BAYAN SATI BIYU
Bayan kamar sati biyu da zuwan Usman makarantar su Humaira, sai ya sake dawowa; amma a wannan karon ba wajen Humairar ya zo ba, ba da ita yake muradin haduwa ba. Saboda haka ma ko sanar da ita bai yi ba, gaba-gadi kawai ya niki gari ya tafi. So yake ya hadu da Binta ko Ruky; tun da ya gan su maitarsa da arwarsa suka doru akansu. Ya so tun a ranar ya samu lambar wayoyinsu, musamman Ruky dayake ganin da alama 'yar hannu ce ta san komai, ba za a sha wahala ba za ta. . .