Siririn murmushi ta yi tare da sakar masa wani kallo mai jefa zuciya cikin saƙe-saƙe kala-kala. Cikin lallausar murya ta ce, "Abban Khakil!""Waye Abban Khakil kuma, me ya faru da shi?"
Cikin ɗariya mai ɗauke da nishaɗi haɗi da walwala ta ce, "Wani kyakkyawan saurayi ne da aka jima ba a yi kamar sa ba a tarihin duniya, sai wata 'yar almajirar yarinya ta yi sa'ar zama sarauniyar birnin zuciyarsa. Shi ne take fatan idan sun tsinci kansu a duniyar ma'aurata, Ubangiji Ya ba su da namiji, ya raɗa masa. . .