Skip to content
Part 25 of 26 in the Series Ƙuda Ba Ka Haram by Sadik Abubakar

Binta na gama karanta takardar nan ta lumshe idanunta, wata kaunarsa take jin tana ratsawa hade da zagaya ilahirin farfajiyar birnin zuciyarta. “Babu shakka zantukan Hausawa tamkar nassi suke, na yarda kowacce kwarya da abokin burminta. Wannan shi ne mijina na hakika, don shi aka gina ni. Ya Ubangiji ina gode maKa bisa wannan ni’ima da zabi da ka yi mini. Ina kuma rokonKa da Ka saka fahimta da zaman lafiya a tsakanina da matarsa. Ya Allah duk abin da zai kawo mana cikas da sabani Ka kawar mana da shi.”

Zantukan da ta yi ke nan a ranta lokacin da ta zauna bisa kujera a tsakar gida, daidai lokacin kuma Baba Abu ta fito daga bayi, zumbur ta mike ta rumgume ta cike da murna tana fadin, “Baba to ya ya kika ga angon naki, na iya zabe ko?”

“Ah! TubarakAllah Ma Sha Allah! Babu shakka wannan angon namu na kwarai ne, da ganin sa dan manya ne kuma zai yi tausayi bisa ga dukkan alamu. Na san ba ki da matsala, irin shashancin nan na zamani duk bai dame ki ba, to amma ina son ki kara kama kanki, ki yi masa dukkan biyayya, kada ki kuskura ki daga masa murya duk abin da zai yi miki. Sannan ki dauki matarsa a matsayin ‘yar uwarki ba kishiyarki ba, kada ki kuskura sa’insa ta hada ki da ita, yaranta yaranki ne. Ki kama su hannu bibiyu, ki ja su a jikinki, duk wahalhalunsu ki dauke mata. Mai d’a wawa ne, da d’ansa ake kama shi. Duk rashin kirkin mutum matukar kana son nasa ka ja shi a jiki, to sai dai ya yi wa wani rashin kirkin amma ba kai ba. Wannan ita ce dabarar zama da kishiya. Ina fatan Allah Ya hada zukatanku, Allah Ya tabbatar da alkairi.”

Binta ta kwantar da kanta a kan cinyar Babar tana sauraren ta a nutse, sai da ta gama maganar duka sannan Bintar ta sauke numfashi ta ce, “Amin summa amin. In Sha Allah zan kiyaye duk abin da kika ce mini, za ki same ni me matukar biyayya da bin umarninki.”

“Yawwa! Allah Ya yi miki albarka, Allah Ya jikan mahaifanki Allah Ya kai rahama kabarinsu.”

“Amin.” Ta amsa muryarta cike da rauni yayin da kwalla ta ciko a idanunta. Iyayenta ta tuno, duk da cewa lokacin da suka bar duniya ba ta da wani cikakken hankali. Share hawayen ta yi sannan ta mika wa Baba kudin nan tare da cewa, “Ga wannan dubu Ashirin ne, kudin aikin da nake taya shi ne. Tun a makaranta ya ba ni na ki karba shi ne ya biyo ni da su yanzu.”

“To ikon Allah! Yo kin ga nan ma wasu kudaden ne ya ajiye, na ce ya bari amma ya ki. Allah Ya saka da alkairi Allah Ya kara budi.”

Nan dai Baba Abu ta ci gaba da yi wa Binta ‘yan nasihohi da jan hankali game da rayuwar aure wacce babu komai a cikinta face hakuri. Kusan kashi 95% na zaman gidan miji hakuri ne tsantsa, cim ma nasarar zama da miji cikin kwanciyar hankali da soyayya da kauna hadi da farinciki duk yana damfare ne da hakuri. Wato matukar ma’aurata sun lazimci dabi’a da siffar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, to babu shakka tabbas sun yi adabo da bacin rai ko tashin hankali. Shi hakuri a zamantakewa ta aure tamkar jini ne a jikin hanta, babu yadda za a yi a iya raba hanta da jini. Idan wani mahaluki ya ce sai ya cire duk jinin da yake jikin hanta; to la shakka zai lalata hantar ne kawai. Haka abin yake yayin da wani sashen na ma’aurata ya ce shi ba zai yi hakuri ba ko kuma shi sai ya yi abin da ransa ya raya masa, to tabbas auren kawai yake son gurguntawa ko kuma ruguzawa ma gabadaya. Allah Ya tsare Allah Ya kare.

A nan nake amfani da wannan dama, nake rokon Ubangiji duk ma’auratan da ke fuskantar kowanne irin kalubale, Allah Ka yaye musu, Allah Ka kimsa musu hakuri da juriya kuma Ka ba su sakamakon hakurin. Allah Ka raya mana zuri’a, Ka kare mu daga sharrin son zuciya da shaidan amin summa amin. To wannan ke nan.

Ita kuwa Humaira, a nata bangaren sabanin yanayin da kawar tata ta kasance a ciki ne ya baibaye ta, wato dai bacin rai ne da bakin ciki, haka ta karashe yini nan cikin rashin sukuni. Damuwarta ba ta wuce yadda Sadik ya fara ba wa Binta kulawa ba. Har dare tunanin hakan bai sake ta ba. Misalin karfe takwas da rabi na daren 8:30pm, Usman ya kira wayarta, ta yi ruri ta yanke. Ya sake kira, da farko ba ta yi niyyar dagawa ba, domin a yau ba ta son yawan magana, amma sai ta daga murya kasa-kasa ta ce, “Hello!”

Ya karba mata da cewa, “Ranki yadade, na ce ko har kin fara barci ne? Ya kike ya garin? Kwana biyu?”

Ta amsa da, “Lafiya kalu, ya aiki ya gidan?”

“Aiki AlhamduLillah, ya school?”

“Lafiya, yau muka yi final paper mun gama level 100.”

“Wow! Congratulations, ina taya ki murna, Allah Ya kara basira. Ki ce kun samu hutu sosai ke nan?”

“A’a wallahi hutun ba me yawa ba ne, break ne sati biyu kawai za mu yi sai mu ci gaba da level 200.”

“Okay, ba komai duk da hakan za ku dan huta.”

“E haka ne ba laifi.”

Shiru suka dan yi, zuwa can ya katse shirun da cewa, “To ya ya mene labari ne?”

“Hmm! Labari yana wajenku manya.”

“Kwana biyu ba mu sha ice cream ba. Tunda an yi hutu ya kamata mu dan fita outing ko kuma ki zo gida.”

Ta dan zare idanu tare da cewa, “Anya kuwa!” Ya dan sauya fuska jin ta ce, anya kuwa. Murmushi me dan sauti ya yi sannan ya ce, “Ban gane anya ba, akwai matsala ne?”

“Ba matsala kawai dai…” Kafin ta karasa maganar ya katse ta da cewa, “Come-on my baby, kin fiye rigima da yawa, tun dazu na ji muryarki da alamun rigima. Shi kenan na gane. Ya batun registration? Zuwa Yaushe suka ba ku?”

“Cikin sati biyun hutun suka ce mu yi.”

“To shi kenan babu damuwa, yanzu yaushe za mu hadu ke nan?”

“Kai ne da lokaci kai za ka fada, ni dai ina nan.”

“To kin ga yau Juma’a ce, Asabar da Lahadi kuma Sakina na nan, ki bari ranar Litinin ba ta nan sai ki zo, na fi son mu hadu a gidan. Abin ya fi armashi.”

“To shi kenan, amma ni dai ina tsoron zuwa gidan nan.”

“Haba ki daina fadar haka! Ai babu damuwa indai ranakun aiki ne, idan Sakina ta fita ba ta dawowa sai lokacin tashi ya yi. Sannan kuma yanzu ma tunda ta fara wannan kasuwancin ba ta dawowa gida sai kusan karfe 4:00pm na yamma. Idan ta bar wajen aiki takan biya wajen wasu abokan cinikinta ta kai musu kaya ko kuma ta karbi kudinta. Saboda haka ki kwantar da hankalinki.”

“To shi kenan sai ranar Litinin din na gode.”

“Yawwa, ni ne da godiya.” Tamkar ya asirce Humaira, indai zai zo da bukatarsa koda ta fara tirjiya sai ya san yadda ya yi ya shawo kanta ta aminta, daga karshe har ma ta ji ta fi shi zakuwar a hadun. To Allah Ya shirya Ya kuma kare matanmu da ‘yan uwanmu daga fadawa tarkon maza irin Usman.

Washegari da safe misalin karfe 11:00am na hantsi, Binta ta kira Humaira, tana ganin sunan ta ki amsawa. Sai da ta yi mata kira uku ba ta dauka ba, a na hudu ne ta amsa da cewa, “Hello!” Daga haka ta yi shiru ba ta kara da ko uffan ba, murmushi Binta ta yi ta ce, “An gai da maji-dadi! Hala ma ba ki tashi daga barci ba har yanzu ko? Na ji ina ta kiran ki ba ki daga ba.”

A yatsine cikin sigar wulakanci ta ce, “Wace take barci har yanzu? Sai ka ce ke, kawai ba na kusa da wayar ne.”

“Okay, ya yi kyau! So ya kike ya gidan ya su Mummy da sauran ‘yan uwa? Da fatan kowa yana lafiya.”

“Kowa lafiya.”

“To madalla, da ma cewa na yi bari na kira na gai da hajjajuna! Ta yaya Sadik me komai dozen, ba da kanki a sare ki je gida ki ce ya fadi!”

Murmishin takaici Humaira ta yi tare da cewa, “Kin dai kira ki tsokane ni, wato na zama abar tsokana a wajenki ko?”

Dariya Binta ta yi tare da cewa, “Wace ni? Ni na isa na tsokane ki, wannan ai kirari na yi miki kawata maganin kukana! Allah Ya bar mini ke ta wajena!”

“Wallahi idan ba ki daina ba zan kashe wayar kuma ko kin sake kira ba zan amsa miki ba.”

“Na lura yau rigima kike ji, da ma ina son na tuna miki idan za ki je banki yin registration zan raka ki, kada ki je ke kadai.”

“To ai kin ga jiya-jiyan nan aka yi hutun ma, ko Abba ban fadawa ba. Amma dai cikin satin farko ina jin ranar Laraba ko Alhamis zan je.”

“Okay, da ma ina son na san ranar ne don na sanar da Baba Abu kafin lokacin, shi kenan Allah Ya kai mu.”

“Amin.”

Ranar Lahadi da dare, Usman ya sake kiran Humaira ya tuna mata da agendarsu ta haduwa, ya ce ta zo da wuri kamar lokutan da ta saba zuwa a can baya, wato misalin karfe 9:00 – 10:00am na safiya, jim kadan ke nan da fitar Anty Sakina. Hakan kuwa aka yi, washegarin safiyar Litinin Humaira ta shirya tsaf kamar za ta tafi makaranta har da daukar kayan karatu, wanda hakan ya ba ta damar shirga wa Mummy karyar cewa makarantar za ta je.

Fitowarta keda wuya ta tari Mai Adaidaita Sahu, kai tsaye sai Gwammaja, unguwar su Anty Sakina. Kafin su isa ta kira Usman din ta sanar masa cewa ga ta nan a kan hanya. Sannan ta saka nikabi ta rufe fuskarta. Kamar yadda ta saba har dab da kofar gidan aka kai ta, tana fita ta shige gidan da sauri.

To sai dai lokacin da Mai Adaidaita Sahun ya shigo layin, Zainab makwabciyar Anty Sakina ta fito kofar gidan neman yaron aike, idonta akan Adaidaitar har ta tsaya daidai kofar gidan. Wuf ta ga mace ta fito ta shiga gidan da sauri, nan da nan kwakwalwarta ta yo mata tariyar abin da ta ji kuma ta gani watarana can baya da ta taba shiga gidan a irin wannan lokaci. Ba ta gane ko Humaira ba ce ko ba ita ba ce, kasancewar rufe fuskar da take yi, ita dai tana ganin mace, don haka a yanzun ma sai ta yi tunanin kawai matan banza ne Usman yake kawowa gida idan Anty Sakinar ba ta nan. Don haka tsayawa ta yi tana tunanin yadda za ta yi, ta gaji ganin wannan cin amanar da ake wa aminiyarta.

“Wasu mazan ma ba su yi ba a rayuwa sam, kaddara da rabon shan wahala ke sa mutum ya aure su. Yau In Sha Allah sai na tona wa wannan mutumin asiri! Cin zarafin ya yi yawa! Dakin matarka ta sunna za ka mayar da shi wajen yin zina? Ka rika jajibo matan banza kuna fasikanci da su, duk fadin duniyar nan ya yi maka kadan sai ka dauko kazantar zina ka kawo kan gadon matarka halattacciya? To yau dubunka ta cika, da ma masu hikimar zance na cewa, ‘Rana dubu ta barawo; rana daya tak ta mai kaya’”

Zantukan da Zainab ta yi da zuciyarta ke nan kafin ta dan tsagaita.

To ita kuwa gogar taku wato Humaira, tana shiga kai tsaye ta nufi falo sallama ta yi sannan ta sa kafa tamkar dakinta babu wata damuwa ko shakkun abin da za ta gani. Gogan naku kwance yake cikin shigar shan-iska yana kallon wani film din romance na Nollywood. Mikewa ya yi zaune hade da sakin murmushi sannan ya ce, “Ko Bature bai kai ki kula da lokaci ba, da fatan kin iso lafiya?”

“Lafiya kalau.” Ta fada tare da zama bisa kujera daura da wacce yake zaune.

“Ya me za a kawo miki? Kodayake ma na ce na daina yi miki tayin komai, nan gidanki ne ki saki jikinki ki yi duk abin da kike so.”

“Na gode, ba na bukatar komai ma, ai safiya ce yanzu na karya.”

“To shi kenan bari a jima, ai dole ayi ciye-ciye bayan an dan ji dadi.”

Ya fada yana kashe mata ido, murmushi ta yi hade da sunkuyar da kai. Ya ci gaba da magana, “Gaskiya karatun naku yana sauri, har kun gama level 100, ba wuya za ku gama Diplomar. Amma HND za ki dora ko?”

“E to, gani nan dai tukunna sai abin da hali ya yi.”

“Haka ne, ki dawo kan wannan kujerar mana.”

Mikewa ta yi ta koma kan kujerar da yake zaunen wato 3 seater, tana zama ya matso kusa da ita sosai tare da shafo bayanta da hannunsa. Ya kwanto da ita a kirjinsa sannan ya yi mata kiss. Sannu a hankali ya fara yi mata duk abubuwan da ya saba har ita ma ta fara mayar da martani. To a nan ke nan.

Zainab kuwa, tsaye take ta zuba wa kofar gidan idanu ko kiftawa ba ta yi, tunanin hanyar da za ta bi ta tona wa Usman asiri take wacce ba za ta kulle da ita ba. Ma’ana dai tana son ta kafa masa hujjar da za a kama shi dumu-dumu da laifi, cikin tunanin nata, wata zuciyar ta ce, “Kawai ki kira Sakina ki ce mata ta dawo yanzu-yanzu za a sayi kaya. Idan ta zo idonta ya gane mata komai, ya fi a ce fada mata kika yi. Domin ba lallai ba ne ta iya yarda, karshe ma idan Usman din ya yi tirjiya sai ki shigar da kanki cikin matsala, don haka ki kira ta ta zo da gaggawa komai zai faru gara ya faru.”

Wannan ne tunanin da Zainab ta nutsu da shi, nan take kuma ta lalubo lambar Anty Sakina ta kira, bugu daya kira ya shiga ta daga tare da cewa, “Assalama Alaikum.”

“Wa alaikumus salamu, kin ga na kira ki daga fitarki ko? Na ce ko za ki iya dawowa yanzu da sauri, wasu ne suke son kaya, ina jin da yawa za su saya.”

“Allah ke! Me kuwa zai hana na dawo? Da ma ba ni da aji sai bayan break, ga ni nan yanzun nan.” Anty Sakina ta fada tare da kashe wayar sannan ta dubi kawarta Anty Zara’u ta ce, “Kin ji wai wasu ne za su sayi kaya, bari na je yanzu zan dawo.”

“Okay, to ba damuwa Allah Ya ba da sa’a, sai kin dawo din.”

<< Kuda Ba Ka Haram 24Kuda Ba Ka Haram 26 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×