Skip to content
Part 15 of 18 in the Series Ƙuda Ba Ka Haram by Sadik Abubakar

Da yake lakca Sadik zai shiga, dalibai na jiransa, bai tsaya lallai sai Humaira ta yi masa magana ba. Binta ce ta saurare shi ta rika amsa masa, kuma ta ji nasihar da ya yi musu sosai, don haka sai ta ce,

“Insha Allah za mu kiyaye, za mu kula sosai ba za mu yi wasa ba. Mun gode Allah ya saka da alkairi Allah ya kara girma.”

Sadik ya sara zai tafi kenan, Binta ta sauri ta mike tare da karbar takardun dake hannunsa tare da cewa, “Kawo na rike maka.”

Mika mata ya yi yana murmushi sannan ya wuce gaba tana biye da shi. Wani irin kududun bakin ciki ne ya turnuke zuciyar Humaira, gaza yin magana ta yi sai wata zazzafar harara da take aikawa Binta. Ita kuwa ko a jikinta sam ba ta san tana yi ba, wai kunu a wani gida.

Binta biye take da Sadik tiryan-tiryan har cikin hall din da zai gabatar da lackar, ta dora masa takardun akan Lecture Stand, sannan ta fito. Dawowa ta yi wajen da ta bar Humaira, tana karasowa ta ga fuskar Humairar ta sauya, dama ta yi tsammanin hakan don haka ba ta wani damu. Ce mata ta yi, “To mu ci gaba ko?”

Banza Humaira ta yi da ita ba ta tanka mata ba, ta sake cewa, “Ya ya lafiya dai? Na ce mu ci gabaa ina muka tsaya ko kin gaji ne? ”

“Ban sani ba, kin ga ya isa haka ba na bukata.”

“Wai mene ne kuma ya faru don Allah? Ko saboda na karbar wa Sadik kayan hannunsa na kai masa aji shi ne abin laifin?”

“To akan me za ki karba ki kai masa? Shi ba shi da hannu ne? Wannan ai shisshigi ne da zubar wa da kanki daraja. Wallahi idan ba ki yi wasa ba sai ya yi miki wulakancin da za ki raina kanki. Wannan ai zubar da aji ne.”

Ta karasa maganar da yin tsaki.

“Haba Humaira ya ya za ki yi masa wannan mugun zato haka? Gaskiya da ganin Sadik mutumin kirki ne, hakan sam ba zai taba zama halinsa ba. Ki duba shawarwarin da ya ba mu fa, tunda muka zo makarantar nan waye ya taba saurarenmu bare har ya ce mana ga yadda tsarin makarantar yake idan ba shi ba? Gaskiya ni dai na dauke shi a matsayin yayana, ba zai ba ni shawarar da za ta cutar da ni ba. Kuma na san kema kin fahimci hakan, kawai idan ba kya son sa ne to ki ce ba kya son sa amma yana da kyawun mu’amala sosai. Ko ba za ki yi soyayya da shi ba, to kema ki dauke shi a matsayin yayanki, zai fi wannan wulakanci da tsanar da kike masa babu dalili.”

“Hmm! Waye zan dauka a matsayin yayana din? Allah ya sawwake, ke din dai da kike kalen dangi ki je ya zama yayan naki. Kodayake ba ma maganar yaya a nan, kawai son sa kike yi ki fito ki fada masa tun da wuri. Amma ki sani Meenat da kika yi gani suna aiki tare ba kanwarsa ba ce, matarsa ce dansu daya da shi, kuma ki lura da ita sosai yanzu haka ma ciki ne da ita. Idan ba ki yarda ba kina iya tambaya.”

Binta ta dan sauya fuska tare da cewa, “Amma gaskiya ban yi zaton za ki yi mini irin wannan fahimtar ba, yanzu na rasa wanda zan ce ina so sai wanda ya nuna yana son ki? Haba Humaira ke fa kawata ce, ba ma kawa ba ke aminiyata ce. Ai koda wasa bai kamata ki yi tunanin zan yi soyayya da mutumin da ya ce yana son ki ba.”

Ta karasa maganar da saukar wasu marayun hawaye masu dumi akan kuncinta.

Humaira ta yatsina fuska tare da cewa, “Kin ga ki rufa mini asiri don Allah kada mutane su zo taru akanmu ,ni ban fada miki maganar da za ta saki kuka ba. Kawai na ce idan kina son sa ki sanar da shi, ni dama ba son sa nake ba. Daga fadar haka kuma sai ki fara kuka, to Allah ya huci zuciyarki baiwar Allah.”

Sun jima zaune a wajen babu wanda ya sake tankawa, sai misalin karfe 11:55am ,wato saura mintuna biyar kenan su shiga lakca ta gaba, Binta ta ce, “Ki tashi mu karasa lecturer venue din saura mintuna biyar.”

Mikewa suka yi suka nufi theater inda za su yi lakcar.

A ranar nan dai  haka suka yini babu walwala, ba kamar yadda suka saba ba. Lokacin da rana ta yi sosai bayan sun sake fitowa daga lakca misalin karfe 2:00pm ,suka yi sallah sannan suka nufi wajen cin abinci. Binta cewa ta yi, ta koshi ba za ta ci ba, da kyar Humaira ta rarrashe ta ta hakura ta dan ci kadan. Sam a yinin nan Humaira ba ta sake ganin fara’ar Binta ba.

Bayan an tashi daga makarantar suna dawowa gida ne Humaira take cewa, “Wai dama haka kike da fishi? Dan karamin abu ki rike shi a ranki? Ni wallahi ba don wannan fishin da kike ba har na manta da komai ma.”

“To ai ke kika ce, ni ta yaya zan manta? Yanzu idan wani ne ya zo ya fada miki cewa ina son Sadik, duk rantsuwar  da zan yi ba yarda za ki yi ba. ”

“Ta ya ya za ki ce ba zan yarda ba?”

“Ga shi kuwa kin tabbatar mini da kanki kina zargina a kan ina son sa. To ni duk abin da kika ga na yi masa ba soyayya ba ce tsakaninmu, ina yi masa ne saboda kirkinsa kuma shi din babban mutum ne yadda ya nuna yana son mu yi karatu ba wasa ba, to gaskiya zan rika bin shawarwarinsa kuma ba zan iya rabuwa da shi ba. Sannan ba zan iya ganinsa a cikin makarantar nan ba na dauke kai ban gaishe shi ba.”

“To na ji, kuma ki sani nima ba cewa na yi kada ki kula shi ba, amma ni dai kada ki sake cewa sai na saurare shi. Ba na ra’ayinsa, kada kuma ki ce wulakanci nake masa kin gane ko?”

“To shi kenan insha Allah ni kuma ba zan sake cewa ki kula shi ba, kina da gaskiya ba a so dole. Allah ya zaba masa mafi alkairi wacce za ta fahimce shi kuma ta ba shi lokacina. Ke ma Allah ya mafi alkairi.”

“Amin ya Allah, yanzu kika yi magana me kyau.”

Ire-iren zantukan da suke yi kenan marasa dadi har aka gidan su Binta ta sauka sannan aka wuto  da Humaira, dama haka suke yi kullum yayin dawowa.

            *BAYAN WATA DAYA*

Damuwa haɗe da tunani sun fara yawaita a zuciyar Anty Sakina, har hakan ya fara bayyana a jikinta, domin duk ta bi ta rame ta yi duhu. Babu rashin ci ko sha, saboda ko da Usman bai kawo kayan abinci ba, takan saya da kudinta tun da tana aiki tana daukar albashinta. To sai dai ta rasa kwanciyar hankali ne, Allah ya jarabce ta da miji mai halin dan bunsuru.

Babu shakka tsananin damuwar da Usman ya jefa ta a ciki ne ya sabbaba mata lalacewa, kallo daya za ka yi mata ka fahimci akwai wadatar damuwa a ranta koda ba ta fada ba.

Wata ranar Asabar din karshen wata ce, Anty Sakinar ta shirya domin kawo ziyara gida, da ma takan zo duk bayan watanni biyu zuwa uku ta gaida su Mummy. Takan bari sai an yi albashi sai ta yo wa su Mummyn ‘yan saye-saye na dan abin da ba a rasa ba, duk dai neman albarka ne da daukaka a rayuwa. A wannan zuwan ma haka ta yi, ta hado sha tara da arziki ta kawo wa mahaifan nata.

Bayan ta shiga an gaisa, jim kaɗan ana zaune ana hira, Mummy ta ƙare wa Anty Sakina kallo sosai ta ga duk ta fada sannan ga shi ta yi ba ki. Duban ta ta yi ta ce, “Wai ba kya jin dadi ne? Ko rashin lafiya kika yi ne? Na ga kamar kin rame.”

Ita da kanta Anty Sakina ta san ba haka yanayinta da jikinta suke ba, babu shakka ta rame din domin duk lokacin da ta tsaya gaban mudubi takan ga hakan. Sannan wasu kayan sawarta da suke dan kama jikinta ta ji yanzu sun yi mata sakwa-sakwa, alamar lallai ta ragu din. Da yake mace ce me tsananin juriya da rashin son bayyana damuwarta ga wani sai ta yi murmushi tare da cewa, “E wallahi kuwa na dan yi zazzabi ne kwana biyu.” “To shi ne ba ki fada ba? Ai da ko Humaira ce na tura ta duba ki, gaskiya ki rage zurfin cikin nan na ki. To yanzu da ba ki samu sauki ba haka za ki ci gaba da zama da ciwo?”

“Hmm! Mummy kenan, zazzabi ne fa kawai ba wani abu ba, kuma ba na son na fada muku hankalinku ya tashi.”

“Wannan ba dalili bane sam kada ki kuskura ki sake yin irin wannan, duk abin da yake damunki ki sanar da mu ko ban zo ba ai ga ‘yar uwarki nan ba sai ta zo ba ta dan taimaka miki wasu ‘yan aikace-aikacen. Kina gudun kada hankalinku ya tashi ke kuma sai ki zauna cikin tashin hankalin kul! Kika sake aikata irin wannan.”

“To Mummy insha Allahu ba zan sake ba, ki yi hakuri.”

Yini Anty Sakina ta yi a gidan kamar yadda ta saba, duk lokacin da ta kawo musu ziyartar ba ta tafiya sai la’asar sakaliya. Tun lokacin da ta shigo, Humaira ta gaishe ta, sai ta koma dakinta ta fara karatun karya, ba ta son ta rika hada ido da Anty Sakina, gani take kamar za ta gane wani abu. A takaice dai kunya hade da tsoro ne suka hana Humaira zama a yi hirar da ita.

Ta nan a dakin nata ita kadai gogan lalataccen gari ya kira ta a waya, kin dagawa ta yi har ta katse. Ya sake harbo mata wani kiran nan ma ta yi ruri ta yanke ba tare da ta amsa ba, domin ba ta iya daga wayarsa idan tana cikin gida musamman idan ya kasance Mummy tana nan ko kuma idonta biyu.

Da ya ɗan numfasa da kiran ne ta samu ta rubuta masa sakon SMS kamar haka;

“Ka ga ban amsa maka waya ba ko? Wallahi ana ta hira ne kuma babu damar na fita waje ne.”

Tana tura masa ya karanta, nan take ya yi mata reply da,

“Okay that’s good! Na san dai yau ba za ki samu damar fita ba tun da ban sanar da ke ba tun jiya, sannan kuma ga Sakina ta zo na san za a ɗan yi hira ko?”

Yana gama rubtawa shi ma sai ya tura mata, ta karanta ta yi masa reply kamar haka;

“E hakane gaskiya ba damar fita sai dai wani lokacin ke nan.”

Tana tura masa ya karanta, ga reply din da ya turo mata,

“To shi ke nan, amma to kamar yaushe ne kuma za ki samu dama?”

Ita kuma sai ta rubuta masa reply da cewa,

“Bari ina zuwa, ɗan bani mintuna biyar.”

Hijabi ta saka ta fito falo ta iske su Mummy da Anty Sakina suna hira, cewa ta yi, “Mummy biro na ya tsaya ina rubutu, ba ni kuɗi na sayo sabo wani a kanti?”

“Hmm! ‘Yan boko manya, ya karatun? Da fatan dai kina ganewa ko?”

Anty Sakina ce ta fadi wannan magana cikin raha, murmushi Humaira ta yi sannan ta ce, “E babu laifi ina ganewa.”

Mummy ta ta ba ta naira hamsin ta ce, “To ga shi sai a je a sayo tun da ana gane karatun.”

Humaira ta karba ta fice daga gidan, barin kofar gidan na su keda wuya ta fito da wayarta ta yi ta wa Usman flashing, nan take ya biyo ta suka fara hira, ya ce, “Wallahi na so a ce yau din nan kin zo gida, tunda ba ta nan saboda kwana biyu ba mu hadu a gida ba ko ya ya kika gani?”

“E hakane, matsalar ke nan da ba ka sanar da ni ba da na san yadda zan yi.”

“To yanzu yaushe kike ganin za mu samu damar haduwa kuma?”

“Gobe Lahadi mana, ko kana da aiki ne?”

“Aa bani da aiki, sai dai ba a hotel nake son mu sake haduwa ba, kin san na fada miki sai muna dan sauya waje fa. Idan zai yiyu dai mu bari sai ranakun aiki da safe idan Sakina ta fita sai ki biyo ta nan kafin ki tafi makaranta ko kuwa ya kika gani?”

“E to, gaskiya matsalar kuma ba ni kadai nake tafiya makaranta ba, tare da kawata muke zuwa kullum tana biyo mini da safe. Sai dai ranar Laraba, da yake ba ma fara lacka sai rana ta yi.”

“Okay, to shi kenan mu bari sai Larabar ma kawai.”

Haka dai suka sake ajiye agenda cewa za su hadu ranar Laraba. Humairar ce za ta je can gidan Antyn ta ta, ta dan kwana biyu ba ta je ba sai dai haduwar hotel da suke kamar yadda Usman din ya ce.

Suna gama wayar ya ta karasa wani kanti ta sayo sabon biron ,ba wai don na ta din ya tsaya ba, da ma dai karya ce ta shirya don ta samu damar fita su yi waya da Usman ne. To wannan ke nan.

<< Kuda Ba Ka Haram 14Kuda Ba Ka Haram 16 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×