Skip to content
Part 19 of 23 in the Series Ƙuda Ba Ka Haram by Sadik Abubakar

Humairah na gama da Usman ke nan sai ga Binta sun iso da Mai Adaidaita Sahun da yake kai su makaranta, ta yi wa Mummy sallama sannan ta fito suka wuce. Shi ma gogan naku ɗan fama, shiri ya fara yi ba bata lokaci ya gama ya fito ya hau mota, bai zame ko ina ba sai makarantar. Su Humaira ba su jima da isa ba, suna tattaunawa a kan wani assignment da aka ba su; Humaira na son Binta ta yi mata.

Kiran wayar Usman ne ya shigo, dagawa ta yi kafin ta yi magana ya ce, “Ina fatan ban riga ku isowa ba ko? Kin gan ni na shigo school din taku.”

Waigowa ta yi kafin ta yi magana ta dubi kofar makarantar, motarsa ta hango ya ɗan saki hanya kaɗan ya tsaya. Lumshe idanu ta yi sannan ta ce, “Gaskiya ka yi sauri; kamar kana bayanmu, ai ni na zaci ba yanzu za ka zo ba. Na hango motarka ai, ka dan kara shigo ciki wajen wasu dogayen bishiyun turare za ka hange ni.”

Taka motar ya yi kadan a hankali ya iso daidai wajen da ta yi masa kwatancen. Binta kuwa saroro ta yi tana kallonta cikin mamaki ta ce, “Waye kuma kuke waya da shi har kike kwatanta masa inda kike? Hala bako ne?”

“Hmm! Sarkin tambaya ke nan, ke dai ba kya iya gani ki yi shiru sai kin tofa. Wani saurayina ne, mun dade ba mu haɗu ba; ma’aikaci ne ba a nan garin yake aiki ba. Hutu ya zo ne shi ne yake so mu gaisa; da wuri zai koma, ya matsu ya gan ni shi ne ya biyo ni school.”

Murmushi Binta ta yi tare da cewa, “ya yi kyau, ni bari na wuce café sai an jima ke nan?”

Canja fuska Humaira ta dan yi sannan ta ce, “Ban gane ki wuce café ba? Ba za ki zo ku gaisa ba? To ai sai ki je din.” Ta karasa maganar tare da galla mata wata masifaffiyar harara, dariya Binta ta yi ta ce, “Allah Ya huci zuciyarki, mene ne abin fadan kuma? Indai gaisuwa ce mu je ya samu.”

Mikewa suka yi suka iso inda ya yi parking, ya dan sauke glashin bangarensa yana sakin wani irin matsiyacin murmushi, sallama Humairar ta yi masa ya amsa sannan suka gaisa. Minti kamar daya haka, babu wanda ya yi magana. Zuwa can ya nisa tare da cewa, “Ya ya karatun dai, da fatan ana ganewa.”

Murmushi suka yi Binta ta dora da cewa, “Karatu Alhamdulillah.”

Hira ce ta barke sosai tsakaninsu game da harkar karatun nasu, hankalin Usman ya fi karkata wajen Binta, sauraren ta yake sosai fiye da Humairar sannan ga wani shegen kallo da yake yawan yi wa Bintar wanda har ita kanta ta fara kosawa da shi, ba ta son ta ce za ta tafi ne Humaira ta yi mata masifa da jaraba.

To da yake abin na Usman ba na hankali ba ne, tamkar ƙuda haka yake, kallon da yake yi wa Bintar ne ya yi yawa har ya fara isar Humairar, ta lura da shi lallai akwai abin da yake kallo tattare da Bintar, don haka sai ta ce, “Tunda ba jimawa za ka yi ba, ya kamata mu je gida ka gai da su Mummy tun kafin ka ce wasu uzurori sun hana ka.”

Da yake shi din gwani ne ya san harkar tasu babu gaskiya, tuni ya fahimci abin da take nufi murmushi ya yi sannan ya ce, “Okay.”

Humaira ta dubi Binta ta ce, “Bari na raka shi gida ya gai da su Mummy yanzu zan dawo, ba don za ki yi mana assignment din nan ba da min je tare.”

Murmishin takaici Binta ta yi tare da yin dan gajeren tunani a zuciyarta, ‘Wane irin saurayi ne wannan da zai biyo ki har makaranta ya dauke ki ku koma gida wai da sunan zai gai da iyayenki? Allah ya kyauta. Inda ranka ka sha kallo in ji masu iya magana.’

Tunanin da Binta ta yi ke nan kafin ta nisa ta ce, “To shi kenan babu damuwa sai kin dawo din.”

Rufe bakin Binta ke da wuya sai ga Ruky nan da ‘yan tawagarta su uku, sun tunkaro wajen da su Humairar suke tsaye. Suna tafe tafiya irin ta marasa kunya, suna juya wasu bangarori na jikinsu dakan iya jan hankalin namiji idan ya kalle su. Suturar jikinsu akwai ya babu ce, hakorin zomo; kaya ne da suka kama musu jiki sosai, duk wani waje me tudu ya fito sarai ana ganin shape dinsa. Kafin su iso tuni Binta ta yi layar zana ta bace bat!

“Hi kawata what’s up? Bako kika yi ne, don na san ba kya kula young babies din cikin school din nan ‘yan kari.”

Ruky ce ta fadi wannan maganar yayin da suka iso daf da motar Usman din, dariya Humaira ta yi tare da cewa,“Ruky ba ki da kirki wallahi, wato ‘yan kari ne ma  to bari su ji ki babu ruwana. Allah Ya sa za mu hadu yanzu da safe, da watakila sai anjima. This is my man; he isn’t living in Kano. Ya zo dan gajeren hutu ne.”

“Wow! Fantastic! Sannun ka; ya aiki?” Ruky ta fada tana kare masa kallo, haka su ma ragowar kawayen nata suka gaishe da shi sannan Rukyn ta dora da cewa, “What’s his name? Ko ba a fadin sunan ne?”

Murmushi ya yi sannan ya ce, “Usman is my name and you?”

Cikin sigar murmushin kwarkwasa ta ce, “Sunana Rukayya, but ana kira na da Ruky.”

“Nice name Ruky! So ya karatu?”

“We thank God.”

Hira ce take kokarin sake barkewa tsakaninsu amma Humaira ta hana, duban sa ta yi tare da sauya fuska ta ce, “Ba ka da isasshen lokaci fa, ya kamata mu je mu gama abin da za mu yi ina son na dawo school da wuri.”

“Okay no problem.”

Ya fada tare da zaro kudi kimanin dubu biyar (₦5000) ya Mika wa Humaira ya ce ta ba wa kawayen nata, Ruky ce ta sa hannu ta karbe tare da yin godiya.

Humaira ta ce, “Ba komai bari mu je yanzu zan dawo ai.”

Bude kofar motar ta yi ta shige, ya yi key ya ja suka fice. Basu tsaya ko ina ba sai Green Desert Hotel, suna isa ya yi order aka kawo musu wani lafiyayyen farfesun kayan ciki da drinks, suka fara gyara musu zama sannan suka shiga aiwatar da abin da ya kai su.

Kamar yadda suka sabar wa kansu tamkar ma’aurata, harka suka yi san ransu cikin nutsuwa har sai da kowa ya gamsu. Sun jima sosai kafin daga bisani suka shiga wanka tare. Suka watsa ruwa sannan suka fito, kwalliya Humaira ta sake sosai suka fito ya dauko ta zuwa makaranta.

To a makarantar kuwa tuni lokacin fara lakca ya yi, wato karfe daya (1:00pm), Binta ta baro café ta nufi hall din da za su yi karatun, malamin da zai yi musu lackar har ya iso ya ma fara, amma shiru Binta ba ta ga keyar Humaira ba, kuma ta duba cikin sabbin kawayen nata wato su Ruky nan ma ba ta ganta ba, hakan ya tabbatar mata da cewa ba ta dawo ba ne kawai.

Ana ta yin lacka har kusan mintuna talatin (30 mins) babu Humaira babu labarinta. Lakcar ta tsawon awanni biyu ce wato course din (two credit units ne), lokacin da aka yi awa daya da fara lakcar shiru dai Binta ba ta ga shigowar Humaira ba; sai ta nemi izinin fita daga ajin domin ta kira wayar Humairar ta ji ko lafiya har yanzu ba ta dawo ba? Daga cewa za ta raka shi gida gai da su Mummy.

Tana fitowa ta lalubi lambar Humaira ta kira, waya ta yi ruri ta yanke ba a daga ba. Ta sake kiran ta nan ma dai waya ta yi ruri babu amsa; kira uku ta yi mata duk a banza.

To ashe a daidai lokacin da Binta take ta faman kiran layin Humairar ba ta san inda kanta yake ba, sam ba ta ji karar da wayar take ta yi ba; amma shi kuwa Usman ya ji lokacin da wayar ta yi ruri a kira na karshe, wanda daga shi Bintar ba ta sake kiran wayar ba sai ta koma ta ci gaba da daukar lakca abinta.

Har aka gama lakcar nan tsawon awa biyu Humaira ba ta shigo ba, domin bai dawo da ita makarantar ba sai  kusan misalin karfe uku na rana (3:00pm). Kafin su iso tuni sun yi sallama; a bakin kofar ya tsaya ta sauka ta shigo tana sauri. Kai tsaye ta nufi hall din da suke yin lakcar duk da dai ta san da wahala ta riski wannan malami; koda ma ta ta riske shi to ba zai bar ta ta shiga ba. To dayake bayan ita wannan lakcar akwai wata, ita ma din awanni biyu ce kuma a dai wannan hall din. Saboda haka idan wancan malami na farko ya fita babu inda suke matsawa malami na gaba zai shigo ya same su.

Tana shiga suka hada ido da Binta, dayake dama a gaba Binta take zama kodayaushe, sai ta fara murmushi; Binta ta kauda kanta saboda takaici, duk da cewa ba ta san dalilin da ya hana Humairar dawowa da wuri ba, amma tana jin haushin ta domin wannan shashanci ne take neman shagaltar da kanta da shi. Karasawa ta yi ta zauna kusa da ita tare da dora hannunta akan na Binta tana fadin,
“Kin gan ni sai yanzu ko? Wallahi yawace-yawace mu kayi har kasuwa na raka shi ya yi ‘yan saye-saye; shi yasa kika ga na dade. Ina fatan dai kin yi mini attendance na wannan jarababben malamin?”

Yanayin yadda take maganar duk babu nutsuwa a tare da ita, hakan yasa Binta ta kara nazartar yanayin nata sosai; sam ba haka jikinta ma yake ba lokacin da suka taho makarantar da safe; ba ma irin kwalliyar da ke fuskarta a yanzu ba ce. Sannan idan har abin da ta fada gaskiya ne cewa yawace-yawace suka yi tunda ya dauke ta, to maganar ta ci karo da kwalliyar da ke kan fuskarta; domin wanda ya yi yawo sosai bai kamata a ga sabuwar kwalliya a fuskarsa ba, koda kuwa a cikin jirgin sama ya yi yawace-yawacen.

Don haka wannan zancen kirkirar sa  ta yi kawai babu kamshin gaskiya a ciki. Wwnann shi ne abin da zuciyar Binta ta fi nutsuwa da shi. Bayan ta gama lura tsaf da yanayin Humairar, sai ta dube ta cikin takaici ta ce,

“Shi yasa kuma na yi ta kiran wayarki har sau uku ba ki daga ba, lallai kun yi yawo sosai. Ai da kin sani ma kawai kin rakashi ko ina kun yi komai a tsanake tunda dai rana daya ce ai babu damuwa.”

Cikin sigar gatse Binta take wannan maganar, amma ita gabuwar sam ba ta fahimta ba; dariya ma ta yi tana fadin, “Ai kuwa dai wallahi da ya ji dadi sosai.”

Nan dai suka ci gaba ‘yan zantuka kafin malami na gaba ya iso. Misalin karfe 5:00pm na yammaci suka fito, dama lakca biyu ce suke da ita kuma kowacce awanni biyu suke yi. Suna tafe cikin Adaidaita Sahu kan hanyarsu ta dawowa, Humaira ta ce da Binta “Ya ya za a yi mu hadu a wannan weekend din? Kin daina zuwa gidanmu kwata-kwata?”

“Hmm! Ke ma din ai kin daina zuwa namu ko? Gaskiya akwai abin da nake son yi, ina da uzuri; wanki nake son na yi.”

“To ranar Lahadi fa? Ko ita ma wankin za ki yi. Ke na ga take-taken kamar so kike mu rabu ko?”

Wata harara Binta ta aika mata tare da cewa, “Wace irin magana ce wannan? Yanzu ba ni ce ya kamata na fadi haka ba, dubi yadda kike neman kulla kawance da su Ruky, ni ban ce za ki rabu da ni ba sai ke, saboda kin fi ni baki?”

“To ai na ga sai wani kauda kai kike ina miki magana.”

“Gaskiya na fada miki ai, har ranar Lahadin ina aiki, ina son kuma na yi guga; idan na samu dama zan leko idan kuma kin ji shiru to shi kenan.”

“Kin ga kawai ki ce ba za ki zo ba kai tsaye, sai kin wani tsaya kina zuke-zuke ba dole ba ne sai kin zo; ki sha birnin zamanki.”

“Hmm! Allah Ya ba ki hakuri Ya kuma huci zuciyarki.”

Haka dai suke ta musayar yawu har suka iso Zaitawa, unguwar su Humaira kenan ta sauka sannan aka wuce da Binta zuwa Jakara.

<< Kuda Ba Ka Haram 18Kuda Ba Ka Haram 20 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×