Skip to content
Part 8 of 16 in the Series Ko Wace Kwarya by Sadik Abubakar

Ya fito ya sake tarar Adaidaita ya kawo shi gida, lokacin Inna har ta fara gyangyaɗi.

Tashin ta ya yi a hankali ya cikin dabara ya sanar mata cewa, “Umma ce ba lafiya, tana zazzaɓi mai zafi. Suna asibiti ko za ki tashi mu je ga Mai Adaidaita Sahu har ƙofar gida, sai ya kai mu ya dawo da mu?”.

Da kamar za ta ce masa ya bari sai gobe mana tunda dare ya yi kusan ƙarfe goma, sai ta ce, “SubhanAllah! Allah Ya sawwaƙe, bari na tashi mu tafi.”

Jamila na kwance ta yi luf ashe ba ta yi barci ba, ta ji duk abin da suke tattaunawa. Fit ta miƙe ta ce, “Ni ma zan je.”

Inna ta ce, “Babu inda za ki, ki zauna yanzu za mu dawo.”

“Allah kuwa sai na je, ni ba zan iya zama ba ni kaɗai ku tafi ku bar ni.”

“Rabu da ita ta zo mu tafi, ɗauko hijabinki.” Cewar yaya Abdul.

Babu jimawa suka iso asibitin, ɗakin da Zaliha take ya kai su, aka gaisa tare da yin ya jiki. Sannan suka rankaya su duka zuwa inda aka kwantar da Umma. Sai a yanzu ne Zaliha ta yi tozali da mahaifiyar tata. Kuka ta saki sosai mai ɗaga hankali ta nufi gadon da gudu za ta rungume uwar, aka riƙe ta.

“INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI’UN! Inna ta faɗa cikin sigar tashin hankali, ta dubi yaya Abdul ta ci gaba da cewa, “Ka ce mini zazzaɓi take, ashe hatsari ta yi?”

Abba ya karɓi akalar zancen da cewa, “Ya faɗa miki haka ne don gudun kada hankalinki ya tashi sosai. Da a ce ya faɗa mini ma ba zan bari ya sanar da muku ba, tunda dare ya yi.”

“Allah Ya sawwaƙe, Allah Ya kiyaye gaba, Allah Ya sa kaffara ce. Allah Ya ba ta lafiya.”

Nan dai aka yi ta nuna jimami da alhini, yayin da ita kuwa Zaliha sai ɓarin hawaye take, Jamila kuma na aikin rarrashin ta. Da kyar ta ɗan numfasa. Yaya Abdul ya kira Inna waje gefe guda ya ce, “Inna don Allah ina roƙon ki wata alfarma ɗaya, ki zauna ki kwana tare da Umma, ba za a sallame ta ba a yau tunda ko jinin ma bai ƙare ba.”

“Haba ɗan nan! Mene ne abin magiyar a nan? Ai ko babu komai tsakaninka da Zaliha ni mai jinyar Umma ce. Tun kafin mu same ku muke zumunci, indai wannan ne kada ka damu.”

“Yawwa Inna, to yanzu bari na je na kawo muku kayan shimfiɗa da sauran abubuwan da za ku buƙata ko?”

Suna gama wannan tattaunawa suka koma can ɗakin jinyar, yaya Abdul ya dubi Abba ya ce, “Na san ba za a samu sallama ba a yau, to ga Inna za ta zauna a nan. Yanzu zan je na kawo mata shimfiɗa.”

“A’a ba za a yi haka ba, sam tana fama da kanta, ka bar ta ta koma gida ta huta.” Abba ya faɗa. Rufe bakinsa ke da wuya Innar ta ce, “Yo ai ba shi ne ya tsara haka ba, ni ce da kaina.”

Nan fa yaya Abdul ya sake sunfayowa gida ya kwashi dukkan wani abu da ya san za su buƙata ya kai musu. Misalin ƙarfe goma sha ɗaya, su huɗu watau, Abba da yaya Abdul sai Zaliha da kuma Jamila, suka yo shirin dawowa gida.

Adaidaita Sahu ɗaya suka hayo, suna tafiya yaya Abdul ya roƙi Abba da ya bar Zaliha su wuce da ita can gidansu, sai su kwana tare da Jamila. Hakan aka yi, Abban suka fara saukewa sannan suka isa gida, har lokacin dai Zaliha hankalinta ba ya jikinta, zuciyarta na can tunanin Ummarta. Ita a yadda ta gan ta ma gani take kamar babu rai a jikinta.

Cikin gidan suka shiga a falo suka zauna, yaya Abdul ya ci gaba da kwantar mata da hankali yana cewa, “Jikin Umma da sauƙi sosai, kawai ciwukan da ta ji jini ya ɗan zuba shi ne ake ƙara mata. In Sha Allah gobe za a sallame ta.”

“Ko motsi fa ba ta yi za ka ce jikinta da sauƙi, ni idan ta mutu kawai ku sanar da ni.” Kuka ya sake ɓalle mata sai da ta ɗan tsahirta sannan ya ce, “Ki yarda da abin da na faɗa miki. Umma jikinta da sauƙi rashin motsi ba wani abu ba ne, allurar da aka yi mata ne.”

Da kyar dai shi da Jamila suka shawo kanta ta tsayar da zubar da hawayen. Jim kaɗan ya ce su shiga ɗaki su kwanta, shi kuma ya kwanta a nan falo.

Sai Asuba ya tashi ya je Masallaci, bayan ya dawo ya tashe su suka yi salla. Jamila ta shiga kicin ta fara haɗa kayan karin kumallo. Shayi na gaske da wainar ƙwai ta yi, yaya Abdul ya sayo manyan burodi irin mai yanka-yanka.

Ta ɗauko wani babban flas ɗin shayi ta maƙare shi fal sannan ta zuba wainar a wani flas ɗin abinci, bayan ta saka takarda a ciki domin kada gumi ya koma wa wainar. Tana gama haɗa wannan, sai ta zuba wa yaya Abdul ta kai masa ɗakinsa, sannan ta haɗo musu ta kawo falo.

Zaliha na can ɗaki ta haɗa kai da gwiwa ta tsunduma kogin tunani. Ji take tamkar ta zama tsuntsuwa ta tashi ta nufi asibitin nan, ta zaƙu matuƙa da son ganin motsin mahaifiyar tata.

“Zo mu ci abinci.” Jamila ta faɗa yayin da ta shigo ɗakin, miƙewa ta yi tare da sakin ajiyar zuciya. Jamila ta dafa ta sannan ta ce, “Ki yi haƙuri, dole ne hankalinki ya tashi. Amma ki riƙa addu’a maimaikon tara damuwar a ranki, ita cuta ba mutuwa ba ce, Umma za ta samu lafiya In Sha Allah.”
Da haka ta rarraso ta suka dawo falon, sai dai ta gaza cin komai.

Sam babu sauran abin da zai yi mata ɗanɗano a harshe muddin ba ta ga tashin Umma ba kamar kowa. Jamila ta buga ta raya akan ta ci ta ƙi, sai da yaya Abdul ya sa baki sannan ta ɗan kurɓi ruwan shayin kaɗan. Suna gamawa suka shirya suka fito suka tari Adaidaita Sahu sai asibiti.

Lokaci ɗaya suka isa da Abba, ajiye shi ke nan yana tsaye a ƙofar yana tunanin ya ya za a yi ya shiga asibitin hannu na dukan cinya? Idan marar lafiya ba ta iya cin abinci ba, ‘yar jinyar fa? Ganin su da flas ya sanya ransa ya yi masa daɗi ya san abinci ne suka zo da shi. Gaishe shi suka fara yi sannan suka wuce.

Ido biyu suka iske Umma, Inna a kusa da ita. Farinciki ya kama su gabaɗaya. Kuka ya sake ƙwace wa Zaliha, ta isa gaban gadon ta kifa kanta.

“Daina kuka Zaliha na samu sauƙi, tsautsayi ne ba ya wuce ranarsa.” Umma ta faɗa cikin sassanyar murya.
Gabaɗayansu suka furta, “Alhamdu Lillah! Allah Ya ƙara lafiya, sannu!”
Yunƙurawa ta yi tana son tashi zaune, Inna ta kama ta ta jingine ta da bango, daidai lokacin jami’ar da ke kula da ita ta shigo duba ta. “Sannu ya ya jikin naki?” Ta tambaya.

Umma ta ce, “Da sauƙi sai dai ƙirjina na ɗan yi mini ciwo.”

“To ba damuwa bari likita ya ƙaraso sai ya duba, yanzu za ki iya cin abinci. Allah Ya ƙara lafiya Ya kiyaye gaba.” Ta fada tana ficewa.

Jamila ta buɗe kayan abincin nan ta zuba shayin a ƙananan kofuna, ta saka wainar da burodi akan faranti ta aje ɗaya a gaban Inna sannan ta ɗauki ɗaya ta matsa kusa da gadon ta fara ba wa Umma, a hankali ta ci ba laifi. Yaya Abdul kuma ya ɗauko magungunanta ya ba ta ta sha. Haka dai suka tsaya tsayin daka a kanta suna nuna tsantsar kulawa. Godiya da sa albarka kawai Abba yake wa yaya Abdul, ko ɗan da ya haifa a cikinsa ƙarshen hidimar da zai yi masa ke nan.

Misalin ƙarfegoma na safe likita ya zo, Umma ya fara dubawa inda ya umarci da a je a yi mata hoton ƙirjin da take ƙorafin tana ɗan jin ciwo. Aka yo hoto sakamakon ya fito likitan ya ce babu wata matsala, bugawa ce ta yi, magani ya rubuta aka ɗora ta a kai. ƙarfe goma sha daya, yaya Abdul ya turo Jamila gida ita da Zaliha su dafo abincin rana, cikin ƙanƙanen lokaci suka haɗa haɗaɗɗiyar taliya dafa-duka wacce ta ji dukkan kayan ɗanɗano da kifi banda.

Suna gamawa suka juya asibiti, daidai lokacin likita ya rubuta wa Umma sallama, kasancewar jikin nata ya ƙwarara, abin da ya yi saura kawai raunukan da ta ji, su kuma sai a hankali za su ƙarasa warkewa. Don haka sai suka juyo gabaɗaya, a gida aka ci abincin.

Duk da sun dawo gida sai marece Inna ta koma gidanta. Dukkan hidima da kuɗaɗen da aka kashe a asibiti daga lalitar yaya Abdul suka fita. Ya yi namijin ƙoƙari sosai da kai komo wajen neman lafiyar Umma. Kuma a haka kullum sai Jamila ta kai abinci gidan har tsawon kwanaki goma, a ranar goman ne Abba ya riƙa jin shigowar saƙon kar-ta-kwana a wayarsa daga banki, albashinsa ne aka sakar masa gabaɗaya.

Takanas ta Kano ya wanki ƙafa da kansa ya shigo kasuwar Kantin Kwari ya zaɓo wa Inna wasu dakakkun atamfofi manya guda biyu, bai zame ko ina ba sai gidan ya haɗa mata naira dubu goma kuɗin dinki. Cewa ta yi, “Ni duk abin da na yi, na yi don Allah ne kuma na yi wa zumunci, a tsakaninmu babu sakayya.”

Shi kuma Abba ya ce, “To ai ko wannan iftila’i bai faru ba ni mai yi miki abin da ya fi wannan ne.”
Godiya ta shiga yi masa tare da jero kalaman fatan alkairi da nasarar rayuwa mai ɗorewa.

Yaya Abdul na kawowa nan cikin zuzzurfan tunani nasa, ya saki ajiyar zuciya sannan ya miƙe tsaye yana ɗan yin tattaki a ɗakin. Wani sabon tunanin ya sake shiga, “Shin ta wace hanya zan sanar da Inna wannan rashin girma da daraja na iyayen Zaliha?”

Tsayin daren nan dai haka ya shanye shi ba tare ya runtsa ba, domin ji ya yi idanunsa tamkar ba su taɓa sanin wani abu ba wai shi barci.

Akan kunnuensa aka yi kiran sallar farko da na biyu, ya fito ya shiga bandaki ya yi alwala ya zo ya fara nafilar Raka’atanil Fajri sannan ya wuce Masallaci. Tunda ya dawo ya gaida Inna ya koma daki bai fito ba sai da lokacin tafiya aiki ya yi. Abincinsa ma bai ci, ya fito ya ce da Inna sai anjima.

To ita ma Zaliha haka ta wayi gari cikin yanayin da ta kwana da shi, ranta sam babu daɗi. Ba ta yi niyyar zuwa maƙaranta ba, domin ba ta san da wane idon za ta iya kallon yaya Abdul ba? Abba ne ya tilasata mata, shi ne ma ya dauke ta da zai fita ya rage mata hanya, a daidai kofar ya ajiye ta, ta shige. Babu wata walwala a tare da ita. Haka shi ma ya kasance, saukin ta daya ma a ranar ba zai shiga ajinsu ba. Har lokacin tashi ya kusa bai sa ta a idonsa ba, hasalima ba ya bukatar hakan, don haka saura mintuna goma a tashi sai ya fice ya riga ta fita.

To ita ma abin da ta tsara ke nan, tana jin nauyin su haɗa ido, ta tsara cewa ana tashi za ta buya cikin zuga ta wuce gida abinta. Koda aka tashi ba ta ga mashin dinsa ba a inda yake ajiyewa. Kai tsaye ta bi ayarin dalibai kowa ya nufi gidan iyayensa.

Yaya Abdul na isa gida ya tarar da Inna ta gama haɗa musu abincin rana, shinkafa da wake ne irin dahuwar kanwa din nan. Sallama ya yi ta amsa tare da cewa, “Yau da wuri ko wani abin dai ka zo dauka?”

Cikin kasalalliyar murya marar kuzari ya ce, “Kodaya, ba na jin daɗi ne sosai, ai lokacin tashi ma bai cika ba na fito.”
“SubhanAllah! Me ke damun ka?”
Ya zauna bisa kujera ya ce, “Kaina ne yake dan yi mini ciwo.”

“Assha! Sannu Allah Ya sawwake, to bari ka ci abinci sai ka sha magani ko?”

Ya dan yi shiru bai ce komai ba, ta mike cikin rawar jiki ta zubo masa abinci. “To ga abincin ka ci tukunna.”

“Inna ba na jin yunwa ai.”

“Kamar ya ya ba ka jin yunwa? Dazu ma fa da safe ba ka karya ba ka fita, sai da na shiga zan dauko kwanukan sai na ga yadda aka ajiye maka haka ka fita ka bar shi. Wai me ke damun ka? Na lura ba haka walawalarka take ba.”

Ya yi shiru dai bai ce komai ba, zuwa can ya saki ajiyar zuciya. Cikin tsananin damuwa Inna ta ce, “Babu shakka akwai abin da ka ajiye a zuciyarka na ɓacin rai ga shi nan har ajiyar zuciya kake. Fada mini abin da yake damun ka?”

Da kyar ya nisa sannan ya ce, “Gidan su Zaliha ne!”

“Me ya faru a gidan nasu?”

“Jiya ne na je muna tsaye da ita, sai Umma ta fito ta rika fadin wasu zantuka marasa daɗi a kaina, daga karshe ta ce Zaliha ba sa’ar aurena ba ce, an yi mata miji na daina yaudarar ta.”

Cike da mamaki Inna ta ce, “Umman ce ta fada maka hakan? Babu mamaki, biri ya yi kama da mutum.

Sheƙaranjiya da muka hadu a gidan yini tana kallo na ba ta iya yi mini magana ba, sai ni na sauke girman nawa na yi mata, ta amsa mata mini a dakire. Amma ina maigidan yake?”
“A lokacin bai kai ga dawowa ba.”

Jinjina maganar kawai Inna take, ta ma rasa me za ta ce masa, da kyar ta iya cewa, “Ka san me nake so da kai? Za ka ji ciwo sosai a ranka, amma ka dauki dangana kuma kada ka sake zuwa din, In Sha Allah Ubangiji zai musaya maka da mafi alkairi. Ka yi hakuri kada ka sa wannan abu a ranka har ya dame ka.”

Inna na rufe baki sai wayarsa ta fara ruri, yana dubawa ya ga Abban Zaliha ne. Sai ya ki dagawa, ta yi ruri har ta yanke. Ya sake kira a karo na biyu Inna ta ce, “Waye ne ka amsa mana.”

“Mahaifin Zaliha ne.” Kafin ya gama ba wa Innar amsa kiran ya sake katsewa. Abba bai yi mamakin kin amsa masa wayar ba, ya riga ya san duk inda ran yaya Abdul ya kai dubu to ya baci. Kuma dole ne ya nuna fishinsa a kansu, don haka sai bai sake kiran ba.

Bayan kamar mintuna biyar sai ya kira, Inna ta ba wa yaya Abdul umarni da ya amsa su ji me zai ce kuma? Duk da dai ba shi ne ya yi abin ba kuma bai sani ba sai dai labari da ya iske.

“Assalama alaikum!” yaya Abdul ya fada bayan ya ƙara wayar gindin kunnuensa.

Daga can cikin wayar Abba ya ce, “Wa alaikums salam!”

“Barka da rana ya aiki?” Yaya Abdul ya gaishe shi a takaice.

“Lafiya Alhamdulillah! Na ji abin Saratu ta yi jiya da dare kafin na dawo.”

Yaya Abdul ya yi sauri ya fito da sautin maganar waje domin Inna ta ji kai tsaye.

Abba ya ci gaba da fadin, ” Watau a zahirin gaskiya ban ji daɗi ba sam! Abin da nake so da kai ka yi hakuri, wannan kuskure ne na mata da shiga sabgar da ba ta shafe su ba. Wannan sam ba huruminta ba ne ko kadan. Abin da ya dace wanda yarinya take so shi ne daidai, auren dole ko ada ana ba wa mutum dama bare kuma zamanin yau. Ka kwantar da hankalinka ko Inna kada ka fadawa abin da ya faru, In Sha Allah Zaliha matarka ce. Wannan haɗi ne na Ubangiji.”

Yaya Abdul ya sauke wani gajeren nishi tare da cewa, “To shike nan Abba ba komai na gode!”

“Yawwa madalla! Allah Ya yi muku albarka, ka gai da mini da Innar.”

Cikin kalar tausayi yaya Abdul ya dubi ta kamar zai yi magana sai kuma ya yi shiru. Da dukkan kulawa ta ci gaba da kwantar masa da hankali da nusarwa ta hanyar kalamai masu sanyaya zuciya, sai da ta fuskanci ya dan rage damuwa ya fara cin abinci.
*****

<< Ko Wace Kwarya 7Ko Wace Kwarya 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.