Skip to content
Part 16 of 30 in the Series Ƙuda Ba Ka Haram by Sadik Abubakar

Zainab ce take kwada sallama, wato makwabciyar Anty Sakina, wacce ta taba ganin Humaira a can baya ta fito daga gidan lokacin Anty Sakinar ba ta nan. Har ma ta shiga gidan ta duba ko Anty Sakinar tana gida ne? Sai ta ga Usman ne shi kadai har ma ya nuna rashin jin dadinsa. Ina fatan masu karatu sun tuno da wannan rana.

To da ta yi sallama ba a amsa ba sai ta karaso cikin gidan daf da kofar falon, nishin mace ta ji, irin alamar ana tarawa da ita. Gabanta ne ya yanke ya fadi, da sauri ta yo baya ta fita daga gidan tana salati da sallallami.

“Oh! Na shiga aljanna babu hisabi ni Zainab, Allah ya taimake ni da ban bude musu labule ba. Ikon Allah! Yau kuma Sakina soyayyar ce ta motsa da rana haka?”

Zama ta yi a dandamalin rumfar kofar gidanta tana jira zuwa jimawa kadan ko waya ne ta yi wa Anty Sakinar game da aron jakar da za ta karba.

Shi kuwa Usman ya haye ruwan cikin Humaira, sun jima suna ta abu daya ta hanyar sauya salo da style iri-iri har sai da suka samu gamsuwa da juna sannan ya daga ta. Mikewa ta yi a kwance kan kujerar domin ta huta, kimanin mintuna goma sha sannan ta tashi ta watsa ruwa ta sabunta kwalliyarta. Usman ya ba ta abin da zai ba ta ya sallame ta, likaf ta saka ta fito.

Zainab na nan zaune ta hangi fitowar Humaira fuska a rufe da likaf, ba ta gane ta ba sam saboda saurin da take yi ta bar layin kada wani ya ganta. Tsakanin mamaki ne ya lullube zuciyar Zainab, ta rasa wane irin tunani za ta yi, idan ta fara wannan sai ta saki ta kama wancan. Sake-sake ne kala-kala birjik a ranta, amma abin da ya tsaya mata a rai biyu ne; ihun da ta ji lokacin da ta shiga gidan da kuma wannan macen da ta fito fuskarta a rufe. To shin wacece wannan din? Kuma mene ne dalilin rufe fuskarta? Wadannan tambayoyin ne tsaye a zuciyar Zainab, a ranta take cewa,

“Idan har ba Anty Sakina bace ke waccan mu’amalar da Usman dazu, to babu shakka wannan matar ce.”

Zargin da ya fara karfafa a zuciyarta kenan, amma domin ta kore zargin tare da tabbatar da gaskiyar lamarin, sai ta lalubi lambar wayar Anty Sakina ta kira. Daga kiran Anty Sakina ta yi da cewa, “Don Allah Zainab ki yi hakuri mantawa na yi ban kawo miki jakar ba lokacin da zan tafi aiki, har kin shirya kenan?”

Juyawa Zainab ta yi ta dubi kofar gidan Anty Sakina sannan ta ce, “Laah! Kada ki damu ai tafiyar yamma zan yi, har kin ma dawo ban fara shiri ba.”

“Okay, to idan kuma kina son ki hada kayayyakin tafiyar ne da wuri, ki yi magana idan Usman bai fita ba sai ya ba ki, na fito da jakar tana nan a falo. Ki duba idan yana nan ki ce nace ya ba ki.”

“Aa wallahi har kin dawo ma, ai na fada miki ba da wuri zan tafi ba, na fi son na yi shigar dare.”

“To shi kenan sai na dawo din.”

“Yawwa a dawo lafiya.”

Ko shakka babu wannan wayar da suka yi da Anty Sakina ta kore mata shakku sannan kuma ta tabbatar mata da cewa macen banza Usman ya gayyato zuwa dakin matarsa ta sunna.

“INNALILLAHI WA’INNA ILAIHIR RAJI’UN. ALLAHUMMA AJIRNI FI MUSIBATI WAKHALIFLI KHAIRAN MINHA.”

Addu’ar da Zainab ta karanta kenan lokacin da ta ji wani dunkulallen abu ya taso daga tsakiyar zuciyarta ya zo daidai makogwaronta ya tokare, ya ki gaba ya ki baya. Wani zazzafan gumi ne ya fara karyo mata duk da cewa yanayin ba na zafi bane, iska ce ma take kadawa. Gwiwoyinta ne suka yi sanyi likis tamkar wacce aka dokewa su da sanda, gaza motsawa ta yi daga wajen, ta zama tamkar gunki. Yanayin bugawar zuciyarta ne ya kara sauri sosai.

Sam ta ma gaza yin tunani daya kwakkwara, da ta fara wannan sai ta bari ta shiga wani, akalla ta shafe kusan rabin awa a cikin wannan yanayi, daga karshe ta sauke wata zazzafar ajiyar zuciya tare da yin  addu’ar ,“Ya Allah ka shiryi dukkan wani namiji me neman matan banza.”

Yunkurawa ta yi da kyar ta mike ta shiga gida.

To Binta dai na can Café din Sadik suna hira da Khadija, har misalin karfe 12:50pm shiru ba ta ga keyar Humaira ba. Saura mintuna goma kenan su shiga lakca, sallama ta yi wa Khadija da cewa, “Saura mintuna goma mu shiga lakca, bari na karasa wajen.”

“To har lokacin ya yi kenan, ga shi kuma Humairar ba ta zo ba, anya ma za ta shigo kuwa?”

“Hmm! To kin gani dai shiru har yanzu watakila tana kan hanya ne.”

“To shi kenan mun gode sosai Allah ya bar zumunci, a yi lakca lafiya sai kin fito.”

“Ni ce da godiya ai, Allah ya saka da alkairi sai anjima.”

Mikewa ta yi, shi ma Sadik mikewar ya yi tare da cewa, “Bari mu fita tare zan je masallaci na ga lokaci ya yi.”

Taren suka fito ya dan tattaka mata zuwa cikin makarantar, suna tafe yake cewa, “Kawar nan taki shu’uma ce, na lura tana da jan aji sosai.”

Murmushi Binta ta yi tare da cewa, “Hmm! Ba jan aji bane kunya ce da ita, tana jin nauyi ne ace tana soyayya da malaminta, amma a hankali za ta rage za ta saurare ka.”

“Anya kuwa, ni ba na ganin alamun haka a tare da ita, sai nake ganin kamar akwai abin da ya dauke mata hankali. Ina jin watakila akwai wanda take so ko?”

“Hmm! Ka daina fadar haka, babu wanda ya dauke mata hankali. Kawai dai ka san halinmu na mata, muna son abu amma ba mu cika nunawa ba cikin kankanen lokaci. Ka dan ba ta lokaci za ta yi nazari.”

Binta na rufe bakinta wayarta ta fara ruri, Humaira ce dagawa ta yi da cewa, “Assalama alaikum, kin shigo ne?”

“E na shigo gani nan ma a kofar hall din, ke kina ina ne?”

“Nima gani nan a kusa da wajen ta baya bangaren gabas.”

Kashe wayar Humaira ta yi ta kewayo ta bangaren da Binta ta fada mata, kwatsam suka hada ido da Sadik, cak! Ta tsaya ta ki karasowa. Hade girar sama da ta kasa ta yi.

“Ranki ya dade sannu da isowa, ashe uzuri kika tashi da shi?”

Sadik ne ya yi wannan maganar cikin sakin murmushi, ko kallon bai ishe ta ba, ta yatsina fuska tare da cewa, “Malama da kin san abin da kike yi kenan da ba ki kira ni ba, domin ni ba shashanci na zo ba. Kin ga idan kin gama kin same ni a aji.”

Tana fada ta juya tare da sakin tsaki, murmushi Sadik ya yi hade da girgiza kai sannan ya ce da Binta, “Okay ki je kada ki makara watakila an fara, sai anjima kenan.”

Gaza motsawa Binta ta yi yanayin fuskarta ya dan sauya, sam ba ta ji dadin abin da Humaira ta yi wa Sadik ba, cikin sassanyar murya ta ce, “Yaya Sadik don Allah ka yi hakuri ka san…”

Ya yi saurin katse ta da cewa, “Me yasa kike haka? Kada ki damu wannan ba komai bane. Ai mu mun saba da ganin mutane iri-iri, ki je ki shiga lakca kawai.”

A sanyaye ta wuce shi ma ya yi tafiyarsa masallaci domin ya yi sallah.

Binta na isa wajen Humaira, ta iske ta zaune kan banci wajen da suka saba zama idan za su yi lakca. Zaman ta yi kusa da ita ba tare da ta ce komai ba, kimanin mintuna biyu zuwa uku ba wanda ya tanka wa kowa. Zuwa can Binta ta katse shirun da cewa,

“Ashe unguwar ma ba nesa bane, ai da kin fada mini na raka ki mun je tare.”

Humaira ta tabe ba ki tare da cewa, “Wa? Wa za ki raka? Ni! Ki rufa mini asiri, na kira mu tafi na hana ki zuwa wajen saurayinki. Ga shi yanzu kin zo kun gana da shi, ai ya yi kyau.”

Shiru Binta ta yi ba ta sake cewa komai ba, Humaira ta ci gaba da cewa, “Ko ba ki ji abin da na ce bane? Magana nake miki?”

“To me kike so nayi ce miki? Tunda haka kika fahimta ai shi kenan. Ni ba na son abin da zai rika kawo mana sabani, kawai mu bar maganar.”

“Da ma haka za ki ce a bar maganar tunda burinki ya cika. Kin ga ni na fada miki dai ki fito ki fada masa kina son sa, kuma ki shirya zama da kishiya, Meenat matarsa ce.”

Shirun dai Binta ta sake yi ba ta tanka mata ba har malamin da zai musu lakca ya shigo.

A wannan rana ma haka sai suka yini ba kamar yadda suka saba ba.

Tabbas abin da Humaira take wa Sadik na wulakanci ba ya yi wa Binta dadi, domin tana matukar son Sadik din, to amma ganin yadda hankalinsa ya karkata kan Humaira yasa ta boye masa abin da ke ranta. Babu shakka ba son Humaira ta karbi tayin Sadik, amma kuma ba ta son wulakancin da take masa. Duk lokacin da Humaira za ta furta mummunar kalma ga ga Sadik, ranta kuna yake mata,  kawai dai tana daurewa ne.

Fatanta dai shi ne Allah ya kauda tunanin Sadik daga kan Humaira, kuma da alama abin da ta yi masa yau din ya taba zuciyarsa kadan. Idan har ta ci gaba da yi masa hakan to akwai yiyuwar ya hakura da ita gabadya.

                 ***         ***       ***

Tunanin abin da Zainab makwabciyar Anty Sakina ta ji ta kuma gani ne ya ki barin zuciyarta, ko bayan da ta shiga gidan guri ta nema ta zube. Tunanin ne ya sake mamaye mata zuciya, “Shin me Sakina ta ragi Usman da shi da har zai rika kawo matan banza gidansa yana fasikanci da su? Me yasa wasu mazan *KUDAJE NE?* Tamkar ‘yan bunsuru haka suke. Matarka mace ce har mace, son kowa kin wanda ya rasa amma shaidan ya nuna maka hanyar tsiya. Hanyar da na sani da cizon yatsa, Allah ya ganar da kai idan me ganewa ne, idan kuma ba me ganewar bane Allah ya yi mana maganin irin ku.”

Tana nan zaune turus jikinta a mace tamkar wacce ta yi wani gagarumin aikin gajiya, jin abin take kamar mijinta ne yake aikata wannan lalatar. Sallamar anty Sakina ce ta kauda mata wannan tunani, dawowarta kenan daga wajen aiki ko nata gidan ba ta isa ba tukunna ta biyo ta fada wa Zainab cewa ta dawo, za ta iya zuwa ta karbi jakar.

Amsa sallamar Zainab ta yi tare da cewa, “An gai da teacher uban karatu, kila dawowar kenan ma ko gida ba ki shiga ba?”

“Wallahi kuwa, cewa na yi bari na fara sanar da ke na dawo ki zo ki karba don ki yi shirinki da wuri. Wallahi dazu da zan fita na yi niyyar kawo miki ita, to sai na sha’afa.”

“Anty Sakina kenan, ai na ce miki ba komai, ba shigar wuri zan yi wa garin ba. Na fi son na je lokacin duhu ya fara yi, ina zuwa.”

Mikewa Zainab ta yi ta nufi kitchen ta zubo musu abinci, shinkafa da wake da salad da cucumber, ta hado da wani sassayan lemon ‘ya’yan itatuwa da ta yi.

Anty Sakina ta ce, “Kin ganki da wani abu ko, wa ya ce ki zubo wannan abincin da yawa haka? Yanzu zan je nima na dora.”

Dariya Zainab ta yi tare da cewa, “To ai sai ki je ki dora mu gani. Babu inda za ki fita sai mun gama da wannan, kuma karo mana wani ma zan yi. Yanzu kin dawo a gajiye wane abinci za ki tsaya dorawa kuma na san Usman ya fita don na ga gidan a rufe bare ki ce saboda shi za ki yi girkin.”

“To ai dai…”

Zainab ta katse ta da cewa, “Kin ga malama ya isa,

<< Kuda Ba Ka Haram 15Kuda Ba Ka Haram 17 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×