Bayan Humaira ta bar wajen su Ruky, wani wajen ta samu ta zauna ta kira Usman, ta ji shi kuma me zai fada mata? Wace karya zai hada? Domin ita dai ta gama yanke musu hukunci. Ta kiran sa lokacin yana gida yana kwance abinsa, daukar wayar ya yi sannan ya shuri takalmansa ya fito waje ya shiga cikin motarsa; kafin ya kai ga amsawa ta yanke. Nan take ya bi ta, tana amsawa ya ce, “Don Allah ki yi hakuri, kin ga ban kira ki ba ko? Wallahi dazun nan wani case din hatsari ne aka kawo ofishinmu kuma ni aka bawa na yi handling dinsa, shi yasa kika ji ba ni da nutsuwa a lokacin.”
“Dama na san wannan mutumin akwai karyar da zai yi don ya kare kansa, yo wani ma ya yi rawa bare dan makada; wani ma ya iya shirya karya bare kuma dan sanda. Daraja daya ka ci ina ganin kimarka amma da sai na karyata ka yanzun nan.”
A ranta ta yi wannan zancen sannan ta ja dogon numfashi ta fesar da wata iska me cike da dumi ta ce, “Ikon Allah! Kuma shi ne na ji har da nishin mace a wajen? Amma kuma babu hayaniya?”
Ya yi dariya tare da cewa, “Humaira kenan, ai wacce aka buge din ce, wata budurwa ce wallahi ta sha wahala sosai. Wannan nishin da kika ji suma ta yi ne; mu mun yi zaton ma ko mutuwa ta yi, amma Alhamdulillah da muka kai ta Emergency ta farfado bayan da likitoci suka hau kanta.”
A yatsine Humaira ta ce, “To Allah Ya kyauta Ya kuma kiyaye gaba.”
“Amin ya Allah! Ya karatun? Kun tashi ne ko kina school din?”
“Ina makaranta amma mun kusa tashin.”
“Ba don ina busy ba ai da na zo na dauko ki.”
Murmushin takaici ta yi tare da cewa, “Aa ba komai ka bar shi ma akwai; Mai Adaidaita Sahun da yake kai mu kuma ya dauko mu kullum yanzu ma na san yana kan hanyar zowa; na gode.”
“Okay, ya yi kyau, da fatan dai babu wata matsala ko?”
“Babu komai da ma dai da na ga kamar motarka ta shigo makarantarmu an dauki wata daliba a ciki shi ne hankalina ya tashi sosai; amma tunda ka ce ba kai ba ne shi kenan.”
Tintsirewa ya yi da dariya sosai a zahiri domin ya kwantar mata da hankali, amma a badininsa gabansa ne ya yanke ya fadi tare da yin tunanin, “Ashe ta ganni? To lallai sai na sauya taku.”
Humaira ta sauya murya cikin shagwaba ta ce, “Dariya ma kake mini ko?”
“I’m sorry babyna, ai ke ce da abin dariya. Ita mota abin Nasara, ba ni kadai ba ne me irin ta, kuma makaranta waje ne na jama’a babu irin wadanda ba za ki gani ba. Ki kwantar da hankalinki kin ji; I wish you all the best.”
Ya karasa maganar da huro mata kiss. Duk wannan zantukan da rarrashin da yake mata a banza domin ta riga ta ga abin da ta gani, don haka dai matsayinsa ya ragu a wajenta.
Haka nan ta ci gaba da zama ita kadai kamar mayya, zuciyarta na kara turnukewa da damuwa har zuwa lokacin da za su shiga lakca ta karshe a ranar. Binta ta baro wajen Sadik ta nufo ajin, kan hanya ta iske Humaira, nan suka rankayo tare. Binta na tambayar ta, “Ya ya ciwon kan? Da fatan ya lafa miki?”
“E da sauki ya daina.”
“To Allah Ya kara sauki, Allah Ya sa kaffara ce. Ina kawayen naki? Ko suna cikin ajin ne?”
“Suna hostel, watakila sai anjima za su karaso.”
Haka dai suka isa ajin, ba jimawa malamin ya shigo, sai dai cikar ajin ba sosai ba. Saboda malamin bai cika zuwa kodayaushe ba sannan kuma lakcar ta yi yammaci sosai; wasu daliban ba su cika tsayawa ba; bugu da kari kuma One Credit Course ne sannan Elective ne, awa daya malamin ya yi ya fita.
Ana tashi, su Humaira suka fito daidai lokacin Mai Adaidaita Sahunsu ya zo, dayake dama ya san lokacin da suke tashi; kai tsaye suka shiga ya nufo gida da su.
To a bamgaren Anty Sakina dai ana iya cewa sai son barka, domin Allah Ya saka mata nasibi a harkar kasuwancin da ta fara, ciniki take sosai. Ta hada kwastomomi da yawa, ana sayan kayayyakin matuka, kama daga masu sayen daidaiku da masu hada kayan lefe; duka dai babu wanda babu. Cikin dan kankanen lokaci sunanta ya fara amo sosai yana kaiwa wuraren da ba ta yi zato ba.
Hakan yasa watarana suna zaune tare da Anty Zara’u a wajen aiki suna hira, Anty Sakina take neman shawarar kawar tata, inda ta ce, “Wai ni kin san me nake son yi kuwa? Amma dai sai mun shawarci yaya Ahmad tukunna. Ina son na yi wa business din nan rijistar CAC ne, ko ya ya kika gani?”
Anty Zara’u ta ce, “Tabbas wannan tunani ne me kyau; riga ni furtawa kika yi amma abin da ke raina kenan ina son na fada miki.”
Tana rufe bakinta sai wayarta ta fara ruri, tana dubawa ta ga sunan yaya Ahmad, kafin ta daga ta ce, “Kin ga ma yaya Ahmad din ne. ”
Ta fada sannan ta amsa tare da kara wayar jikin kunnenta ta ce, “Assalama Alaikum warahmatullah wabarakatuh.”
“Wa alaikumus salamu warahmatullah, kina wajen aiki ko?”
Ta amsa masa da cewa, “E, ina can. Ya ya aka yi?”
“Kin ganni nan zan kai Farida asibiti ne, ina jin watakila haihuwa ce, ko za ki nemi izini wajen Principal dinku ki zo yanzu?”
Cikin firgici marar tsanani ta ce, “To shi kenan insha Allah gani nan yanzu kuwa; ka sanar da hajiya ne?”
“Aa ban sanar da ita ba, saboda ciwon kafarta ba na son ta ce za ta zo, ke din ki zo kawai.”
“To ga ni nan.”
Ta fada tare da janye wayar daga kunnenta ta sauke numfashi; a firgice Anty Sakina ta ce, “Ya ya dai lafiya? Mene ne ya faru?”
“Matar yaya Ahmad ce take nakuda, shi ne ya dauke ta zuwa asibiti. Bari na je tunda bai fada wa hajiya ba.”
“Subhanallah! Allah Ya sauke ta lafiya, Ubangiji Ya ba ta me sauki; sai mu tafi tare ko?”
“Aa ki bar shi ma, kin san halin wannan sabuwar Principal din yanzu sai ta yi zaton karya muke yi, da ma ta sanya mana ido. Za mu yi waya kawai.”
Nan da nan Anty Zara’u ta fito ta nemi izinin shugabar makarantar ta fice. Kai tsaye ta nufi Intercontinental Hospital, da ma shi ne asibitin da suke zuwa duk wanda ba shi da lafiya a dangin nasu. Tana isa ta iske yaya Ahmad yana zaune a Reception ya hada kai da gwiwa, “Yaya Ahmad ya ya me jikin?”
Ya dago kai da cewa, “Har kin iso, Alhamdulillah! Tana can labour room.”
“Ikon Allah! Da ma ta dade da fara nakudar ne?”
“E to, tun jiya dai take ce mini ba ta jin dadin jikinta, to da ma yau ne cikar EDD dinta.”
“To Ubangiji Allah Ya budi idonta lafiya, amma gaskiya ya kamata ka fada wa hajiya.”
“E, da ma yanzu nake so idan kin zo sai na je na dauko ta, na san idan na yi mata waya to cewa za ta yi za ta fito ta taho da kanta.”
“To shi kenan ka je din ni ina nan.”
Fitowa ya yi ya nufi inda ya aje mota; ya bude; ya shigo ya fice.
To a can dakin haihuwa kuwa, matarsa Farida ce take kan gwiwa, likitoci na kanta suna baje kolin basirarsu amma abin sai dai hamdala. Alamu sun nuna haihuwar na son zowa da gardama, bayan likitocin sun yi bincikensu na ilimi sun gano cewa ta fara nakudar ne tun kusan awanni takwas da suka wuce; a tsaitsaye take yin ta ne. Sun yi ‘yan dabarun da za su iya yi amma dai shiru.
Yaya Ahmad na isa gida bayan sun gaisa da hajiyarsu ya ce, “Da ma Farida ce, tana asibiti tare da Zara’u, ina jin watakila haihuwa ce ta zo mata; EDD dinta ya cika yau.”
A rude hajiyar ta mike tare da cewa, “Mu tafi ai ba zama za ka yi ba.”
Ganin yadda take neman rikicewa ya sa shi cewa, “Hajiya ki kwantar da hankalinki, babu matsala fa. Da ma za ki zauna kawai ba sai kin je ba, tunda Zara’u tana can, kuma ba ki da lafiyar kafa.”
Ko sauraren maganar da yake ba ta yi ba, ta fito daga falon tana takawa dakyar ta nufi wajen mota, alatilas shi ma ya fito ya bi bayanta domin ya san babu abin da zai hana ta zuwa asibitin nan koda rarrafe ne sai ta je. Bude mata kofar motar ya yi ta shiga; shi ma ya shiga suka nufi asibitin.
To bayan barin yaya Ahmad asibitin, Anty Sakina ta kira Anty Zara’u lokacin da aka tashi daga makaranta, ta ce mata ga ta nan zuwa asibitin. Mintuna ba su fi biyar ba da komawar yaya Ahmad da hajiya sai ga wayar Anty Sakina ta kira Anty Zara’u ta ce ta fito ta yi mata iso zuwa cikin asibitin. Suna shiga Anty Sakina ta gai da hajiya cikin matukar ladabi da girmamawa sannan suka gaisa da yaya Ahmad ta yi musu ya me jiki?
Guri daya suka zauna su biyu wato Anty Zara’u da Anty Sakina, yaya Ahmad ma shi da hajiya suka zauna waje daya suna zuba idanu su ga likitocin sun fito musu da albishir me dadi. Kusan mintuna talatin suna nan babu likitan da ya fito wajensu, zuwa can sai wata daga cikin masu duba Farida ta leko ta ce da yaya Ahmad likitan yana son ganinsa a ofis. Cikin sauri ya mike ya nufi ofis din babban likitan. Bayan ya shiga suka gaisa da likitan ya ci gaba da dube-duben wasu takardu yana rubuce-rubuce kusan mintuna biyar, sannan ya dubi yaya Ahmad ya ce, “Ranka yadade, mun yi duk abin da ya dace amma haihuwar nan ba ta zo ba; bincike ya nuna Farida ba za ta iya haihuwa da kanta ba.”
“Subhanallah! Subhanallah! Subhanallah! To ya ya za a yi kenan doctor?”
“Ka kwantar da hankalinka babu damuwa, tiyata za a yi mata.”
“To babu matsala kuma?”
“Insha Allah babu wata matsala, yanayin halittar kugunta ne haka. Akwai mata irin wadannan wanda ba sa taba iya haihuwa da kansu saboda kugunsu baya budewa lokacin da za su haihun. Kugun me ciki na budewa lokacin da za ta haihu, hakan ne ke ba su damar haihuwa cikin sauki da kansu.”
Hakan dai doctor ya yi ta yi wa yaya Ahmad bayanai, daga karshe yaya Ahmad ya sanar da hajiyarsu, ba su da wani zabi face wanda likitan ya ba su; don haka nan take yaya Ahmad ya rattaba hannunsa, tabbatar ya amince a yi wa matar tasa aiki a ciro jaririn. Cikin sa’a da nasara aka yi aikin lafiya aka zaro jaririya kyakkyawa me kama da Anty Zara’u sak, tamkar an tsaga kara.
Nan aka sallame su misalin karfe 5:00pm na yammaci, sai a lokacin Anty Sakina ta komo gidanta, tana can asibitin har sai da aka gama komai.
Bayan kwana biyu da yi wa Farida operation, sai ta fara wani zazzafan zazzabi, nan da nan suka koma asibitin cikin dan kankanen lokaci jikinta ya rikice, ba ta cika awanni biyu ba a asibitin nan rai ya yi halinsa, ta ce ga garinku nan. Kwananta ya kare, tata ta yi kyau, Allah Ya jikanta.
Wannan mutuwa ta Farida ta zama babban tashin hankalin da suka jima ba su ga irinsa ba, kai tun mutuwar Alhaji, Abban su yaya Ahmad din rabon da wani abu ya kidima su. Kowa da kowa, yaya Ahmad, Anty Zara’u, Hajiya da sauran dangi babu wanda bai yi kuka ba, kuka sosai sun sha shi har aka rasa wanda zai rarrashi wani. Saboda da tsananin kuka sai da idanuwansu suka rikide suka sauya kala suka jajir sannan fuskokinsu suka kumbura suka yi sintum. Har aka yi bakwai hajiya ba ta daina kuka ba, ana zaune sai dai a ga hawaye na kwaranya a fuskarta.
Farida ta kasance yarinya me tsantsar tarbiyya da biyayya, ga ilimi da nutsuwa ga kunya. Auren zumunci suka yi da yaya Ahmad, ‘yar kanen hajiya ce wacce hajiyar ta dauko ta tun lokacin da aka dauke ta daga nono. A hannun hajiyar ta girma, karatunta da komai a nan ta yi shi, lokacin da ta gama makaranta hajiyar ta yi wa yaya Ahmad tayin ya qqaure ta, babu musu ya amince, dama yana son ta sosai, daga yadda yake ba ta kulawa da wasannin da suke yi irin na al’adar Bahaushe da ake cewa wasan dan mace da dan namiji. Sun shaku sosai fiye da tunanin duk mai tunani; amma me rabawa ta raba su, sai hakuri. Muna fatan Allah Ya maye wa yaya Ahmad da mafi alkairi amin.