Skip to content
Part 23 of 23 in the Series Ƙuda Ba Ka Haram by Sadik Abubakar

BAYAN SATI DAYA

To kawo yanzu dai  bamgaren makarantar su Humaira, sun kusa kammala ajin farko wato level 100, bai fi saura mako biyu ba su fara rubuta jarabawar second semester (wato, zango na biyu). To a iya cewa ba ta sauga zane ba a bamgaren Humaira, domin tana nan dai babu yabo babu fallasa ko a ce ma gara jiya da yau. Ita dai da ma ta kasance irin mutanen nan ne masu karancin fahimta karatu, ana matukar shan wahala kafin su fahimci inda malami ya dosa. Sannan kuma ga rashin mayar hankali da ba ta yi, ta saka shashanci da sakarci a rayuwarta. Zuwa makarantar kawai take amma sam kwalliya ba ta biyan kudin sabulu.

Ita kuwa Binta abinta sai san-barka, domin arziki ne ya ci uban na da, ma’ana ta ribanya kwazonta sosai. Duk da cewa ta samu maki mafi yawa a tsangayar tasu hakan bai sa ta yi wasa ko kuma ta ce ai ita ta samu tudun dafawa ba, a madadin haka sai ta sake bude wuta, ko ba komai ta ci gaba da rike kambunta na gwarzuwar daliba mafi kwazo a ajin nasu.

Haka nan kuma ba ta gajiya ba wajen ba wa kawar tata shawarwarin da fahintar da ita abin da ba ta gane ba. To sai dai ita Humaira ba ta bukatar hakan sam, ta fi ganewa zama cikin su Ruky suna haduwa suna shashanci tare. Kowa dai ya san wace Ruky da kawayenta, ba karatu baya ne a gabansu, ba sa bibiyar darusa, su dai ‘yan follow up ne. Aikinsu shi ne bibiyar malamai masu budurwar zuciya da halin dan akuya domin samun maki, koda irin jeka da hanlinka din nan ne. Wato dai suna yin tsarin nan ba ni gishiri na ba ka manda. Ba irin kokarin da Binta ba ta yi ba akan ta ganar da Humaira illar rashin mayar da hankalinta akan karatu amma sam ba ta ji, ta sa auduga ta toshe kunnenta. Wanda ya yi ya nisa ba ya jin kira.

Duk da cewa Binta na zuwa café din Sadik tana taya shi aiki, hakan bai hana ta ware wani lokaci ba don yin bitar karatun da aka yi musu tare da Humairar, amma sai ta ki bayarda hadin kai.

Bayan cikar wa’adin makonni biyu suka fara jarabawa kamar yadda aka tsara, shirin zaune ya fi na tsaye, in ji masu iya magana. Binta ta shirya wa jarabai sosai fiye da shirin da ta yi a baya, ta yi karatu matuka har sai da ta ji ba dadi. Don haka duk jarabawar da ta shiga cikin fara’a da murmushi take fitowa daga hall din. Sabanin gogar taku, ita kam babu abin da ya dame ta. Takan fito ne fuskarta kadaran kadahan, kwatankwacin yadda ta yi jarabawar zangon farko haka wannan din ma ta kasance.

Suna kammala jarabawar hutun makonni biyu ne aka ba su kuma a cikinsa ne ake son su yi registration na aji biyu, wato level 200. Ranar da suka gama jarabawar kafin su bar makarantar, Sadik ya ce da Binta yana son ganin ta kafin ta tafi gida akwai maganar da za su yi. Gabanta ya yanke ya fadi, nan take ta fara sake-sake, “To wace magana za mu yi da shi ne? Allah Ya sa dai abin da nake tunani ne, sai dai kuma fa yanzu ina matukar jin Anty Meenat. Na lura da take-taken yaya Sadik so yake ya jirge burinsa na Humaira akaina, anya kuwa abin nan zai yiyu?”

Tunanin da Binta ta yi ke nan jim kadan bayan Sadik din ya sanar da ita. Wani nishi ta ja sannan kuma ta sake nutsawa cikin wani tunanin kamar haka, “To amma kuma fa burina ke nan, ina son yaya Sadik sosai wallahi. Mutumin kirki ne matuka, koda ba na son sa muddin ya nuna mini bukatarsa to ba zan juya masa baya ba. Shi din dan halak ne ya cancanci a ba shi ajiyar zuciyar domin ya san kimarta kuma zai kula da ita yadda ya dace.”

Tana kaiwa karshen wannan tunani ta saki wani lafiyayye kuma lallausan murmushi tamkar a gaban Sadik din take, Humaira ce ta ce da ita, “Ke kuma kanki daya kuwa kike ta murmushi ke kadai, ko wani daddadan albishir aka yi miki ne?”

“Hmm! To ai shi murmushi ba sai an yi wa mutum albishir din komai ba zai yi shi. Yin murmushi sunna ce, kuma idan mutum ya tuna wani abin farinciki ma zai yi murmushi.”

A yatsine Humaira ta dubi Binta ta ce, “Allah ko? Yo ke wane abin farinciki za ki tuna da zai sa ki nishadi da murmushi da ya wuce karatu, kullum kina cikin kallon takarda. Ki bi dai a hankali wallahi kada ki samu matsalar ido da kuruciyarki, masu idon ma ya suka kare bare kin zama musaka.”

Ta karasa maganar da sakin wata matsiyaciyar dariya, murmushin Binta ta ci gaba da yi tana cewa, “Haka dai kika ce, amma Dan Adam a rasa abin da zai sa shi farinciki? Kuma wa kika taba jin cewa karatu ya makantar?”

Daidai lokacin da suke wannan tattaunawa karfe 1:00pm na rana ne, wato fitowarsu daga jarabawar karshe ke nan. Wasu daliban ma har sun fara tafiya gida, Humaira ta ce, “To na ji, bari na je wajen Ruky mu yi sallama kafin mu tafi ko?”

A yatsine Binta ta amsa mata da cewa, “Idan kin gama ki same ni a wajen Sadik.”

“Wace za ta zo wajen Sadik? Allah Ya tsari gatari da saran shuka, idan kin ga flashing kawai ki taho mu tafi kin ji amma ni ba zan zo ba.”

“To na ji.” Binta ta fada tare da kama hanyar café din. Ta tsani tarayyar Humaira da Ruky, da a ce tana da yadda za ta ta raba su da ta yi, kawancen ba na alkairi ba ne sam.

Tana isowa café din ta iske Sadik ne shi kadai, “Ina Anty Meenat din?” Ta tambaya.

“Yau ta tafi asibiti, watakila ma ba za ta zo ba daga can gida za ta wuce.”

“Ayya! Allah Sarki! Jikin ya fara nauyi ko? Allah Ya sauke ta lafiya.”

“Amin Ya Allah.” Ya fada fuskarsa cike da murmushi. Suka yi shiru na wasu ‘yan dakiku ba wanda ya yi magana, zuwa can ya katse shirun da cewa, “An kammala jarabawa ko? Sai hutu ke nan.”

Ta saki murmushi me dan sauti tare da cewa, “E amma ai ba hutu ba ne me yawa.”

“Haka ne, ba shi da waya kam. To yanzu za ki wuce gida ke nan?”

“Hmm! A’a zan tsaya mana tunda na ga akwai aiki kuma Anty Meenat ba ta nan, aikin yawa zai yi maka.”

Cikin yalwataccen murmushi ya ce, “No, kada ki damu da wannan aikin, ba karewa yake ba, sai dai mu yi abin da muka yi. Idan babu damuwa ina son mu je gida na gai da magabatanki.”

Farinciki hade da tsoro ne suka ziyarci zuciyarta lokaci guda, abin da take buri yana neman faruwa, a hannu guda kuma ta fara tunani da wace fuska za ta kalli Meenat idan abin ya tabbata? Gaskiya akwai cakwakiya a wannan lamari, Allah Ya shiga lamarin idan hadin na Ubangiji ne ba makawa sai abin ya tabbata, to sai ya kimsa wa zuciyarta dangana da fahimta. Tunanin da Binta ta yi ke nan wanda ya tsawaita mata yin shiru ba ta ba wa Sadik amsa ba, katse mata tunanin ya yi da cewa, “Ya ya dai kika yi shiru? Ko akwai matsala ne?”

“Hmm! Babu wata matsala, kawai ina tunani ne Humaira ba za ta yarda mu tafi tare ba. Ba za ta shiga motarka ba, kuma ka ga tare muke tafiya. Idan na ce ta tafi ba za ta ji dadi ba, sai ta ga kamar na yi mata wulakanci ne. Kawai zan yi maka Kwatancen layinmu, idan ka zo sai ka yi mini waya, ko ya ka gani?”

“Good! Haka ne, kin yi tunani me kyau. To ban sani ba ko akwai wani abin da za ki rika yi a gidan kafin ku dawo karatu, da ina son ki ki rika zuwa koda kwanaki uku ne ,saboda kin ga Meenat jikinta ya yi nauyi na san dole ta rika hutawa.”

“To shi kenan zan fada a gida In Sha Allah za a amince.”

“Yawwa!” Ya fada tare da bude wata drawer kusa da shi ya dauko Scratch Card na makarantar wanda idan dalibi ya biya kudin registration a banki za a ba shi, da Scratch Card din ake amfani wajen yin online registration. Mika mata ya yi tare da cewa, “Ga wannan ki ajiye shi idan an bude muku portal sai ki yi registration na level 200.”

Cike da murna da farinciki take duban sa, musayar murmushi kawai suke wa juna, ta gaza magana. Ya sake bude wata drawer ya dauko kudi naira dubu ashirin cif ( ₦20000), ya mika mata yana cewa, “Wannan kuma kudin aikinki ne na wata daya, karbi mana.”

Sunkuyar da kanta ta yi ta ki karba, ya ci gaba da magana, “Cewa ki karba, kudinki ne.”

Mursisi ta ki koda dago kai, a sunkuye ta ce, “Yaya Sadik don Allah ka bari, ni wane aiki na yi da har za a ba ni kudi? Wannan Scratch Card din ma da na san za ka sayo shi wallahi da ba zan zo ba.”

“Ban gane ba za ki zo ba, shin akwai abin da kika tambaye ni ne a ciki? Registration da na yi miki kyauta ce tawa, sai dai idan kuma ladan ne kike mini rowar samu. Wannan kudi kuma na fada miki hakkinki ne dole ne ki karba.”

“To shi kenan na gode sosai Allah Ya kara girma da daukaka, Allah Ya saka da mafificin alkairi. Amma ka bar kudin na gode, bari na je na samu Humaira tana jira na kada ta yi fushi.”

Ya dan sauya fuska alamun fushi sannan ya ce, “Hmm! Kamar ba kya fahimtar abin da nake cewa, su wadannan kudade ba kyauta ba ce na yi miki, guminki ne wanda Allah Ya yi umarni da a ba ki. Kin yi mini aiki a nan tsawon wata guda, don haka wajibi ne na biya ki kudinki. Ko Meenat ma da kike gani haka nake ba ta kudinta duk wata, yanzu haka ga nata zan ba ta idan na koma gida. Ina fatan yanzu dai kin fahimta?”

Ta yi murmushi me dan sauti sannan ta ce, “E na gane duk abin ya kake nufi, amma ni na yafe nawa hakkin ka bar shi.”

“Hmm! To ko dai kin rena ne?”

Ta yi saurin dago kai hade da sakin wata siririyar dariya sannan ta ce, “Lah Yaya Sadik! Wace renuwa kuma zan yi, to ni wane aiki ma na yi har da zan rena kudin da za a ba ni? Ni dai kawai na ce ka bar shi ne ban yi don kudi ba.”

Ganin yadda ta kafe, ya buga ya raya ta karba ta ki sai ya kyale ta. Duban ta ya yi ya ce, “To shi kenan tunda kin ki karba, yanzu sai ki yi mini kwatancen unguwar taku.”

“Hmm! Yawwa, idan ka zo Jakara daidai ofishin ‘Yan Sanda sai ka yi mini waya.”

“Okay, In Sha Allah za ki ji ni bayan La’asar.”

Rufe bakinsa keda wuya sai wayarta ta fara ruri, Humaira ce ta kira ta, tana dagawa kafin ta yi magana Humairar ta magana da masifa, “Ke malama idan kin gama ina jiran ki, ki zo mu wuce. Idan kuma ba zai bar ki ba ki tafi to ki sanar da ni.”

Dayake wayar Binta na da kara sosai, Sadik ya ji duk abin da Humaira ta ce. Binta ta dan bata rai kadan sannan ta ce, “Ke wai me ya sa kike haka ne? Komai abin masifa ne,  ke din ba uzurinki kika tafi ba wajen su Ruky.”

“Okay, lallai ba shakka, dole ki hayayyako mini ya fara zuga ki ko?”

“Kin ga ni ya isa haka gani nan kawai.”
Binta ta fada tare da kashe wayar ta juya ga Sadik, murmushi kawai yake saki. Muryarta a sanyaye ta ce, “Yaya Sadik don Allah ka yi…”

Ya yi saurin katse ta da cewa, “Ba komai kada ki damu, ni ai ba sai kin fada mini wace Humaira ba? Ko kin manta ne? Ki je ku ta fi kawai sai kin ji ni anjima din.”

Jakarta ta dauka ta mike ta fito, shi ma fitowar ya yi, ya biyo bayanta da naira dubu biyu a hannu ya ce, “To karbi kudin mota ko?”

Ba ta son su sake ja’inja da shi, don haka sai ta zari dubu daya ta bar masa dubu daya, tana sakin murmushi ta wuce. Tana isowa wajen Humaira, wata hararar renin wayo Humairar ta jefe ta da ita, dayake Binta ba ta son su rika sa’insa sai ta yi kamar ba ta gani ba ,ta saki fuska cikin sigar wasa ta ce, “Ke dadina da ke saurin fushi, don Allah ki rika shan ragowar ruwan alwala ko kin rage saurin hawan nan.”

“Haka ma za ki ce ko? Na ga alama Sadik so yake ya raba mu, kin fi jin maganarsa sama da ta kowa. Duk abin da ya ce miki shi kike yi, ki kula dai wallahi matarsa ‘yar Katsina ce, asiri ne da su kamar me. Idan kina son rasa mijin aure kwata-kwata har abada, to ki ci gaba da yin soyayya da mijin ‘yar Katsina.”

Dariya ta yi sosai har sai da Humaira ta fara jin haushi sannan ta ce, “Wallahi na dade ban ji abin dariya ba kamar wannan maganar taki, gaskiya za ki yi kyau da fitowa a irin shirin nan na comedy. Yanzu wato ke tsoron asirin Katsinawa ne ya sa tun farko ba ki karbi soyayyar yaya Sadik din ba lokacin da ya nuna yana son ki?”

Tana fada ta sake tintsirewa da dariya, a wannan karon har da dafa kafadar Humairar sannan ta ci gaba da cewa, “To tunda ke tsoron asiri ya sa kin rabu da kyakkyawan namiji, daya tamkar da dubu. Mutum me cikar kamala da kwarjini wanda ya san kima da darajar ‘ya mace, to ki saurara ki ga yadda zan yi soyayya da shi kuma na mallake shi a hannuna a matsayin mijina. Ba ‘yar Katsinawa ba ko ‘yar bokayen Indiya ce ba ta isa ta hana Allah ikonSa, da yardar Allah sai na auri yaya Sadik. Allah ba zai jarabce ce shi da son mu ba, mu biyu kuma kowacce ta watsa masa kasa a ido ba. Ke dai tunda ba kya yi, to ni zan share masa hawaye, zan shayar da shi zumar soyayyar da yake muradi matukar ina numfashi a doron kasa.”

<< Kuda Ba Ka Haram 22

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×