shi, kin dai ji wa’adin da na ba ki.”
Miƙewa suka yi tare, Umma ta nufi ɗakinta ita kuma ta kira shi ya shigo. Kafin ya iso ta daidaita yanayinta amma ba kamar da ba. A falo suka zauna kamar yadda suka saba, gaishe shi ta sake yi cikin tsananin kunya da girmamawa.
“Ina Umma?” Ya tambaya.
Ce masa ta yi, “Tana na ɗaki, da ta yi sallah ta kwanta. Wataƙila ma ta yi barci.”
“To Ma Sha Allah! Abba kuma na san bai dawo ba, sai anjima ƙila kafin na tafi ya dawo.”
Murmushi kawai ta saki ba ta ce komai ba, shiru suka yi kinamin mintuna biyu. Can ta nisa da cewa, “Ya ya su Inna da Jamila?”
“Suna nan lafiya kalau. Inna fishi take da ke, ta ce kin yi mata yaji ba laifin tsaye bare na zaune.”
Dariya ta yi ta ce, “Ai kullum ina cewa Jamila ta gai da mini ita, ina jin dai ko mantawa take.”
“Hmm! Saƙon gaisuwa daban zuwa kuma daban. Masu iya magana na cewa, ‘zuwa da kai ya fi aike.'”
“To shike nan a ba ta haƙuri In Sha Allah zan zo na yini ma.”
Sun ɗan taɓa hira sosai gwanin sha’awa, sai dai lokaci zuwa lokaci yakan ji ta yi shiru har alamun tunani su ɗan bayyana a fuskarta. Lamarin da ya sa shi tambayar, “Shin me ke faruwa? Na san dai ba barcin wuri kike yi ba bare a ce ko barci ne ke son fizge mini ke.”
Siririn murmushi ta sakar masa tare da cewa, “Koɗaya, ba wani barci kuma lafiyata ƙalau!”
“To shike nan Ma Sha Allah! Allah Ya ƙara lafiya.”
ƙarfe tara da rabi (9:30pm) ya miƙe ya ce, “Bari na koma ko?” Rufe bakinsa ke da wuya sai ga sallamar Abbanta nan, sannu da zuwa haɗe da gaisuwa cikin girmamawa yaya Abdul ya yi masa.
Abban ya ɗora da tambayar, “Ya ya mahaifiyar taka? Da fatan duk kuna lafiya?”
Kansa sunkuye cike da kunya ya amsa, “Lafiya ƙalau, ta ce ma tana gaishe ku.”
“Madalla! Muna amsawa, ka yi mini gaisuwa do Allah!”
“In Sha Allah!” Yaya Abdul ya faɗa tare da fitowa, Zaliha ta yo masa rakiya inda ya aje mashin ɗinsa, ya hau ya fice.
Ita kuma ta komo ta iske Abba zaune a falo, har lokacin Umma ba ta fito daga ɗakin da ta ƙume kanta ba saboda sam ba ta son ta haɗa ido da yaya Abdul.
Sannu da dawowa Zaliha ta yi Abban nata tare da gaishe shi kana ta miƙe ta nufi kicin ta ɗauko masa abincinsa sannan ta zauna kusa da shi ta yi shiru.
“Ina mahaifiyar taki ne?” Ya tambaya bai gama rufe bakinsa ba sai ga ta ta fito, fuska a tamke kamar wacce aka aikowa manzon mutuwa. Zama ta yi daura da shi ta ce, “Sannu da zuwa.”
“Yawwa sannu dai, ya yinin gidan?” Ya amsa.
Zaliha ta miƙe za ta shige ɗakinta, Umma ta dakatar da ita da cewa, “Komo ki zauna gara a yi ta a gabansa shi ma ya ji ya sani. Domin na ga wani iyashegen ma daga wajensa kike samun ɗaurin gindi.” Komawar ta yi ta zauna wajen da ta tashi.
“Mene ne ya faru kuma?”Abba ya tambaya.
“Umma don Allah ki bari ya gama cin abinci tukunna. Ni na ce miki zan yi duk abin da kike so ɗin ba sai rai ya ɓaci ba.” Zaliha ce ta yi wannan furucin cikin rarraunar murya wacce kuka ke daf da kufce mata.
Wani irin kallo mai razanarwa Umma ta jefe ta da shi tare da cewa, “Iye! Ba shakka, lallai abin naki ya tumbatsa! Watau ke ce za ki tsara mana yadda za a yi? Sai ya gama cin abinci sannan zan yi masa magana, kada na faɗa masa maganar ɓacin rai ya gaza ci ko?”
“Ya isa haka, Zaliha tashi je ki abinki.” Abba ya faɗa, miƙewa ta yi domin cika umarnin mahaifin nata ta shige ɗakinta.
Cikin hayaniya Umma ta ce, “Da ma na faɗa ɗaure wa yarinyar nan gindi kake, shi yasa yanzu take neman sauya mini.”
Ya katse ta da cewa, “Kina son dai ki butulce wa Ubangiji da ya ba ki salahar yarinya kamar ta. Yanzu mene ne laifinta akan ta ce a bari na gama cin abinci, sai ki faɗi duk ma abin da kike so faɗa. Kuma ai sani ta yi duk wanda aka tara da maganar ɓacin rai ba lallai ba ne ya samu sukunin cin abinci, kuma bai kamata a ce lallai sai tana gabanmu za ki faɗa mini laifinta ba.”
“Sannan kuma a cikin maganganunta na ji inda take cewa za ta bi sharaɗin da kika gindaya mata. Ina son ki rika bin al’amura a hankali, idan ba haka ba watarana za ki tsunduma cikin kogin nadama. Tsalle ɗaya mutum yake ya faɗa rijiya sai ya yi dubu bai fito ba.”
Cika ta riƙa yi tana batsewa yayin da yake maganar, ya ɗan tsahirta kaɗan kafin ya ɗora da tambayar, “To mene ne ya faru yanzun faɗa mini?”
“Kai ma ka san zancen, maganar wannan shashashan yaron ne da yake ɓata mata lokaci. Ga mutumin kirki ya zo yana son ta ba shi dama ta ki, indai ba maganar Abdullahi ka yi mata ba sam ba za ka ga farincikinta da walwalarta ba. Kuma ka san komai amma ka ƙyale ni da ita babu abin da ka yi a kai. To ka sani na ba ta watanni biyu akan ta rabu da shi sannan ta saurari Alhaji Saminu, shi nake so ta aura kawai.”
Kafin ta dire zancen nata Abba ya kwashe da dariya, ji ta yi kamar ya watsa mata barkono a zuciya. Sai ta sake yowa sama kamar kumfa, “Na zama mahaukaciya ke nan, ina faɗa maka laifin yarinya amma dariya kake mini, to ni da ku mu zuba!”
Cikin yanayin dariyar ya ce, “Watau ni daɗina da ke akwai ki da mayar da ƙaramin abu babba da kuma saurin yanke hukunci, amma kin ki ɗaukar darasi daga sakamakon da ke faruwa a sanadiyar yanke hukunci cikin fishi da gaggawa ba tare da bin abu a hankali ba. Matsaloli sun faru a baya waɗanda wannan halin naki ne ya janyo su, amma har yau ba ki san Annabi ya faku ba.”
“Yanzu wannan maganar ce ƙarama? A wajenka ne take ƙarama amma ni dai matuƙar ina numfashi ba zan bari ‘yata ta auri wannan yaron ba, haka kawai ta je ta shiga wahala. Alhaji Saminu za ta aura.”
“Ki dakata ki nutsu, ki mayar da hankalinki jikinki ki fahimci abin da zan tunatar da ke, domin kin riga kin san su, tuna miki zan yi, wataƙila tunatarwar ta yi amfani. Kamar yadda Allah Ya yi umarni, “ku tunatar domin tunatarwa tana amfanar muminai.”
Ya ɗan dakata kaɗan ya ja numfashi sannan ya ci gaba da faɗin, “Ki tuna a lokacin da na zo neman auren ki, mu nawa ne samari da muke tsayawa a ƙofar gidanku? Aƙalla mun kai bakwai, a iya sanina duk cikinmu ni kaɗai ne marar nauyi. Dukkansu sun fito ne daga gidajen masu farcen susa, bugu da ƙari suna da sana’o’i masu maiƙo, amma ni a lokacin aikin ma bai tabbata ba domin ban zama cikakken ma’aikacin gwamnati ba, sai bayan na aure ki da watanni shida sannan aka shigar da ni cikin jerin gwanon ma’aikata masu cikakken albashi.”
“Shin me yasa kika zaɓe ni a wancan lokacin kika kafe ni kike so, duk da ga ‘ya’yan masu yatsu da yawa, waɗanda suke cikin daula? Wannan ke nan! Sannan kuma ina so ki yi nazarin rayuwarmu ta aure, a yadda na aure ki har yanzu a haka muke ko kuwa? Shi arziki da ajali da auren duk lokaci ne da su, kuma Allah Ya riga ya tsara wa kowanne bawa ƙaddararsa, don haka ba abin da kike so za ki ce dole shi zai faru ba, kada ki manta hatta kanki ba ke kike da iko da shi ba. Sau nawa kikan so yin abu amma ya gagare ki komai sauƙinsa. Wanda yake sama, Mamallakinmu gabaɗaya Shi ke tsara mana yadda komai zai gudana, mu dai namu aikin addu’a kawai. Ina son ki bar wa Allah zaɓi, Shi Ya san abin da ya fi zama alkairi ga kowanne bawa, mutum bai isa ya ƙetare ƙaddararsa ba.”
“A cikin Ƙur’ani Mai Girma Allah Yana cewa, “Sau da yawa mutane sukan so abu amma sai ya zama sharri a kansu; haka nan sau da yawa mutane kan ƙi abu amma sai ya zama alkairi a gare su. Allah Shi Ya sani ku ba ku sani ba.” To idan haka ne kuwa ashe ba wa Masanin komai zaɓi shi ya fi alkairi ga bawan da ke neman nasarar rayuwa da kuma kyakkyawan ƙarshe.”
Ya sake ɗan tsahirtawa ya haɗiyi yawu tare da numfasawa, sannan ya zarce da faɗin, “Wa’adin watanni biyu da kika ba ta ki janye shi, ki ƙyale ta. Allah zai sanya mata nutsuwa akan wanda Ya zaba mata a matsayin miji.”
“To na ji, amma ta dakatar da shi da shigowa ciki, ba na so gaskiya!”
“Wannan sam ba aikinta ba ne, sam wannan ma ba maganar yi ba ce.”
“To kai ɗin ka dakatar da shi, idan kuma kai ma ba aikinka ba ne to ni zan faɗa masa.”
Cike da mamaki ya ce, “Wai ni kam Saratu bari na tambaye ki, shin kin manta waye Abdullahi ne? Ɗan aminina ne fa, yanzu har kin manta alkairan da yake miki ke da ‘yar taki? Tun tana tsumman goyo yake ɗawainiya da ita har kawo yanzu bai taɓa kasawa ba. Duk da gazawar tasa da kike gani, idan ya yi wa ƙanwarsa abu sai ya yi wa Zaliha ma kwatankwacinsa. To ki saurara ni ba zan hana shi shigowa gidan nan ba, kuma ni ina roƙon Allah Ya ƙaddara Zaliha ta zama matarsa, haka ne kawai sakayyar da zan iya masa bisa hidimta mata da yake. Idan da na so ni ya kamata na nuna iko a kanta na ce sai ta aure shi, amma ban yi hakan ba domin shi auren dole ba ya taɓa haifar da alkairi sai ɗimbin nadama. Don haka ina mai gargaɗin ki, kul kika kuskura kika tunkari yaron nan da wannan maganar. Kuma babu ruwanki ma da tarayyarsa da Zaliha.”
Wani zazzafan numfashi ta ja ta fesar da iska mai cike da ɗumi, ta miƙe tsaye kansa kamar za ta doke shi. Ta fara zuba masifa, “To na saurare ka na ji irin hukuncin da ka yanke, don haka kai ma ina son ka buɗe kunnuwanka ka ji ni. Duk abin da ka taka daidai nake da kai, wallahi Zaliha ba za ta taɓa auren yaron nan ba, abin da kake cewa yana yi mata ai ba tambayarsa aka yi ba ko roƙon sa. Kuma ba cikin tsiya ya gan ta ba, shin me ma ya taɓa yi mata, ya zo ya faɗa sai a biya shi.”