Sauri take gudun kada wani ya ganta, duk da duhun daren da ake amma haka ta rika zabga sauri tamkar zata tashi sama. Tsak! Ta tsaya cike da tashin hankali ganin kamar mutum ya gifta ta gabanta cikin babaken kaya. Ja da baya ta fara yi gabanta na tsananta faduwa. Hasken motar da ta fara hangowa ne ya saka ta sauke ajiyar zuciya tare da kara saurin barin wurin, domin bata yadda da inda take ba. Bude gidan baya tashi ta shige inda Ninaah da Zuzuuh suke sai ita cikon ta uku. A gaba kuma Fu’ad ne ke tuki sai Ammar da Haris a kujerar mai zaman banza. “Beb kin so fa ki bata mana lokaci, domin mun jima a wurin nan.” Ta tsinkayo Muryar Fu’ad na fada. “Ba zaka gane bane, baro cikin gida a irin wannan lokacin ba ƙaramin tashin hankali bane.” Fadar Ibina “Bari ke dai Ibina! Da kyar na baro gida, kadan ta hana asirina ya tonu.” Cewar Zuzuuh. “Haba Guy’s! Mu je mana ni fa na kagara mubar garin nan kafin asirin mu ya tonu, don kunsan ko wane lokaci ana iya kama mu, ga jirginmu karfe bakwai na safe zai tashi.” Ihu suka ɗauka a tare ganin suna daf da cimma burinsu. Gudu suke tsalawa cikin duhun daren ga ruwan sama da bai karasa daukewa ba. Karfe dayan dare suka sauka garin Abuja, kai tsaye Hotel suka nufa domin anyi masu booking din komai, gajiyar da suka kwaso ita ta saka suka kwantawa da wuri zuciyoyinsu fal da farin cikin ƙudurinsu. Karfe bakwai suka farka a gigice domin a tunaninsu sun maka sai Haris ke fada masu sai fa takwas jirginsu zai tashi. Shirye suke cikin kaya na alfarma, wanda kallo daya zakai masu ka fahimci gayu da kuma wayewa ta bi jikinsu. Abinda Ninaah bata taɓa ji ba shi ne ta fara jinsa, wato tuhumar kanta anya ta yima iyayenta adalci? Sai kuma wata zuciyar ta fara fada mata kada kuyi wasa da cikar burin ki, domin kuwa ranar huce takaici kai ya cire. Sanarwa aka fara don haka a tare suka shiga jirgin da yake niyyar tafiya kasar Umbull
Ammar ne ya fara magana “Ni fa a matse nake mu isa kasar nan kodan mu bazama ganin abubuwan mamaki” Haris ne ya karbe zancen “Ni dai damuwata daya ce, kada muje mutanen nan basu zo tarbar mu ba” “haba dai! Ai in kaga ana rashin daukar Costomers da muhimmanci to a naija ne, amma can mu gama magana da Company nin sune da zasu bamu wurin zama da komai hatta duk wuraren da zamu ziyartan su zasu kai mu” Fu’ad ya karasa maganar. ” Yau fa ba zanyi bacci ba, haba dai gani a kasar da nafi kauna” cewar Ninaah. Tuntsurewa suka yi da dariya a tare. Nan suka cigaba da labari har jirgi ya sauko. Babu bata lokaci aka zo aka dauke su. Kamar yadda aka nuna masu wurin a online kafin zuwan su, a haka suka samu masaukin nasu. Katon daki mai dauke da gadaje shidda sai kujeru da sauran abubuwan bukata babu abinda babu. Tsalle Ibina tayi ta faɗa saman gadon tare da furta. “Rayuwar ‘yanci Assalamu alaikum!” Tuntsurewa da dariya suka yi suna mata shegantaka cike da kaunar juna. “Kunga! Kada ku takurama masoyiya ta” cewar Fu’ad. “Fadama wanda bai da masoyi a kusa, Ammar ka fa ji abinda yake fada ko” Zuzuuh ta karasa maganar tare da kashe mai ido. “Beb zo ki kwanta ki huta, kada su dawo kan mu.” Haris ya fada tare da kallon Ninaah.
“Jama’a a fidda batun wasa ni fa yunwa nake ji.” Cewar Ninaah “Kura ci da gashi, daga saukar mu ko wanka ba muyi ba sai ki hau ciye-ciye.” Cewar Ammar, Haris ne ya cabe zance. “Kada fa ku sako min masoyiya a gaba, kinga rabin rai je ki ci abinci kiyi nat! ” Shigowar ma’aikatan wurin dauke da abinci mabanbanta ne ya saka su yin shuru tare da hadiye yawu. “Wow! Wannan rashana duk mu kadai” Fu’ad ya karasa maganar yana kokarin daukar abincin. Saukin rike ma shi hannu Ammar yayi “kaga Malam mu je kowa yayi wanka, muyi sallar azahar sannan a Ci. “Ci ya na gaba da sallah fa” “mu je kawai” Ninaah ta faɗa. Ɗaya bayan ɗaya suka yo wankan tare da gabatar da sallah domin lokacin azahar ya shiga. Nan fa suka fara shirin cin abinci “Drink din nan ban yadda da shi ba, kamar giya.” Ibina ta faɗa tana jujjuya lemun. Amsar shi Haris yayi yana kare ma shi kallo “Da gaskiyar ki fa, to amma sun rubuta non alcohol.” “Ku miko shi nan ku gani, tunda har suka rubuta ba giya a ciki tabbas sai na sha” Ammar ya karasa maganar tare da bude kwalbar ya kafa mata kai. “Zuzuuh nake don haka masoyi gama sha nima sai nasha, in mutuwa ce mu mutu tare, bare ma nasan bamu mutuwa sai munyi aure” Dariya suka kwashe da ita a tare ganin da gaske Zuzuuh take don har ta karasa shanye lemun. Ma’aikacin wurin dake laɓe yana kallon duk abinda ke faruwa murmushin mugunta ya saki ganin sun sha lemun. Tafiya ya yi domin ya sanar ma Shugabansu ce wa an samu waɗan da suka sha. Kamar yadda aka tsara karfe hudu na yamma cikin shigar kananun kaya suka fito motar Hotel din ta dauke su. Ba ƙaramin yawo suka yi ba domin basu dawo gida ba sai dare. A gajiye suka yi wanka suna labarin abubuwan da suka gani a fitar su. Zuzuuh ce tari ya sarke, sannu suke jero mata cike da tausaya wa. Duk Ammar ya rude, bayan ya lafa ta sha ruwa tana mayar da numfashi. Daki yayi tsit domin sun tsorata matuka, babu fa abinda ta ci amma ta hau tari ga idanunta lokaci daya sunyi jajur. Miƙewa tayi da nufin ta shiga Toilet, jirin da taji yana dibarta ne ya sakata dafe bango. Tamkar wadda aka fizgo haka suka ga ta baro bangon tare da yanke jiki ta zube ƙasa tana shure-shure. ƙasusuwanta suna wata irin lankwashewa. Cikin hanzari Ammar ya nufi inda take, sai dai kafin ya ƙarasa sai gani suka yi shi ma ya yanke jiki ya fadi. Cike da tashin hankali suka rasa wa zasu taba domin su biyun sai shure-shure suke. Cikin karfin hali Fu’ad ya kira daya daga cikin ma’aikatan wurin suka nufi su Ammar. Shure-shuren ya tsaya sai dai jini ne ke fita ta hanci da kuma bakinsu. Wata mace ce ta shigo dakin dauke da ɗan karamin akwati, na bada taimakon gaggawa. Nurse din saitin fuskar Zuzuuh ta kanga kanta don taji shin tana raye, sai dai kafin ta dago kanta ji tayi Zuzuuh ta cafke wuyanta tare da kafa mata hakoranta da suka yi tsini tamkar wuka. Ihu Nurse din keyi tana neman taimako, su Haris ja da baya suka fara yi cikin zallar rudewa. Ba zato ba tsammani sai gani suka yi Ammar ya daka tsalle tamkar an harbo shi a kibiya. Nan fa suka fara gudun ceton rai, kafar Ibina Ammar ya fizgo da karfin tsinya tare da jefa ta da daki bango. Ƙarar data saki ita tayi sanadin dakatawar guje-gujensu. Ibina ce a gefe kwance cikin jini kanta ya fashe jini na tsartuwa…