Skip to content
Part 3 of 16 in the Series Ko Wace Kwarya by Sadik Abubakar

Bai ƙara tanka mata ba, ya mayar da hankalinsa kan abincinsa. Bayan ta gama bambaminta ta wuce ɗaki tana huci kamar kasa.

To ita kuwa Zaliha tsaye ta yi a ƙofar ɗakinta daga ciki, ta ji duk zantukan da iyayen nata suka yi. Kan gadonta ta faɗa yayin da kanta ya ci gaba da sara mata, “INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI’UN!” Jimlar da ta riƙa maimaituwa ke nan a kan harshenta.

Kimanin mintuna biyar tana wannan yanayi kafin ta shiga magana da zuciyarta.

“In Sha Allah ba zan zama silar samun saɓani tsakanin iyayena ba, Ya Allah Kai Maji roƙon bayinKa ne. Ina roƙon Ka ka daidaita zukatan iyayena, Allah ka sa wannan cacar bakin da suka yi ita ce ƙarshe!” Tana gama addu’ar ta miƙe ta ɗauro alwala ta fara nafilolin da ta saba yi.

To gobara na neman tashi tsakanin Zaliha da mahaifiyarta, muna fatan Ubangiji Ya kashe wutar kafin ta kai ga yi musu illa.
*****

Waye Yaya Abdul?
Cikakken sunansa shi ne Abdullahi Alhassan, matashin saurayi ne mai kimanin shekaru ashirin da bakwai zuwa da takwas (27-28). Fari ne mai matsakaicin jiki da tsayi, yana da doguwar fuska wacce sajensa ya kewaye ta. Dogon hanci ne da shi da baki madaidaici, idanunsa gwanin ban sha’awa. A takaice dai shi ma kyakkyawa ne irin ajin farkon nan.

Mahaifinsa Malam Hassan, ma’aikaci ne a ma’aikatar ilimi ta jahar Kano. Kafin rasuwarsa sai da ya riƙe miƙamin babban darakta na ma’aikatar. Hakazalika shi ne limamin da ke jan salla a Masallacin unguwar tasu. Babban aminin Malam Sirajo ne, watau Abban Zaliha. Ya rasu shekaru biyar da suka gabata ya bar mace daya (Inna) da yara biyu (Yaya Abdul da Jamila).

Mahaifiyar yaya Abdul, ‘yar cikin birnin Dabo ce unguwar Sagagi. Ta fito ne daga gidan ilimi. Mahaifinta babban malamin ne yana da tsangaya wacce wanta ya gada bayan rasuwar mahaifin nasu, ana kiran sa Gwani Murtala.

Yaya Abdul ya samu haddar Ƙur’ani Mai Girma tun kafin ya kammala ƙaramar sakandire. Sannan ya yi karatun littafan addini da dama a wajen wan mahaifiyarsa. Yana da digiri a fannin tarbiyya (Education), yanzu haka yana koyarwa a makarantar Sheikh Bashir Arrayan. Bayan nan kuma yana karantarwa a wata Islamiyya da ke nan unguwar tasu mai suna NURUL UMMA.

Tun daga matakin reno yake koyar da Zaliha ita da ƙanwarsa Jamila, dayake kusan yanki ɗaya suke bambancin layi ne kawai.

Tun Zaliha na ƙarama Allah Ya saka masa ƙaunarta, a wancan lokaci yana son ta ne saboda ƙwazonta da jajircewarta akan karatu, sannan ga ta da kunya da ladabi matuƙa. Ta shiga ransa fiye da tunanin mai tunani. Yadda yake kula da ita da sha’aninta har haushi Jamila take ji.

Tafi-tafi har suka kammala firamare suka matsa sashen ƙaramar sakandire na makarantar, tafiya na tafiya dai Zaliha na ƙara girma tana ƙara yin wayo, tana ƙara zama budurwa.

Bayan sun sake matsawa babbar sakandire, cikar kyawunta da surar budurci suka bayyana a tare da ita. A lokacin ita kanta ta fahimci kulawar da yake ba ta ta musamman ce. Ta ji ya shiga ranta matuƙa, tana son sa sosai. Ta sha tsangwama da nuna baƙin ciki a wajen ƙawayenta na boko da na Islamiyya, kasancewar su ma son yaya Abdul ɗin suke amma bai ba su dama ba.

Lokacin da ya sanar da Inna, ce masa ta yi, “Yo da ma idan ka ga kare yana shinshina takalmi, idan aka ƙyale shi ɗauka zai yi.”

Ya sunkuyar da kai haɗe da dariya ya ce, “Ni da ma na san duk abin da nake ana kallo na ai.”

Cikin murmushi ta ce, “wannan shi ne burin mahaifinka, ya kudurce a ransa idan har Zaliha ta kawo munzalin to zai shawarce ka da ka nemi auren ta. Sai ga shi Allah Ya ƙaddara ba zai gani ba. Allah Ubangiji Ya sanya alkairi; Allah Ya tabbatar Ya haɗa zukatanku.”
“Amin Ya Allah!” Ya amsa a kunyace.
To, wannan shi ne abin da ya faru a farkon al’amarin kafin daga bisani Jumina (Watau Umma) ta fara kassara dangantakar.

Washegari ya kasance Asabar ne babu makarantar boko, ta Asuba ce kawai ke gaban Zaliha. Ana fitowa daga sallah ta saɓi jakarta ta fice bayan ta yi wa Umma sallama. Kodayake ba ta amsa mata ba domin haushinta take ji, a bahagon tunaninta yarinyar ba ta da wayo ne. Ya ya za a yi ga gidan hutu da jin daɗi, inda za ta huta wani nata ma ya dandali arziki amma za ta kafe akan faƙiri mabuƙaci? Wanda bai ma gama tsayuwa da ƙafarsa ba. Aziyar zuciya ta sauke sannan ta miƙe ta shiga haɗa musu abincin karin safe.

Tana yin aikin ta fara tunanin, “To ko dai na bar maganin nan tunda ta ce ta amince da Alhaji Saminun? Amma kuma za ta yi abin babu soyayya da ƙaunarsa a ranta, sai rashin biyayya da rashin kunya su biyo baya. Ya zama tilas na ba ta maganin na takura mata sai ta yi amfani da shi.”

Wannan tunani da ta yi, ya kawo mata wata dabara cewa, ta zuba garin maganin na sawa a abinci cikin wainar ƙwan da za ta soya, watau a cikin wacce Zalihar za ta ci. Hakan kuwa ta yi, ta gama kafin ta dawo daga makarantar.

Fitar Abba ke da wuya sai ga Zaliha ta dawo, kai tsaye ɗakinta ta wuce ta zauna bayan ta yi sallama. Kimanin mintuna biyar zuwa goma, Umma ta kira ta murya a daƙire, “Kina ina ne? Ko ni zan kawo miki abincin saboda isa?”

Fitowa Zaliha ta yi cikin yanayin tausayi ta zo ta ɗauki abincin nata, ta juya za ta koma. “Ina kuma za ki? A nan nake son ki zauna ki ci.” Umma ta faɗa a gadarance tana bin ta da harara.

Tsayawa Zaliha ta yi cak! Ga tunaninta wani sabon faɗan ne za ta yi mata. Babu yadda ta iya haka ta zauna tare da ajiye kayan abincin. Shiru-shiru ba ta buɗe ba bare ta fara ci, Umma sai harara take galla mata, ɗago kan da za ta yi suka haɗa ido, da sauri ta sunkuyar da kanta ta buɗe abincin.

Gutsirar wainar ƙwan ta yi ta haɗa da burodi ta saka a baki, cin abincin kawai za ta yi amma ba don tana jin yunwa ba. Ta tauna ta haɗiye, sai ta ji wani ɗan bauri na magani ya kama mata harshe.

Kallon wainar ta yi, sai yanzu ta lura da kalar wainar ba yadda aka saba gani ba ne, wani irin fatsi-fatsin magani ne a jiki. Sake gutsira ta yi wani ɓangaren daban domin ta tabbatar haka wainar take ko kuwa. Ajiye wacce ta gutsira ɗin ta bayan ta fahimci dukkan wainar haka take. Sai ta ci gaba da cin burodin kawai tana karɓar shayin.

Duk abin nan da take Umma na kallon ta, ganin ba ta da niyyar sake cin wainar ya sa ta ce mata, “Me yasa ba kya haɗawa da wainar kin bar ta tana shan iska?”

“Na ƙoshi ma wallahi! Kaina ne yake mini ciwo, burodin ma ya ishe ni.”
“Zaliha watau ɓacin rai kike so ki cusa wa zuciyarki har wani ciwon ya zo ya same ki ko? Yanzu ba za ki fahimci abin da nake nema miki ba?”

Kuka ne ke shirin suɓuce mata, da kyar ta haɗiye shi ta nisa tare da cewa, “Umma ni ba fahimtar ki ba ne ban yi ba, amma da wane idon za mu kalli su Inna? Sannan wane kallo duniya za ta yi mana?”

“Ke dakata, ni za ki faɗawa duniya? Kada ki sake fadlɗa mini irin wannan maganar, kuma maza ki ɗauki wainar nan ki cinye kafin na saɓa miki.”
“Umma wallahi ba zan iya ci ba, zuciyata ce take tashi shi yasa na bari.”

Wani irin wulaƙantaccen kallo ta yi mata sannan ta ce, “Ban gane zuciyarki ce ke tashi ba? Ke bari dai na faɗa miki ki ji, wannan maganin baki ne na karɓo miki. Shi na saka a wainar, kuma ki gama ga na wanka can yana jiran ki.”

Gabanta ne ya yanke ya faɗi, wane irin maganin baki kuma? Tun da can ba a nemi maganin bakin ba sai yanzu? To ma wai wane baki, bayan ga addu’o’in Azkar da suka zame mata tamkar ruwan sha, jiddun walahairan cikin yin su take. Babu shakka akwai wani abin a ƙasa.

Tunanin da da ta yi ke nan kafin ta buɗa baki ta ce, “Umma wane maganin baki ne wannan? Don Allah ki rufa mana asiri, kada ki sake zuwa wajen masu ba da irin wannan magani. Addu’o’in da kike yi mini da bakinki mai albarka ba dare ba rana sun isa Allah Ya tsare ni daga sharrin duk wani abin ƙi.”

Harara mai razanarwa ta aika mata tare da faɗin, “Sannu uwar daɗin baki, to ni ina son sai kin yi amfani da su, idan kuma za ki nuna mini ban isa da ke ba ne sai ki yi abin da kike so.” Tana faɗa ta miƙe ta bar ta a wajen.

Wani sabon tashin hankalin ke nan! Tunani mai zurfi Zaliha ta sake afkawa, saƙe-saƙe kawai take a ranta game da wannan al’amari da ya kunno kai gidan nasu. Anya kuwa ba duk akan aurenta ba ne? Wani sashe ke nan na tunanin nata, “Ya Allah ka shigo cikin wannan lamari, Allah ka ganar da mahaifiyata gaskiya ka ba ta ikon bin ta; Allah ka nuna mata ƙarya ka ba damar kauce mata.” Tana gama wannan addu’a ta tattara kayan ta mayar kicin ta, ta yi wanke-wanke sannan ta gyare ko’ina na gidan nasu. Bayan ta kammala ta komo falo ta zauna.

Umma kuma na can ɗakinta. Wayarta ce ta fara ruri, ta ɗauka da sauri. Ƙawarta Yahanasu ce, ɗagawa ta yi da cewa, “Assalama Alaikum!”
“Wa alaikums salam, barka da hantsi da fatan kin tashi lafiya?”
“Barka dai, lafiya ƙalau. Ya kwanan gidan ya yara? Ya gajiyar tafiya kuma? Na gode fa Allah Ya saka da alkairi Allah Ya bar zumunci.”

“Gajiya ta bi lafiya, ba komai mene abin godiya kuma? Ai yi wa kai ne. Ya ya abin dai da alamun nasara ko?”
“Kayya kin san halin yaran zamani! Gardama ce da su, ina jin sai mun sake komawa wajen nan. Domin yin farko ma bai yi amfani ba sai zubarwa aka yi, fur ta ƙi ci. Kamar mai aljanu.”

“Yo ke ma ban da abinki, wa ya kai ki zubawa a gabanta? Ai binne mata shi za ki yi a ƙasan abincin, lokacin da za ta kwaso da shi ta danna a baki ma ba ta sani.”

“Hmm! Sam ba a gabanta na zuba ba, dabara ma na yi cikin ƙwai na haɗa na soya mata waina, gutsira ɗaya ta yi ta ce wai zuciyarta ke tashi. Ƙarshe dai fitowa na yi na ce mata maganin baki ne. Wallahi ‘yar nan sai ta tsaya tana faɗa mini Ƙauli-da-Ba’adi.”

“To shike nan ki rabu da ita, ai idan ta san wata ba ta san wata, indai boka ne ya san yadda zai yi da ita.”

“To ai ko sai dai hakan, duk da cewa tana iƙirarin ba za ta bijire wa umarnina ba, ba zan zauna ba domin babu soyayyarsa a ranta. Ko da an yi auren za ta riƙa bijire masa. don haka yanzu ta riga ta fahimci so ake ta yi amfani da maganin, to ba kuwa za ta yi ba. Mafita ɗaya dai bokan ya san yadda zai ɓullo mata. Yanzu yaushe kike ganin za mu koma?”

To wannan ba abu ba ne da za a bari ya ɗauki lokaci, gobe ko jibi idan kin samu dama sai mu je.”

“Shi ke nan to, Allah Ya saka da alkairi na gode, Allah Ya kai mu goben.” Ta faɗa tare da kashe wayar sannan ta fito da nufin ta zo ta duba ko Zaliha ta kammala aikace-aikacen. Me za ta yi tozali da shi, idan ba Zalihar ba durƙushe akan gwiwoyinta, tana zubar da wasu zafafan hawaye masu tsananin ɗumi da tayar da hankali.

Tsuru-tsuru ta yi, tana jin da ma ƙasa ta tsage ta fada don kunya. “Babu shakka yarinyar nan ta ji duk abin da muka tattauna. Wannan wace irin yarinya ce haka?”

Ɗan gajeren tunanin da ta yi ke nan a tsaye. Zaliha ta yunƙura tare da dafa ƙafafuwanta, cikin muryar da kuka ya raunana ta ce, “Ummana me yasa za ki biye wa ruɗin duniya da shaiɗanun mutane? Na yi miki alƙawarin zan auri wanda kike so, akan me za ki bari shaiɗan ya yi galaba a kanki? Har ya nemi ya raba ki da imaninki! Umma shekara da shekaru kina bin Allah da ɗa’a da, kina bin umarninSa da haninSa amma a yini guda ki ɓata nagartattun ayyukanki? Umma ta dalilina ba na son ki rasa imaninki, ina roƙon ƙi don Allah ki fasa zuwa wajen bokan nan! Idan Alhaji Saminu ya zo zan faɗa masa ya turo magabatansa na yarda zan aure shi.”

Tana maganar tana kwararar da hawaye, amma ita kuwa Umma ko a jikinta, wai an yakushi kakkausa. Idonta ya gama rufewa akan naira, babu abin da take hange illa irin alherin da za ta tatsa a jikin Alhajin idan ‘yar tata ta amince ya zama sirikinta.

Zaliha ta ci gaba da magana cikin kukan, “Ki yi haƙuri da duk abin da ya gabata na ɓacin rai da na haddasa miki, ki yafe mini.”

Sai yanzu ta buɗa baki ta ce, “Ba ki taɓa ɓata mini rai ba har zuciyata ta soyu kamar wannan lokacin. Ke sanin kanki ne babu yadda za a yi uwa ta cutar da ‘yarta. Farinciki nake nema miki da ni kaina. Bai kamata na ƙyale ki ki jefa kanki wajen da za ki sha wuya ba, daga ƙarshe a zo a yi abin da ake cewa, ka sayar da akuya amma ta dawo tana ci maka danga. Yanzu aure ake yi wajen da mutum zai huta ya ji daɗi, danginsa ma su huta. Allah Ya yi miki farin jini da kyau, sam ke ba matar ƙaramin mutum ba ce.

Kunya mai cike da takaici ta turnuƙe zuciyar Zaliha, “shin me Umma take nufi da wannan maganar? Da ma idan mace tana da kyau da farin jini sai ta zama abar alfahari? Ta zama kamar wata hajar kasuwa? Har a ce ta fi ƙarfin wani saboda ƙarancin abin hannunsa, sai mai kuɗi?” Tunanin da ya kewaye zuciyarta kafin Umman ta ɗora da faɗin, “Ki cire Abdullahi daga ranki kin ji, Allah Ya yi miki albarka. Ki je ki yi wanka ki huta, ni bari na ɗora mana abincin rana.”

“Amin Umma na gode!” Ta faɗa sannan ta miƙe ta nufi ɗakinta. Ajiyar zuciya uku ta sauke a jere daidai lokacin da ta aza ƙugunta bisa gefen gado. Zuciyarta ta shiga hakaito mata wata daddadar hira da suka taɓa yi ita da sanyin idaniyarta.

“Shi ne ɗazu a makaranta ina ba da hadda kake cewa na sake ko? Kuma daidai nake yi.”

Cikin sigar shagwaɓa take maganar, dariya ya yi sannan ya ce, “Ba wani daidai da kika yi, kin fiye ƙorafi dai. Ba ki ga ba ke kaɗai ba na yiwa haka ba.”
“Allah kuwa daidai na yi, har sau biyar fa ina maimaitawa, kuma ba gyara mini ka yi ba.”

Ya sake tintsirewa da dariya ya ce, “Kin san me? Watau daɗin muryarki idan kina karatun Ƙur’ani ta daban ce. Kunnuwana ba sa taɓa gajiya da sauraren daddaɗan sautinki.”

“Hmm! Za ka fara tsokanar taka ko? Ina wani daɗi a muryar da take karkarwa?”

“Allah ba zancen wasa ko tsokana, gaskiya ce. Don haka ma daga yanzu idan za ki yi hadda naɗar sautin zan yi, sai na riƙa saurare kodayaushe na yi buƙata.”

“Cabɗijan! Ai kuwa shiru zan yi na ce ban iya ba, ko kuma na ƙi zuwa ranar karɓar haddar.”

Cikin dariya ya ce, Bulala goma ce ba yawa, kin dai sani.”

“E na yarda ko ma ɗari ce a yi mini.”
“Da ƙarfi fa zan yi miki, ba kamar yadda zan yi wa sauran ba.” Ya ƙarasa da ƙyalƙyala dariya.

Murmushi ta yi ba tare da ce komai ba. Suka yi shiru cikin daddaɗan yanayi da nishaɗi. Zuwa can ya nisa da faɗin, “Ina roƙon Allah Ya ba mu ‘ya’ya masu kama da ke, masu irin halinki, masu basirarki da kunyarki.”

“Hmm! Kai ko, na fuskanci yau zolaya kake ji. Tun da ka zo kake tsokana ta. Duk waɗannan nagartattun siffofin da ka zayyano ai kai kake da su.”
“Ko kuma ke ɗin ce mai zolayar ba.”

<< Ko Wace Kwarya 2Ko Wace Kwarya 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×