Skip to content
Part 13 of 18 in the Series Ƙuda Ba Ka Haram by Sadik Abubakar

Su Humaira na wanzuwa cikin makarantar, ta rufe Binta da fada ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba, akan me Bintar za ta karbi kudin aikin da Sadik ya dawo musu da shi?

Cikin sanyin murya Binta ta ce: “Don Allah ki saurara mana, me yasa kike haka ne? Mutumin nan fa ba yaro bane irin shashashan nan, da ganinsa ya san me yake yi ba shiririta bace a ransa. Sannan kuma ki duba shi ma fa malami a wannan makaranta, bai kamata ki yi masa irin wannan ba tunda har ya fesar miki da abin da ke zuciyarsa tare da neman yardarki. Ina ganin indai ba kina da wani ba to ki ba shi dama.”

“Ke dakata don Allah, haka kawai daga ganin mutum sai ki ce na na shi dama. Ban san shi ba ban san halinsa ba.”

“Hmm! To ai duk wanda za ki hadu da shi a karon farko dama ba ki san halinsa ba, sai a hankali za ki fahimta idan kin ba shi dama.”

“To gaskiya ni ba zan iya sauraren sa ba bare ma har na ba shi dama.”

“Hmm! Wulakanci dai babu kyau kuma ba shi da dadi, duk mutumin da karya bullensa ya nuna yana son ki koda wasa yake bai kamata ki ji haushinsa ba ko ki yi wulakanci.”

“Kin ga ya isa kin ji, ni fa ba wulakanci na yi masa ba, kawai dai ba zan iya yin soyayya da shi bane. Ina fatan kin gane?”

“Wane ba za ki iya tsaya wa ki yi soyayya da shi ba? To mene ne hakan idan ba wulakanci ba? Mene ne da shi na kushe wa? Watakila ki ce ya yi miki tsufa ko? To ni dai gaskiya ina ba ki shawara ki yi tunani.”

“To wai ke da kika damu da wannan maganar haka, kin san matsayinsa ne? Ita din wannan macen da suke aiki tare wace? Na tabbatar dai ba kanwarsa bace, domin da kanwarsa ce ba zai gaza cewa mu bar kudin aikin ba a gabanta kyauta ya yi mana. Amma kina gani sai dai ya yi mana alama da hannu. Nima shawarata gare ki idan kina son sa bisimillah! Allah ya taimaka, ni na yafe.”

“Me kike fada haka Humaira? Ke fa kawata ce kuma ke ya nuna yana so ba ni ba, kuma ki sani don na yaba da halinsa ne yasa nake ba ki shawara akan ki saurare shi.”

“To shi kenan na ji tunda shawara ce kike bani ba umarni ba na gode.”

Murmushi kawai ta yi ba ta sake tofa komai ba, a ranta take cewa: “Haka lamarin Ubangiji yake, mai wuka baya samun nama.”

Cikin makaranta suka nutsatsa kai tsaye suka nufi ofisoshin da za a saka musu hannu akan takardun nasu. To wannan kenan.
*****

SHIN WAYE SADIK? WACECE MEENAT?

To kamar dai yadda ya gabata a baya shi Sadik shi ne mamallakin wannan café, sannan kuma shi din malami ne a ita wannan makaranta. Miji ne ga wannan matar wato (Meenat) da suke aiki tare. Ita ma daliba ce a makarantar, tana matakin karshe na babbar Diploma da take yi wato (HND). ‘Yarsu daya da Sadik sai kuma wani cikin da take dauke da shi.

Sadik ya yi amfani da wannan dama ta karatun da take yi a makarantar wajen taimaka masa a bangren café din. Gwanin sha’awa suke tafiyar da rayuwarsu, kusan kowa ya san cewa matarsa ce shi yasa ma ba kasafai ta fiye zantuka da maza ba, matsawar ba aiki mutum ya kawo ba. Tana da tsananin kamun kai da kunya, sannan ta iya mu’amala da jama’a masu mabanbanta tunani. Wannan kenan.

Shi kuwa Usman a nasa bangaren sam ba ya nuna damuwarsa da irin zaman doya da manjan da suke yi shi da matarsa, a yanayinsa ba shi da niyyar daina wannan mummunan hali nasa. Kawo yanzu dai ya yi nasarar mallakar tunanin Humaira fiye da tunanin duk wani mai tunani, ta kai ta kawo Humaira har so take yi ya ce yana da bukatar su haɗu. Ba wai kwaɗayin kuɗin da zai ba ta ba, ita ma yanzu tana matukar buƙatar haɗuwa da shi domin ta fara jin daɗin harkar da suke tamkar matar aure haka take bukatar namiji.

Wannan bukata ta sa ta matsu sosai weekend ya zo su hadu a hotel din kamar yadda ya tsara musu. Ranar Juma’a da dare ta yi masa flashing domin ta ji shin maganar fitar tana nan ko kuma ya sanya shawara. A nata tunanin da zai gane ma gara su rika hadu wa a hotel din ya fi mata sirri akan ta rika zuwa gidan Antynta, wannan shi ne burinta.

Dakiku ba su wuce goma ba da yi masa flashing ya biyo lambar, ta daga tare da yin sallama, “Salama alaikum.”

Usman ya amsa, “Wa alaikumus salam, ranki ya dade.”

Cikin sigar murmushi ta ce: “Ina yini ya aiki?”

“Lafiya kalau aiki mun gode Allah. Ya gidan ya su Mummy? Da fatan kowa yana lafiya?”

“Kowa kalau Alhamdulillah!”

Shiru na ‘yan dakiku suka yi ba wanda ya ce komai, zuwa can Usman ya yi murmushi mai ɗan sauti tare da cewa: “Hmm! Ya promise ɗinmu? Gobe Asabar ko kuma mu bari sai Lahadi, yaushe kike available?”

Murmushin ita ma ta yi, ya tabo mata abin da take muradi. Nisa wa ya yi tare da cewa: “Duk yadda ka ce ayi.”

“E to ni dai I am available, da ma ke nake tunani ko kina da uzuri. To babu damuwa goben ya yi. Kamar wane waje kike so mu je?”

“Hmm! To ni ina na sani, wannan ai sai kai. Duk inda ka ce haka za ayi.”

“Okay to bari mu samu hotel na outside ko, inda babu jama’a sosai ina ga zai fi. Idan Allah ya kai mu goben misalin karfe 10:00am na safe zan fito da motata, zan tsaya a daidai Gidan Manbayya sai ki hayo Adaidaita Sahu ki zo. Amma fa kin san dole ne ki zama very strict saboda mutane, if possible kawai ki saka irin kyallen nan baki wanda yake rufe muku fuska.”

Murmushi ta yi hade da cewa: “Hmm! Shi ke nan babu matsala insha Allah zan yi hakan.”

“Yawwa good girl! Shi yasa nake kara son ki, kina matukar birge ni akwai ki da saurin fahimta.”

Dariya ta yi ba tare da ta sake cewa komai ba, sallama ya yi mata hade da huro mata sumbata ta cikin wayar.

Wa iyazubillah! Kai jama’a mu kiyayi Allah fa. Mutanen duniya sai a hankali, ku ji yadda ake kulla wa da tsara inda za a hadu ayi zina a saba wa Ubangiji. Abin takaici wai suna tsoron kada mutane su gan su, sun manta cewa babu abin da mutanen za su iya yi musu koda sun gan su domin ba mutane bane suka hana yin zinar. Shi din wanda ya hana zinar yana jin su yana ganin su, amma sun manta da hakan.

Wato tsoron mutane suke yi fiye da tsoro wanda ya samar da mutanen. Ya Allah ka sa mu fi karfin zukatanmu, Allah ka kore mana sha’awar haramun komai dadinta, Ya Ubangiji ka wadata zukatanmu da abin da ka mallaka mana. Ya Allah masu lalata ‘yanmata ka shirye su, ka ganar da su tafarki madaidaici. Duk wata budurwa Allah ka ba ta miji na gari me tausayi, Allah ka shiryar mana da zuri’a amin summa amin.
***

Washegari da safe, misalin karfe 9:30am Usman ya yi shirin da zai yi domin hadu wa da Humaira kamar yadda ya tsara. Duk da kasancewar ba wani zaman dadi suke shi da Anty Sakina ba, amma yakan zauna a gidan duk ranakun weekend. Koda zai fita sai dai wajen yammaci haka koda kuwa ba za su kula juna ba zai zauna ya shari barcinsa da ya saba.

To amma a yau babu wannan batu, shirin da ya yin ne yasa Anty Sakina ta magantu da cewa: “Ina zuwa da safe haka?”

Ba tare da ya dube ta ba ya mayar mata da martani da, “Zan fita ne, ko akwai wani aikin da zan yi miki ne idan na zauna a gidan?”

“A’a ba aikin da za ka yi mini, a dawo lafiya.”

Ita ma Humaira a nata bangaren shirin ta yi tsaf! Sai dai ta rasa wace karya za ta yi wa Mummy domin ta samu damar fita? Ba dai zai yiyu ba ta yi karya da makaranta tunda yau Asabar ce ba a karatu sannan kuma ba ma su fara lakca ba bare ta ce suna yi har a Asabar din. Saboda haka sai ta hada karya da kawarta Binta, cewa wai za ta je gidansu ta karbo wasu takardu.

Ba tare da wata tuhuma ba Mummy ta amince mata sakamakon ta fuskanci alamun tarbiya da kamun kai har ma da nutsuwa tattare da Binta, kai a zahiri ma ta yi farinciki kwarai haduwar Humaira da Binta a matsayin kawaye abokan karatu.

Humaira na fito wa daga lungunsu  ta tsayar da Mai Adaidaita Sahu ta fada masa cewa, daidai Manbayya House zai kai ta. Da yake babu wani nisa sosai ko ciniki ba su tsaya yi ba, nan da nan ya yi kai ta. Gabanin su karasa Usman ya kira ta ya ce: “Ina nan fa na karaso tun dazu, ke kawai nake jira.”

Cikin murmushi ta amsa da cewa, “To nima gani nan daf da wajen minti daya ma ya yi yawa zan karaso.”

“Okay, to idan kin karaso za ki ga motata daga can gaba kusa da kwanar layin ‘yan Azara, ina ciki kawai ki taho ki shigo.”

“To shi kenan babu damuwa.”

Tana sauke wayar, Mai Adaidaita Sahu ya shawo kwanar Gidan Manbayya, daidai gate din ya tsaya. Ta biya shi kudinsa ta fito, kai tsaye ta nufi wajen motar Usman ta bude ta shiga kamar yadda ya umarce ta. Tana shiga ya yi wa motar key suka yi gaba.

“Gaskiya kina kula da lokaci sosai, hakan na birge ni. Kina mutunta lokaci, ba ki taba ba ni lokaci ba kika saba.”

Hirar da Usman ya bude musu ke nan bayan sun fara tafiya murmushi kawai Humaira ta yi ba ta ce komai ba, ya ci gaba da cewa: “So ya kike y garin ya a jin dadi?”

“Hmm! Jin daɗi ai sai ku manya.”

Dariya ya yi tare da cewa, “Wane mu, ku din dai ai ku ne manya. Idan babu ku to mu ma babu mu. Karyar kiri ta mai ce.”

“Hmm! Haka dai ka ce, mu ma takamar tamu taku ce.”

Tafiya suke suna hira tamkar mata da miji har suka isa wani hotel da ake kira GREEN DESERT, a shataletalen Hajj Camp (sansanin alhazai na Kano). Hotel ne mai matukar kyau da tsari sannan kuma akwai sirri a wajen. Yana daga cikin wani lungun quarters, ba kowa bane zai fahimci akwai hotel a wajen sai in ya lura da sunansa da aka rubuta daga saman ginin.

Kai tsaye Usman ya tinkari babbar kofar hotel din, mai gadi ya bude masa ya shige ya yi parking, suka fito. Reception ya nufa ya biya kudin daki VIP sannan suka wuce. Suna shiga dakin ya rage kayan jikinsa ya shiga ya watsa ruwa, bayan ya fito Humaira na zaune a bakin gado ya yi oda aka kawo musu drinks da dan abin taba wa suka ci kafin a shiga sha’ani.

Bayan kamar mintuna talatin zuwa arba’in (30-40 minutes) da barin Humaira gida, Binta ta shirya da nufin kawo mata ziyara. Ita kam Binta ba ta saba da yin karya ba idan tana son fita zuwa wani wajen, duk inda za ta je fada wa Baba Abu take sam ba ta boye mata, bare ma ba cika yawace-yawace marasa kan gado ta yi ba. Don haka kai tsaye ta sanar da kakar ta ta cewa, za ta je gidan su Humaira. Addu’a Baba Abu ta yi mata da cewa: “To babu komai, ki kula sosai a dawo lafiya Allah ya kiyaye.”

“To Baba insha Allah zan kula, sai na dawo.”

Ta fada tare da mikewa ta fito, kai tsaye ta nufo gidan su Humaira, ta shiga ta gaida Mummy cikin ladabi da girmama wa. Mummy ta masa gaisuwa ta dora da cewa: “Sabani kuka yi kenan, yanzun nan Humaira ta tafi can gidan naku.”

Kan Binta sunkuye ta ce: “Ikon Allah, to bari na yi sauri na koma can din. Na gode Mummy.”

Mikewa ta yi ta fito, tana barin lungun su Humairar ta kira wayarta, waya ta yi ruri ta yanke ba a daga ba. Ta sake kira waya ta sake yin ruri dai har ta katse ba a daga ba.

“To ko ta saka wayar ne a silent ne? Ana ta kira shiru babu amsa.”

Binta ta fada yayin da take sake jaraba kiranta a karo na uku, haka dai waya ta yi kara har ta sake yanke wa. Duk kiran wayar nan da Binta take yi har sai uku ba kakkautawa, babu wanda Humaira ta ji. Wayar na ajiye kan drawer kusa da gadon da suke kwance ita da Usman. Hankalinta ya gama gushe wa, sha’aninsu kawai suke yi, koda yake shi Usman ya ji wannan kiran na karshe amma bai kula ba.

Ita kuwa Binta tunani ta fara yi cikin ranta, “Anya kuwa lafiya wannan baiwar Allah, ana ta kiran waya amma shiru. Bari na sake jarabawa ko Allah zai sa a dace, daga wannan kiran dai idan ba a amsa ba to kila wayar tana silent kuma ba ta kusa da ita.”

Kiran ta sake yi a karo na hudu, sai a lokacin ne Humaira ta ji karar wayar kafin ta yi wani abu wayar ta katse.

“Ina zuwa na ji kamar ana kira na a waya ko?”

Ta fada tare da yunkura wa ta janye jikinta daga jikin Usman, mika hannu ta yi ta dauki wayar. Dubawar da za ta yi ta ga missed calls har sau hudu, bude wa ta yi ta ga Binta ce, kira ta danna ta bi ta, Binta ta daga wayar da cewa, “Ina fatan dai ba ki taho ba ko? Ki jira ni yanzu zan karaso, sabani muka yi.”

Cikin sigar fargaba Humaira ta ce: “Ina za ki karaso?”

<< Kuda Ba Ka Haram 12Kuda Ba Ka Haram 14 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×