Skip to content
Part 18 of 18 in the Series Ƙuda Ba Ka Haram by Sadik Abubakar

Binta ta nuna matukar takaici da rashin jin dadin makin da Humaira ta samu, abin ya dame ta a rai sosai. Hakan yasa ta samu Humaira a karkashin wata bishiya suna hutawa, ta fara mata nasihohi da jan hankali kamar haka, “Wai shin mene ne matsalarki? Gaskiya ni na rasa gano kan wannan lamari, ban ji dadin results din da ya fito a haka ba. Yanzu fa kina matsayin probation ne, ya zama tilas mu canja tsarin karatun nan. Ba zai yiyu mu cigaba da tafiya a haka ba, sam Mummy da Abba ba za su ji ba idan kika fada musu abin da kika samu a first semester. Ina ganin zai fi kyau kawai ki bari sai mun yi jarabawar second semester, idan aka hada makin da na baya aka raba biyu zai dan kara yawa koda maki biyu ne (2 points) kika samu a ND I ya fi. To sai gaskiya hakan ba zai samu ba sai kin sake daura sabuwar damara.”

Cikin yanayin ko in kula alamar abin bai ma dame ta ba, a wulakance ta dubi Bintar ta ce, “To wai wace irin damara kike so na daura kuma? Ba dai karatu bane ina yi sai me kuma?”

“Hmm! Ba haka za ki ce ba, nima kuma ban ce ba kya yin karatu ba, amma shin mene ne ba kya ganewa? Abin da nake nufi kenan, sannan kuma dama ina son na ba ki shawara. Ya kamata ki raba kanki da Ruky, matukar kina son rayuwarki ta yi kyakkyawan karshe. Kowa ya san halinta, ki duba irin kayan da take sawa kawai ya isa ya nuna rashin tarbiyarta sannan ba ta jin kunyar zama cikin taron maza.”

“Kin ga mu bar wannan maganar kawai, tunda kema kin fara zama ‘yar sa ido.”

“Hmm! Humaira ya kamata ki yi tunani da nazarin maganganun da nake fada miki, shin wai kin manta nasihar da Mummy ta yi mana?”

“Ban manta ba, amma kula kawa sai ya zama laifi? Ai na ga ba maza nake kulawa ba ko malama ustaziya.”

“Hmm! Humaira kenan, hakane ba maza kike kulawa ba amma da ki kula Ruky gara ki kula namiji matukar ba maganar banza ya neme ki da ita ba, domin akwai maza mutanen kirki wanda taimakon ki ma za su yi. Ita kuwa wannan yarinyar da kike gani ba mutunci bane da ita, sannan babu me yi mata kallon wacce ta fito daga gidan mutunci. Muddin kika ci gaba da kula ta to babu shakka kema mazan za ki rika kulawa. Yadda ta zama kamar karya kema haka za ki zama, domin haka Hausawa ke cewa, abokina barawo shi ma barawon ne, kuma zama da madaukin kanwa shi ya ke kawo farin kai.”

“Ni dai zancen nan ya fara isa ta, wai to da kike cewa na rabu da ita, ba ki ga results dinta bane ya yi kyau? Idan wasa take ta ya ya za ta samu (3.75 points)?”

“Shi kenan na ji ba ta wasa da karatu, yanzu karatun za ta rika koya miki kenan?”

“E mana, tunda ke yanzu kin samu Sadik ba ki da time dina ai sai ki je ki karata da shi. Nima sai ki kyale ni na samu wadanda za su bani time dinsu.”

Wata dariyar takaici Binta ta yi sannan ta ce, “Ni ban kyale ki ba fa, ki ma daina fadar haka. Kwana biyu ne na ga kin sauya ba kya son zama da ni, idan muka fito daga lakca sai na ga kin tsaya da su Ruky, sai ku bata kusan mintuna ashirin kina tare da su. Ni kuma ki bar ni a tsaye ni kadai, kuma kin san ni ba zan iya shiga group dinsu ba, shi yasa nake tafiya can wajen Sadik din.”

“To ai shi kenan, tunda haka kika zaba, ni dai ban ga wani aibin Ruky ba. Da ma haka mutane suke zarar sun ga mutum yana sabgarsa shi kenan sai a saka masa ido.”

“Hmm! Ba za ki gane ba Humaira.”

To haka dai tarayyar Binta da Humaira ta ci gaba da kasancewa cikin nakasu ba kamar yadda suka faro tafiyar ba sakamakon sauyawar da Humaira take shirin yi daga tafarkin daidai zuwa na rudin shaidan da son zuciya, ban da ma abin da ke faruwa tsakaninta da Usman wanda Bintar ba ta sani ba, wanda yake haifar da nadama.

Shi kuwa Usman, lokacin da ya dawo gida a ranar da aka kawo wa Anty Sakina kayayyakin nan, iske ta ya yi tana ta ware kayan. Kowanne tana hada su da ‘yan uwansu, shadda da atamfa da leshi da materials da code lace da takalma da jakunkuna da sarkoki da dai sauran kayan ado da kawa na mata har ma da maza yara da manya.

Tsananin mamaki ne ya kama shi saboda yawan kayan da ya gani turus! “Shin wannan kayan lefe ne ko kuwa? Kai gaskiya wannan sun fi karfin kayan lefe. To ma wai me ya kawo wannan kayan nan? A ina ta samo wannan kayayyakin haka kuma na waye?”

Tambayoyin da suka sarke makogwaron Usman kenan, sun ki fitowa bare ya samu amsarsu. Kuma Anty Sakina kadai ke da amsoshin, sannu da zuwa ta yi masa ta ci gaba da aikita. Daki ya wuce ya sauya kayan jikinsa sannan ya sake komowa falon ya zauna bisa kujera tare da sake zuba wa kayan maganansa (idanu). Ya kalli kayan ya kalli Anty Sakina, ita kuwa ba ta ma san yana yi ba, wai *kunu a wani gida.*

Kimanin mintuna goma sha biyar suna a wannan yanayi, shi yana faman kallon kaya zuciyasa cike da ta’ajibi, ita kuwa sai sha’aninta take. Zuwa can ta mike ta nufi kitchen ta kawo masa abinci da ruwa, sannan ta ta koma kan kayan ta fara dibar wasu tana kaiwa daki.

Ba ta yi niyyar sanar da shi ba game da wannan sana’a da ta fara, to amma sai wata zuciyar ta ce mata, ki fada masa ai yana da hakkin ya sani tunda a karkashinsa kike, mijinki ne kuma shugabanki. Duk da abin da yake miki din na rashin dacewa, kada ki biye masa kema ki zama mai laifi. Ki yi hakuri ki fada masa kawai.

Wannan ne tunanin da Anty Sakina ta yi sannan kuma ta lura da shi din a kage yake da ya san matsayin kayan, amma ba zai iya tambayar ta ba. Bayan ta dan rage yawan kayan daga falon, ta koma ta zauna ta har lokacin bai fara cin abincin ba. Dubansa ta yi ta ce, “Ya ya dai lafiya na ga ba ka fara cin abincin ba?”

“Zan ci.”

Ya fada fuskarta ba yabo babu fallasa.

Anty Sakina ta nisa tare da cewa, “Ka yi hakuri ban fada maka ba, na fara sayar da kayayyaki ne kamar yadda ka gani. Abin ne ya zo cikin sauri.”

Shiru ya yi kusan mintuna biyu bai ce komai ba, ita ma ba ta sake magana ba, zuwa can sai ya ja wani munafikin numfashi sannan ya ce, “Alright, ya yi kyau Allah ya ba da sa’a.”

Yana fada ya bude plate din ya fara cin abincin, ita kuwa Anty Sakina ci gaba da yi masa bayani ta yi da cewa, “Kawata Zara’u wacce muke aiki tare ita ce ta yi wa yayansu magana shi ne ya ba ni kayan idan na sayar sai na ba shi kudinsa na sake karbar wasu.”

“Hakane dama ana yin irin wannan, kema za ki samu naki alherin, Allah ya taimaka.”

Haka dai suke magana yanayinsa kadaran-kadahan, wato shi bai nuna farincikinsa ba kuma bai bayyanar da akasin hakan ba. Har ya gama cin abincin  ya yi wanka, bayan sallar Isha kuma ya yi shiri ya sa kafa ya fice yawon barikinsa wanda ya zame masa tamkar ibada.

To da alama dai Anty Sakina za ta samu dan saukin tunani da damuwa dangane da halin mijin nata, don haka idan ya yi niyya ya ji tsoron Allah ya tuba ya bari kansa; idan kuma bai bari ba, to ga shi nan ga duniya. Kowa ya debo da zafi bakinsa, kuma kowa ya kwana lafiya shi ya so. Karshen alewa dai ba ya wuce kasa.

Idan mutum ya shuka alheri to babu komai jimawa zai sunkuya ya girbi alheri; idan kuwa sabanin haka ne, to sai mutum ya shirya girbar kishiyar alheri. Domin ba za ka taba shuka masara ba, sannan ka ce kana son ka girbi dawa. Yadda ka tsara tafiyar da rayuwarka haka za ta kasance, tafarkin dai guda biyu ne kuma kowanne a bayyane yake. Zabi dai ya rage na me shiga rijiya, idan ya gadama ya shiga ta matattakala; idan ya so kuma ya tsunduma.

Allah Ubangiji muke roko da Ya kara bamu ikon kaucewa son zuciya da rudin shaidan; Allah Ya shirya mu shirin addinin musulunci, Allah Ya shiryi zuri’armu Ya tsare mana su. Mugun ji da mugun gani Allah Ya yi mana katangar karfe daya su.

            BAYAN WATA DAYA

To kawo yanzu dai a iya cewa Sadik ya fara kauda kansa daga kan Humaira, ya fara fita daga shirginta, domin ya fahimci ba wai jan aji bane take masa; wulakanci ne kawai. Bugu da kari ma, tarayyatarta da ‘yan group din su Ruky, wannan ya kara tabbatar masa da cewa lallai ita din ba irin yaran da ya dace ya saurara bane bare har ya rika bibiyar ta tana daga masa kai. Tun yana tambayar Binta ina Humaira idan ya ganta ita kadai har ya gaji ya watsar.

Yanzu dai alamu sun fara nuna yana son tsaida hankalinsa akan Binta, wacce ita dama tuni ta fara nuna alamun akwai wani abu da take son bayyana masa koda ba yanzu ba. Ganin yadda ta mayar da shagon café din nasa wajen zamanta duk lokacin da ba ta da lakca, yasa ya yi kokarin kulla wata kyakkyawar dangantaka tsakanin Bintar da Khadija, har ya umarci Meenat din da ta rika koyar wa Binta yadda ake wasu ‘yan aikace-aikacen da computer. Ba tare da nuna wani abu ba, Meenat ta karbi umarninsa. Babu mugunta haka ta rika nuna ta yadda ake sarrafa na’ura mai kwakwalwa; ‘yan aikace-aikace irin su photocopy da lamination da binding har ma da typing din document duk Binta ta fara iyawa. Cikin kankanen lokaci, ta iya aikin café sosai; dama dai ga duk wanda ya san Binta ya san ta da kaifin basira, ba zai yi mamakin hakan ba.

Gwanin sha’awa Khadija da Binta suke tafiyar aikin café din, akwai kyakkyawar fahimtar juna sosai a tsakaninsu. Hakan  ya yi wa Sadik dadi matuka a ransa, musamman idan ya zo ya iske suna aiki suna ta hira abinsu. Bugu da kari masu kawo aiki sukan yabi yadda sunayen Khadija suke kulawa da su, suke sakin fuska faran-faran cikin wasa da dariya.

Wannan zuwa shagon café din da Binta take da fara yin aikin sam ba su yi wa Humaira dadi ba, amma babu yadda za ta yi da ita. Domin ita Humairar da bakinta ta ce wa Binta, ta je wajen Sadik din tunda haka ta zaba. Babu shakka wannan abu ya kara tangarda dangantakarsu.

A halin yanzu dai babu wani abu da ke hada Binta dadi Humaira face tafiya makaranta tare da kuma dawowa; wajen zamansu ma na aji yanzu ba kasafai Humairar kan zauna tare da Bintar ba. Wani lokacin can baya take komawa ta zauna tare da su Ruky; ita kuwa Binta ba ta taba yarda ta zauna koda a tsakiya ba bare kuma can karshen baya. Kodayaushe tana bencin gaba, idan har ba ta samu wajen zama ba a bencin gaba ta kwammace ta zauna a kasa daga gaban domin ta ssurari lakca sosai.

Wata ranar Laraba, Usman ya bukaci haduwa da Humaira. To dama duk ranar Laraba ba sa fara lakca sai rana ta yi; sai ya yi amfani da wannan dama. A wannan karon ba a gida yake so su hadu ba, a hotel za su hadu kamar yadda ya tsara. To sai dai bai sanar da ita ba kafin ranar, sai da gari ya waye. Har ta yi shirin makaranta tana jiran isowar Binta su tafi, kiran wayar Usman ya shigo. Kofar gida ta nufo sannan ta amsa wayar, bayan sun gaisa ya ce, “Am sorry, kin ga na kira ki yanzu da safe ko? Ban sani ba ko kina da time, ina son mu dan sha ice cream ne kafin ki shiga makaranta tunda yau ba ku da morning lecture, ko ya ya kika gani?”

“Hmm! A ina ke nan?”

“Hmm! A Green Desert Hotel mana.”

“Okay, to sai dai yanzu kuma ga shi na shirya za mu tafi makaranta.”

“No worry, kada ki damu wannan ba matsala ba ne, ni ma yanzu shirin zan yi. Ki tafi school din zan zo sai na dauke ki mu tafi.”

“Okay to shi kenan.”

Haka ta amsa ba tare da ta yi wata tirjiya ba, sam ba ta iya yi wa Usman musu akan duk wata bukata da zai bijiro mata da ita. Tamkar mahaifinta haka take karbar umarninsa, ita a halin yanzu ma bala’in son sa take. Babu namijin da take ganin ya dace da ita kamar Usman; abubuwan da yake mata na mu’amalar aure yasa take ganin tamkar shi kadai ne namijin da zai iya yin hakan.

Babu shakka Usman ya iya romancing sosai, ya iya abubuwan da ke motsa wa mace sha’awa da jin dadi; haka nan hatta a kwanciyar shi din gwani ne, sai kin gamsu da shi matuka. Yana da juriya sosai, yana jimawa sosai a sama; sannan ya san salo iri-iri da style wanda ake dadewa ba a gaji ba. Hakika duk wacce Usman ya hadu da ita, musamman irin su Humaira da ba su taba sanin wani da namiji ba, to gani za su yi babu wanda ya kai shi kwarewa a wannan fagen. To Allah ya kyauta.

<< Kuda Ba Ka Haram 16

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×