Skip to content
Part 24 of 30 in the Series Ƙuda Ba Ka Haram by Sadik Abubakar

Wani irin wulakantaccen kallo Humaira ta bi Binta da shi sannan ta ce, “Allah Ya jarabce shi da son mu ko dai Ya jarabce shi da so na? Ke ai ba son ki yake ba, ke ce dai kike ta cusa kai kina masa tallar kanki amma sam ba ya son ki, ni yake so. Don haka ki gyara lafazin bakinki malama.”

“Hmm! To Alhamdulillah! Na ji aje a hakan, ni dai na san yaya Sadik ko a mafarki ba zai ce ba ya so na ba. Domin ba a fi ni zannuwa ba, to ba za a baɗa mini kwarkwata ba. Ina da sura da diri ba yabon kaina nake ba, zance ne ya kawo hakan kuma komai hassadar mahassadi idan ya bude idonsa ya dube ni zai shaida haka, to don haka Allah na gode maKa da ba Ka ba ni izza da wulakanci ba. Kuma ina son ki sani na fi ki da na ce ina son sa, ke kuwa fa? Bullensa ya karya ya gabatar miki da bukatarsa amma sai kika yi fatali da ita, ba ki duba kima da martabarsa ba.”

Cike da tsananin mamakin yadda Binta ta zage sai fada mata maganganun da ranta yake so take yi, ta dube ta sannan ta ce, “Lallai yau kin fito mini a asalinki, da ma ashe haka kike? Ba shakka na yarda da maganar mutane, ‘mutum shege ne.’

Binta ta yi wani shegen murmushi me cusa takaici sannan ta ce, “Ban gane na fito miki a asalina ba, da ya nake? Magana ce ta gaskiya, bawan Allahn nan ya ce yana son ki, ke kuma kin ce ba kya son sa, to ba shi kenan ba sai ki rabu da shi ya yi sha’anin gabansa; duk ma wacce zai so ke ina ruwanki? Amma kin dame shi, kodayaushe zancensa. Kuma tun farko sai da na ce miki ki tsaya ki yi tunani game da shi, samun namiji kamar yaya Sadik me tausayi da kulawa abu ne mai matukar wahala a zamanin nan, amma sai kika yi kunnen uwar shegu da ni. Saboda haka ban ga dalilin da za ki damu kanki ba. Kuma gaskiya na fada miki ba zan iya zuwa makarantar nan ba ba tare da na je wajensa ba, hasalima kin ga ya koya mini aikin café ina taya shi.”

“To shi kenan tunda kin ce haka, kin yi da ‘yar halak. Idan na sake fada miki gaskiya duk abin da kika yi niyya ki yi mini.”

“Allah Ya huci zuciyarki, ni ban ce ba na son ki fada mini gaskiya ba, amma yanzu mene ne illar yaya Sadik? Malami ne babba fa a makarantar nan, duk da ba ya koyar da mu ai yana da matsayin da za mu girmama shi. Ko ba ki duba komai ba ai kin duba darajarsa ta malami, kin san da wahala ya ce yana son ki ba auren ki zai yi ba, duk da cewa akwai masu irin wannan hali amma shi dai daban ne.”

“To ai shi kenan ke ba kin ce za ki share masa hawaye ba? Allah Ya ba ki sa’a.”

Binta ta yi dariya sannan ta ce, “In Sha Allah!”

Haka suka yi ta fadi-in-fada Mai Adaidaita Sahu yana sauraren su bai ce musu ta tafasa sauke ba har aka zo Zaitawa gidan su Humaira ke nan. Ranta ya yi masifar baci da kalaman Binta, tunda suke ba su taba sa-‘insa me tsayi da ita ba wacce ta rika fada mata magana son ranta irin wannan ba. Don haka ta ji haushin ta sosai, kafin su isa kan layin su Humairar, Binta ta ce, “Hutun nan na sati biyu ne kacal! Ya ya za mu yi ne?”

A yatsine Humaira ta ce, “To sai aka yi ya ya ke nan? Registration kike magana ko me?”

Binta ta yi murmushi tare da cewa, “Game da komai mana, don Allah kada ki yi fushi akan wannan maganar ki ki zuwa gidanmu har a koma makaranta, na san za ki iya yin fushi. Please komai ya wuce ki zo.”

“Wa? Ki rufa mini asiri, haka kawai na yi asarar kudin mota, ke da kin ce kin samu aiki a wajen Sadik, na zo kuma ba kya nan.”

Binta ta yi dariya sosai sannan ta ce, “Dadina da ke mita, ya kamata maganar Sadik ta wuce haka.”

“To gaskiya batun registration da za a yi a cikin hutun nan akwai matsala, ban san ya za mu yi ba? Kin ga dai yanzu ba kamar da ba ne, kudi sun yi karanci a hannun mutane.”

Wani irin lallausan murmushi Binta ta yi fuskarta cike da annuri, babu wata alamar damuwa game da maganar Humairar, bude jakarta ta yi ta zaro Scratch Card din da Sadik ya ba ta. Mikawa mata ta yi tare da  cewa, “Yi hakuri don Allah tun farko ban nuna miki ba mantawa na yi, da ma dazu ne yaya Sadik ya ba ni ya ce ya biya mini kudin registration na level 200.”

Wani dunkulallen abu ne ya yunkuro ya zo daidai kirjin Humaira ya tokare mata, gabadaya yanayinta ya rikide ta koma tamkar fara’a ba ta taba bayyana a tare da ita ba. Hakan ya sa ta gaza magana na dan wani lokaci, Binta ta ci gaba da cewa, “Abin da ya sa ban fada miki ina tsoron masifarki ne, duk ranar da za ki je bankin ki biya naki ki biyo mini sai na raka ki.”

Sam Humaira ba ta ji me Binta ta ce ba, ba magana kawai ta gaza yi ba, hatta da masarrafar sautinta sai da suka kurumce na wucin-gadi. Ganin yadda ta yi shirun ne ya sa Bintar ta ta taba ta tare da cewa, “Ya ya dai lafiya na ji kin yi shiru?”

Da kyar ta iya gayyato wani munafikin murmushi me kama da babu ta ce, “Ba komai wallahi mantuwa na yi ne a wajen su Ruky, ga shi na bar su suna hada kayansu kila ma yanzu sun fita bare na koma. Gaskiya Sadik ya kyauta, Ma Sha Allah! Na taya ki murna, Allah Ya sanya alkairi, ke kin fita ke nan saura mu.”

Ta fada tare da mayar wa da Binta Scratch Card din, daidai lokacin an zo dab da kofar gidan su, wuf ta dire daga Adaidaita Sahun tana cewa, “Sai mun yi waya.” Ta shige gida ba tare da ta dubi Binta ba.

Wannan ne karon farko da suka yi irin wannan rabuwar, tsananin bakin ciki ne ya turnuke wa Humaira zuciya, sam ba ta so hakan ta faru ba. Abin da ta kudurce a ranta sai sun zo biyan kudin registration din ta yi wa Bintar gori, ta ce ta je Sadik din ya biya mata tunda ta ki rabuwa da shi. Tana shiga ta nufi dakinta ta zube kan gado tana cizon yatsa hade da sake-sake marasa amfani. “Babu shakka wannan mutumin aurenta zai yi, na ga alama. Shi ya sa ma take fada mini duk maganar da ta fito daga bakinta. Dan Adam ke nan! Ka yi masa rana, ya yi maka dare; ka janyo shi cikin inuwa kai kuma ya hankada ka tsakiyar rana. To kin yi da ‘yar halak, ba ni ba ke, tunda wuyanki ya yi kauri, kin isa magana, kina ganin karanki ya kai tsaiko shi kenan.”

Tunanin da Humaira take ta yi ke nan a kwance kimanin mintuna goma sha biyar (15 minutes) sannan ta mike ta fito falo.

To ita kuwa Binta ranta fes yake ba ta da wata damuwa, kai hasalima farincikin da take ji yau na musamman ne, Sadik zai zo gidansu kuma tana da yakinin maganar aure ce za ta kawo shi. Tabbas wannan rana tamkar ranar sallah haka take jin ta a wajenta. Tana isa gida ta fara yi wa kakar tata albishir da zuwan babban bakon nata, da ma dai tana sanar da ita yadda yake ba ta kulawa da yadda ya amince ta rika zuwa café dinsa har ya koya mata aiki. Baba Abu ta yi murna da farinciki sosai.

Nan da nan Binta ta mike ta gyare ko ina a gidan nasu, kasancewar ba wani babban gida ba ne cikin kankanen lokaci ta gama komai, ta shiga dan madaidaicin bayin gidan ta yi wanka sannan ta yi kwalliyarta me ban sha’awa. Riga da siket na atamfa ta saka, ta yi matukar kyau sosai fiye da yadda ta saba zuwa makaranta. Misalin karfe 4:10pm na yammaci, wayarta ta fara ruri. Tun gabanin ta dauka ta fara sakin wani siririn murmushi ta san gwanin nata ne ya yi iso, daga wayar ta yi tare da karawa a kunnenta da ke dauke da wani dan madaidaicin dan-kunnen daham, cikin wata lallausar murya me kama da ta  yara ta ce, “Assalama Alaikum Warahmatullah!”

Jin yanayin sallamar da sautin muryar tata ya hasko masa hoton fuskarta dauke da murmushi da annuri. Kwatankwacin yanayin ne shi ma a tare da shi, ya amsa mata da cewa, “Amin Wa alaikumus Salamu Warahmatullah Wabarakatuh!”

“Barka da isowa, kana daidai ina? Bari na fito?”

Murmushi ya saki me dan sauti tare da cewa, “Ya aka yi kika gane na iso?”

“Jikina ne ya fada mini, kuma hancina ya zuko mini kamshinka.”

“Hmm! Ba ki da dama wallahi! Ina daura da ofishin ‘yansandan.”

“To shi kenan, ga ni nan, ba ni minti daya.”

Hijabinta ta zumbula ta fito, dayake gida daya ne tsakanin ofishin ‘yansandan da nasu, lekowar da za ta yi ta hangi motarsa. Tunkaro wajen ta yi tana ci gaba da sakin kayataccen murmushinta me jan hankali, kafin ta iso ya sauke gilashin da ke bangarensa. Tana isa kamshin turaren da ta fesa ya daki hancinsa har cikin tsakiyar zuciyarsa.

“Sannu da zuwa.” Ta fada hade da rusinawa.

Ya amsa mata da cewa, “Yawwa! Ranki yadade.”

Sai kunya ta baibaye mata fuska, sunkuyar da kanta ta yi tare da cewa, “Wannan ai title dinku ne. Ka gyara parking ko?”

Ya yi gaba kadan dadidai kofar gidan ya fito, ta ce, “To Bisimillah!”

Gaba ta yi, ya bi bayanta kai tsaye ta shiga da shi dakin Baba Abu, da ma tuni ta shimfida masa tabarma. Zama ya yi ya gai da Baba Abu cikin matukar ladabi da girmamawa. Bayan sun gaisa Baba Abun ta dora da cewa, “An gode sosai da abin arziki, Binta tana fada mini duk abubuwan da kake mata na alkairi. Allah Ubangiji Ya saka da alkairi, Allah Ya jikan magabata Ya kuma raya zuri’a.”

Kansa sunkuye ya ce, “Babu komai Baba, ai Binta yarinyar kirki ce. Halinta ne ya ja mata, na dauke ta a matsayin kanwata.”

“Kai madalla! Allah Ya saka da mafificin alkairi, Allah Ya kara girma da daukaka.”

Ya amsa da, “Amin summa amin. Da ma cewa na yi bari na zo na ga gidansu na kuma gai da manyanta.”

Binta na jin ya kawo nan a maganarsa, sai ta yi wuf ta mike ta fice daga dakin. Shi kuwa ya ci gaba da cewa, “Baba ina son idan babu damuwa a ba ni dama mu sasanta da Binta, ina da mata daya, ita ma a makarantar take karatu sun san juna ma sosai. Shi ne na ce bari na fara neman izinin magabatanta.”

Baba Abu ta dan gyara zama sannan ta ce, “To Ma Sha Allah! Babu wata damuwa, wannan daidai ne. Da ma haka ake son al’amari ya fara daga wajen manya. To sai dai wani hanzari ba gudu ba, Binta Marainiya ce, ba ni ce na haife ta ba. Iyayenta duka biyun sun rasu tun tana karama. A hannuna ta girma. Ni na haifi ubanta. Na yi farinciki da Allah Ya sa ba ta bi rudin yaran zamani ba, sai ta zabi babba me hanklali. Fatana Ubangiji Ya kara hada zukatanku, akwai kanen mahaifinta zan sanar da shi. In Sha Allah babu matsala ta bangarenmu, Allah Ya tabbatar da alkairi.”

“Allahumma amin! Allah Ya jikan mahaifan nata, Allah Ya yi musu rahama. In Allah Ya yarda Baba na yi miki alkawarin zan rike Binta da amana zan kauda mata tunanin maraici. Addu’arku kawai muke bukata.”

“To Madalla! Allah Ubangiji Ya yi muku albarka, Allah Ya sa albarka a ciki.”

“Amin Ya Allah! Ni zan koma Baba.”

Ya fada yana karkacewa ya zaro wasu kudade masu kauri ya ajiye gabanta tare da mikewa.

“Kai haba yaro! Har da wata dawainiya haka? Banda wacce ake yi wa Binta kullum, gaskiya ka bar shi Allah Ya saka da alkairi.” Bai jira ta kai ga aya ba a zancenta tuni ya mike ya fito daga dakin.

Duk maganganun da suka yi shi da Baba Abu, ba abin da ya tsere wa kunnuwan Binta, domin da ta baro dakin labewa ta yi a tana sauraren su, sai da ta ji alamar zai fito shi ne ta yi sauri ta bar wajen ta shiga dakinta. Yana fitowa tsakar gida ita ma ta fito, Baba Abu ma ta fito tare da cewa, “Oh! Binta ko ruwa ma ba ki kawo masa ba.”

Ya yi murmushi ya ce, “Ba komai Baba, a koshe ma nake, sai anjima.” Ya fada tare da ficewa, Binta ta rufo masa baya zuwa waje inda ya aje mota. Tsaye suka yi kowa fuska fal da annuri, musayar murmushi kawai suke wa juna. Kusan minti guda suna a wannan yanayi ba wanda ya yi magana, zuwa can ya ce, “Shi ne kika tashi kika gudu ko? Da ma na tambayi Baba ne akan ta bar ki ki ci gaba da zuwa kina taya ni aiki tunda Meenat ba ta da lafiya.”

Ta yi dariya tare da cewa, “Ma Sha Allah! Ai kam gara da ka zo neman izinin Baba din, domin sasantawar ta fi armashi.”

Dariyar shi ma ya yi sannan ya ce, “Wai don Allah kin ji abin da na ce da ma?”

Cikin sigar kunya ta ce, “Hmm! Duk abin da kuka tattauna ina ji, a tsakar gida fa na zauna, da na ji alamar fitowarka ne na shiga dakina.”

“Kai amma ke din nan ko!” Ya fada yana kare mata kallon da yake kara fito masa da kyawunta, wani yanayin farinciki da jin dadi ne da ba zai iya kwatanta su da komai ba suke kewaya zuciyarsa. Binta ta kwashe da dariya sannan ta ce, “Me na yi kuma.”

“Hmm! Babu abin da kika yi.”

“Hmm! Yaya Sadik ke nen! Duk take-takenka na san inda ka dosa. Dan Hausa ai ba Bagwari ba  ne.”

Ya kara murmusawa sannan ya ce, “To ya ya ina fatan dai za a ba ni sarautar wannan makeken birni na cikin kasaitacciyar zuciyarki, zan shugabanci wannan birni bisa tsantsar amana da adalci da kyautatawa. Zan wanzar da dawwamammen farinciki marar yankewa da walwala a cikinsa, zan shafe duk wani bakin tarihi da ya taba faruwa a cikin wannan birni komai kankantarsa. Zan dasa bishiyun kauna da soyayya a duk wani lungu da sako na wannan birni, domin samar da sassanyar iska me dauke da kamshin furannin soyayya da wadannan bishiyun za su rika fitarwa.”

Cike da mamaki take sauraren yadda yake zayyano wadannan kalamai wanda ba ta taba jin wani da namiji ya furta su ba. Mamakinta a nan, shi ba yaron matashi ba amma ya san irin wadannan zafafan kalaman soyayya na ‘ya’yan zamani. Tsahirtawar da ya yi ne, ta dube shi da wani irin salon kallon kauna me tunkuda sakonni tsakiyar zuciyar wanda ake yi wa kallon, ta ce, “Yaya Sadik, kimarka da darajarka da mutuncinka sun wuce sai ka nemi izinina don yin soyayya da ni. Kamar yadda ka fada wa Baba cewa ka dauke ni a matsayin kanwarka, to ni ma haka na dauke ka a matsayin yayana. Ba bukatar kanka ba, ko wani ne ya zo neman soyayyata ta bangarenka to ya samu bare kuma kai kanka. To ai kai din na musamman ne, duk wacce ta same ka ita ce ta yi sa’a ba kai ba; haka nan duk wacce ta rasa ka ita ta yi asara ba kai ba. Fatana a nan shi ne, ka kiyaye jumlolinka na karshe da ka furta wa Baba.”

“Na gode sosai, kuma kada ki damu za ki yi mamaki na, Allah Ya yi mana jagora. Ina ne gidan kawun namu? Kuma yaushe kike ganin ya kamata mu je mu gaishe shi?”

“Ba nisa nan bayan layinmu ne, amma ka bari sai Baba ta yi magana da shi tukunna zan sanar da kai.”

“To shi kenan, bari na karasa gida ko watakila Meenat ta dawo daga asibitin yanzu.” Ya fada yana bude kofar motar ya shiga ya dauko wani *Envelope File* ya miko mata tare da cewa, “Yawwa kin ga ma zan manta, wannan wani aiki ne aka kawo ki fara duba shi a gida kafin ki samu lokaci sai ki zo ki yi shi.”

Tana karba ya yi wa motar key ya sulale yana mata dariya. Gida ta koma, tana  shiga ta bude file ta zazzage abin da ke ciki. Kudi ta gani da wata takarda, naira dubu ashirin (N20000) dinta ta aiki ce da ya yi fama da ita ta karba ta ki. Murmushi ta yi sannan ta bude takardar ta fara karanta rubutun da ke jiki kamar haka:

“Idan har kika dawo mini da wannan kudin, to tamkar kin ce ba kya so na ne. Kuma ki sani hakan sai ya fi taba mini zuciya akan wulakancin da kawarki ta yi mini.”

<< Kuda Ba Ka Haram 23Kuda Ba Ka Haram 25 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×