Skip to content
Part 26 of 26 in the Series Ƙuda Ba Ka Haram by Sadik Abubakar

To, nan da nan Anty Sakina ta fito daga makaranta ta tari Mai Adaidaita Sahu shata domin ta yi sauri, ya kawo ta gida, tana sauka ta hangi Zainab tsaye a kofar gidanta, wajenta ta fara zuwa cike da murna ta ce, “Ke kawata ki ce babbar harka kika samo mana, ina masu sayen kayan suke?”

Wani guntun murmushin takaici hade da bakin ciki ne ya ziyarci Zainab, gabanta ya yanke ya fadi, ta nisa tare da cewa, “Ki shiga gidan tukunna bari na yi musu magana za mu shigo yanzu.”

“To shi kenan sai kun shigo din.” Anty Sakina ta fada tare juyawa ta nufi cikin gidanta

Ita ma Zainab, nata gidan ta shiga da kyar take daga kafafunta, zuciyarta cike da zullumin abin da kan iya biyo baya. Babu shakka tilas abubuwa mararsa dadi za su faru, to amma ba yadda ta iya illa ta sanar da aminiyarta din, ba za ta taba barin abin a ranta ba. Kujera ta nema ta zauna ta zuba tagumi hannuwa bibiyu rantse-rantsuwa ka ce sakon mutuwa aka aiko mata da shi.

Kai tsaye Anty Sakina ta tinkari falo bayan ta shiga gidan ta bude labule ta jefa kafafuwanta, abin da idanuwanta suka fara cin karo da shi ya sa ta tsayawa cak! Usman ne a tu’be tun’bur da shi haihuwar uwa da uba, bisa ruwan cikin macen da ba ta iya ganin fuskarta ba. Ita ma din a tube take sam’bal da ita, sai zullo yake hade da yin wasa da duniyar fulaninta. Banda nishi da ihunta babu abin da ke tashi a falon, ba su san ma wani mahaluki ya shigo ba. Mutuwar tsaye Anty Sakina ta yi wacce har jakar dake hannunta ta zame ta fadi ba ta sani ba, karar faduwar jakar ne ya kai kunnen Usman, ya waigo don ganin mene ne? Da sauri ya sauka daga kan Humaira, hakan ya sa ta yunkurawa ta mike zaune da nufin sauya salon kwanciya, me za ta gani in ba Antynta ba tsaye akansu?

Hada idon da Anty Sakina ta yi da Humaira ya sa ta yanke jiki ta fadi sumammiya bayan wani duhu da ya taso ya rufe mata idanu hade da jiwa. Cikin tsananin firgici hadi da kidima, Humaira ta nemi kayanta ta mayar jikinta, shi ma munafikin kayan nasa ya saka yayin da ita kuwa Anty Sakina take take kwance a sume.

Humaira ta sabi jakarta ke nan za ta fita sai ga sallamar Zainab nan, “Assalama Alaikum!” Shiru ba a amsa ba, ta sake kwada wata sallamar daidai lokacin da ta isa kofar falon, “Ba yanzu na ga shigowar Sakina ba?” Ta fada jin ba a amsa mata ba har sau biyu. Labulen ta daga, cirko-cirko ta ga Usman da Humaira sun yi alamun rashin gaskiya ga shi nan bayyane a fuskokinsu, yayin da idanuwanta suka yi tozali da Anty Sakina kwance a kasa shame-shame tamkar matacciya, sai ta razana sosai ta ce, “Subhanallah! Me ya faru? Lafiya? Yanzun nan fa muka gama magana da ita a kofar gida? Tana fada ta zube gwiwoyinta a kasa kusa da Anty Sakinar tare da tallabo kanta tana salati, “LA’ILAHA ILLALLAHU MUHAMMADUR RASULILLAHI! Wai me ya faru ne? Me kuka yi mata ina magana kun yi banza da ni?

Ta dago kai ta kalle su, sai a lokacin ta lura ashe Humaira ce, cikin wani irin mamaki ta ce, “Da ma kina cikin gidan nan Humaira? Ke ce na gani an sauke fuska a rufe da nikabi kin shigo da sauri?” Ta karasa maganar da sakin wani zazzafan tsaki hadi da hararar Usman sannan ta kama habar zanenta ta fara yi wa Anty Sakina furfita, ta fahimci dan gajeren suma ta yi ne.

Humaira ta motsa alamar za ta fita, Zainab ta ce “Ina za ki? Babu shakka ba ku da gaskiya, biri ya yi kama da mutum. Haka nan zikau babu abin da zai sa Sakina ta fadi ta suma. Humaira kin ba ni kunya, kin ba ni kunya, hakika kin ba ni kunya. Da a ce ba a nan kika aikata haka ba, ba zan ga laifinki ba duba da yadda zamani ya gurbace, to amma ki rasa wanda za ki saurara sai mijin ‘yar uwarki ciki daya? Shin yanzu da wace fuska za ki iya kallon ta? Da wane idanu za ki iya duban iyayenku? A ce yau kin yi sanadiyar mutuwar auren yayarki ta hanyar lalata, ba wannan ba ne karon farko da kika taba zuwa gidan nan, Ubangiji Ya nuna mini har sau biyu. Karo na farko na shigo kunnuwana suka ji mini abin da ban taba tsammani ba, na fita. Ban taba tunanin ke ce ba, sai dai abin ya ci gaba da zama a raina ina fatan Allah Ya kawo ranar da za a daina yi wa Sakina wannan cin amanar. Kwatsam yau ma sai Allah Ya sake nuna mini mace ta shigo gidan nan alhali ba Sakinar ba ce kuma ba ta nan bare a ce bakuwarta ce. Ashe ke ce, da ke ake cin zarafin ‘yar uwarki, to yanzu ga abin da kika janyo mata nan.”

Ta dan tsagaita da maganar ta mayar da hankali wajen yi wa Anty Sakina furfita, kafin ta juyo ga Usman wanda ya ji kamar kasa ta tsage ya fada saboda kunya, kansa ya sunkuyar tamkar wanda ke gaban surukarsa. Ta fara da cewa, “Kai kuma ka sani duk yadda za a ga laifin Humaira bai kai naka ba ko kusa, ko Shari’a ma hukuncin da za ta yi maka ya dara nata, domin kai ne babba. Ka san kowace Humaira, matsayin kanwarka take, idan har za ka iya yin abin da bai kamata da ita ba, to babu shakka za ka iya yi da kanwarka. Wannan wace irin masifa ce ka dora wa kanka? Duk matan duniyar nan da ke zaman kansu ba su ishe ka ba sai ka nemi ‘yar uwar matarka? Ka ji kunya, wallahi ka ji kunya Usman!”

Tana kawowa nan a maganarta, sai Anty Sakina ta farka hade da bude idanu, ta yunkura za ta mike, Zainab ta ce, “AlhamduLillah! Sannu kin ji, koma ki zauna ki huta tukunna.”

Anty Sakina ta fashe da wani irin kuka mai tsananin taba zuciya, cikin kukan take cewa, “Allah Ya isa tsakanina da ku, ba zan taba yafe muku ba duniya da lahira. Usman tun a duniya sai Allah Ya saka mini a kanka. Ka cuci rayuwata ka yi mini raunin da ba zai taba warkewa ba a zuciyata, Allah Ya isa.”

Ta koma kan Humaira wacce tsananin tashin hankali ya sa ta fara jikewa da gumi, “Ke kuma ki bace mini da gani kafin na tashi, idan kika bari na mike wallahi sai dai a yi ko ni ko ke! Matsiyaciya munafuka Allah Ya isa tsakanina da ke.”

Zainab ta katse ta da cewa, “Ki yi hakuri ki daina yi mata Allah Ya isa, ‘yar uwarki ce, ba yadda za ki yi da ita. Hannunka ba ya rubewa ka yanke ka jefar, kuskure ne dai ta riga ta yi.”

Anty Sakina ta sake kufula tare da zaburowa cikin wani sabon kukan tana cewa, “Ba za ki fice mini daga nan ba sai na dauki wani abin na jefe ki da shi munafuka!”

Simi-simi Humaira ta fito daga falon ta fice daga gidan, kafin kiftawar ido har ta yi layar zana daga layin, ta iso bakin titi. Kirjinta sai dukan uku-uku yake, cike da rashin sanin ina za ta dosa, ta tsaya, “Yanzu idan na koma gida watakila ko zama ba zan yi ba za ta biyo bayana, na shiga uku na lalace! Yaya Usman ka cuce ni ka jefa ni cikin masifa! Wayyo Allahna ina zan sa kaina?”

Mintuna kusan biyar tana tsaye a bakin hanya tana wannan tunani, zuwa can ta yanke shawarar tafiya gidan su Binta, wayarta ta zura hannu a jaka da nufin ta dauko ta fara kiran Bintar, sai waya ta ce dauke ni inda kika aje ni. Ashe lokacin da ta shiga gidan wayar tana hannunta ta ajiye ta a kan kujerar da ta fara zama, nan da nan ta tuno da hakan, ta ciji yatsa tamkar za ta gutsire shi. Mai Adaidaita Sahu ta tsayar ta ce da shi ya kai ta Jakara.

To can gidan kuwa, Zainab ce take ta ba wa Anty Sakina baki hade da dannar kirji, hawaye sun ki dakatawa da kwaranya daga idanunta, ta tsani gidan gabadaya. Wani mugun haushin Usman take ji tamkar ta kashe shi.

“Ki yi hakuri don Allah, na kira ki kin zo kin tarar da bacin rai da tashin hankali, wallahi ba zan iya jurar ganin ana yi miki wannan cin zarafin ba na yi shiru. Tun ba yau ba Allah Ya haska mini, to kasancewar ba ni da wata kwakkwarar hujja ya sa ban fada miki ba. Kin san sha’ani irin wannan idan mutum bai yi taka-tsantsan ba sai reshe ya juye da mujiya. Ban yi haka da nufin cin zarafin wani ba sai don na kubutar da ke daga cututtukan da zai iya goga miki, domin duk mutumin da bai tsayar da kafarsa a waje daya ba to yana tattare da hatsari, Allah Ya kiyaye, ni zan koma na dora girki ne. Allah Ya kiyaye Allah Ya rufa asiri.”

“Babu abin da zan ce da ke sai godiya, wallahi na gode sosai Allah Ubangiji Ya saka miki da alkairi. Zainab na dauke ki ‘yar uwa ba aminiya ba, na gode ki je ki duba girki.”

Zainab na ficewa daga gidan, Anty Sakina ta mike a fusace ta yo kan Usman ta kama wuyan rigarsa ta funcika cikin tsiwa ta ce, “Idan ka haifu cikin uwarka da ubanka ka rubuta mini takardar shaidar saki uku, zama ni da kai ya kare har abada ka je ka aure ta. Allah Ya isa tsakanina da kai macuci mazinaci fasiki wanda ba ya tsoron Allah! Na gode wa Allah da ban hada haihuwa da irin tsiya ba, irin Allah wadai!”

“Sakina ina…”

Ba ta bari ya kai koda karshen jumlar farko ba ta katse shi, cikin zakalkala ta ce, “Kai wallahil azim sai ka rubuta mini takardar nan tun kafin na yi maka abin da ba za ka taba mantawa da ni ba, aurena da kai ya kare, ko ni ma zaman zinar za ka yi da ni? Na tsane ka matuka!”

“Ya kamata ki saurare ni.”

“Usman ina bin ka ta lalama ka ki ko? Wallahi idan har ba ka rubuta mini takardar nan ba yanzu, to zan yi maka abin da sai ka yi nadamar zuwa duniya bare har ka aure ni. Tun muna ni da kai ka ba ni.”

Mikewa ya yi ya dauko takarda da alkalami ya fara rubuta mata sakin, kansa ta zo ta tsaya ta ce, “Saki uku nake bukatar ka rubuta mini, idan ya so sai ka kawo duk wacce za ka kawo.”

Saki ukun ya rattaba mata, ta karba tare da cewa, “AlhamduLillah! Allah na gode maKa. Kuma ina so ka sani in Allah Ya yarda sai ka wulakanta, tun a duniya sai sakayyata ta bayyana a jikinka.”

“To ya ishe ki haka.”

A zafafe ta ce, “Lallai rashin kunyar taka ta kai, kai nan har kana da ikon da za ka sa na yi shiru, me yasa ka taba ni? Bari na tuna maka yanzu ba na karkashinka, ba ka da iko da ni. Kuma magana dole na fadi abin da raina ya so, taba ni ka yi, ehe!”

Ba yadda ya iya, gaskiya ta fada, don haka tilas ya kyale ta ta yi masa tatas, ta yi masa wankin babban bargo. Da ya gaji da tsiwar tata sai ya koma cikin daki, kan gado.

Mikewa ta yi za ta biyo shi dakin sai ta ga wayar Humairar a kan kujera, ta sa hannu ta dauka sannan ta shige dakin. Iske shi ta yi kwance a kan gado, habawa ai sai ta ji kamar ana watsa mata garwashi a zuciya, nan fa ta ce ina wutar da za ta saka shi? Sabon shafin masifa ta bude, “Kai malam idan ba da kudinka aka hada aka sayi wannan gadon ba ka sauka, wannan gadon ba na mazinaciya ba ne.”

Shi ma sai ya fusata, domin zantukan nata sun fara yi masa daci, ya yi mata kawaicin amma ba ta gani ba, mikewa ya yi tsaye ya falla mata mari tare da cewa, “Tunda kin ce ba a karkashina kike ba, to ba zan juri wadannan zantukan naki ba, ki kama kanki ko na yi miki dukan tsiya.”

Tuni ta dafe kuncin da ya dauki zugi da radadi ta ce, “Wallahi ba shi ka ci wannan marin, sai na rama ko kuma hukuma ta rama mini.”

Tana fada ta saka hijabinta ta fice daga gidan.

<< Kuda Ba Ka Haram 25

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×