To kawo yanzu dai a iya cewa zullumi da ɓacin rai sun fara samun muhalli a zuciyar Zaliha, kallo ɗaya ya isa ya labarta maka lallai yarinyar na cikin damuwa, musamman ga wanda ya san ta a baya kasancewar ta mai fara’a da yawan murmushi. To sai dai a halin yanzu waɗannan siffofin sun fara raguwa a tare da ita.
Cikin ɗan ƙanƙanen lokaci har ta fara rama ta lalace, tunanin safe daban na marece daban. Yini biyun hutun ƙarshen makon da ake ciki, sam ba ta je makarantar Islamiyya ba, sai ta Asuba kawai, sannan kuma ta rufe wayarta gabaɗaya. Dalilin da yasa hankalin yaya Abdul ya tashi ke nan, kodayake Jamila ta faɗa masa suna haɗuwa da Asuba. Duk da haka ya sha alwashin idan har Litinin ta zo ba ta je boko ba, to ya zama tilas ya je gidan ya ji ba’asin rashin zuwan nata.
Washegari Litinin ta shirya, suna gama karin safe takarta ta saɓa ta ce, “Umma zan tafi.”
“Ki duba kan furji akwai kuɗi ki ɗauki wanda zai ishe ki, sai kin dawo Allah Ya tsare.” Umma ta faɗa ba tare da ta dube ta ba. Naira hamsin kawai ta ɗauka, ita ma don kada ta fita ba komai a hannunta ne.
Haka dai zaman nasu ya sauya, kowa ba ya son haɗa ido da kowa. Ita dai Umma haushi ne ya hana ta sakar mata fuska, ita kuma Zalihar maganar zuwa wajen bokan nan da ta ji ce ta tsaya mata a rai. “Yanzu mahaifiyata ce wacce ta tsugunna ta haife ni take zuwa wajen boka? Shin yaushe Umma ta san wannan mummunar hanya mai hallakarwa?” Tambayoyin da ke yawan taso mata ke nan, kuma har yanzu ta gaza tantance amsoshin da tunaninta ke ba ta. “Shin son abin duniya ne ko kuma dai ruɗin shaiɗan ne?”
A kodayaushe ta yi wannan tunani takan rufe da yin addu’a ga mahaifiyar tata, Allah Ya ganar da ita hanya madaidaiciya, laifin da ta yi a baya kuma Ya shafe mata su….
A makarantar ma haka yanayinta ya kasance, ba wani kuzari da walwala. Lokacin da suka fito tara ne, suka nufi wajen ɗan lambu na cikin makarantar. Ƙawarta Hamida Ibrahim take tamabyar ta, “Wai ni kuwa lafiya kike, na ga kamar kin rame kuma babu walwala a tare da ke?”
Dogon numfashi ta ja kafin ta ƙarasa sauke shi ajiyar zuciya ta kufce mata. “Ikon Allah! Me ke damun ki haka har da aziyar zuciya?”
Cikin muryar da kuka ke son kufcewa ta ce, “Watan jarabawata ya kama, kawai ki taya ni da addu’a. Na shiga wani halin tsaka mai wuya, fatan da za ku yi mini Allah Ya ba ni ikon cin wannan jarabawa.”
Cikin yanayin tashin hankali Hamida ta ce, “SubhanAllah! Me ke faruwa ne? Ki yi mini bayani yadda zan fahimta. Wani abin ne ya faru a gida?”
Kukan da take tattalin kada ya bayyana ya ƙwace mata, cikinsa ta riƙa cewa, “Umma ta ce dole na rabu da yaya Abdul saboda wani mutum ya fara zuwa wajena, kasancewar na ƙi sauraren sa shi ne har wata ƙawarta ta ja ta wajen ‘yan tsubbu.”
“INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI’UN! Yanzu Umma ce da kanta ta taka ta je wajen masu da’awar sanin gaibu ? Allah Ya yafe mata. To me ya yi zafi haka?”
“Abin da ya tsaya mini a rai ke nan, na rasa me ya rufe mata ido har take neman hallaka rayuwarta. Na sha kuka sosai, daren jiya da shekaranjiya gaza barci na yi. Duk lokacin da na tuno yadda na ji suna tattaunawa da ƙawar tata a waya cewa za su sake komawa, ba na sanin hawaye ya cika a idona, sai dai na ji ɗuminsa yana sauka bisa kuncina.” Kukan ne ya sake cin ƙarfinta alatilas ta yi shiru.
“Ki yi haƙuri, ki daina kuka. Wannan al’amari addu’a kawai yake buƙata. Sannan a hankali cikin dabara ki faɗakar da Umma ki ja hankalinta ta hanyar da ta dace. Amma Abba bai sani ba ko?”
“Bai san ta je wajen bokan ba, amma ya san da maganar shi wancan mutumin.”
“Kai amma abin babu daɗi, ko a da ma auren dole bai haifar da komai ba sai ɗimbin nadama bare yanzu da ilimi ya yawaita. Shi yaya Abdul ya san mutumin yana zuwa wajenki?”
“Bai sani ba, dayake dududu bai fi sati biyu da fara zuwa ba.”
Cikin tsantsar nuna kulawa Hamida ta riƙa kwantar mata da hankali, da ƙarshe ta rufe da faɗin, “Komai muƙaddari ne daga Ubangiji, abin da Allah Ya tsara shi ne zai tabbata. Wannan abu ba lallai ba ne ya zo a yadda Umma take so, Allah Ya riga Ya tsara miki komai na rayuwarki, bawa ba ya taɓa kauce wa ƙaddararsa. Fatanmu dai shi ne ƙaddarar ta zamo kyakkyawa. Ki saki ranki, yawan tunanin ma ba shi da amfani. Sannan kuma zan ja kunnenki ba don hakan ya kasance halinki ba, kada ki kuskura shaiɗan ya sa ki ɓata wa Umma rai akan wannan abin, addu’a za ki lazimta har Ubangiji Ya kawo miki ɗauki. Babu halin da bawa zai kasance a ciki face da sanin wanda Ya ƙage shi, idan bawan nan ya ƙasƙantar da kai ya risinawa Allah matuƙar risinawa, ya roƙe shi mafita to babu shakka zai taimake shi matuƙar taimakawa. Koda bai dauke masa dukkan damuwar ba, zai rage masa kaso mafi yawa, Allah Ya yi mana jagora.”
Wannan doguwar nasiha ta ratsa jikin Zaliha sosai, har ta ɗan samu sauƙin raɗaɗin da ke cin zuciyarta. Lokacin tara ya ƙare suka koma aji aka ci gaba da darasi.
Har yanzu yaya Abdul bai gan ta ba, bai shigo ajinsu ba, kasancewar ba shi da su a jadawalin karatun yau. Haka nan lokacin da aka fita tara bai zauna a makarantar ba.
To bisa al’ada kamar yadda suka saba kullum idan an tashi daga makarantar, takan jira yaya Abdul ɗin ya rako ta. Idan ta fito takan tsaya a waje ‘yan mintuna kamar biyar har cinkoson dalibai ya ragu sannan ya fito. Tana tsayen kuwa sai ga shi ya iso da murmushi kwance a fuskarsa ya ce, “Gimbiya sarautar mata! Kwana biyu mulkin ne ya motsa aka kashe mana waya kuma ba a neme mu ba?”
Cikin ƙoƙarinta na mayar masa da martanin murmushin da yake mata ta ce, “Ina yini?” Duk ƙoƙarin da ta yi na ɓoye damuwar da ta samu gurbi a ranta sai da ya fahimta. Don haka sai yanayinsa ya sauya ya ce, “Me ya same ki? Me ke damun ki?”
Shiru ta yi ba ta amsa masa ba. Cikin kosawa da son sanin me ya samu gimbiyar tasa, a ƙanƙanen lokaci har ta sauya haka ya sake cewa, “Tabbas ba lafiya ba wani abin na damun ki. Ko ba ki da lafiya ne?”
Sunkuyar da kai ta yi, ta rasa wace amsa za ta ba shi. A gefe guda kuma zuciyarta na tuƙuƙi, kuka ne yake son suɓuce mata.
“Magana nake kin yi shiru kina ji na? Tunda na kira waya kwana biyu na ji shiru, zuciyata ta fara kissima mini ƙila wata matsalar ce. Ki yi haƙuri abin da ya sa ban zo ba wata daura ce ta so cikin gaggawa aka tura ni can ƙasar Nijar, sai daren jiya misalin ƙarfe sha biyu na iso gida.”
Duk jarumtar da take ta hana hawaye taruwa a idonta lamarin ya gagare ta, saukarsa ta ji akan kuncinta. A dabarance don kada ya gani ta share tare da ƙwarara murya ta ce, “Ka yi hakuri, na ɓata maka rai kana magana na yi shiru.”
“Ba wannan na tambaye ki ba, me ya same ki?”
Shiru ta sake yi ba ta ce komai ba, ya ci gaba da faɗin, “Kuka fa kike yi, yanzu da ma akwai abin da za ki iya ɓoye mini? Kuma har na riƙa tambayar ki ki ƙi faɗa mini, kada ki yarda zuciyata ta fara hasaso mini rashin yarda da ni ne yasa ba za ki faɗa mini ba.” Cikin kakkausan harshe ya yi wannan maganar.
Muryarta a raunane ta ce, “Wani ne yake shirin wargaza mini rayuwa ya raba ni da farincikin da na jima ina tattali da burin dawwama a ciki har lokacin da numfashina na ƙarshe zai fita!” Kukan da ya zo mata ƙahon zuci ya tokare, ya kufce mata da ƙarfi har da sauti mai tsananin taɓa zuciya.
Kukan nata ya yi masifar taɓa ransa, tsananin ƙuna ya ji ƙirjinsa na yi. A hankali ya riƙa maimaita fadin, “INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI’UN!” Duk da cewa a ƙudundune ta ba shi maganar, ya fahimci komai kuma ya tabbata wannan ba ƙaramin al’amari ba ne. Shi kansa ya shaƙu da ita, yana ƙaunar ta a ransa. Ita yake wa dukkan wani tanadi, da wahala idan ya rasa ta ya sake jin wani farinciki a ransa. Ita kaɗai yake kallo a matsayin wacce Allah Ya ƙaddara ta zama matarsa, ita ce mace ta farko da ya taɓa kalla har ya ji ta dace da zama uwargidansa kuma uwar ‘ya’yansa. Wannan ɗan littafi ya yi kaɗan ya bayyana yadda masoyan suke tsara wa kansu kyakkyawar rayuwa suke fatan Allah Ya tabbatar musu. To sai dai ga wata jarabawa nan daga Allah tana shirin samun su.
Ɗan lokaci mai tsayi suka yi babu abin da ake ji sai sautin shasshekar kukan Zaliha, nisawa ya yi tare da cewa, “Ya isa haka, ki daina kukan. Mu tafi.”
Ta sake sauke ajiyar zuciya ta share hawaye sannan suka tafi. Suna fara tafiya ya ce, “Ki kwantar da hankalinki idan anjima da dare zan zo.”
“To!” Kawai ta ce. Kafin su isa inda za su rabu ta ɗan daidaita yanayinta, sai dai idanunta sun yi jajir sun kumbura kaɗan.
Suna isa wajen ta ce, “Idan ka zo ka yi mini waya. “Babu damuwa!” Ya amsa tare da juyawa.
“Idan na zo na kira ta?” Wannan maganar ta sa ya fara hasaso ko matsalar daga iyayenta ne? Kuma babu shakka daga wajen Umma ne.
Tana isa gida kai tsaye banɗaki ta nufa ta wanke fuskarta don ta ɗan rage jan da idonta ya yi sannan ta wuce ɗakinta. Sauya kayan makarantar ta yi da na zaman gida. Umma na can cikin ɗaki, zuwa ta yi ta gaishe ta tare da sanar da ita cewa ta dawa, kana ta komo ta zauna. Tunani kuma ya ce ga shi nan, ta yi zugum da ita abin tausayi.
Ta nitsatsa cikin duniyar tunane-tunane kala-kala. “Shin me zan faɗa wa yaya Abdul ya gamsu da ni? Wane bayani zan yi masa? Duk abin da zan faɗa masa da wahala ya fahimce ni. Wane irin kallo Innarsa za ta yi wa magabatana? Da wane zan kalli Jamila? Shin wane hali ma zai shiga? Na fi jin tausayin sa fiye da kaina, domin son da yake mini ya fi wanda nake masa. Ya Allah! Kai ne mai hukunta dukkan al’amura.”
“Zaliha!” Muryar Umma ke nan wacce ta fito daga ɗaki har ta iso falo Zalihar ba ta sani ba, sakamakon ta yi nisa a cikin tunanin da take, kiran ne ya katse mata tunanin. A ɗan firgice ta zabura.
Cike da mamaki Umma ta ce, “Na lura so kike ki ɗora wa kanki wata larurar ko? Akan wannan abin da rayuwarki nake son gyara miki. Dubi yadda kika fara yin zuru-zuru da ke sakamakon tunani da rashin cin wadataccen abinci. Ki tashi ki je ki ɗauko abincin ki zo ki ci a gabana, na lura idan ba na matsa miki sai ki lahanta kanki da yunwa.”
Miƙewar ta yi ta ɗauko abincin ta dawo ta ajiye. Umma ta ci gaba da fadin, “Abin da nake tsara miki Zaliha ba wai don na cutar da ke ba ne, uwa ba ta taɓa cutar da ‘yarta. Ni burina ki yi rayuwa cikin wadata da jin daɗi. Shi wannan mutumin da nake miki kwadayin ki aura babban mutum ne mai arziki, komai a cikin wadata za ki same shi, ba ke kaɗai ba hatta mu ma sai mun ci arzikinsa domin mai alheri ne. Ki duba kuɗaɗen da ya ba ki tun a zuwansa na farko amma kika ƙi karɓa, shi ne wanda ya dace da darajarki da ƙamarki ba Abdullahi ba, ke ba tsararsa ba ce, ba shi da kuɗin da zai iya auren ki.”
Tsananin ƙunar rai da takaici ne ke kama Zaliha idan ta ji mahaifiyar tata na faɗin irin waɗannan kalamai wanda ba su da maraba da na wanda ba shi da ilimi. “Shin wai arziki da talauci duk ba na Allah ba ne? Yakan azurta wanda Ya so, Ya kuma talauta duk wanda Ya so babu mai tuhumarSa. Shin wai yaushe ‘ya’ya mata suka zama haja ne? Allah Ya ganar da dukkan iyaye masu hali iri na Umma!”
Abin da Zaliha ta riƙa faɗa cikin zuciyarta ke nan lokacin da ta yi shiru. Uwar ta ci gaba da cewa, “Ki saki ranki ki kwantar da hankalinki ki ci arziki, na tabbata alherin da za ki samu a wajensa ba ƙarami ba ne, ko matansa ba su samu ba. Domin yana son ki kuma ke ce ƙarama a cikinsu, don haka zai kula da ke fiye da tsammaninki.”
Zaliha ta nisa tare da sauke numfashi sannan ta ce, “Shike nan Umma ba komai na fahimce ki.”
“Yawwa ko ke fa, maza ki ci abincin kada ya yi sanyi, ni bari na tashi na yi salla.”
To bayan sallar Isha misalin ƙarfe takwas da rabi, 8:30pm yaya Abdul ya iso kamar yadda ya alkawarta mata. Wayarta ya kira ya sanar da ita kamar yadda ta buƙata, tana ganin kiran gabanta ya faɗi. Duk kuwa da cewa da ma abin da take jira ne. Karon farko ke nan da gabanta ya yanke ya faɗi sanadiyar ganin kiran wanda a da idan ya kira ta cikin nishaɗi da annuri take ɗaga wayar. Duniya mai juyi, wai da kwaɗo ya ji shi a ruwan zafi.
Ɗaga wayar ta yi tare da karawa a kunnenta ta ce, “Sannu da zuwa, bari na fito.”
“Ba damuwa!” Ya faɗa cikin yanayi marar walwala
Hijabinta ta saka ta nufi wajen Umma ta ce, “Zan ɗan fita waje.”
“Waye ya zo?” Umma ta tambaya.
“Yaya Abdul ne!” Ta faɗa cikin tararrabin kila ma ta hana ta fitar ko kuma ta balbale ta da faɗa.
“Shike nan zan bar ki ki fita amma kada ki jima, na yi miki wannan alfarmar ne don ki san yadda za ki yakice shi a hankali. Na san ba za ki iya cire shi a ranki lokaci guda ba, sannan daga yau ma ba sai ya sake shigowa ba, ya tsaya can wajen har ya gaji ya ƙyale ki. Idan kuma kika daɗe a wajensa ni na san abin da zan yi miki.”
Zaliha ba ta sake cewa komai ba ta fito kofar gidan. Da sallama ta isa wajen da yake tsaye, ta gaishe shi ya amsa mata. Yanayin nasu sam ba daɗi, tamkar a mafarki suke ganin abin. Su da suka saba yin hira cikin farinciki da amince a sirrance cikin gida, amma yau su ne a waje cike da damuwa? Wannan wane irin sauyin lamari ne?
Tun bayan gaisuwar sai da suka shafe kimanin mintuna biyar zuwa bakwai suna tsaye ba wanda ya sake furta koda kalma ɗaya ne. Shi ne ya katse shirun bayan ya nisa ya ce, “Shi waye mutumin kuma a ina ya gan ki?”
“Watarana ne na je babban kantin bakin titi, shi ma ya tsaya zai yi sayayya, ya yi mini magana amma ban kula shi ba. Ashe ya biyo ni a baya har gida.” Cak! Sai ta tsaya da maganar.
Ya ce, “To sai aka yi ya ya kuma?”
“Shi ne Umma ta ce idan ban saurare shi ba, ba ita ba ni!”
Murmushin takaici ya yi sannan ya ce, “Ki fito kawai ki ce mini kina son shi, kada ki jingina wa Umma komai. Wannan ba wani abu ba ne, kuma na gode wa Allah da Ya nuna mini haƙiƙanin halinki tun yanzu. Ki je ki aure shi ina miki fatan alkairi.”
Kuka na gaske irin mai saka zazzafan ciwon kai ne ya suɓuce mata, sunkuyawa ta yi ta dafa ƙafafuwansa zuciyarta na tsananin tafasa da jin waɗannan kalamai nasa. Ashe da ma zai iya hakura da ita? Ita da take alƙawarta wa zuciyarta cewa koda ba ta auri wanda ba shi ba, ba za ta taɓa mantawa da ƙaunar da yake mata ba. Ta yi alƙawarin ta bar masa birnin zuciyarta har abada shi ne sarki, amma ashe shi ba haka abin yake a wajensa ba? Shi ɗin da take ganin za ta samu sauƙin raɗaɗin da take ji, wanda a tunaninta shi ne kaɗai ne magani da salama amma sai ya ɓige da ƙara harziƙa ta.