Skip to content
Part 21 of 30 in the Series Ƙuda Ba Ka Haram by Sadik Abubakar

Humaira na nan zaune inda ta kifa kanta, sai ga kawayen Ruky nan su uku sun iso wajen da take, “Salama alaikum, ya ya na gan ki ke kadai zaune kin kifa kai? Lafiya kuwa?”

Guda ce daga cikinsu kenan wacce ake kira Laila ta yi wannan maganar, yayin da Humairar ta dago kai da cewa, “Wallahi dai kam kin ganni kaina ke dan yi mini ciwo kadan, ya ina mutuniyar ne, na gan ku ku kadai?”

“Yo mu ma ita muke nema, mun yi tunanin ko kuna tare.”

“Hmm! Na kira wayarta har sau uku tana shiga amma sai ta yi rejecting; daga karshe sai ta kashe wayar. Amma ki kira ta ko za ki sa’a ta amsa.”

“Kamar ya kenan ban gane ba? Rukyn kika kira ta yi miki rejecting? To bari ni na kira ta din.”

Wayar ta dauko cikin sigar gadara da nuna isa hadi da kwarin gwiwa ta lalubo lambar ta danna mata kira, dakiku kalilan na’ura ta fara magana kamar haka, “The number you are calling is switch off; please try again later thank you.”

Cike da mamaki Laila ta zaro idanu ta dube su, ba ta ce komai ba sai ta sake lambar a karo na biyu, kwatankwacin abin da ta ji a farko shi ta sake ji; hakan ya tabbatar mata da abin da ta Humaira ta fada gaskiya ne.

“To ita kuwa ina ta shiga haka kuma ta kashe wayarta? Babu damar a ji ko a ina take; anya kuwa lafiya?”

Humaira ta yi murmushi me cike da takaici sannan ta ce, “Ku kwantar da hankalinku duk a inda take lafiyarta kalau, za ta dawo, watakila wani ne ya dame ta da kira shi yasa ta kashe wayar.”

“Anya kuwa, ai da wahala ki nemi Ruky a waya ba ki same ta ba, ni dai na fi tunanin ko wani abin ne ya same ta amma Allah Ya kiyaye.”

“Hmm! Kodayake addu’a kika yi, amma ni na fada muku lafiya lau take kuma za ku gani.”

“To shi ke nan Allah Ya tabbatar da alkairi.” To wannan ɓangaren ke nan.

Ita kuwa Rukyn na can Usman yana jagwalgwala ta yadda yake so; yana ta bare gyadarsa a kanta; sai da ya yi ya gaji don kansa sannan ya daga ta. Mintuna kamar biyar tana kwance tana hutawa, sannan ta mike; kallon ta kawai Usman yake, ya kura nata mayun idanuwan nan nasa yana nazarin yadda ya ji ni’ima a tare da ita. Duk da cewa ya saba harka da mata iri-iri, amma wannan ya ji ta ta musamman ce. Sam bai yi tunanin za ta yi armashi haka ba; “Lallai ba kowanne abinci ba ne ake gane dadinsa ta hanyar ganin ido kawai, sai an dandana. Wannan yarinyar da zahirin da kuma badinin duk ta hada, babu shakka za mu yi harka da ita sosai.”

A ransa yake wadannan zantukan sambatun, zuwa can kuma sai ya saki wani arnen murmushi tare da cewa, “Bari na mayar da ke school ko? May be kuna da sauran lecture.”

Murmushin ta yi ita ma sannan ta ce, “As you wish.”

Dubu goma ya lalo ya kama hannunta ya dora mata tare da cewa, “Take this and manage it before the end of this month. Thank you so much baby! You really made my day so bright.”

Tunda ya aza mata kudin a tafin hannunta ta ji wani arnen dadi ya kama ta har gabanta sai da ya fadi saboda tsananin murna da farinciki; rungume shi ta yi sosai tana fadin, “Thank so much, don’t worry. Mun zama daya, feel free to call me at anytime. I’m ready to serve your needs. Na gode.”

Ire-iren kalaman godiyar da ta rika jero masa kenan, babu shakka ya saka farinciki a ranta fiye da tunaninta; tunda take ba ta taba harka da babban mutum me harkar arziki ba irin Usman.

“Tabbas na samu mutumin da zan tattara hankalina akansa; hakika duk lokacin da zai neme ni zan amsa masa kiransa, ko me nake yi zan bari har sai na gama da shi, Allah Ya kashe ya ba ni.”

Tunanin da take yi kenan, Usman ya dube ta ya ce, “Tashi mu je na sauke ki ko?”

“Okay.” Ta fada tare da kama hannunsa ta mike hade da manna masa Wani dan iskan kiss sannan suka fito suka nufo wajen da ake ajiye ababan hawa. Shi da kansa ya bude mota kofar motar ta shiga sannan shi ma ya shigo suke fice. Fara tafiyarsu keda wuya, ta latsa wayar domin ta ga ko karfe nawa? Duk da ba wata dadewa suka yi ba, sai ta ga waya a kashe; ba ta yi mamakin ganin hakan ba domin ta manta a wani hali ta ajiye wayar? Kunna ta kawai ta yi.

Usman ya dube ta fuskarsa cike da murmushi ya ce, “Sai yaushe ke nan za mu sake haduwa?”

Cikin sigar shagwaba irin ta ‘yan bariki ta ce, “Ni yanzu ma ba na son mu rabu wallahi.”

Ya yi dariya sannan ya ce, “Kada ki damu, as you said we’re one now! So anytime za mu iya haduwa.”

“E, haka ne amma ba na son ka tafi ka bar ni.”

Tana fada ta dauki wayarsa ta saka masa lambarta ta mika masa sannan ta ci gaba da cewa, “There’s one thing da nake son na tambaye ka shi ne, shin mene ne matsayin Humaira a wajenka?”

Ya dan yi dum, bai ce komai ba tsawon dan wani lokaci, Ruky ta ci gaba da magana, “I’m asking you, ko ba ka ji ni ba ne?”

Murmushi ya saki tare da cewa, “No, ba haka ba ne, just tana kusa da unguwarmu ne shi ne muke dan gaisawa. But I’m not interested; kin gane ai.”

Ruky ta sauya yanayinta kadan sannan ta ce, “Ba komai ai mace ce, idan ma kana da ra’ayinta daidai ne. A hanya za ka sauke ni na samu Keke Napep ya karasa da ni, kada kawayena su gan mu tare, wasu sun gane ka tun wancan ranar.”

Hakan kuwa aka yi, dama shi ma tunaninsa kenan, yana gudun kada Humaira ta sake gan shi. Don haka suna hawa kan titin BUK, ‘yar tafiya kalilan suka yi ya nemi waje ya yi parking tare da tsayar da wani Mai Adaidaita Sahu, tana fitowa daga motar ta shige Adaidaita Sahun ,shi kuwa Usman ya juya ya nufi gida abinsa.

Usman ke nan! ƘUDA BA KA HARAM duk abin ya gifta gabanka sai ka taba koda ba a so. Usman ƘUDA sarkin kwadayi, Usman komai ka samu rabon gaba ya fi bawa. Usman, na Sakina mai halin ɗan taure.

Wannan shi ne Usman, kuma kaɗan ke nan daga irin miyagun halaye da ya tara.

Nan da nan Mai Adaidaita Sahu ya iso da Ruky makaranta, cike da fara’a fuskarta ta shiga cikin makarantar, kai tsaye wata majalisa tasu ta nufa, dayake ta duba agogo lokacin lacka ta gaba bai yi ba. Don haka tana da yakinin mutanen nata suna can ana ta cigiyarta. Suna hango ta aka fara shewa da murna, “Wai ina kika shiga? Daga fitowa sai mu neme ki ko sama ko kasa, kuma kin kashe wayarki. Wallahi har kin fara samu tunani.”

Dariya ta kwashe da ita tana fadin, “Haba my babies, ku kwantar da hankalinku lafiyata kalau fa! Wani uncle dina ne ya yi mini waya wai ya shigo Kano, shi ne ya ce na zo mu gaisa kafin ya wuce.”

Laila ta yi tsalle hade da ihu ta ce, “Wow! Hajiyata ki ce yau aljihunmu a cike yake; ai dama tunda na hango ki kina sakin similing, na san dawa ta yi nama. Sai a ba mu namu kason.”

“Hmm! Laila ke nan, ke dai ba ki da zance sai na kudi.”

“Kudi ai abin so ne hajiyata! Kuma shi ne ma sai ki tafi ke kadai don kada mu ma mu samu wani abin a wajensa, ba ki da kirki wallahi.”

“Laah! Haka ma za ki ce? Ai na ga lokacin duk ba ku fito ba kuna aji, kuma ya ce mini a kan hanya yake yana sauri.”

“To ai shi kenan, yanzu dai mu je Capteria kawai dama yunwa muke ji.”

“Haba! Meye kuma Capteria? Ku zo mu je hostel kawai na yi mana girki me dadi.”

Hakan aka yi kuwa domin wannan kudi da Ruky ta samu duk da ba su san ko nawa ba ne, ba su isa su ci su ba, sai idan za ta sayi wani abin su ma ci a dalilin haka. Hostel suka rankaya suka fara shirya wata hadaddiyar indomie da kifin gwangwani.

Humaira dai tana zaune a wannan waje da kawayen Ruky suka same ta  ta hada kai da gwiwa. Sam hankalinta ya gaza kwanciya, kiran layin Rukyn ta sake yi ko Allah zai sa ta shiga, cikin sa’a kuwa ta ji ta fara ruri; Ruky na ganin sunan Humaira a gilashin wayarta gabanta ya dan fadi kadan, da kamar ba za ta daga ba amma sai ta amsa da cewa, “Ya ya aka yi kawata kina ina ne? Ko ta samu ne shi ne kika guje mu?”

Wani kududun bakinciki da takaici ne suka taso wa Humaira, basarwa ta yi ta ce, “Ke din kina ina? Ba ki ga kirana ba har sau uku kina rejecting, daga karshe ma sai kika kashe wayar.”

“Anya kuwa ba matsalar network ba ce, wallahi ni ban ga kiranki ba kuma ban yi miki rejecting ba, ta ya ya ma zan kashe miki waya? Kin ga yanzu dai ki hostel muna tare da su Laila.”

“Okay, to gani nan.”

Ruky na aje waya Laila ta ce, “Hala Humaira ce ko?”

“Ita ce mana take korafin wai ta kira ni na kashe mata waya, ni kuma wallahi ko kiran ma ban gani ba bare na yi rejecting.”

“Ai kam dai dazu muna tare da ita muna cigiyar ki, ni ma har kiran naki na yi a lokacin a kashe muka ji wayar taki.”

“Hmm! To ai sai kun san yadda network yake, kuna tare da mutum gaba-da-gaba ma sai ka kira shi a ce maka a kashe wayar take.”

Mintuna kamar biyu zuwa uku sai ga Humaira nan ta iso hostel din, tana shiga idonta akan Ruky, murmushi Rukyn ta sakar mata tare da cewa, “Sarkin complain, kamar ba ki san sharrin network ba.”

Humaira ta dan tabe baki sannan ta ce, “Hmm! Matsalar network kuma sai a neme ki a rasa cikin makaranta kaf, wallahi akwai inda kika je.”

Dariya Ruky ta yi tare da cewa, “E mana, na dan fita ne. Uncle dina ne ya zo shi ne ya yi mini waya na je muka hadu.”

“Kutmelesi! Lallai wannan ta yaga mini wajen hada zance da iya karya. Yanzu na tabbatar da abin da idanuwana suka gani gaskiya ne; ita ce Usman ya dauka suka fita.”

A zuciya Humaira ta yi wannan maganar, yayin da bugawar zuciyar ya karu da sauri wanda hakan ya so ya bayyana bacin rai a fuskarta. Wani zazzafan nishi ta ja tare da dafe goshi.

“Lafiya dai?” Ruky ta tambaye ta cikin sigar firgici, yayin da Laila ta waigo ta karbe zancen da cewa, “Wai Humaira har yanzu kan bai lafa miki ba, ki je ki sha magani mana.”

Ruky ta ce, “Au kanta ne yake ciwo? Bari ina da maganin ciwon kai sai na ba ki, sannu Allah Ya sawwake. Ki dan kwanta ki huta.”

Humaira na ciccije lebe ta ce, “Aa ki bar shi ma na gode; bari na je wajen Binta a café din Sadik, watakila ma gida za mu tafi tunda lakca daya ce ta rage mana kuma ba lallai bane malamin ya shigo.”

“Okay, to shi kenan ki kula sosai fa, Allah Ya sawwake.”

“Amin.” Humaira ta fada tare da ficewa daga dakin.

“Shegiya, an fada miki ni din ta wasa ce? Ba ki ga komai ba ma; sai ya daina sauraren ki kwata-kwata a lokacin za ki san wacece Ruky? Ko matar aure ce ta sake na yi hulda da mijinta; idan ba ta yi da gaske ba sai ya rabu da ita. Domin indai zai shige ni sannan ya shige ya kuma, to zai ji ta a bushe kamar dusa, bare kuma ke budurwarsa wacce ba auren ki zai yi ba har ki tashi hankalinki, saboda ke sakarai ce.”

Zantukan da Ruky ta yi da zuciyarta kenan kafin Laila ta katse ta da cewa, “Ai mu ma ba za mu koma lackar nan ba kawai tunda babu tabbacin za a yi ta, ni dai na gaji.”

Ragowar ma suka amsa da, “To ai shi kenan sai mu huta kawai.”

Nan dai suka gama girkin na su, suka ci suka sha suka yi tanbelensu son ransu babu mai kwabar su.

<< Kuda Ba Ka Haram 20Kuda Ba Ka Haram 22 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×